Showing 3001 words to 6000 words out of 24634 words
maryata dan ni ba na ta wata Uwani dan yau za mu daki amarci ni da Dududuwalle dan ko amarcin da kansa sai ya yi kukan dole dan ba ƙaramar gurza zan masa ba, kafin dai in je bikon Uwani ta dawo gidan mun mori amarcinmu san kowa ƙin wanda ya rasa. Malam Ashiru ya faɗa yana hango irin yadda zai kwashi ganima
"Taɓ lallai akwai ƙura wai ɗan dako ya hango ayarin udawa"
"Bari in shiga daga cikin tun da na ji matan nan sun daina hayaniya da alama duk sun fice kar fa in bar amarya tana jiran ango "
"Uwaniiiii" Malam Liman ya faɗa cike da tsokana.
"Hahhhh ka ce dai tauraruwa mai wutsiya jinta ba alkairi bane, tun da ni ba ganinta nake ba bare na ce ganinta ba alkairi bane" Cewar Malam Ashiru yana ƙanƙame ledar kazarsa ya shiga dogara sandarsa da ke masa jagora ya bar Malam Liman na ta dariya.
Ya zo dai dai inda zai shiga gida daga gefe almajiransa ne suke zazzaune a kan wani dogon icce wanda suke zauna wa idan an yi ruwa su yi karatu, ƙaran sautin karatunsu ya ji ya ce
"Kai kowa ya karanta ƙulhuwallahu ƙafa uku Allah kaini wajen amarya a sa,a sai kuma kowa ya tafi ya kwanta yau ba ranar karatu bace kar ku hana sabuwar amarya bacci"
Haka suka bi umarnin Malam ɗin bayan sun karanta ya sallame su suka ɗuru a shagunan da suke kwana. Yana fara tafiya suka shiga leƙensa
Binsa da kallo ya suka yi, ganin ya yi gaba yana gyara riƙon ledar kazar kamar wanda za a ƙwace masa. Haka ya shiga zauren gidan ya maƙale ledar a hamatarsa ya tura ƙofar gidan cikin lalume ya garƙama uwar sakata ya janyo wani ƙaton dutse ya ƙara tokare ƙofar ya ce
"Kar tsakar dare kishi ya hana Uwani bacci ta tarki zuwa gidan nan to ahir ɗinki Uwani yau dai da sabuwar amarya zan yi amarci" Ya faɗa yana dogara sandarsa ya shiga gidan bakin nan nasa har kunne.
"Inna kar ki kuskura ko da wasa ki yi magana kin san dai ni ina da baiwar yin kowace murya dan haka ni zan yi muryar Duduwa ke kuma kina daga gefe a matsayin Duduwa" Lami ta faɗa cikin raɗa.
Inna Uwani da ke zaune bakin gado sai ƙamshin madarar turare take ana zaune a bakin gado ta gyaɗa wa Lami kai ganin Malam Ashiru ya taho ɗakin.
"Assalamu alaikum amarya fara mai farar aniya" Malam da ya bankaɗo labulen ɗakin ya faɗa yana wani lashe baki kamar tsohon maye fuskarnan kamar gonar auduga, wata uwar harara da Inna ta doka masa tamkar idanunta za su faɗo ƙasa wani kishi ne ya tsarga mata a take ta tashi a zuciye ta je za ta bangaza shi ya hantsila, da sauri Lami ta je ta shiga tsakani sai sannan Inna ta lura da katoɓarar da kishi ya kusa sanya wa ta yi, da hanzari ta koma ta zauna.
"Wa alaikumus salamu, angona ka sha ƙamshi" Cewar Lami da ta yi murya sak Duduwa wani daɗi ne ya ratsa zuciyar Malam ya sako sandar tasa ya shigo yana ta faman washe bakinsa mai wani uban wawulon da babu haƙori a wurin, Inna kuwa har lokacin tana aika masa saƙon harara.
"Ikon Allah, sannu da zuwa gidan mijinki na alheri na ji daɗi da na kasa zawarawanki a ina zan zauna"
"Ai kai ɗin ne ko laraba wa sai sun sara maka wajen kyau da iya tsara mace, zauna a nan ga kujera nan" Cewar Lami.
Har lokacin bakinsa ya ƙi rufuwa shi kaɗai ya san daɗin da yake ji a ransa ga kaza ga kuma amarya yau sai ya zaɓa ya darje. Hannu ya kai yana laluma kujerar da ke gaban gadon irin ta robar nan, sai da ya dafa ta sannan ya ajiye sandarsa har lokacin ledar kazar tana maƙale a hannunsa. A zuciyarsa kuwa sai haɗiyar yawu yake yi. Inna sai da ta bari ya juya zai zauna ta ɗan matsar da kujerar a hankali ba tare da wani ƙara ba, aikuwa Malam da ya tafi da ƙarfin jiki ya zauna jaɓak a ƙasa ya wutsila ya yi wanwar a tsakar ɗakin, shi a gefe ledar kazar ma a gefe ya ji zafin faɗuwar amma saboda shegen kwaɗayi da sauri ya tashi zaune ya shiga lalumen ledar amma abin ammaki bai taɓo ledar ba, ledar kuwa tana hannun Lami sai da ta ɗauki wata ƙatuwar cinya sannan ta ajiye a ƙasa ta ce
"Wayyo angona sai da na ji faɗuwar nan taka har maƙwallaton zuciyata, ashe baka ƙarasa kan kujarar ba" Ta faɗa cikin muryar tausayi.
Malam kuwa bai samu damar amsawa ba dan burinsa kawai ya ji ya damƙo ledar kazarsa ko hankalinsa zai kwanta, sai da ya ji ya lalimo ledar ya ɗauka da sauri, ya damƙe yana sauke ajiyar zuciya, sannan ya kai ledar wajem hancinsa ya shinshina ya tabbayar da ledar kazar ce sai ya shiga washe baki dan ya wayance tare da ƙoƙarin tashi zaune dan a laluman ledar bai sani ba har rubda ciki ya yi yake tafiya a tsakiyar ɗakin da jan ciki, shi ne cikin wayancewa ya miƙe yana haɗiyar wani miyau da ya taru a bakinsa dan yana ɗaukan ledar ya ji yawunsa ya tsinke, dan bashi da burin da ya wuce ya ji tsokar naman nan a bakinsa dan tsoro yake kar ya falka ya ga ma mafarki yake bai ci ba, ya fi so ko da zai falka daga bacci to ya samu ya ci kazar a mafarkin amma ba ya ma fatan haka ta kasance.
"Malam ya na ga duk ka ruɗe"
"Lah ba komai Duduwata" Ya faɗa yana tashi tsaye riƙe da ledar.
"To dawo bakin gadon kuda da ni ba sai ka hau kan kujearar ba" Lami ta faɗa cikin wayancewa. Tsabar zumuɗi bai ɗauki sandar ba haka ya miƙe dan zalama ledar kazar ce kawai a hannunsa, yana shirin zama a kan gadon a gaban gadon, ya taka wani ɗankunne mai tsinin barima wataƙila ɗaya daga cikin ƴan kawo amarya suka jefar a tashin sani, zafin zugin ɗankunnen da ya gama shigewa cikin ƙafar tasa, sai ya saki ledar kazar ya zame zai zauna yana riƙe da ƙafar ji kake ƙum, ya buga fuskarsa a jikin katakon gadon wanda har ya sa laɓɓan bakinsa suka bugu da jikin katakon tsabar gigicewa. Lami ta yi wa Inna nuni da ta taimaka masa da sauri Inna ta kama shi sai Lami ta zo daga wajen take magana.
"Wayyo sannu, ni dai yau ko dai tsakaninmu da marcinmu aka shiga yanzu a ce tun da ka shigo ɗakin nan kake faɗuwa kamar ginin ƙasar da ya shekara arba'in babu yaɓe"
Malam hannunsa ya janye daga na Inna ya shiga lalume.
"Ina ledar kazar nan kwa Duduwa" Da sauri Lami ta miƙa wa Inna ledar bayan ta ɗauki wata ƙatuwar tsoka ta saka abakinta dan ta ɗazu ma cinye wa ta yi.
"Ga ta nan Malam" Cewar Lami cikin muryar Duduwa ita kuma Inna ta miƙa masa, bayan ta zare masa ɗankunnan daga ƙafar haka dai ya damƙe ledar kazar yana jin zugin laɓɓansa ya tashi ya ƙarasa ya zauna a kan gadon da taimakon Inna, da duk tunaninsa amaryarsa Duduwa ce bai san ba ita tana can cikin buhu a ƙasan gadon ɗakin Inna Uwani.
Zaman da ya yi sai ga shi ya miƙe tsayi da sauri yana yin wurgi da ledar kazar, tsabar ganin yadda ya yi daga Inna har Lami dariya suke kawai marar sauti dan Lami har da kwanciya a ƙasa tana kallon yadda Malam ya yi hajaran majaran shiga aljannar alƙali.
"Wiiii, yiiii wuuuu" Kawai yake yi yana wani sambatu sai zagaya ɗakin yake riƙe da mazaunansa, a haka ya ƙarasa jikin bango ya jingina bayansa yana sakin kuka. Lami dakyar ta tsayar da dariyarta dan har da hawaye ta yi muryar Duduwa ta saki kukan kissa ta ce
"Ni ya zan yi ko dai wani ne ya jefeka, wanda ba ya son ganin mun ci amarcin nan tun da ka shigo ɗakin nan nake ganinka cikin ƙaƙanika yi, kamar ba jarumi ba"
"Yi shiru Duduwalle, wallahi abin ne ya zo mini bagatatan samun biyan kuɗin hajjin kishiya, in banda da'ira cuta bayan rai ya za a yi a samu allura a kan gadon amaryar da ta tare yanzu...
"Allura Malam?"
"Allura ce yanzu hakan tana cikin mazaunaina ta yi luntsum a cikin tsoka"
Inna kawai kwanta wa ta yi a kan gadon tsabar dariyar da ke cinta dan sai da ta rufe bakinta da hannunta dan kar sautin ya fito, saboda furucin Malam sai ya tuna mata da halin da ta shiga ɗazu a tsakanin dangan kara da ƙaya ta shige mata cikin mazaunai, banda Lami ta cire mata da bata san inda za ta saka ranta ba kuma har yanzu wurin ciwo yake dan ɓarin mazaunan nata ma wanda ƙayar ta shiga bata bashi ƙarfi idan tana zaune saboda ba ya zaunuwa, bare kuma shi da allura ƙarfe ce har ta fi ƙaya zafi.
"Bari in taimaka maka" Cewar Lami tana yi wa Inna signa, Inna ta taso daga gadon tana danne dariyarta ganin Malam ɗin sai gaba yake yana baya tamkar mazari, ga hawaye sai fitowa suke daga makancaccan idanunsa. Dakyar ta samu ya juyo mata bayan aikuwa ta saka hannuna cikin wandon a saitin inda allurar take dan dama Lami ce ta soka allurar a wajen dan kar ya zargi komai shi ya sa aka ce ya zauna a kan kujera dan ta san dole zai ce zai dawo kan gadon kusa da ita.
"Wallahi duk kunya nake ji, a ce amarya da ni saukar yanzu tsal ɗin nan a gidanka amma na saka hannu a wandonka ai abin da kunya faɗa da mai gari ranar sallah" Lami ta faɗa da muryar Duduwa.
"Kayya Duduwa ai ana bikin duniya ake na ƙiyama wa ya ce miki ana batun kunya a nan wurin ai ranar biyan buƙata rai ba a bakin komai yake ba, kula ki zara hannun ki cire mini allurar, ke da za a yi mai ɗungurugum ( Mu,amalar auratayya) Mene ne dan kin saka hannu a wandon ango"
Inna tana ɗan danne dariyarta ta taɓa wajen allurar ta danna ta shige duka sai ɗan tsinin da bai gama shigewa ba, hannu ta saka cike da mugunta ta danna allurar ciki aikuwa Malam ya yi wani uban tsalle ya zandama ihu tare da sakin wani marayan kuka ya ƙanƙame Inna, irin yadda yara suke ƙanƙame mutum in ya riƙe su za a musu allura.
"Ai bari ba shegiya bace da ubanta, ai da alheri uwar kishiya ta hau kura" Cewar Inna a zuciyarta.
"Sannu Malam ban san a nan allurar take ba" Cewar Lami da ta lura da abin da Inna ta yi masa. Malam kuwa bai samu damar magana ba sai kai ya gyaɗa kamar ƙadangare haka Inna ta matse gefen mazaunin nasa daga cikin wandon Lami kwa ko ta kansu bata bi ba ta juya musu baya, har sai da Inna ta yi dibarar fito da allurar bayan ta gana masa azabar haushinsa da take ji na kishiyar da ya mata. Hannunsa ta kamo ta zaunar da shi a bakin gadon tana bashi haƙuri a kan wata ƙila ƴan kawo amarya ne wata ta ajiye allurar bata sani ba.
"Duduwa amarya ina ledar kazar nan?" Cewar Malam bayan ya ji shi a zaune. Wata harara Inna ta aika masa tare da ɗakko ledar kazar ta dangwara masa a kan cinyarsa. Aikuwa ko haushin ɗora masa a cinya bai ji ba domin kirarin da ake yi wa amare na amarya bata laifi. Hannunsa har karkarwa yake wajen buɗe ledar ya kai hannu yana ɗan tatttaɓa naman, hannun ya saka a baki ya suɗe aikuwa da sauri ba shiri ya saka harshensa ya shiga lashewa saboda wani raɗaɗin yajin kazar da ya luntuma hannu a kan yajin shi ne ya taɓa bakinsa da ya buge ɗazau dan gabaɗaya bakin ya yi tozo ya kumbura dan Malam ɗin har ya sauya kama.
"Kai ta yaya zan ci naman nan duk burin da na ci a kansa ga shi na ƙare da kumburarren baki, haka kawai baki ya mini zuntuntum sai ka ce tozon raƙumi" Ya faɗa a ransa yana daurewa bai ce komai ba saboda kar amarya ta ɗauke shi ragon namiji dan kar ta cigaba da ɗaukansa kamar ba jarumi ba.
Hannu Inna ta miƙa cikin ledar za ta ɗauki naman dan ita ma yawu ya taru a bakinta dan har ɗisa ma sai da ya yi saboda son ta ji naman a bakinta an daɗe ba haɗu da gasasshiyar kaza ba shekaru aru-aru, wai shekara dubu annabi lada in ji bahaushe. Ai kafin ta ɗauka Malam ya yi saurin dafe mata hannu sai da ya riƙo hannun nata, ya sa hannunsa ya taɓa tafin hannun nata ya ji bata ɗauki naman ba, sai ya ɗauke shi daga kan ledar kazar ya dangana mata hannun da jikinta ya ce
"Haba amarya ai bana son ki yi aiki ki wahalar mini da kan ki"
"Ai ba wahala bace a cin nama ina aiki" Lami ta faɗa Inna kuwa sai harararsa take.
"A hannu zan ke danƙa miki amaryata" Ya faɗa yana ɗan jan ledar gabansa. Wata ƙatuwar tsoka ya ɗakko, Inna kuwa da sauri ta miƙa hannu dan ƙarfin hali kaɗan ya rage ta ce masa ga hannun nawa tun da ba gani yake ba, sai dai idanun nashi a buɗe suke kasancewar makantar daga baya ta same shi, amma kuma tunawa da ta yi cewa Lami ce take maganar Duduwa sai ta yi shiru ta dakata ta ga iya gudun ruwansa.
*JALLI JOGA*
NA
MAMAN AFRAH
FCW
Page5️⃣➡️6️⃣
Sai da ya duƙunƙune tsokar a wuri ɗaya, ya dunƙuleta a hannunsa sannan ya nufi bakinsa da ita amma cikin rashin sa'a naman ya yi girma kasancewar fatar bakin a kumbure take dan yajin jikin naman ma da ya taɓa wajen kumburin da sauri ya janye naman ya lashe wurin yana jan iska dan zafin yajin ya ragu a wajen kumburin. Amma dan ƙarfin hali ɓarawo da sallama haka Malam ya saka ɗaya hannun nasa ya ɗaga laɓɓan dan ya ci alwashin naman nan duka zai tura a baki haka ya danna tsokar nan ta cika bakin ga kumburin leɓan sai bakin ya koma kamar shantu, ya yi wani zototo, Malam na kiciniya da wajen wawulonsa da babu haƙori wajen tauna naman wani uban raɗaɗin zafin yajin da ya shiga kumburin ashe ya ɗan fashe wajen wani zabura da ya yi babu shiri ya tofo naman yana damƙe wa a hannunsa na hagu. Kallon kallo aka shiga tsakanin Inna da Lami ganin Malam yana tanɗar baki a take suka fara dariya marar sauti.
Kafin ya gama jin raɗaɗin yajin Inna ta yi saɗaf-saɗaf ta ɗakko haƙarƙari ta yaga a bakinta ta miƙa wa Lami sauran.
"Amarya ungo nan ni wannan laɓɓan nawa ba zasu barni in ci da daɗin rai ba sai dai ko in ke ci da gutsure-gutsure" Ya faɗa kamar ya yi kuka, ya miƙa wa Inna wani da ya ɗakko ɗin yana cewa
"Ai soyayya ruwan zuma buɗe bakin in baki" Ya faɗa yana miƙa hannu ya shafo bakin Inna sannan ya miƙa naman Inna kuwa ta buɗe bakin ya saka mata aikuwa cikin mugunta ta haɗa da yatsunsa guda biyu ta gantsara masa cizo ai da sauri ya warce hannunsa yana danne zafin cizon da ta kafa masa haƙoranta masu tsini dan kar ta ga ragwantarsa.
"Malam ɗina cizon so ne fa na maka, ina sonka" Lami ta faɗa da muryar Duduwa.
"Aikuwa na tsinci shi har cikin zuciyata ni ma ina sonki Dududuwa" Malam ya faɗa kamar zai yi kuja amma ya, ya iya da abin da ya fi ƙarfinsa ai dama faɗan da ya fi ƙarfinka maida shi wasa dan babu yadda zai yi amma tabbas ya sha azaba a cizon, wuri uku kenan suke masa raɗaɗi, mazaunansa, inda allura ta shige masa, bakinsa inda ya kumbura ga kuma yatsunsa biyu da yake jin dafin haƙorin amarya a jiki, dan ƙafarsa bata masa ciwo inda ya taka ɗankunne.
Inna tana gama taune nama da ta haɗiye, ido Lami ta ƙifta mata dan dama komai a shirye suka yi, dan haka Inna ta miƙa hannu ta maƙalo wuyan Malam da hannu biyu, Malam jin hannun amarya a wuyansa dai ya ɗauka
soyayya ce za a nuna masa dan haka bai san lokacin da ya manta da duka ciwukan da suke damunsa ba wani irin washe baki ya yi dan ya san an zo kan gaɓa wato cin amarci, don a ganinsa tun da kaza ya ƙi ciyiwa da daɗi rai ai gwara ya ci amarcin kar ya yi biyu babu. Dan haka cikin zumuɗi ya saki naman hannunsa wanda ya saka a baki ya fiddo ya damƙe a hannun hagu amma duk da ya shirya kwasar ganima da romon so da ƙauna hakan bai sa ya manta da ledar kazar amarci ba hannu ya sanya ya janyota aikuwa Inna ta saka hannu ɗaya za ta ɗauke ledar hannun nata ɗaya kuma yana wuyan nasa. Janyewa ya yi ba tare da ya ce komai ba ita ma ta ƙyaleshi ta mayar da hannun wuyan nasa.
"Ina sonki Duduwalleta, duk duniya babu macen da ta kaiki, sauran duk muna mata ne ke kaɗai ce mace sabo...
Kafin ya kai ƙarshen maganar Inna ta fara ƙoƙarin aiwatar da abin da za ta masa dan kirarin da ya yi wa Duduwa wani haushi da kishi ya turnuƙeta hakan ya sa bata yi wata-wata ba ta miƙa bakinta kan bakin Malam. Shi kuwa gogan tunaninsa kiss za a masa na soyayya dan haka a ransa yake raya cewa an zo wajen. Bai zata ba bai tsammata ba sai ji ya yi Inna ta haɗe kumburarrun laɓɓansa ta damƙe