Showing 12001 words to 15000 words out of 34150 words
Chapter 5 - KYAUTAR ZUCIYA Book Complete By Bilkisu H. Muhd.txt
a mota aka maida ita makaranta, sannan ya dawo ofis xin Dr. Samir inda kowa ke faxin albarkacin bakinsa a kan al’amarin Nurat.
“Hakan na da kyau, ban yi tunanin akwai irin waxannan iyaye ba. babu wadda ta burge ni sai mahaifiyarta wacce ta xora ta a wannan turba”. In ji Salim.
Principal ya karve zancen, “Cikin class mate xinta ita ce mafi qanqantar shekaru, ga su nan ganxama-ganxama amma babu wadda ta kai ta qoqari. Qwaqwalwarta tamkar computer, irinsu ake ma laqabi da gifted. Na daxe ban ga yarinya kamarta ba, yadda xalibai da malamai ke qaunarta bai sa ta giggiwa ba, gaba xayanta ma tsoro ne da ita, ba ta shiga cikin mutane sosai. Ba qaramin abu ne zai sa ka ji bakinta a class ba, kullum ka ganta wala’Allah a makaranta ko a gida cikin hijabinta zumbulele kamar mai shirin tafiya masallaci. Su kansu malamai mata in sun zauna hirarta suke babu wanda ya tava kawo qararta’.
Haka ya yi ta bada labarinta, har sai da Deedat ya ji a cikin zuciyarsa babu masaqar tsinke, bai tava jin yadda yake ji game da ita ba a kan wata mace ba, shin me hakan ke nufi? Me ke shirin faruwa da shi?
“Ammi ta ce duk lokacin da na bari namiji ya tava min hannu zan samu cikin shege, idan na samu cikin shege mutuwa za ta yi”.
Sautin muryarta ya dinga yi masa kuwwa a kunne, ya shiga kai-komo, gaba xaya ya kasa samun nutsuwa. Bathroom ya shiga, gaba xayansa ya shige cikin shaya yana jin ko hakan zai saukar masa da nutsuwa. Babu abin da ya ragu, sai ma rikicewa da ya qara yi. Doguwar riga ya saka jallabiya mai yankakken hannu, ya yi zaman dirshan a kan carpet, kuka yake yi kamar qaramin yaro. Ya riqe kai yana juyawa cikin tafin hannunsa.
“Sun cutar da ni, sun cuce ni”.
Wani irin zazzavi mai zafi ya rufe shi har haqoransa na gwaruwa, barci ya sace shi. A can cikin baccin nasa babu abin da yake gani sai fuskar Nurat.
Tana zaune a farfajiyar gidan riqe da littafi a hannu tana karatu. Harxe hannu a qirji yana kallonta yana murmushi, bai qi ya tabbata a haka cikin kallon kyakkyawar fuskarta ba.
Jikinta ne ya ba ta akwai mutum tsaye a kanta, ta xan xago kai suka yi ido biyu. Ta yi saurin kawar da kai tare da faxin, “Zauna mana”.
Ta nuna masa kujera.
“Ban ji shigowarka ba”.
Yana murmushi, “kina zaune har na zo na shige na yi ciki, kin ga ke kam idan kina karatu ba kya ji ba kya gani”.
“Yaya Zaruk mun fa kusa fara jarabawa, ina son in karvi kyaututtuka a gurin Dad da Ammi, har ma da Yayata’.
Ya tafa hannu, “Da kyau yarinya mai wayo. To ki qara da tawa, zan yi miki kyautar da babu wanda zai yi miki irinta”.
Ta yi murmushi, cikin satar kallonsa.
“To, yanzu xan gaya mini kalar kyautar”.
“No, ki dai bari zan ba ki mamaki”.
“Allah ya nuna mana lokacin”.
Ta xan yi shiru tana tunanin wani abu.
“Wannan yarinya akwai magana a bakinki”.
“Yaya Zaruk inda a ce kowa zai riqe kyautarsa a yi mini alqawarin auren Yaya Aazeen, zan fi jin daxin haka fiye da komai”.
“Har yanzu ba ki bar wannan zancen ba? na ce da ke shi aure lokaci ne da zarar lokacin ya zo komai zai zamo labari”.
“Amma Yaya Zaruk Yayata ba ta rasa masoya ba, girman kanta ne ya rasa masoyan nata su tarke ta. Ka sani kuma ba ta da kirki kamar ba ‘yar gidan nan ba”.
“Ki bar ni da ita, ni ne nan zan yi mata miji, kuma ko ba ta so zan sa ta aure…”
Zumbur! Kamar wadda aka tsikara, “Yayana!”
“Na’am, qanwas?”
Ta gyara zama cikin muryar raxa, “Ashe kenan za ka iya taimaka mini na yi wa Yaya Aazeen miji?”
“Kina nufin ke za ki samo mata wanda za ta aura? To ta ya ya?”
“Mun haxu da shi ne ta sanadiyyar sava lamba, sau tari ina karvar wayar Yaya Aazeen na yi game ko na kira qawayena. Rannan na karvi wayar na sanya lambar qawata Hasina, ina kira aka xauki wayar, maimakon in ji muryarta sai na ji muryar namiji. Da farko na zaci yayanta ne, na ce da shi ina neman Hasina, sai ya ce ba ta nan. Hasina qawata ce sosai, sun tashi sun koma Lagos, na daxe ina neman layinta tun daga ranar na dinga bibiyar layin mutumin, ya iya magana, ba shi da wulaqanci, yana da tsananin haquri”.
Kawai Zaruk ya dinga binta da kallo.
“Mutumin da ba ki sani ba, ta ya ya ki ka iya xorar da halayyarsa?”
“Saboda a lokacin da na fahimci raina min hankali yake yi raina ya vaci, na kasa tanqwara zuciyata, na yi ta jifarsa da magana”.
Zaruk ya watsa mata harara.
“Ke xin har wani iya magana ki ka yi? Yaushe ne ma ki ka koyi magana?”
“Allah da gaske nake yi, ita magana zuwa ta ke yi. Ya ci gaba da haxiye duk wasu kalamaina, sannu a hankali muka fara sabawa da shi, idan ban kira shi ba na kan dinga jin kamar na rasa wani abu muhimmi. Bana son a ce zumuncinmu ya sha ruwa, ina ji a jikina yayata za ta so shi da zarar sun haxu sai dai idan na tuna ba shi ne irin mijin da ta ke mafarkin samu ba, ina jin tsoro, domin na fahimci shi xin ba wani mai qarfi ba ne”.
*💖💕KYAUTAR ZUCIYA💖💞*
*NA*
*BILKISU H.MUHAMMAD*
_(Matar Auwalu By fos zage)_
*Free page 8*
*_Wanan littafin na kudine akan 300 kacal in kinsan zaki biya don ki fitarmin dashi Dan Allah ki barmin kayana yar uwa_*
*Ga jerin sunayan litattafai na da zaku samu a kasuwa*
*1. IZZATU*
*2. MULKIN MALLAKA*
*3. KAUNA CE*
*4. DACEWA*
*5. RASHIN RABO*
*6.TARAIRAYA*
*7. JINI BIYU*
*8. AKWAI BAMBANCI*
*9. TSALAR KAUNA*
*10. YA YI SAKE*
*11. ILLAR SABO*
*12. SO DA SANKARA*
*13. RASHIN RABO*
*14. WATA RAYUWA*
*15. HUBBAN SHADIDAN*
*16. BAKIN K'AZAFI*
*17. MATSALAR KAUNA*
*18. KYAN KUSKURE*
*19. WA YAFI SONTA?*
*20. GABA DA SO*
_NOW_
*KYAUTA ZUCIYA*
```Duka wanan litattafan sunanan akasuwa zaku sameso a shagunan sai da litattafai inasha Allah```
*_Wanan littafin na kudi ne, Mai bukata karanta shi zai turo 300 ta wanan account number din_*
*_2277439558 UBA Bank_*
Bilkisu H Muhammad_* *_idan an turo sai a turawa wanan number alter 08031307884 domin tabbatar da an turo din idan kuma VTU za'ayi ita dai number za'ai da ita ko katin MTN na 300 din sai in saki a group paid insha Allah_*
*_____________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*_____________________________________*
*G* aba xaya ta dage sai zuba ta ke yi, tunda suke da ita bai tava sanin tana da magana haka ba, maganganunta yana jin zubarsu tamkar yayyafin wuta. Kullum idan ya yi magana sai a ce masa nawa ta ke? Ga shi ya yi sake har son wani ya shige ta. Ya sauke ajiyar zuciya.
“To ta ya ya za ki haxa wannan soyayyar?”
“Ina son tafiyata da shi ta sauya salo”.
“Ban fahimta ba”.
“Na ce da shi sunana Aazeen, ina amfani da komai na Yayata a zuwan ni xin Aazeen ce, hakan ya yi?”
Kawai jinjina mata kai yake yi.
“Amma ya ya Zaruk ka san me? Ya qi cewa yana sona, ina son in tursasa masa furta hakan”.
“To idan ya qi fa?”
“Yanzu Yaya Zaruk koya min za ka yi”.
Ji ya yi kamar ya tsinka mata mari, dole ya danne zuciyarsa, murya sama-sama, ‘Ke xin fa mace ce”.
Da sauri ta katse shi, “No, cewa za ka yi ita xin fa mace ce”.
Tilas ya bi yadda ta ke so.
“Ok, na ji ita xin fa mace ce, duk inda mace ta ke ana son ta darajja kanta, ki ci gaba da bi da shi a hankali, zai yi yadda ki ke so xin. Amma ya kamata ki ba ni lambarsa…”
Da sauri ta katse shi, “No, ba yanzu ba, idan komai ya yi daidai kai kanka sai ka fi samun qwarin gwiwar kiransa”.
Miqewa ya yi, “Ok, ba matsala”.
Ya fice ba tare da ya sake cewa komai ba, wannan yanayi da ya shiga ya kamata ta iya fahimta, sai dai ko kaxan ba ta kawo komai ba, asalima daxi ta ke ji tana ganin kamar ya ba ta qwarin gwiwa ne.
A wannan dare Zaruk ya kasa bacci, yana ta juye-juye a gado, son Nurat kullum qaruwa yake yi a ransa, musamman yanzu da komai nata ya bayyana. Nurat yarinya ce mai sanyin hali da son mutane, tana da shiga rai, tana da surutu amma ga waxanda ta saba da su, domin sam ba ta da saurin sabo, idan ta ga dama sai ka rantse ba ta magana saboda yanayinta mai sanyi ne. Akwai ta da tsoro, xaya daga cikin abin da ta tsana shi ne mu’amala da maza, duk yadda suke da namiji ta kan yi xari-xari da shi.
Nurat mai kyau ce, sai dai ba kowa ke gane hakan ba, dalilin kwalliya ba ta dame ta ba, ba ta saka xamammun kaya kullum cikin hijabi, ko da a gida ne in ta yi wanka ko hoda ba ta damu da ta saka ba, ballantana kwalli. Ba za a kira ta da baqa ba, ba kuma za a ce da ita fara tas ba, idan ta tsaya a kusa da baqin mutum lokaci xaya za ka iya ce mata fara, sai dai idan ta tsaya a kusa da fari. Kalarta na xaukar hankali, ita ba golden ba, ita ba choculate ba, abin da ya fi komai xaukar hankali a tare da ita shi ne diri, duk yadda ake son mace ta kai, tana da wushirya, muryarta a xan xashe ta ke, damvareren baqin da ke kwance a goshinta, wanda ake wa laqabi da tabon sallah ya yi matuqar qara mata kwarjini da kyau. Idanunta manya farare qwal, gashin girarta a haxe da xan uwansa. Abin da Nurat ta fi so a rayuwarta shi ne, Aazeen, tana matuqar qaunar ‘yar uwar tata.
Ya miqe zaune, “Kina qaunar Yayarki, da ita za mu yaqe ki. Aazeen tawa ce, sai yadda na tsara mata”.
*** *** ***
“Yaya Aazeen ana kiranki a waya fa”.
Sai da ta maimaita faxa kusan sau uku, sannan Aazeen ta yi firgigt.
“Mtsew! Qyale su”.
“Yaya Aazeen ba ki da lafiya ne?”
“Ina cikin damuwa ne kawai Nurat, tunanina da hankali gaba xaya sun koma ga mutumin nan, ina ji a jikina tamkar zai kusanto ni. Ina ji tamkar shi ne mijina, ban san shi ba amma kullum sai ya zo min cikin mafarkina. Wannan karon ne kaxai wani abun ke neman fin qarfina, amma ban tava neman abu na rasa ba, sai ya zamo mallakina ko da hakan zai zamo sanadiyyar rasa komai nawa”.
“Yaya Aazeen komai naki fa ki ka ce?”
“Eh mana, ban da abinki idan na rasa komai shi ne zai dawo min da ninkinsa. Ba ki san matsayinsa ba ne, har ma fa ya fi shugaban qasa kuxi”.
“To idan bai zama yadda ki ke so ba fa?”
“Kin ga Nurat, muddin yana da kuxi ko ya dai yake zan yi maleji, ai ba xaure shi zan yi a qafa ina yawo da shi ba”.
“To idan ki ka samu wanda ki ke so ba”.
Ta kai mata dukan wasa, “Allah ba zai sa in kamu da soyayyar wani ba, wannan zuciyar ba ta san so ba sai jin daxi da holewa, gwara ma idan na samu mai kyau na dinga kare yawa in mayar da shi fulawa kawai”.
“Yayata kina son mai kyau’.
“Eh mana, shi ya sa nake matuqar sonki”.
Nurat ta yi dariya.
“Yanzu idan ki ka haxu da mai kyau za ki so shi?”
“Mai zai hana?”
Wani daxi ya kama Nurat, tabbas haqanta zai cimma ruwa, ta fara samun yadda za ta villowa lamarin, ba za ta bari shaquwa da Adamu ya tashi a banza ba, sai sun zamo xaya.
Ji ta yi an zunguro ta. Ido biyu ta yi da Aazeen, Aazeen ta kanne mata ido xaya.
“Tunanin me ki ke yi? Gaya min, ko kin kamu ne?”
Ta yi murmushi, “Haba ‘yar maniniyata, kawai kina maganar maikyau na tuna da wani, ni ban ma tava ganin mai kyawunsa ba, za ku dace da shi”.
Tsaki Aazeen ta ja daidai lokacin wayarta ta sake xaukar ruri, ta miqe tana faxin, “Ke kin cika shirme’. Xaki ta shige.
Zuciyarsa tamkar ta faso qirji, son Nurat na neman halaka shi ta ina zai fara? Ya zai yi? Da sauri ya fito a xakinsa. Zainab matar yayansa na zaune a babban sitroom riqe da waya a hannu tana game. Kawai ya zube a kujera, ta xan dube shi, yadda yake ta faman huci.
“Man, waye ya tava mana kai?”
Kansa a qasa bai ce da ita komai ba, za ta sake yin magana ya yi saurin katse ta.
“Ban san haka nake sonta ba, ta yi tasiri a zuciyata, ba zan iya rayuwa ba tare da ita ba. lokaci ya yi da zan tinkari su Papa da maganar kada na mutu”.
‘Duk ita kaxai? Wace wannan haka?”
Ya furzar da huci.
“Nurat! Ina sonta, ina matuqar sonta. Ina jinta tamkar numfashina, ina jinta a can qarqashin zuciyata’.
Ta yi murmushi cikin sigar wasa ta dungure mishi kai.
“Da Allah can, sunan wacce ka ke ihun ita ce ruhinka ka mance Aazeen za ka ce”.
“Oh God! Kina tunanin mantuwa na yi? Nurat wadda na xebi shekaru ina dakon sonta, Nurat ita xin dai nake nufi”.
Ido buxe ta ke dubansa.
“Allah ba zai yi ma Nurat haka ba”.
A zahiri ta yi murmushi, “Haba dai, me za ka yi da wannan ‘yar mutsilar yarinyar da ba ta gama sanin ciwon kanta ba? Aazeen xin dai. Aazeen ita ce wadda za ku yi matching, gogaggiya kamar kai. Amma Nurat is too younger…”
“Stop Aunt! Kawai ki fito ki ce ni xin ban cancanci zama mijinta ba, saboda ni ban da kirki, ni ba na qwarai ba ne. To ina son ki sani zan sauya, zan iya yin komai a kan in mallake ta”.
Ta karyar da murya, “No, ba fa nufina kenan ba. Wai ni ina son in ce qarama ce ita”.
Tsaki ya ja ya miqe yana jin iya ci gaba da tsayuwa a gurinta zai iya marinta. Juyowa ya yi ya dube ta da idanun nan jajir, haka ne ya sa ta shiga hankalinta.
Ya tarar wayarsa na faman ruri, lambar Aazeen ya gani, da sauri ya xauka. Muryar Nurat xin ce ta ratsa kunnuwansa, wata irin ajiyar zuciya ya sauke.
“Yaya Zaruk”. Ta kira sunansa a can vangarenta, ta kuma rasa da me za ta fara, don haka ta yi shiru.
Ya katse shirun da faxin, “Gaya min, kina son ganina ne?” Ya faxa yana mai roqon Allah ya sanya ita ma ta jarabtu da sonsa.
“Nurat, gaya mini kada ki damu, kin ji?”
“Um-um… da man ce maka zan yi ina son kiran Adamu jiya mun fara hira da Yaya Aazeen, sai nake jin kamar zan dace, za ta iya amincewa”.
Ya cije leve, ji ya yi kamar wani tsini ya soke shi. Da qyar ya danne zuciyarsa.
“Ya kamata ki fara shawo kanta kafin ki jajibo shi”.
“Ai na ce da kai ta fara amincewa”.
“To shi kenan, ki bari gobe in na zo sai mu ga ya za mu yi”.
Ta yi murmushi mai sauti. Ba ta sake jiran me zai ce ba ta yi saurin katse wayar.
Ciki ya yi da wayar ya riqe kai yana faman huci.
“Zan nemo shi, ba zan amince ba. zan yi wani abu a kai, bana tsoron duk abin da zai faru. I don’t care, zan gaya ma Papana dole ne in tabbatar da za ki zamo tawa, kina wasa da rayuwa ta, ba zan tava amincewa da wannan ba, kullum ana raina min hankali da faxin ke xin qarama ce, da zarar na taso sai a danqwafe ni, an bar zuciyata da masifa, shekara da shekaru ina azabtuwa. Wallahi na yi alqawari ko kallonki wani ya yi da zummar so sai na vatar da shi, bana tsoro, ba zan xaga qafa ba, dole ne ki zamo tawa. Ni ne kaxai na san muhimmancinki ba zan yarda ba, ina! Haka ba za ta tava yiwuwa ba, kai xin ma sai na gano ko kai waye na sani duk da ba ka santa ba da zarar ka xora ido a kanta ba za ka barta ba”.
Ya ci gaba da sambatunsa kamar wani tavavve ko qaramin yaro.
Idan ta tuno hirarsu da Aazeen duk sai daxi ya kamata, yanzu ta ina za ta fara? Ta yi shiru cikin tunani. Ta yi murmushi, me ya sa ta damu da yawa? Me ya sa zuciyarta ta nace da son haxa dangantaka da Adamu?
Ta gyara zamanta, “Qila shi ne sanadin gyaruwarta, sai kun haxu zai gane wace ke na sani, ba zai guje ki ba a lokacin da ya san halayyarki, don haka nake son in kama zuciyarsa da zummar ke ce, kuma ai ni ma mace ce, zan iya har ma sai na jira Yaya Zaruk ya koyar da ni, mutumin da yake ta faman ja min rai? Zan ba shi mamaki, sai dai kawai ya ji ana yi”.
Ta miqe tsaye ta shiga zaryar yadda za a yi ta sato wayar Aazeen.
Da sauri ta yi sitroom inda ta riski Aazeen zaune sanye da wasu maqalallun kaya, ta xora qafa xaya kan xaya cikin duba novel book.
“Yayata, ko za ki ba ni wayarki zan kira Aisha?”
Ba ta yi magana ba, kawai ta yi mata nuni da wayar. Da sauri ta xauka ta koma xaki. Sai da ta kulle ta murxa key ta koma ta zauna a kan gado.
“Ke ce kuwa?”
“Mai ka gani?”
“Ba ki saba kira a irin wannan lokacin ba shi ya sa nake jin kamar ba ke ba ce”.
“Ni kaina ban san lokacin da na kira ba, kawai ina wasa da wayar na ga kawai hannuna ya kai ga lambarka’.
“Amma kuma kin tava ce min ba ki yi saving ba…”
“Uhum”. Kawai ta yi.
“Lallai na qara matsayi, na ji daxin haka qanwata”.
“Ai da ma kana da matsayi”.
“Ok, yanzu ba ni labari”.
Ta xan yi jim kamar ba ta kan wayar.
*💖💕KYAUTAR ZUCIYA💖💞*