Showing 6001 words to 9000 words out of 34150 words

Chapter 3 - KYAUTAR ZUCIYA Book Complete By Bilkisu H. Muhd.txt

14 Jan 2025

2490

rai. Su dai burinsu idan suka tashi da safe Allah-Allah suke yi su wuce gurin neman kudi, idan suka tashi a kasuwar su wuce majalisar gulma, wanda su abokan nasu ke dora musu wani tunanin ko layin rashin mutunci. A nan suke koyon tsumulmula, suke koyon son mata. A nan ake cusa musu ra’ayin su kara aure, ba za su tashi dawowa gida ba sai matar ta yi bacci, yaransa sun yi bacci. Kai wani ma saboda tsabar kwarewa da yawon majalisa yaransa ba su gama sanin waye shi ba, wani fannin in matar ba ta samu damar yin bacci ba, daga ta yi musu sannu da zuwa a ciki za su amsa suna faman cika da batsewa, wai kada ta raina su, za su baka abinci idan ba masu ci a waje ba ne, da zarar sun dirka a ciki sai kwanciya, sai dai ka ji yana jan minshari, shi ke nan ke an mayar da ke dutse kin zamo mai zaman ‘ya’yanki.
“Ammina ta kasa gane inda na dosa ita dai kullum na fitar da mijin aure, ba zan taba biye mata ba. Mijin da zan yi rayuwa da shi dan gaske ne, wanda zai ba ni hakkina a duk lokacin da na buqata. Ai ni da na ga mijin da zai iya ina ganewa, har yanzu ban ganshi ba”.
Tana matuqar son namiji wanda ya kai qololuwa gurin haduwa, kyawun, suffa da na aljihu, shahararren mai kudi shi ne burinta, don haka a kullum ta ke mafarkin kasancewa da Ahmad Deedat. Tana ji a ranta kamar shi din ajiyarta ne.
Kiraye-kirayen sallah ne ya katse mata tunani. Mikewa ta yi hade da kashe kayan kallon ta nufi dakin Ammi, wadda da alamun kiran sallar bai ratsa ta ba. Ta shiga dukan filon da Ammin ke kwance a kai.
A firgice ta bude ido, tana tunanin ta makara. Jin alamun za a tada sallar a masallaci ta yi, da sauri ta miqe har tana ture Aazeen.
“Haba Ammi, ki bi a hankali mana, ba fa ce miki aka yi tashin alkiyama za a yi ba”.
Ba ta bi ta kanta ba ta fice abinta.
Aazeen ta koma bedroom dinta ta mike a gado, tuni bacci ya yi awon gaba da ita.
karfe goma da rabi sun hallara a dinning room, Alhaji Usman ya dubi Hajiya Rahma, “Ya dai?”
“Me ka gani?”
“Na ga kamar kina da damuwa”.
Ta kada kai, “Ko daya”.
Nurat ko littafi ne a hannunta tana dubawa.
“Nurat ki aje littafin nan ki ja abinci duk kin daga hankali, in dai ba kya cin abinci zan fa hana ki”.
Ta ajiye alqur’anin a gefe tana cin abincin. Tana leka surar da ke a bude.
Aazeen ce ta fito cikin kayan bacci manne da waya a kunne. Da alama waya ta ke amsawa, gaba daya ita suke bi da kallo.
Bathroom ta nufa.
“Ran gida me ya samu bathroom dinki?”
“Ina ganin kamar rariyar ce ta toshe”.
“Ok”.
Ta shige bathroom din. Mintina biyar ta diba a ciki ta fito da kayanta a jike sharkaf! Wai nan alwala ta daura.
Ammi ta cika fal da takaici, kokarin zama ta ke a dinning.
“Kin ga ki fara sitirta jikinki, idan ki ka yi sallah sai ki yi break ”.
“Tab! Ammi, sallah ba zai yiwu cikin wannan yanayin ba, kin ga kuwa yadda nake jin yunwa?”
Kokarin zuba dankali ta ke a plate.
“Magana fa nake yi”. In ji Ammi.
“Oh my Mom, please ki kyale ni”.
“Haba Rahma ke kuwa ki kyale ta mana, ai shi ci shi ne gaba da komai”.
Dole ta yi shiru tana jin zuciyarta duk a jagule. Ta sani tun farko shi ne masomin rusa tarbiyyar Aazeen, yadda yake yi din ne ya sanya ta ke tuhumarsa da abubuwa iri-iri. Ta sani wannan ba shi ne so ba, me ya sa ita Nurat bai ba ta irin wannan tarbiyyar ba? Shin a cikinsu waye ya fi so kenan? Yana nuna ma Aazeen duk wata gata da soyayya, ba ya son bacin ranta. Ita kuma Nurat tsangwama, da kyara. Yana shigowa gida sai ya fara tambayar ta yi sallah? Ta je islamiyya da ire-iren wadannan tambayoyin. Shin wa ke nan yake kauna?
“Dankali kawai na gani, ban ga farfesun da na ce ladidi ta yi min ba?”
“Kira ta, kila karasawa ne ba ta yi ba, ai babu wanda zai ketare umarninki Rangida”.
Ta bude murya baki daya cikin kwala mata kira.
A sukwane ta karaso tare da durkusawa a gabanta. Ta watsa mata harara.
“Ina kayan karyawata?”
“Yanzun nan na hattama, bari na kawo miki”.
Da sauri ta yi waje, sai ga ta da kayan karyawar ta jere a gabanta.
Janye plate din Ammi ta yi a gabanta.
“Kada ki taba komai a nan ba tare da kin je kin sauya kayan jikinki ba”.
“Haba Ammi, kashe ni za ki yi? Na ce da ke yunwa nake ji. Ni kam gaskiya a’a”.
Ai kuwa ta shiga yi mata fada, takaici kamar Aazeen za ta mutu. Baqin cikinta wai Ammi ta yi mata fada a gaban mai aiki. Juyin duniyar nan ba ta mike ba, ta bude farfesun a qufule, cikin neman wanda za ta huce a kansa. Ta dubi Ladidi.
“Cewa na yi ki saka min curry? Uban waye ya sa ki? Kawai ba ki yi shawara da ni ba kin yi abin da ki ke so ko?”
A sanyaye, “Ki yi haquri, na ga ai kullum ina yi miki amfani da shi”.
“Shut up! Ina magana kina yi?”
Gaba xaya ta dauki plate din farfesun ta watsa mata a fuska. Wata gigitacciyar qara Ladidi ta saka. Da gudu Nurat ta mike tare da rungume ta a jiki. Ladidi na ta ihu tamkar wadda ake kokarin zare mata rai. Da taimakon Nurat suka nufi famfo.
“Man kana ganin abin da Aazeen ta aikata ko?” Hajiya Rahma ta fada tana kallon Alhaji Usman.
“Ita ta ja ma kanta. Ya kamata ta dinga kiyaye matakan aikinta, tunda ba kyauta ta ke aikin ba”.
“Dad, ina son gaya maka. su Zee fa na tafe”. Aazeen ta fada ba tare da ta nuna nadama a abin da ta aikata ba. Gaba daya ma sun mance da ita Hajiya Rahmar, hirarsu suka shiga na yadda za su sauki bakin nata.
Miqewa ta yi cike da takaici, har lokacin tana jin ihun kukan Ladidi, Nurat na faman ba ta haquri.
A can shashin masu aiki, Ladidi ta yi matashi da cinyar Nurat ta dage sai bushe mata idanu ta ke faman yi, hankalinta a tashe, yadda idanun suka kumbure sun yi jajir da kyar ta ke motsa su. Hawaye sai faman tsinkowa suke daga idanun. Cikin muryar kuka.
“Ladidi sannu, za ki warke. Yana yi miki zafi? Sannu”.
Ta rude matuqa, jikinta sai bari yake, zuciyarta fal haushin Aazeen. Karin bakin cikinta shi ne na halin ko’inkular da akai wa Ladidi akalla ya kamata su zo su duba halin da Ladidi ke ciki, yanzu ya za ta yi idan Ladidin ta makance?
“Nurat ina son dora girki”.
Cikin tausayawa, “Haba ta ya ya za ki iya wani girki? Ki bari ni zan yi kokari in ga na yi”.
“A’a Nurat, ki rufa min asiri”.
“Kada ki damu babu wanda zai fahimci haka. Ina zuwa… amma dai akwai duk abin da zan bukata ko?”
Ladidi ta jinjina kai.
“Ok, yanzu ki kwanta ki huta kafin ki tashi na gama kin ji”.
“Na gode Nurat”.
Ta bi Nurat da kallo tana jin qaunarta a ranta. Halayyarta daban da na iyayenta, kamar yadda ta lura kowa na gidan bai damu da damuwar wani ba, sun dauki rayuwarsu tamkar na turawa, musamman Aazeen wadda duka dabi’unta irin na ubanta ne. Ita kam Hajiya Rahma babu wanda ya fahimci inda ta sa gaba, ba za a dai a kira ta mara kirki ba, kodayake ba lallai a fahimci wace ita ba, saboda ba ta cika shiga shirgin mutane ba, sabanin Nurat wadda ba ta wuce shekaru sha bakwai ba, yarinya mai mutumci da shiga rai, wadda ba ta xauki kanta da zafi ba, ba ta da wahalar sha’ani, kunyarta shi ke kara mata daraja a idanun jama’a, don hakan ya zame mata tamkar wani ado.
Tazarar da ke tsakanin kicin da dakunan da ke gidan ya sanya babu wanda ya lura da kai-komonta. Wanke-wanke ta fara yi, ta ci uwar damara. Bayan ta gama ta shiga dogon tunanin abin da za ta dafa wanda ba zai ba ta wahala ba. taliya ta ayyana a ranta, amma ta ya ya za ta sarrafa kayan miya? Ita ba ta taba kwatanta shiga kicin don sarrafa wani girki ba.
Komawa ta yi dakin Ladidi, don ta gaya mata yadda za ta yi. Bacci ta ke yi lakadan, har da su minshari. Murmushi ta yi ta koma ta shiga tunanin yadda za ta yi. Tunawa ta yi da tana da littafin girki, da sauri ta nufi ma’ajiyar littattafanta. KADARAR KITCHEN wanda Bilkisu Salisu Funtua ta rubuta ta nemi guri ta zauna, tare da dubo abin da ta ke son dafawa. Ta mayar da littafin ma’ajiyarsa, ta koma kicin ta debo kayan miya ta wanke, ta soma yanka albasa.
Ji ta yi wuqa ta shige hannunta, ta kwalla kara tare da sakin wukar yadda ta ga jini na zuba ne ya sanya ta rudewa.
A sukwane Zaruk ya dano kicin din ya kai hannu zai riko hannunta. Da sauri ta maida hannun baya cikin tsananin tsoro.
“Ki bari in gani, ba ki ga jini ne ke zuba ba?”
Ta yi saurin maida hawayen da ke qoqarin silalo mata.
“Kada ka damu, kawai jinin ne, amma ai babu zafi”.
“Oh God! Wai ke me ma ya kawo ki kicin? Wa ya aike ki?”
Ta fara in’ina, ya daure fuska.
“Na ce da ke waye ya aiko ki kicin?”
Za ta yi magana ya mike a fusace zai fita.
“Don Allah ka yi haquri, zan gaya maka. Ka dawo don Allah Yaya Zaruk”.
Ya koma ya zauna cikin kafe ta da idanunshi.
“Ke nake ji”.
“Ladidi ba ta da lafiya shi ne nake taya ta”.
Ya sake xaure fuska.
“Ita din ce ta ce ki taya ta?”
Cikin rawar murya, “A’a, to gaya min”.
Dole ta zabi ta ba shi labarin yadda abin ya faru. Ya ja tsaki ya janyo mata kujera.
“Maza zauna”.
Ba ta da zabi dole ta bi umarninsa. Komawa ta yi ta zauna, nade hannun rigarsa ya yi ya shiga aiki tukuru. Ta dinga kunshe dariya a ciki, ga mamakinta Zaruk ya iya komi.
Ya dube ta a sakarce, “Nurat, fito ki yi dariyarki a bayyane”.
Ta dabarbarce, “Da gaske Yaya Zaruk ba dariya nake yi ba”.
Jalof din taliya ya yi, sai plaintain da ya soya farfesun kifi. Ya diba a cokali ya mika mata. Ya yi mata alama da ta yi testing.
Ta karba tana dandanawa. Ya kafe ta da ido.
“Ya ki ka ji?”
“Yaya Zaruk, ashe ka iya girki?”
Ya harare ta, “je ki yi maza ki shirya dinning ko?”
“An gama Yayana”.
Da sauri ta yi abin da ya ce. Bayan ta gama shirya komai ya ce da ita, zai je ya siya ma Ladidi magani. Yana fita ta shiga wanka.


Zaruk ta hango da Hajiya Rahma zaune suna cin abinci, ta sakar masa murmushi. Karasawa ta yi ta zauna. Ba a jima ba Alhaji Usman suka shigo da Aazeen rike da ledoji a hannu, su ma joining suka yi zaman cin abincin.
“Yau Rangida babu korafi, da alama abincin ya yi dadi”.
Nurat ta dubi Zaruk ya sakar mata murmushi.
“No Dad, kawai dai ina jin yunwa ne”.
“Da ma ai ke ba a taba iya miki”. Hajiya Rahma ta ce da ita.
“Ladidi ta cancanci tukwici kenan?” In ji Zaruk yana kallon Nurat, ya faki idonsu a hankali ya dinga motsa baki yana nufin zai fada.
Ta yi saurin kada kai tana rokonsa. Mikewa ya yi tsaye.
“Ni zan wuce Ammi, a yi wa kuku godiya sosai”. Ya fada yana murmushi.


ABUJA
“Ummi ya kamata ki saba, na yi tafiya zuwa qasashen waje bila’adadin, na zaga duniya komai bai same ni ba, nan zuwa Kano tafiyar mintina ne, da zarar jirginmu ya sauka shi kenan an wuce gurin. Ko kina tsoro ne kada jirgi ya fado da dan lelenki?”
Deedat ya fada yana kokarin tallafo kuncinta da hannayensa biyu. Ta sauke ajiyar zuciya cikin damu
“Ba haka ba ne, kawai dai ina tsintar kaina cikin rudu duk lokacin da ka ambata cewar za ka Kano. Bana samun nutsuwa, ban san me ya sa haka ba”.
Ya yi murmushi cikin kokarin kwarara mata gwiwa.
“No, Ummina kada ki mance kirarina, in ka san ni ni ne, in ba ka sanni ba, ba ni ba ne. Ummina. Kowa ya san ba ni ba ne, kin ji sam ba ni ba ne babu wanda ya san ni, kuma ma ban da ke da abinki addu’arki fa na tare da ni, ba zan mutu
*💖💕KYAUTAR ZUCIYA💖💞*



*NA*




*BILKISU H.MUHAMMAD*
_(Matar Auwalu By fos zage)_










*Free page 5 6*








*_Wanan littafin na kudine akan 300 kacal in kinsan zaki biya don ki fitarmin dashi Dan Allah ki barmin kayana yar uwa_*




*Ga jerin sunayan litattafai na da zaku samu a kasuwa*


*1. IZZATU*
*2. MULKIN MALLAKA*
*3. KAUNA CE*
*4. DACEWA*
*5. RASHIN RABO*
*6.TARAIRAYA*
*7. JINI BIYU*
*8. AKWAI BAMBANCI*
*9. TSALAR KAUNA*
*10. YA YI SAKE*
*11. ILLAR SABO*
*12. SO DA SANKARA*
*13. RASHIN RABO*
*14. WATA RAYUWA*
*15. HUBBAN SHADIDAN*
*16. BAKIN K'AZAFI*
*17. MATSALAR KAUNA*
*18. KYAN KUSKURE*
*19. WA YAFI SONTA?*
*20. GABA DA SO*




_NOW_
*KYAUTA ZUCIYA*


```Duka wanan litattafan sunanan akasuwa zaku sameso a shagunan sai da litattafai inasha Allah```




*_Wanan littafin na kudi ne, Mai bukata karanta shi zai turo 300 ta wanan account number din_*
*_2277439558 UBA Bank_*
Bilkisu H Muhammad_* *_idan an turo sai a turawa wanan number alter 08031307884 domin tabbatar da an turo din idan kuma VTU za'ayi ita dai number za'ai da ita ko katin MTN na 300 din sai in saki a group paid insha Allah_*




*_____________________________________*


*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*_____________________________________*












*“N* o, Ummina kada ki mance kirarina, in ka san ni ni ne, in ba ka sanni ba, ba ni ba ne. Ba ni ba ne Ummina. Kowa ya san ba ni ba ne, kin ji sam ba ni ba ne babu wanda ya san ni, kuma ma ban da ke da abinki addu’arki fa na tare da ni, ba zan mutu ta hanyar da ki ke tunani ba, a kan gadonki zan mutu, a kan kafafunki, yanzu ki yi min addu’a zan tafi kwana bakwai kacal zan yi ai kamar yau ne ko Tawan?”
Ta dinga murmushi a gefe daya kuma idanunta na fidda kwalla ta shafa sumarsa.
“Ka kula da kanka yarona, Allah ya yi maka albarka”.
Gaba daya suka dunguma har zuwa get inda ya shiga mota zuwa airport, ba ta bar get ba har sai da motar ta bace ma ganinta, ta juyo gida cike da kewarsa.
Hango shi ta yi zaune ya dora kafa daya kan daya yana kada su. Gabanta ne ya yi wani irin bugawa, ta shiga maimaita innalillahi…
Ya mike ya karaso gabanta yana tintsira dariya.
“Ya yi babar mai kudi, babar Richman da kyau”.
Ya sake tintsirewa da dariya.
“Da alama kina cike da kewarsa, kina tsoron kada ya mutu ko? To ai da saura, domin har yanzu ba wanda ya san shi ne da zarar an fahimci waye shi ina tabbatar miki ko awa daya ba zai kara ba, ni ne kuma zan tona masa asiri, ni din nan ni ne ajalinsa. Yanzu ki shiga ki debo min rabona in tafi, na sani ke ma saboda wannan din ki ke nuna mishi cewar kin fi kowa kaunar…”
Kyakkyawan marin da ta wanke shi da shi ne ya sanya shi kasa karasa maganarsa. daki ta shiga, sai ga ta da bandir din ‘yan dubu-dubu guda biyu.
Cikin muryar kuka ta soma magana, “Bana son ka kara minti daya a gidan nan, ka bace min da gani”.
Ya karbi kudin ya cilla su sama ya cafe, ya sumbaci kudin.
“Kin fanshi kanki, sai gani na biyu”.
Durkushewa ta yi ta dora kai a kujera, ta rushe da wani irin kuka.


KANO
Gida ne madaidaici ba za a kira shi na masu kudi ba, daga waje gidan bai wani hadu ba, a cikin gidan duniyar ta ke, don duk wani abin more rayuwa an tanade shi a ciki. Mutane biyu ne ke kula da gidan wadanda suke amintattunsa ne, su ne ke kula da komai na gidan.
Tunda ya shigo Kano bai iso gidan ba sai da ya je ya gama duk wasu harkokinsa, sannan ya nufi gidan. A harabar gidan ya yi parking. Idris ya yi saurin karasowa ya bude masa murfin motar cikin yi mishi sannu da zuwa.
“Ya na ganka kai daya Ina Adamu?”
“Ya fita karba wa Madam take away”.
“Madan? Wacce?”
“Nabila”.
“Nabila kuma, yaushe ta zo?”
“Tun dazu”.
Nan da nan yanayinshi ya sauya, bai sake bi ta kan Idris ba ya yi gaba.
Ya yi arba da ita ta fito daga wanka daure da tawul. Ya yi saurin kawar da kai. Ya sake tamke fuska.
“Ke ba kya jin kunyar abin da ki ke aikatawa ko?”
Ta yi dariya, “Saboda na ganka in fita da gudu in dauko hijabi in yaba ko ya ya Deedat? To ma me zan boye maka? Ka yi min wanka, ka sanya min kaya, Yayana mijina. To me ya rage?”
“Wannan abubuwan duk sun faru ne lokacin da kina karama, yanzu kin girma, ya kamata ki kiyaye”.
Ya shige bed room.
Ta yatsina fuska, “karamin abu kana son maida shi babba”.
Yana zaune a kan gado da laptop a gabansa yana tura wa abokan kasuwancinsa sako ta mail dinsa. Ta shigo sanye da wasu fitinannun kaya, sai faman karairaya ta ke. Ta zauna a kusa da shi.
“Na tsorata da rashin dawowarka, har na soma tunanin yadda zan iya kwana a gidan nan ni kadai”.
Ya rufe laptop dinsa ya kallo ta.
“Wannan ya zamo zuwanki na farko da na karshe a gidan nan, muddin ki ka kara tako kafarki gidan nan wallahi sai kin yi da na sanin zuwanki. Kuma yanzun nan ki shirya na kai ki gidan Salim, gobe ki wuce gida”.
Kuka ta saka masa.
“Yanzu saboda na zo ne duk ka ke gaya min ba dadi? Mene ne laifina? Sati na biyu ban sanya ka a idona ba, na dawo gida a do kance a ka ce ka taho, ba zan iya kwana guda

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login