Showing 9001 words to 12000 words out of 34150 words

Chapter 4 - KYAUTAR ZUCIYA Book Complete By Bilkisu H. Muhd.txt

14 Jan 2025

2489

ba tare da na ganka ba shi ya saka na biyo ka, kuma ai Mom ta san da zuwana, kowa ya san gurinka na taho”.
“Okey su su Mom sun san gaskiya suka take? Ina ganin hakan bai dace ba”.
“Ai su ma sun san abin da ya dace, amincewa da kai da suka yi ne ya sanya su barina na taho”.
“Idan sun amince min ke kuma fa? Shin ba su san ke din fitinanniya ba ce?”
“Yaya Deedat ka san abin da ka ke cewa kuwa?”
Mikewa ya yi zai fita, ta yi saurin shan gabansa.
“Ko ma me ce ce ni ai mijina na yi mawa, aure ne kawai ba a daura ba, akwai baikonka a kaina. A wata ruwayar ma tamkar ka aure ni ne…”
“Shi ya sa ki ke ta bibiya ta? Ai don an yi baiko bai zamo lallai a ce ni ne mijinki ba”.
“Hakan ba zai taba yiwuwa ba. Allah ma ba zai sa haka ba, na sani ina da rayuwa mai tsawo a gaba inda ba kai ne mijina ba, ba zan yi tsawon rai ba. Don kai Allah ya halicce ni, dole ne sai mun yi aure”.
Ta kuma sanyaya murya.
“Ka gaya min me ya sa ba ka damu da ni ba? duk lokacin da na yi maka maganar aure, sai ka nemi kashe min jiki. Zancenka kullum ba ya wuce aure nufin Allah ne, aure lokaci ne. ta bangaren iyaye ma cewa ka ke yi a kara maka lokaci, me ya sa ba ka jin tausayina? Me ye laifina? Ina son ka sani rayuwata ta ginu ne da soyayyarka, ban san me ake nufi da soyayya ba sai a dalilinka. Kai ne nutsuwa ta, idan ba ka son na ci gaba da bibiyarka ka amince a daura aure ko da ba a tare ba, zan iya jiranka zuwa duk lokacin da za ka gama shirinka”.
“Dadina da ke ba kya rabo da shirme. Kin cika shirme. Ba ni da lokacin tsayawa jin wannan maganganun naki, ni ban san me ye so ba, bana son kuma na sanshi. Zan yi aure kawai don cika umarnin Allah da Manzonmu. Ke ma haka nake so ki saka a ranki, sai ki samu sassauci a ranki. Kada ki kara yi min wani zancen so, don ba burge ni za ki yi ba, maimakon haka ma sai matsala da za ki kara ma kanki”.
kokarin barin gurin yake yi, da sauri ta riqe shi kamkam da qarfin da bai san tana da shi ba.
“Nabila, me ki ke nufi da hakan?” Ya fada cikin kausasshiyar murya.
“Yaya Deedat, ni mace ce mai tsananin bukata, na kai kololuwa. Idan ba ka bari an yi auren nan ba, zan iya aikata komai. Ka tausaya min don Allah”.
Da karfi ya watsar da ita gefe ta zube a kan carpet, tana faman maida numfashi.
“Yaya Deedat karya ka ke yi, burga ka ke yi. Na sani kai namiji ne mai girman kai, amma akwai mutanen da suka fi ka girman kai, sai dai ba su nunawa a irin wannan lokacin, ko shi sarki idan aka zo wannan gabar sauke rawaninsa yake yi. Da farko na san ba za ka ce ba ni da kyau ba, na san kuma ina da kirar da duk wani namiji zai so ya mallake ni. Zan fi yarda da cewar sona ne ba ka yi sam! Bana kuma burge ka, to ina son ka sani, idan ba ka bari an yi auren nan cikin wannan lokutan ba zan samu hanyar da zan sama wa kaina mafita, kuma dole ka aure ni, ni ajiyarka ce”.
Ta mike a fusace ta fita.
Ya koma ya zauna a kan gado, maganganunta ne suke dawo masa.
“Ummina, ban yi ma Ummina adalci ba”.
Da sauri ya mike, kokarin ficewa daga gidan ta ke. Da gudu ya cimmata ya damko hannunta ta shiga kiciniyar kwacewa. Tsawar da ya daka mata ne ya sa ta shiga taitayinta.
Bai saki hannunta ba har sai da suka dangana ga falo. Ya zaunar da ita, ya kasa zama sai faman kai-komo yake, ya koma ya dire gwiwoyinsa a gabanta yana son rarrashinta. Tausayinta yake ji musamman yadda idanunta suka tattasa saboda tsabar kuka. Ta ya ma zai iya wanke mata zuciya.
Ya lura Nabila babu abin da ta ke bukata irin tarayya da soyayya, ga shi bai iya ba, ya zai yi da ita? Ya dan cije lebe.
“Oh God! Nabila bana son cutar da rayuwarki shi ya sa nake ta jan lokaci, ke mace ce wadda ba za ki iya rayuwa ba tare da mijinki na nuna miki soyayya ba, ni duk irin wannan abubuwan ban sansu ba. Ban taso a gaban iyayena na ga hakan ba, na taso cikin tsangwama da qyama, Ummina ba ta tare da Babana, ni ban iya ba ban san ya zan yi ba”.
Duk sai ya dinga ba ta tausayi, kalaminsa sun taba mata zuciya, abin da ya tsana dai shi ta yi, ta dora hannunta a kan nashi.
“Yaya Deedat na fahimce ka, ka daina tuno da abubuwan da suka wuce, ni zan iya zama da kai, zan koya maka yadda za ka kula da ni, zan rayu da kai a yadda ka ke. Kada ka damu ni ina sonka”.
“No, Nabila kina buqatar miji jarumi wanda zai dinga kulawa da ke. Na ji mutane na cewa ci da sha ba shi kadai ake bukata cikin rayuwar aure ba. ana bukatar kulawa, kin ga ni kuma ban da isasshen lokaci, asalima ni ba mazauni ba ne yadda al’amuranki suka nuna kin fi son ko da yaushe kina tare da mijinki”.
“Sai dai ko rayuwa da ni ne ba ka son yi, amma ni zan rayu da kai a hakan’.
“No Nabila, akwai abin da ya rage da nake son gaya miki. Amma sai na komo gida, wannan shi ne zai zamo maganarmu ta karshe da ke, idan ki ka amince za a iya yin bikin a duk lokacin da ki ka shirya kin ji?”
“Me ya sa ba za mu yi maganar yanzu ba?”
“Dare ya riga ya yi, ina jin barci saboda gobe da wuri zan fita, ki bari kwana biyar kacal zan yi, ina komawa gida zan gaya miki”.
Washegari da sassafe ya sallame ta bayan sun gama karin kumallo.


ANNUR INTERNATIONAL SCHOOL makaranta ce wadda ke tashe, ta yi ma makarantu da yawa zarra, sam babu ragon Malamai, duk cikin malaman makarantar da yawancinsu a waje suka yi karatunsu, haka yawancin xaliban ciki Deedat na daukar nauyinsu su fita karatu waje, kudin makarantar bai cika tsada ba, sai dai duk da haka masu hannu da shuni suna barin tsadaddun makarantu su kawo su wannan, saboda karatun da ake yi a cikinta. Wannan makaranta sunanta ya kewaye gida da waje, ba wani ne mamallakin Annur International School ba face Ahmad Deedat.
karfe bakwai da rabi Deedat ya isa makarantar kamar yadda Maigadi ya sani, shi din abokin principal ne, gurinsa yake zuwa don haka yana yin parking din Lipan maigadi ya karasa gare shi yana yi masa sannu da zuwa.
“Ai kuwa Principal yanzun nan ya fita, sai dai na san ba nisa ya yi ba”. Maigadi ya fada.
“Okey bari na jira shi”.
“Ko a kawo maka abin zama?”
“A’a kada ka damu”.
Ya koma bakin aikinsa, shi kuma Deedat ya koma gindin wata bishiya ya tsaya yana kallon daliban da ke shigowa. Hankalinsa ya kai ga Nurat wadda ke ta faman sauri hade da waiwaye, abin da ya ja hankalinsa ke nan, ya san duban abin da ta ke waiwaye. Idanunsa suka kai ga wasu samari. Da alama ita suke bi.
“Na gaya maka in dai Nurat ce kun yi kun gama ba ‘yar hannu ba ce. Ita muguwar bagidajiya ce, sam ba ta waye ba saboda gidadanci, ko ‘yar kwalliyar nan ba ta yi”.
“Na ce ku sanya min ido duk gidadancinta sai na wayar da ita, zan ba ku mamaki, ni ne fa, kwana uku kawai za ku ba ni duk abin da ta ke takama da shi sai na sauke mata shi, na yi alkawari sai na sauya mata tunani”.
Gaba daya suka sa shewa.
Ya kasa gaskata abin da iska ya debo wa kunnuwansa. Ras! Ras!! Ya ji gabansa na bugawa, hankalinsa ya yi mugun tashi. Yana son gano yaran sai dai ya kasa tantance su. Tuni suka bace ma ganinsa, daga can nesa ya sake hangensu sun sha gabanta yana kallo ta ja da baya, ta kuma fada wani ajin, su kuma suka dauki wata hanyar.


“Ta ya ya aka samu irin wadannan yaran a cikin makarantar nan? Wannan babban kuskure ne, ba za mu laminci haka ba, duk inda yaran nan suke dole ne a zakulo su, ba za su bata mana sunan makaranta ba. Ba zai yiwu ba, wannan ba abu ne wanda za a bari ya wuce ba”.
Duk yadda suke da Principal, wato Zaid bai iya daga masa kafa ba. hankalin Zaid ya yi matukar tashi.
“Dole ne za mu nemo su, za mu je ajin da yarinyar ta shiga, hakan zai taimaka mu gano su”.
Karfe goma sha daya aka fito break, haka ne ya ba wa Deedat da Principal damar zaga ajujuwan don ganin abubuwan da suke buqatar gyara ko sakewa.
A can aji Nurat na zaune tana nazarin littafinta na English, Faisal Nura da Abdul suka kutso kai cikin ajin. Ba ta yi aune ba ji ta yi kawai an wafce littafin, a tsorace ta dago kai lokacin da ta lura da su ne jikinta ya hau bari.
“Ke ba ki ji ba, magana fa ake yi miki’.
Tamkar ba da ita suke ba, hakan ne ya sa su gaba daya suka katange ta, babu ta inda za ta iya guduwa. Faisal ya sa hannu yana shafar kuncinta, kawai ta naxe hannayenta cikin hijabi ta kuma runtse ido, kwalla suka soma tsinkawa a idanunta.
“Me ye a hannun naki da ki ke boyewa?” Abdul ya fada.
“Ni kuma sai na sumbaci hannun”. In ji Faisal.
“Don Allah ku yi hakuri”.
Hakan bai sa sun fasa kudirinsu ba, Faisal ya kai hannu ya damko hannunta. Ta qwalla ihun kuka, daidai lokacin Principal da Deedat suka kunno kai. Da sauri ya saki hannun, gaba daya suka yi tsuru-tsuru.
Wata uwar tsawa Principal ya daka musu, ta sake rushewa da kuka, Principal ya yi matukar tsorata a yadda ya ga kamannin Deedat sun sauya.
“Ina iyakacin kokarina ban san ta ya ya ake samun irin haka ba. ban taba cin karo da wannan matsalar ba, dole ne ku cancanci hukunci mai tsauri. Sai kun gwammace ba ku taba yin makaranta ba”.
Deedat hankalinsa na ga Nurat, tabbas ita ce yarinyar dazu, duk ya ji tausayinta.
Principal ya kira Displine master a waya, ba a wuce minti biyu ba sai ga shi. Ya umarce shi da ya yi ofis da su ya yi musu horon da ba a taba yi wa wani dalibi ba. daga nan ya sanar da assambly din gaggawa. A nan ma a hukunta su, daga nan a kore su ga iyayensu, kora na har abada.
su faisal sun cika samari amma hakan bai hana su kokawa ba, tare da ban haquri, musamman yadda suka rigaya suka san muguntar Displine master a lafiya ma yana mugunta ballantana wannan ganga-gangan laifin. Yau ne karo na farko da suka taba yin da na sani a irin kura-kuran da suke tafkawa, shi kam deedat duk hakan bai burge shi ba, ya fusata sosai, inda ya danganta laifin ga Principal.
Fuu! Ya yi waje, da sauri ya rufa masa baya cike da zullumi.
Can cikin ofis Deedat ya rikicewa Principal, ta inda yake tuhumarsa. Rantsuwa ya dinga yi yana yi masa magiya da ban hakuri, gaba daya ya gama jikewa sharkaf da gumi.
“Dole ne ka zamo jajirtacce, na tsorata da al’amarin nan, idan ita yarinyar ta sanar wa da iyayenta da me za mu kare kanmu? Wannan sakacin zai iya janyowa a rufe makarantar baki daya, ka sani rufewar ba zai dame ni ba, kamar yadda talakawan da suke mora za su dame ni”.
Cikin muryar lallashi Principal ke fadin, “Zan sanya idanu, hakan ba zai sake faruwa ba”.
Malama Aisha ce ta turo kai, inda ya umarce ta da ta kira Nurat. Shi kam Deedat ya shiga kai-komo, al’amarin ya gigita shi. Shesshekar Nurat ya tabbatar masa da sun karaso.
“Principal me ke faruwa da Nurat haka, na ga yarinyar ta shiga rudani da yawa”.
Principal ya dubi Nurat.
“Ko dai sun yi miki wani abin ne bayan abin da idanunmu suka gane mana?”
Fir! Ta ki magana.
“Ita ya kamata ta jata ta tambaye ta”. Deedat ya fada, kamar ya san halinta, Nurat akwai kunya. Principal ya dan ja ta gefe ya shaida mata abin da ya faru. Malama Aisha ta nufi ofis dinsu da ita, inda ta dinga tambayarta cikin dubara.
Da kyar ta iya budar baki cikin shesshekar kuka.
“Ammina ta ce duk lokacin da na bari namiji ya taba mini hannu, ciki zan samu, in…”
Daidai lokacin Principal da Deedat suka kutso kai cikin ofis din nata. Deedat ya kasa jurewa shi ya sa ya azalzali da a biyo sahu. Ganinsu ya sa Nurat tsuke baki.
“Ke nake saurare Nurat, ba komai ki yi magana kin ji”.
Kawai Nurat ta yi kasa da kanta.
*💖💕KYAUTAR ZUCIYA💖💞*



*NA*




*BILKISU H.MUHAMMAD*
_(Matar Auwalu By fos zage)_










*Free page 7*








*_Wanan littafin na kudine akan 300 kacal in kinsan zaki biya don ki fitarmin dashi Dan Allah ki barmin kayana yar uwa_*




*Ga jerin sunayan litattafai na da zaku samu a kasuwa*


*1. IZZATU*
*2. MULKIN MALLAKA*
*3. KAUNA CE*
*4. DACEWA*
*5. RASHIN RABO*
*6.TARAIRAYA*
*7. JINI BIYU*
*8. AKWAI BAMBANCI*
*9. TSALAR KAUNA*
*10. YA YI SAKE*
*11. ILLAR SABO*
*12. SO DA SANKARA*
*13. RASHIN RABO*
*14. WATA RAYUWA*
*15. HUBBAN SHADIDAN*
*16. BAKIN K'AZAFI*
*17. MATSALAR KAUNA*
*18. KYAN KUSKURE*
*19. WA YAFI SONTA?*
*20. GABA DA SO*




_NOW_
*KYAUTA ZUCIYA*


```Duka wanan litattafan sunanan akasuwa zaku sameso a shagunan sai da litattafai inasha Allah```




*_Wanan littafin na kudi ne, Mai bukata karanta shi zai turo 300 ta wanan account number din_*
*_2277439558 UBA Bank_*
Bilkisu H Muhammad_* *_idan an turo sai a turawa wanan number alter 08031307884 domin tabbatar da an turo din idan kuma VTU za'ayi ita dai number za'ai da ita ko katin MTN na 300 din sai in saki a group paid insha Allah_*




*_____________________________________*


*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*_____________________________________*














*D* eedat ya kasa jurewa shi ya sa ya azalzali da a biyo sahu. Ganinsu ya sa Nurat tsuke baki.
“Ke nake saurare Nurat, ba komai ki yi magana kin ji”.
Kawai Nurat ta yi qasa da kanta.
“Ummi ta ce, duk lokacin da na bari namiji ya tava min hannu zan samu ciki in haifi shege, idan na haifi shege mutuwa za ta yi, kuma su… su… sun tavan hannu…”
Ta qarasa cikin saka gursheqen kuka.
Deedat ya harba cikin tunani, gaba xaya jikinsa ya hau tsuma, wani irin tsoro ya ziyarci zuciyarsa tare da wani irin abu wanda ya kasa tantance ko me ye.
“Amma wannan zancen banza ne ta ya za a xora ki a kan wan…”
Deedat ya yi saurin dakatar da Malama Aisha, “Haka ne, Ammi ta yi gaskiya, ai na ga hannunsu bai tava naki ba sosai, yanzu za mu je asibiti in har da cikin za su gaya mana. Ki daina kuka kin ji ko”.
“Ina jin tsoro, za ta gane hakan ta faru, bana son na samu shege kowa zai tsane ni, bana son samun xan da ba shi da tsarki”.
Ba ya son jin kalamanta, da sauri ya yi waje, idanuwa sun sake rinewa, “Za mu je asibiti”. Ya faxa lokacin da ya bar ofis xin.
A can harabar makarantar Doctor Salim amininsa ya kira inda a taqaice ya ba shi labarin abin da ke faruwa, tare da sanar da shi ga shi nan tafe, yana kuma son a yi mata duk abin da zai sa ta samu nutsuwa. Ya yi saurin katse wayar daidai lokacin da Principal ya yi parking xin mota a gabanshi. A can baya ya hangi Nurat gidan gaba ya shiga, yana gano yadda hawaye suke faman tsinkowa daga idanun Nurat. Ya yi saurin kawar da ido, yayin da gabansa ya dinga dukan uku-uku, yarinya ce qarama, sai dai akwai ta da kwarjini. Lokaci-lokaci ya dinga satar kallonta har suka isa asibitin.
Abin da ya bai wa Nurat mamaki, yadda sunan makarantar da na asibitin suka zamo xaya.
Dr. Samir sun tsara komai da Nurse kafin su qaraso, sirinji ya xauka ya yi umarnin da ta miqo hannunta zai xauki jini domin gwaji. Nan fa idanunta suka yo waje, ji ta ke kamar ta sa gudu, sai ga wasu sababbin hawayen.
Dr. Samir babu wani abin da za a yi, maimakon xaukar jinin?” Deedat ya faxa.
“Dole dai sai dai jinin”.
Babu yadda ta iya haka ta runtse ido, ya shiga shirin zuqo jinin, inda Deedat ya xauko wayarsa a fakaice ya shiga xaukarta ta yadda babu mai lura da abin da yake yi.
Bayan an gama Nurse ta yi wani xaki da jinin, sun zauna sai ga sakamako ta shigo da shi. Ta miqa wa Dr. Salim, ya duba cikin gintse dariya a ciki, saboda yadda ya ga alamun tsoro qarara a idanun Nurat, sai da ya xan yi ‘yan rubuce-rubuce sannan ya sake xago kai cikin dubanta. Idanun nan sun yi luhu-luhu saboda kuka, tana jin kamar ta matsi bakinsa ya yi magana, Deedat kam yana iya jin bugun zuciyarta na tsananta, da yake shi ne a kusa da ita.
“Ina taya ki murna xalibar kirki, ba ki da matsala”.
Cike da farin ciki ta sake wani irin murmushi, dukan kumatunta suka lotsa. Wani irin wushirya mai xaukar hankali suka bayyana. Da sauri Deedat ya shiga xaukarta.
“Doctor na gode”. Ta ce.
Ya miqa mata ambulan, “Doctor na bar maka”.
Ya yi murmushi.
“Ki dai tafi da shi”.
Ta karva.
“Abu na gaba ina son kada wannan maganar ta fita ko a gida kada ki faxa kin ji ko?”
“Insha Allahu babu wanda zai ji”.
Cikin farin xiki ta ke magana.
Deedat ya shiga duniyar tunani, yana tunanin a inda ya san wannan muryar, sai dai duk iya yinsa haka ya haqura.
Sai da Principal ya sanya ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login