Showing 12001 words to 14779 words out of 14779 words
su!
Ta kalli mama A'isha tace bari naje na shigo dashi ya iso..
tana isa taga mubeen a hannun shi ta isa da murmushi a fuskar ta dimple ɗin ta ya losa ta gaida shi tare da miƙa ma mubeen hannu ya makale kafada.... Mubeen mami ce jeka kaji..
Yaron ya yi dariya tare da faɗin "dady mamina ce ita ma wannan ko zata rinka sai mun alewa da madara irin na hajiya?"
Kafin ya bashi amsa har mereeh tace ehhh "mubeen zan sai maka harda yogout" ai da sauri yaro ya miƙa hannu ya tafi gunta suka shiga ciki sun gaisa da mama A'isha sosai taji daɗin haɗin nan inda ya faɗa mata ai gidan da zai saka ta daban da na dayar sun sha fira mereeh dai ta tashi ta shiga kitchen ta haɗa mai abinci ta kawo inda mama A'isha ta koma ciki ta barsu, mubeen na kan cinyar ta tana bashi a baki shima yana ta mata surutu sosai ya ce'' ita mummy tana dafa mana nama harda da dady muke ci tana bamu a baki ko dady"
Murmushi tai tace" idan ana cin abinci ba'a surutu kaji mubeen?" Ya ce tom mami zaki gidan mu ko ki rinƙa min wanka da kwalliya sai mutafi gidan hajiya ko? Ta bamu madara!
Haka dai yaro yai ta surutu sosai har suka kammala ta gyara mai jikin shi, sukai mata sallama suka tafi tazo kwashe kayan da abban mubeen yaci taga kuɗi 20k ta kira shi tare da faɗin ka manta kuɗin ka!!
Noo na baki ne saboda karramani da kika yi thanks so much My baby mereeh' mubeen sai kuka yake nan zai kwana wai...
Ohh Allah sarki baby mubeen wata rana zai kwana' yanzu ai sai yasa mamanshi ta daure ni...dariya ma Maganar ta bashi sosai sukai sallama!
...
..
. wallahi Hajiya da gaske yake aure zai yi ni kuma har ga Allah bazan iya aje aiki na ba don Allah ki faɗa min ya zanyi da raina Hajiya ta faɗa cikin kuka!!
hamdiya tunda "abban mubeen ya furta maki auren nan tabbas sai yayi shi, tun farko kece baki bashi kulawar da ta kamata nafada maki akwai ranar da zaki zo kina da nasani kan aikin ki amma kika nuna ke a'a ba wannan maganar yau ga ranar tazo" hajiya wallahi ina san mijina kuma ina san aiki na, yanzu dai ba abinda zaki mun wanda zai fasa ko ki mai magana ya janye??
Innalillahi "Hajiya ta faɗa tare da faɗin don uban ki hamdiya so kike ki turani bin malamai? Idan wani ya baki shawarar haka wallahi maza ki tuba karda naji kin je gun wani don hana auren nan idan ko kika je zaki ga matsala"
tana jin Hajiya tai wannan maganar ta kashe wayar ta' tare da kwantawa kan kujerar tana rusar kuka a haka ya dawo ya sameta tana kuka da sauri ya isa gare ta tare da faɗin "Lafiya mummyn mubeen?"
ta rungume shi ta ce'' abban mubeen don Allah kada ka kara auren Please zan samo mai aiki da gaske nake maka"
What kina da hankali kuwa? Mai aiki ita ce girki na? Gyara min ɗaki? Wanke min kaya? Ohh my god mai kike nufi hamdiya dani so kike ki ɗauke ki sakarai komi? Please foget da wannan maganar bana san ta!!
Mubeen da murnar shi ya ce" mummy munje gidan su mami har ta ban abinci a baki shima dady a filat ta zuba mai munci abinci mai daɗi mummy harda sobo ko dady" sai hankalin ta ya koma kan mubeen tace wacece mami kuma?
Mummy sabuwar mami dady yace zai min ta rinƙa min wanka harda abincin mai daɗi mu rinƙa zuwa gun wasa da ita, ya ida maganar tare da tsalle....
Fatsume zaune take kan abin sallah yau dai satin su biyu da aure alhamdulilahi tagama shan wahalar Yanzu sai dai kuma jikin hamma habu ya dau zafi ana ta magani...
Please contuie
Ana ta shirye shiryen biki ta kowane ɓangare suna ta murna "maryam tadawo daga kasar waje daman taje karo karatu ne, yanzu saboda bikin tadawo gida don ayi biki sai takoma"
Yau dai walima' ƙawayen ta na makaranta da asibiti sunzo taya ta murna ana cikin yine sai ga hamdiya tazo da zugar ta aka fara fada dole aka shige cikin palo, maryam ta daga waya ta kira abban mubeen ta fada mai abin da ke faruwa ko minti 30 ba'ai ba sai gashi yazo ya kora su ita kuma bai ce komi wani kallo ya watsa mata ya yi gaba, duk abinda ake suna kallo ta windom sai da suka fita sannan sukai addua aka bar walimar haka....
.........aunty ita ce ke kula da "jannat alhamdulilahi tana samun sauki sosai kwananta uku kila yau a sallame su"........ Aunty kila yau dai a sallame mu ko??
Ehh jannat tunda an samu sauki...
Wajen ƙarfe 8:30 dr yazo ya rubuta mata magunguna da sallama aunty taje ta siyo maganin sannan tahada masu kayan suka tafi gida, har yanzu alhaji bai barta tazo ganin taba amma kullum dai suna waya sosai taji jikin da sauki, motar aunty suka hau suka tafi gida kai tsaye...
Ko da suka isa wanka jannat tai tare da shan tea mai zafi ta kwanta sai barcin gajiya, ita kuma tacigaba da aikin gida!
.............
Sameer tunda ya saki "jannat yake holewar shi wannan daban ta anjima daban kuɗin shi dake account dasu yake ta facaka, yana kashe ma ƴan mata kudi sosai kullum a haka yake abinci sai dai ya siya yanzu harka ta ɓudi har maza yana amfani da alhazawa kamar me".....kamar kullum yau ma yana zaune ƴan mata sun kai biyar kowacce kuma tana shafa jikin shi kamar me shi kuma yana kwance yana jin su..
Da yamma ya sallamai su duka' wacce take uwar daka bata fito ba ya shiga cikin dakin suka daura,. Cikin dare ko gobara ta kama gidan har dakin da suke da ƙyar aka fidda sameer jikin shi duk yaci wuta ita kan ba ma a gane fuskar ta..
Yau ya kama asabar an ɗaura auren mereeh da Imran kan sadaki dubu ɗari uku' sai murna kowa ake inda aka kai amarya gidan ta bai haɗa su da matar shi ba kowa nashi daban-daban ne saboda bai san tashin hankali...
Ƙarfe 8pm ya shiga cikin gidan hamdiya tare da mata sallama zai tafi tace ita bata san wannan ba sai dai su tafi tare ya ce ina, haka dai ya tafi ba dan ranta taso ba ya tafi gidan amarya mereeh can ya iske sauran kawayan ta suka mai sallama daman shi suke jira su tafi kar su barta ita kaɗai, ya masu sallama mai tsoka inda suka yi alwala tare da Sallah ya mata tambayar addini kuma ta bashi amsa kaza ce suka fara ci ita dai duk a tsorace take suka gama ta wanke baki suka haye gado daga nan ne zance ya sauya tana kuka tana rokon shi da ya kyale ta amma ina yaki haka sai da ya yi abin da ya keso sannan..
.... Fulani komi ya watse mata wulakanci sosai ya ke mata mai martaba dan sauƙin ta ɗaya har yanzu hankalin shi bai dawo sosai ba, bai tambayi su hanan ba gashi yanzu duburar ta bata riƙe bayan gida idan taji shi to tai sauri ta tafi in ba haka ba anan zai zubo, tana san zuwa asibiti tana soron a kira mata wani ciwon hatta gaban ta ya koma wani iri ba ƙyan gani...
Fulani wai Lafiya kike ne cewar mai martaba?
A'a mai kagani kuma? Lafiya ta lau sai dai idan idanun ka ne.
Oh shikenen sai naga kamar kin rame da yawa shine dalilin tambaya.
...................
Alhamdulilahi jannat Alhaji ya yafe mata yanzu haka tana gaban mummy tana kula da ita sosai tadawo jannat ɗin ta sosai ta ƙara ƙyau kamar ba ita ba Samari ko da masu mata sai kunno kai take harda wanda yake zuwa siyan wainar fulawa gidan ta harda shi, ita ta ma rasa wane zata zaba cikin su, wanda ya fi kwanta mata dai Umar mai siyan wainar fulawa!
......hanan an samu tunda har ana ɗan iya buɗe baki tai magana amma ba wanda zai ji Sakamakon da bata iya ko buɗe bakin, sati ukun da ya basu ya cika kuma yau ne suke so su tafi ko sati ne su samu a can....
........wayyo Allah hamma bayana don Allah ka min addu'a mutuwa zanyi a taimaka min wayyo Allah na zan mutu ni fatsume!
Duk ya bi ya ruɗe ya kira baffa yana gani ya ce" wannan asibitin birni zamu tafi gaskiya tunda cikin bakwai ne kila bakwaini zata haifa" Allah sarki kamar ya kurma ihu haka yake ji mota suka samo suka tafi ya kira Yan uwan innar fatsume aka tafi tare sun isa kenan na kuda ta kara kamata gadan gadan ba'ayi minti 30 ba ta sulbulo ƴar ta mace mai kyau mai kama da hamma tunda lafiyar ta lau aka sallame su tare da faɗa masu ƙaidojin kula da yarinyar banda jagula, suka isa gida aka ɗaura ruwan wanka inda aka sa ma jariri yar lalle duka jikinta na Hausa sai da yayi minti 10 aka wanke tare da mata wanka aka sa mata kayan sanyin ta ita ma mai jego aka mata wanka an sha dai kuka wai ruwan zafi da ƙyar aka mata shi ko.......
A'a sannu malam naga ai ana cikin hidima tunda muka iso!
Murmushi ya mata tare da faɗin kuyi hakuri wallahi wai yar waje na ce ta haihu Yau shi ne fa, amma suna cikin koshin lafiya.
Masha Allah cewar mummy tai mai Barka nan ya fara masu maganin sai ihu hanan take tana kuka sosai, mummy kuma fita tai don har ga Allah bata iya ganin yadda hanan ke wahala, haka dai akai ta mata magani tana kuka mummy taje ma fatsume Barka da daddare lokacin angon jego bai dawo ba.....
Sai ƙarfe 8:30 ya dawo gida ta bashi labarin yan birni sun zo mata barka ya ce angode!
Cikin dare ikon Allah bakin hanan ya fara magana ta ce'' mummy tashi yau Allah ya yanke min wahala"
Kamar a mafarki mummy taji Maganar hanan da sauri ta tashi don ganin gaske ne ko a'a aiko suka kama murna har da kuka fita sukai sukayi alwala tare da yi ma Allah godiya, da safe sun karya hanan tace zata je tai mata barka ita ma...
Amarya dai ana shan kula gun mijinta kullum da safe yana zuwa don ganin hamdiya haka da daddare ya mata sallama ya dawo gida, yau ma ya shiga ya iske ta kwance wai bata lafiya ya mata tambayar duniyar nan mai take ji taki faɗa haka ya fita shi da mubeen ya dawo gida, mereeh taji daɗin ganin yaron da ya kawo mata shima sai murna yake yaga mami ta dauke shi zai mai dashi yaro yace a'a fa sai kuka haka aka barshi ya kwana gidan amarya..
Sameer kafa ta lalace gashi ba kuɗin aiki sai dai suka tattara suka dawo gida sai tsutsa ƙafa ke yi, ya ce inna don Allah kuce jannat ta yafe min don Allah nan ya basu labarin irin cutar da ya mata sun tausaya mata sosai, suka ce ma alhakin ta ne ya kama shi...
.....an sa ranar bikin jannat da Umar duka wata ɗaya saurayi ne soyayya take sami da bata sami ba ada yanzu ko har ta manta da wata damuwa..
...... hamma yana zaune bakin gado ita kuma fatsume tana zaune daga can sai mai ma jariri yar wanka tana mata, hanan tai sallama ta shiga suka gaisa tai mata Barka bata lura da mutum ba sai ji tai ance Yanzu mai zaki ci bana san ki zauna da yunwa gashi kina jego....
Ji tai kamar Muryar....ta daga kai don gane ma idon ta waye aiko ta tashi da sauri tare da faɗin innalillahi wallahi wannan ɗan uwa na ne ta fita da gudu sai wajen mummy!
Shi ko kallon ta ya yi yace ko bata da hankali ne oho...
Mummy ita tsoro ma abin ya bata ta riƙe ta tare da faɗin hanan lafiya kike wannan gudun kuwa?
Mummy hammad ɗin ki nagani Wallahi shine hanmad shine Allah kuwa ki tashi muje ki gani..... tunda hanan ta fara magana gaban mummy ke fadi tace muje to..
Daidai lokacin ya fito sukai ido biyu da mummy ya daga hannu zai yi magana ya faɗi ƙasa sumamme...
Da sauri mummy ta tafi gun shi tare da rungume shi tana kuka, sai ga baffa jin kukan su su fatsume sun tsaya kallon ikon Allah...
Ke Fulani idan har baki nemomin matata ba da yara na sai na maki hukunci mai zafi.
Ita kanta Fulani a zaba take sha ba kaɗan ba saboda gaban ta har tsutsa yake fitar wa, masu mata iskancin ma sun gudu ganin Yadda ta koma kuka take mai cin rai gashi ta koma gun boka ya rasu ga wannan abu da mai martaba ya bullo dashi yanzu ina zata sa kanta..
Bayan wata uku
Mereeh anyi kyau yanzu tana da ciki wata biyu inda rainon mubeen ya dawo hannun ta kula take samu sosai har ta bangaren Hajiya bata da Malama..
Jannat anyi bikin su na cikin rufin asiri gidan ta mai kyau gashi ya sama mata aiki...
.......
Ɗaukar shi baffa ya yi ya fara mai magani kwanan shi uku ya dawo haiyacin shi, ya na tashi ya fara da salati tare da kiran don Allah kada ku kashe ni mummy hanan mai martaba Please help me....
Baffa sai mai addu'a yake nan dai baffa ya basu labarin Yadda ya samai tare da aura mai yar shi don ya warke..... mummy taji daɗin taimakon da ya masu sosai ga hanan ta warke ga danta ga jikar ta.
Fatsume ce ta shigo Tare Da faɗin baffa hamma habu ya dawo tunanin shi ko alhamdulilahi.
Mummy tace zo nan ƴata ta isa gare ta tana sunne kai ita kunya shi ko hamma kallon soyayya mai zafi yake ma fatsume..
Sai a sannan ne wasu abubuwan suke dawo mashi ta bashi tausai yarinya ta ci sunan Marigayi ya Maryam ana kiran da ilham ranar suna suka tarkata harda baffan aka tafi burni can, ba da jimawa ba wai ana sallama da mummy a waje.
Fita tai don ganin waye mai idon ta zasu gani inba mai martaba ba rufe ido tai ta buɗe ko gizo yake mata nan ya duka yana bata hakuri sosai kuwa tace ta yafe mai ya shiga cikin gidan ya gamsu zaune shi ma aka bashi Labarin abin da ya faru...
Gida a zoo road ya ba hammad shi da matar shi...yar tsohuwa makociyar su mummy aka ɗaura aure da baffa mai martaba ya canza masu gida sosai ya yi ƙyau inda Binta ta samu miji tai aure ita..
Bayan wasu shekaru
Sakkowa yake daga kan bene ta biyo shi a baya tana ohh Allah wai yanzu hibban haka zamu yi da kai wallahi naso zuwa amma kaki yarda ko?
Rungume ta ya yi tare da faɗin zairah na kalli cikin ki so kike ki wahalar mun da baby ne? Ki hakuri mutafi da ilham...
Yar ƙwalla ta share ba dan yaso ba haka suka tafi tare bazaka taba cewa fatsume ce ta koma haka ba.
Fulani kuma an haukace tuburan..
Mereeh an haifi yan biyu' an sa sunan baba da mama..
Sameer kuma an yake ƙafa Bara yake fita yanzu
Jannat an samu ciki sai shan lallaba take
Matar hammad an kara haihuwa Yan uku ɗaya namiji sauran mata yasa sunan mai martaba macen Fatima sunan matar shi sai humaira
Tammat bihamdulilahi
Alhamdulilahi anan nakawo karshen littafin HAMMAD ZAIRAH
Taku har kullum BOOS LEDY WRITER
Sai mun hadu ana gaba