Showing 24001 words to 24634 words out of 24634 words

Chapter 9 - JALLI JOGA FREE Book Complete by Maman Afra .txt

23 Jan 2025

3837

ita da Inna suka rufe ɗaki suka shiga watandar kazar amarya Duduwa suna ci suna santi Inna na saka wa Lami albarka.


Bayan ya sallame sallar ko azkar bai yi ba bare addu'a ya kai hannunsa ya taɓo ledar da tunaninsa ta kazar ce jin ɗumin rogon sai ya sauke wata nannauyar ajiyar zuciya dan shi ko addu,a ma ba zai tsaya yi ba burinsa bai wuce ya kai kazar nan ya damƙata a hannun amaryar Duduwa ba ya huta da fargaba da kuma masifarta. Ƙafarsa ya since daga jikin tazugen ya since ledar rogon ma da tunninsa kaza ce ya ajiye tazugen ya ɗauki ledar ya lalumi sandarsa ya fito yana wani washe baki kamar gonar auduga cikin sanɗa ya shigo tsakar gidan gudun kar Inna ta ji shigowarsa ta fito ta masa zancen ƴan tsakin da ya aika mata aikuwa cikin nasara ya samu ya shige ɗakin Duduwa da ko sallama bai yi ba gudun kar a jiyo muryarsa sai da ya shiga tsakar ɗakin sannan ya buɗe murya har da wani zaƙaƙa muryar shi ala dole ya shigo da ledar kaza. Duduwa ganin shi da baƙar leda kuma yana washe baki sannan ko a sallamarsa ta lura da ƙwarin gwiwarsa ya shigo sai ta ji wani irin daɗi ua ratsata tare da dabaibayeta dan hakan yana nuni tare da tabbtar mata yau akwai asuwaki da gasasshiyar kaza.




Malam tashi ya yi yana rawar ƙafa ya je ya bankawa ƙofar gida sakata ya dawo yana zuwa lokacin an fara kiran sallar ishsha'i sai kawai suka yi sallar tare da amaryarsa. Bayan sun idar da sallah Duduwa har da rungume Malam tana jin daɗi a ranta dan ya gama mata komai kuma ya fitar da ita kunya da gorin jama'a. Shi kwa gogan sai wani washe baki yake Duduwa tashi ta yi ta je ta banka ƙofar ɗaki da ƙarfi dan Inna ta jiyo haushi ya hanata bacci dan ta san amarci za su ɓarza ita da Malam ga gasasshiyar kaza a gefe.


Bayan ta dawo ta ɗakko sabon plate daga cikin loka ta kawo ta ajiye.


"Baka ji ba ji nake kamar in goya ka in zaga garin nan da kai dan daɗi" Ta faɗa tana ƴar dariyarsu ta masoya.


*INNA*


Tatas suka cinye kazar suka sha ruwa abinsu tate da yi wa Allah godiya.


"Taɓ Inna wallahi har hangowa nake irin badaƙalar da za a sha da Malam da Duduwa matuƙar ta ga rogo ne a ledar nan akwai badaƙala! Dan sai ta kusa murɗewa Malam kai kina ji fa dan ƙarfin hali har ƙofa suka rufe wato mu an haɗa su da jariran ƴan tsaki ai dama haka ne" Lami ta faɗa tana dariya.


"Ai na san halin Duduwa babu sauƙi sai an yi yaƙin duniya na uku a gidan nan idan ta gano haka" Inna ma ta faɗa tana dariyar.


*Duduwa*


Tun da ta kawo masa farantin take haɗiyar yawu dan yau Allah ne kaɗai ya san irin cin ƙetar da za ta yi wa kazar nan saboda an daɗe ba a haɗu ba.


"Taɓa kai da ba gani kake ba ai sai yadda hali ya yi dan lallaɓawa zan ke ina sunkutar narkekiyar tsoka in barka da ƙasusuwa" Ta faɗa a ranta tana dariyar ƙeta a zuciyarta dan har ta hango yadda wasan zai kaya domin kuwa mai kaza ne zai tashi da kai da ƙafa.


"Kam bala'iiiii Ashiruuuu wannan gardin fa da ka juye a faranti wace shegiyar ce za ta ci?" Cewar Duduwa tana zaro idanu ganin Malam ya ɗaga baƙar ledar ya juye a farantin ta yi ido huɗu da dafaffan rogo mai gari sai tururi yake.
A nan na kawo ƙarshen free pages wanda yake buƙatar cigaban har ƙarshe ya tuntuɓe ni a whatsapp ta wannn number 09013181851

7
8
9

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login