Showing 18001 words to 21000 words out of 34150 words

Chapter 7 - KYAUTAR ZUCIYA Book Complete By Bilkisu H. Muhd.txt

14 Jan 2025

2491

daxa dama wani ni na kasa nishaxantuwa ba”.
Ta miqe yana magana ta yi saurin ficewa a xakin.
Tun daga harabar gidan ta ke faman qwalla mata kira, ba ta ji motsinta ba har ta ratsa sitroom inda ta ga Ammi zaune a kan darduma da alamun sallah ta idar. Ba tare da ta ce komai ba, kodayake matar da ba ta yi sallama ba me za ta iya cewa? Kawao ta bi ta da kallo gurin nema mata shiriya.
A can xaki ta tarar da Nurat tana gyaran littattafanta, ba ta saba ganinta cikin wannan yanayin ba, don haka duk ta gama tsorata. Zama ta yi a kan kujera ta xora qafa xaya kan xaya tana faman haxa su, wannan shi ne alamarta duk lokacin da ranta yake a vace haka ne ya sa Nurat ta qara kiximewa, ba qaramin abu ne yake sanya ta haka ba. gabanta ya shiga bugawa tsawon mintina uku kamar ba za ta yi magana ba, sai faman huci ta ke.
“Ki gaya min ina son sani da wa ki ke yin waya a cikin waya xina?”
Ta ji tambayar ba-zata, tsananin ruxewa ta yi, ji ta yi tamkar numfashinta zai xauke.
“Wayyo Allah”. Ta ce a zuciyarta.
Wata irin tsawa Aazeen ta daka mata.
“ke nake sauraro ki yi min bayani, ko ke kurma ce?”
“Um-um…Aa’, um daman… da man… ba…ba…”
“Wannan wace irin magana ki ke yi haka, munafuka? Za ki buxe baki ko sai na yi miki xankaren duka? Shegiya lumbu-lumbu wutar qaiqayi, da an yi magana Ammi ta ce ke qarama ce, ko ke ustaziyya ce, nan kam ke baqar shaixaniya ce, wallahi in ba ki gaya min gaskiya ba yau sai kin raina kanki”.
Ba ta san sa’adda ta sa kuka ba, cikin shessheka, “Ni ban aikata komai ba, ban yi komai ba”.
“To gaya min yadda aka yi ki ke bin maza a cikin wayata, har kina amfani da sunana ki yi min magana”.
Ta ce cikin xaga murya.
‘Wayyo Allah na shiga uku Yayata kada ki yi mini mummunan fahimta. Kada ki zarge ni, don Allah ba zan aikata ba daidai ba, ki yarda da ni”.
“Idan kina son in rufa miki asiri, ki buxe baki ki gaya min gaskiya, in ba haka ba sai kin gane shayi ruwa ne”.
Hankalin Nurat ya sake tashi, duk lalacewar Aazeen hakan bai sa Nurat ta raina ta ba, Amminsu ta koyar da ita yadda za ta girmamata. Tana tsoron Aazeen ba ta ajiye mata kara ta tsallake, tana matuqar tsoron vacin ranta. Waxannan abubuwa su ke qara dasa wa Aazeen qaunarta, haka ne ya sa ba ta cika takura ta ba, wani fannin tana sane ta ke biye mata su yi ta shirme, duk kuwa da cewar ta bata shekaru takwas.
“Wato soyayya ki ke yi ko? Gaya min me ki ka sani game da so?”
Ta shiga rantse-rantsen cewar ba haka ba ne.
“Ba soyayya ki ke ba, me ki ke yi?”
Gaba xaya ta rasa kalmar da za ta kare kanta da shi.
“Okey, to me ki ke yi?”
“Da gaske nake Yaya, ban san me ki ke nufi ba, ban san me soyayyar ba. Ban tava ganinsa ba, ban san yadda ake yi ba, ki yarda da ni kawai dai na saba da shi ne saboda ke…” Ta qarasa zancen cikin shaqaqqiyar murya mai tattare da tsoro cikin kallon Aazeen xin.
“Okey, wato kina nufin ke ce za ki aurar da ni kenan?”
Ta shiga sintiri, ta koma ta tsaya.
“Oh ni yanzu kin gama zubda min mutunci kenan?”
Ta kai mata hauri da qafa. Jikin Nurat na krayma.
“Ki yi haquri, na tuba ba zan sake ba”.
“Sai kin gaya min ta yadda ki ka sanshi, idan ki ka yi min qarya sai na gaya wa Ammi na ke wadda kullum ke yi miki kallon yarinya mara wayo”.
Ta sake kiximewa, cikin sarqewar murya ta soma magana.
“Na saba da shi ne ta dalilin mistake xin lambar Anisa qawata wadda suka koma Lagos, ta ba ni lambarta shi ne kiran ya shiga wayarsa. Hakan ne ya sa muka saba da shi a dalilin ya ce shi yayanta ne. Na kan kira shi akai-akai ina tambayarsa labarinta, a haka muka saba, sai daga baya ya ce da ni bai ma santa ba. Yana da kirki haka ya sa muka ci gaba da gaisawa…”
“To me ya sa lokacin da ya ce da ke bai santa ba ki ka ci gaba da bibiyarshi? Kuma na duba na ga kaf ke ce kaxai ki ke kiranshi, tabbacin shi talakan talas ne?”
*💖💕KYAUTAR ZUCIYA💖💞*



*NA*




*BILKISU H.MUHAMMAD*
_(Matar Auwalu By fos zage)_










*Free page 11*








*_Wanan littafin na kudine akan 300 kacal in kinsan zaki biya don ki fitarmin dashi Dan Allah ki barmin kayana yar uwa_*




*Ga jerin sunayan litattafai na da zaku samu a kasuwa*


*1. IZZATU*
*2. MULKIN MALLAKA*
*3. KAUNA CE*
*4. DACEWA*
*5. RASHIN RABO*
*6.TARAIRAYA*
*7. JINI BIYU*
*8. AKWAI BAMBANCI*
*9. TSALAR KAUNA*
*10. YA YI SAKE*
*11. ILLAR SABO*
*12. SO DA SANKARA*
*13. RASHIN RABO*
*14. WATA RAYUWA*
*15. HUBBAN SHADIDAN*
*16. BAKIN K'AZAFI*
*17. MATSALAR KAUNA*
*18. KYAN KUSKURE*
*19. WA YAFI SONTA?*
*20. GABA DA SO*




_NOW_
*KYAUTA ZUCIYA*


```Duka wanan litattafan sunanan akasuwa zaku sameso a shagunan sai da litattafai inasha Allah```




*_Wanan littafin na kudi ne, Mai bukata karanta shi zai turo 300 ta wanan account number din_*
*_2277439558 UBA Bank_*
Bilkisu H Muhammad_* *_idan an turo sai a turawa wanan number alter 08031307884 domin tabbatar da an turo din idan kuma VTU za'ayi ita dai number za'ai da ita ko katin MTN na 300 din sai in saki a group paid insha Allah_*




*_____________________________________*


*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*_____________________________________*








*T* a runtse ido ta buxe, wasu zafafan hawaye suka sulalo kan kuncinta.
“Ban san dalilin da ya sa na ci gaba da kiranshi ba, kuma ban sanshi ba, bai tava ganina ba, sau xaya na tura masa da hotonki ta facebook…”
“What? Oh ni! Na shiga uku, ki ce duk kin gama tallata ni, shin Nurat kin gaji da ni? Kin tsane ni ko shi ya sa ki ke son na bar gida ko?”
“Ba haka ba ne, ki yi haquri. Ina sonki, kada ki yi min mummunar fahimta, na tuba”.
‘To bari ki ji, daga yau kada in sake ganin wayata a hannunki”.
Ta yi waje tana faman huci.
Nurat ta kwanta lamo tana maida numfashi, gaba xaya ta dinga jin haushin kanta. Me ya sa ta aikata haka ba ta yi tunani ba? Ba za ta sake ba, ta daina! Daga yau ta tsinke alaqa da Adamu, babu ita babu shi, sai dai a kan kanta ta qaryata kanta, tana ji ba za ta iya ba.
“Dole ma in iya”. Ta faxa a fili, “Ai daman ban sanshi ba, dole ne na cire shi a rayuwarmu”.
Qarfe goma sha biyu da rabi na dare tana faman juye-juye a kan gado, tana faman qasa da warwara, ta miqe zaune ta rafka tagumi.
“Ko da mutuwa aka yi sabo ake wa kuka, na saba da kai sosai, na xauka komai zai zo da sauqi ashe ba haka yake ba? ina ji kamar na rasa abu mai muhimmanci a rayuwa ta, to idan ya daina jina ya zai yi? Na tabbata zai yi kewata, to ya zan yi?”
Ta miqe tsaye zumbur.
“Kai ba zan iya ba, ba zan iya tsinke wannan alaqar ba, duk me hakan ke nufi? Ba kya jin kunya, to inda a ce Yaya Aazeen ta amince haka za ki ji kenan?” Zuciyarta ke raya mata hakan ta cije leve a bayyane kamar wata tavavviya, ta buxi aki, “Ba don ni nake yi ba, babu shi a raina, kawai ina qaunar kasancewarsu da Yayata. Ina jin tausayinsa, na yi masa alqawarin Yayata za ta kasance da shi ko da kuwa me ye zai faru sai na cika wannan alqawarin, ta ya ya?”
Zuciyarta ta tambaye ta, “Yaya Zaruk! Shi ne ya faxo mata a rai, da sauri ta yi waje.
Lokacin da ta isa qofar xakin Ammi sai ta shiga sanxa, a hankali ta buxe qofar. Ta yi sa’a Ammi na xakin Dad, ta hangi wayarta a kan gado. Ta xauka wuf! Ta yi waje kamar mara gaskiya.
A can cikin xaki ta murxa key tare da lalubo lambar Zaruk.
Shi ma Zaruk tunanin Nurat ya hana shi sukuni, ya ji wayarsa na ruri. Waye zai kira shi a irin wannan lokacin? Kamar ba zai xaga wayar ba, ya dai miqa hannu ya xaga.
Lambar Ammi ya gani, cike da mamaki ya kara a kunne. Muryar Nurat ta ratsa kunnensa, ya saki ajiyar zuciya.
“Me ya hana ki bacci?” Kai tsaye ya tambaya.
A gaggauce ta soma faxin, “Yayata ta juyan baya, ta qi amincewa da Adamu, ban san ya zan yi ba”.
“Wayyo Allah”. Ya ce a ransa kamar zai yi kuka.
‘Nurat me ya sa ba za ki mance wannan mutumin bab? Aazeen ba ta rasa komai ba, don me ya sa za ki tsananta? Tunda ta nuna ba ta so ki haqura, muddin kuma ba ke ce ki ke son nasa ba”.
“Yaya Zaruk me ya sa za ka ce haka?”
“A’a to, in ba haka ba, tunda ba ta ra’ayi kurum ki haqura’.
Za ta yi magana ya katse ta.
“Kin ga, in har ba haka ba ne, ki yi min alqawarin za ki fita harkarsa”.
Ta raunana murya.
“Ba zan iya ba, na riga na yi mishi alqawarin zan aure shi…”
“What? Kin san me ki ke cewa? Nurat mutumin nan ko dai aljani ne? za ki aure shi fa ki ka ce?”
“Ina nufin za ta aure shi”.
“Saboda ita xin kaza ce, ko saboda ‘yarki ce, ke ce ki ke da ikon aurar da ita? Me ta tsare miki haka?” Ya faxa cikin xaga murya.
“Haba Yaya Zaruk, in ba ka fahimci ni ba, bana ganin akwai wanda zai iya fahimtata kuma”.
‘Ba zan tava fahimtar taki ba har abada, mahaukaciya kawai. Yanzu ki gaya mini za ki fita a rayuwarsa ko kuwa?”
Ya soma qular da ita, xuf! Ta katse wayar.
Ya yi cilli da wayar yana jin zuciyarsa tamkar ta faso qirjinsa, ga dare ya yi ballantana ya yi wani abu a kai. Tuni ya janyo kwalin taba ya kunna ya shiga zuqa, ya kusan shanye kwali guda ba tare da ya samu wata nutsuwa ba. yana jin tamkar an tsawaita daren, idanuwan nan sun yi jajir ko kaxan bai runtsa ba, kan safe ya yi wani zuru-zuru.
Ita kam Nurat a safiyar tunda sassafe ta shirya tsaf don tafiya makaranta.
Hajiya Rahma da Alhaji Usman zaune suna karyawa ta fito.
“Da wuri haka?” Dad ya tambaya.
“Yau muna da test”.
“Amma dai kin karya ko?”
“Ammi bana jin yunwa”.
Ba ta tsaya sake jin komai ba, za ta fice, Aazeen ta fito ita ma cikin shirinta.
“Bari na sauke ta, ni ma yau fitar wuri zan yi, muna da manyan baqi a ofis”.
A gidan baya Nurat ta zauna, hakan na nufin Nurat xin na fushi da ita ta fara tuqi babu wanda ya kula wani har zuwa get xin makarantar.
Kusan tare suka yi parking da Deedat, bai sauka a kan Vespansa ba ya hangi Nurat na qoqarin fitowa a mota. Gabansa ya yi wani mugun bugawa. Da sauri ya maida ido ga motar don ganin wanda ya kawo ta, duk da bai ganta tartar ba ksancewar gilas xin motar ba mai haske ba ce. Ya shiga tunanin inda ya santa. Vacewa ganinta da ya yi ya sanya ya gaza tuno komai, zai maida kallonsa ga Nurat ita ma ta vace wa ganinsa.
Ina tsantsar qaunarta ina sonta, ita kaxai na tava so a rayuwa ta, ina ji tamkar ba zan iya rayuwa ba tare da ita ba, kafe shi principal ya yi da ido cikin mamaki, har yana ji kamar ba Deedat xinsa ba ne.
Deedat mai kunya da aji ya kan yi haquri a kan abin da yake so, ya danne. Tabbas al’amarin yana girmama, gane abin da yake qauna abu ne mai wahala. Sai ga shi yau ya dubi qwayar idonsa ya furta masa yana son xalibarsa.
Abin da kansa ya haramta, ya dubi Deedat cikin sauke ajiyar zuciya.
“Ina jin komai tamkar cikin mafarki, amma ina zuwa”.
Qarasowa ya yi qofa ya murxa key ya dawo ya zauna.
Deedat ya dube shi, wani irin duba, duban da ya sanya Principal ya sake gaskata abin da bakinsa ke furtawa.
“Xalibarka ta kasa goguwa a zuciyata, ban tava sanin haka soyayya ta ke ba, yarinya ce qarama wadda ba tsarata ba, amma zuciyata ta kasa sukuni da sonta. Ban tava cin karo da abin da nake matuqar qauna ba irinta. Ka gaya min ya zan yi? In ka yi la’akari da waye ni, za ka tabbatar da cewar lalacewa ta zo min, wannan shi ne jarrabawa ta. Allah ya jarrabe ni da abin da ba zan tava samu ba, ita xin…”
“No, kada ka ce haka”. Principal ya yi saurin katse shi.
“Babu mahalukin da za ka so alaqa da shi irin wannan, ya ce zai guje maka ko da kuwa bai sa matsayinka ba, kwarjininka da kalaman da ke shimfixe a fuskarka kaxai zai sa ka samu komai da kowa, ballantana idan aka gane waye kai”.
“Abin da bana so kenan, ina son samun macen da za ta so ni don Allah ba don komai nawa ba. Ina son samun soyayyar gaskiya”.
Principal ya dafa kafaxarsa cikin xan bubbuga shi.
“Da yardar Allah za ka samu abin da ka ke so”.
“Ina zuwa”.
Wayarsa ya xauko ya shiga laluben wata lamba.
“Malam isma’il ka bai wa Nurat littattafan nan ta kawo min yanzu”.
Shi kam Deedat ya maida kai ga wayarsa yana tura saqonni. Bai fahimci abin da principal ke qoqarin yi ba.
“Assalamu alaikum”.
Wani irin bugawa gabansa ya yi, da sauri ya xago kai idanunsu suka gauraya. Ta xauke kai, shi ma komawa ya yi yana satar kallonta. Ta durqusa cikin girmama ta gaishe su. Ta aje littattafan a kan tebur.
“In ji Malam isma’il”.
Miqewa ta yi za ta fita.
“Am.. xan dawo in xan sa ki aiki kafin na dawo, ki duba ki ware min books xin kowane aji a cikin waxanda ki ka kawo da na gurin nan, ina zuwa”
Ya miqe cikin sauri, “Deedat ba ni minti biyar ina zuwa”.
Ba tare d ya jira me Deedat zai ce ba ya yi saurin ficewa.
Ita kam ta duqufa ware littattafai, hakan ne ya ba shi damar qare mata kallo.
“Kina buqatar in taya ki ne?”
Bai san sanda wannan furucin ya kufce a bakinsa ba.
Ta xan xago kai cikin dubansa.
“Na gode na ma kusan gamawa”.
Ya shiga tunanin ta ya ya zai taqalo hira tsakaninsa da ita. Ya nufasa.
“Kafin malam ya kira ki ya ba ni labarin kina da qoqari sosai qanwata”.
Ta yi murmushi.
“Ko ba haka ba ne?”
“Ya dai faxa ne, amma akwai waxanda suka fi ni”.
Ya dinga jin wani irin nishaxi mara isaltuwa.
“Ya sunanki qanwata?”
Ta xan dube shi a kaikaice.
“Sunana qanwata”. Ta faxa cikin murmushihar kumatunta nalotsawa.
“Kin amince ki zamoqanwata?”
“Eh mana ai da ma kai xin Yayana ne”.
“Na gode da wannan matsayin”.
*💖💕KYAUTAR ZUCIYA💖💞*



*NA*




*BILKISU H.MUHAMMAD*
_(Matar Auwalu By fos zage)_










*Free page 12*








*_Wanan littafin na kudine akan 300 kacal in kinsan zaki biya don ki fitarmin dashi Dan Allah ki barmin kayana yar uwa_*




*Ga jerin sunayan litattafai na da zaku samu a kasuwa*


*1. IZZATU*
*2. MULKIN MALLAKA*
*3. KAUNA CE*
*4. DACEWA*
*5. RASHIN RABO*
*6.TARAIRAYA*
*7. JINI BIYU*
*8. AKWAI BAMBANCI*
*9. TSALAR KAUNA*
*10. YA YI SAKE*
*11. ILLAR SABO*
*12. SO DA SANKARA*
*13. RASHIN RABO*
*14. WATA RAYUWA*
*15. HUBBAN SHADIDAN*
*16. BAKIN K'AZAFI*
*17. MATSALAR KAUNA*
*18. KYAN KUSKURE*
*19. WA YAFI SONTA?*
*20. GABA DA SO*




_NOW_
*KYAUTA ZUCIYA*


```Duka wanan litattafan sunanan akasuwa zaku sameso a shagunan sai da litattafai inasha Allah```




*_Wanan littafin na kudi ne, Mai bukata karanta shi zai turo 300 ta wanan account number din_*
*_2277439558 UBA Bank_*
Bilkisu H Muhammad_* *_idan an turo sai a turawa wanan number alter 08031307884 domin tabbatar da an turo din idan kuma VTU za'ayi ita dai number za'ai da ita ko katin MTN na 300 din sai in saki a group paid insha Allah_*




*_____________________________________*


*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*_____________________________________*








*M* amakin yadda ta biye mishi yake yi. Ita xin ma haka ne, tana mamakin yadda ta kasa share shi, yau shi ne karo na farko da ta saki jiki da mutumin da ba ta san waye ba. babu alamun shashanci a tare da shi, ba mutum ne wanda za a iya rainawa ba. yana burge ta da yawa, da alama mutumin kirki ne, kuma ma ai shi xin babba ne, ba za ta iya biris da shi ba.
Miqewa ta yi.
“Ya na ga kin miqe?”
“Na gama”.
“Ai cewa ya yi ki jira shi, ko dai ni ne na cika ki da surutu?”
Murmushi kawai ta yi.
“To bari in jira shi”.
Zamanta ya yi daidai da shigowar Principal, “Kada dai kin gama?”
“Eh tun xazu”.
“Okey sannunki”.
Ta yi saurin nufar qofar ficewa.
“Qanwata babu sallama?”
Tsoro ya kamata, ba ta iya cewa komai ba ta yi saurin ficewa.


*** *** ***
“Haba Malam a kan yarinya qarama ka ke neman lahanta rayuwarka? Tunda na shigo ka ke faman xaxxakar sigari, ba ka san wannan hayaqin matsala ne a lafiyarka ba?”
“Faisal zuciyata ta kasa samun nutsuwa, ina ma zan san inda wannan xan iskan ya ke? Ban tava kisa ba,amma da na soma a kansa. Ya zo ya rusa min komai, wani abin takaici wai ba ta sanshi ba ma, ina ga idan tasanshi?”
“Zaruk sam rayuwa ba za ta yi daidai da ita ba, yarinyar da ta ke ‘yar qauye sam ba ta da wayewa, yarinyar da kwalliya ma ba ta dame ta ba, idan ka ce ita ce za ka aura za ka zamo kullum cikin jin kunya, don ba za ta fidda ka jin kunyar abokai ba, tunda ba ka rigaya ka furta mata ba ka nemi Aazeen ita ce daidai da kai”.
“Kana son ka ce

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login