Showing 18001 words to 21000 words out of 24634 words

Chapter 7 - JALLI JOGA FREE Book Complete by Maman Afra .txt

23 Jan 2025

3835

Matar da aka saka ita ce bata kome sai miji ya ce ya mayar da ita matar da ta yi yaji kwa har yanzu akwai dama a hannunta Inna, ke ce uwata ke ce ubana, mahaifina ya rasu tun kan in zo duniya, mahaifiyata ta mutu a wajen haihuwa ta wacce ta zame miki tilo da kika haifa a duniya, ke ce komai nawa ba kya bari na yi baƙinciki kuma ban san mene ne maraici ba dan haka ni ma sai inda ƙarfina ya ƙare wajen ganin farincikin ki".




"Yanzu ya za a yi wajen komawar kenan? Kin san dai Yaya ba zai bari in koma ba in dai ba a zo biko ba bare ma dama shi haushina yake ji da na taho ya fi so ma in zauna a gidan ko na gane shayi ruwa ne, ni kuma saboda kar Duduwa take firirita cewar ina gida na bar mata mijin shi sa nake son na koma"


"Wannan duk ba komai bane Inna ki bar komai a hannuna, kin manta yau ne lahdi Kaka Lado zai yi tafiya garin nan mai nisa gaisuwar Babar abokinsa kuma ya ce kwana biyu zai yi saboda sai an kwana a hanya, to idan ya tafi za yi komai"


"Tabbas an yi haka yau ne zai tafi ni ai na manta kwata-kwata Allah miki albarka Lamisa ya jiƙan gyatumarki da tsohonki"


"Amin Inna"


"Yo da banda abin Yaya a ce wai dan ka tsufa ka kwashe shekaru aru-aru a gidan aure wai baka yi yaji ba sai yake kiran wani tsofai-tsofai da ni sao ka ce wata jakar zabira"


Dariya suka saka daga ita har Lamin dan Inna har ta ji saƙayau jin za ta koma ta san kuwa sai yadda hali ya yi.


Wajen ƙarfe tara Yaya Lado ya musu sallama ya tafi suka masa fatan sauka lafiya duk da shi ma ba wata lafiyar kirki ce da shi ba gashi kuma jikin tsufa dan dama su kaɗai iyayensu suka haifa shi da Inna yanzu kuma sun daɗe da rasuwa. Yaya Lado na tafiya Lami ta fasa asusunta ko Inna bata faɗa wa ba, haka ta tafi kasuwar garinsu ta siyo robar ɗaure-ɗaure mai uban yawa tare da tsakiya (beat) Sai dogayen wanduna kala huɗu da wasu body hug guda biyu, sai wani kamfacecen kambas irin na ƴan ball second hand ta siyo da wata damɓareriyar sarƙa da ɗankunne.




Wata doguwar rigar buba ta leshi irin gwajon nan na Lagos ta siyo mai fankaɗeɗan ɗankwali. Daga nan gidan su tsigi-tsila mai kitso ta wuce ta je ta tarar tana yi wa wata kitso bata gama mata ba amma jin Lami ta ce za ta biya ta kuɗi masu tsoka ya sa tsigi-tsila ta saka wa matar kai ta biyo Lami.


Suna zuwa Lami ta jibgewa tsigi-tsila robar ɗaure-ɗauren ta ce ta yi wa Inna ɗaure-ɗaure na ɗiban magana haka Inna ta washe baki tana murna tun da take ma ba a taɓa mata ɗaure-ɗaure ba ko da tana budurwa ma amma saboda ta turawa Duduwa haushi ta yarda tsigi-tsila ta kama kan nan ta fara tamke mata shi kaar yadda Lami ta nuna wai tsawon ƙarin gashin da za a yi sai ya zo gadon baya kamar gashin ƴan indiya. Sai da aka jibgewa Inna robar nan a kanta yaraf-yaraf kamar wata ƴar bori, aka zo aka bi ɗaure-ɗauren da beat (Tsakiya) Sai da aka gama tsaf aka sharɓa mata wata uwar fulawar baƙin lalle kamar an goga dayis duk ta kwaɓe amma Inna kamar an tsomata a aljanna sai faman sheƙawa Lami da tsigi-tsila albarka take dan ta kira ɗaure-ɗauren nata da fulawar da suna da Duduwa tagumi.


Da la'asar lis ayarin ƴan mata da masu waƙe wanda suke yi in za a kai marya da Lami ta gayyato su suka yi wa gidan Yaya Lado tsinke.




Inna tana ɗaki ta sha wanka an kyankyatsa leshi wuyan nan sanye da damfareriyar sarka sai walwali take kan nan da ya sha ɗaure-ɗaure da ƙarin roba yaraf-yaraf sai bin bayanta yake banda wanda aka yi wo shi ya yi gaba tsawonsa har wajen cibiyarta ko idanunta sai ta janye robar take ganin mutane. Kambas ɗin nan an ɗaure maɗautin taminjau ga wata uwar jagira da Lami ta gyara mata ɗaurin ɗankwalin aka yi shi wani gwaggwaro haka Lami ta sinyo jakin Yaya Lado daga jigon da ake ɗaure shi Inna ta hau aka ɗora kullin kayan Inna a gaba wasu kayan kuma wasu suka ɗauka. Tunda suka fito mawaƙiyar take waƙa sauran ƴan matan suna amshi, haka suka keto ta cikin garin kowa yana kallon ikon Allah abin da ba a taɓa yi ba a garin dan sun sa budurwa ake ɗorawa a doki a kaita gidan miji amma bazawara ko ƙaramar bazawara ce inda ta taɓa aure to ta girmi zuwa gidan miji a doki amma sai ga shi tsohuwa tukuf har da furfura an ɗakkota a kan jaki kuma ma ba wai sabon aure ba komen yaji, yajin ma da ba a je biko ba har da masu waƙar amarya da kuma masu amshi bugu da ƙari ma kitson kanta kaɗai ma abin kallo ne. Mata da yara sai turuwar fitowa suke suna kallon ikon Allah, wata bazawara da Lami ta gayyato ta ita kuma daga an yi tafiya ɗaya biyu sai ta carara wata uwar guɗa.


A haka suka yi wa gidan Malam Ashiru tsinke. Malam da Duduwa da ke tsaye a ƙofar ɗaki yana so ya shiga amma ta hana shi dan ta ce idan jar babu kaza ko inda take kar ya kuskura ya tunkaro shi kuma ya je ya buga ya buga amma bai samo ko rancen biyar ba. Ana cikin wannan dambarwar suka fara jiyo waƙa da guɗa sun doso cikin gidan gabaɗaya saranda suka yi kowanensu yana so ya tabbatar da abin da kunnesa yake ji yo wa jin dai gidan aka doso sai suka fara tunanin ko dai ƴan kai amaya ne suka yi ɓatan kai.


"Iye shama arayye, shama ayye ruwa lilo iyeee ayye shama ayye ruwa lilo shama arayye"


"Iye kece amarya, ko wacce jani talau bayanki take iyee ayye shama ayye ruwa lilo shama arayye" Wannan waƙar ita ce wacce aka shigo ana faman yi ga guɗa tamkar mai guɗar za ta tsinke hancinta. Inna kuwa da ke daman jaki da ƙullin kayanta sai langi take irin na ƴan mata da suke yi a kan doki, idan ta yi girgiza sai ta tafi da baya kamar za ta kwanta sai ta yi langi a haka aka shigo da ita cikin gidan. Galala Duduwa ta saki baki tana kallon abin mamakin da ya kusa kasheta a tsaye dan mutuwar tsaye ta yi.




"Mai nake ji ne haka a gidan nan, Duduwa ba kya faɗa musu ba sun yi ɓatan kai nan ba gidan da za su kawo amaryar bane?"


"Yo wane irin ba gidan bane Malam tayani gani wai makaho ya so gulma"


"Wato makaho ne marar galihu da za a ce ya so gulma ba dole ya ce a taya shi gani ba tun da bashi da idon ganin, kuma da kike cewa in tayaki gani da wane idon zan gani"


"Malam Uwani ce fa ake yi wa wannan waƙen da guɗa tana saman jakin Yayanta Lado"


"Uwani kuma a saman jaki?"

Ai tsabar mamaki ma Duduwa ta kasa magana binsu kawai take da kallo babu abin da ya fi tafiya da hankalinta irin lashin jikin Inna da kuma ɗaure-ɗauren robar da ta ga ya mayar da Innar tamkar wata tauraruwa ga wata damfareriyar sarƙa ita gabaɗaya kayan jikin Innar ma bata san su ba duk iya ƙawancensu bata santa ba da su. Ganin kambas ɗin ƙafar Inna da zanen fulawar hannunta sai ta ji tamkar ta kurma ihu ko ita amaryar jiya bata yi wannan kyan ba, hannu ta kai da sauri ta shafo gashi gaban goshinta da bai taka kara ya karya ba da aka mata zanen hausa aka saka tsakiya dan duk a turawa Inna haushi sai ga shi ita an mata ɗan yayi wanda tsawonsa ya kai cibiyarta daga baya kuwa har gadon baya.


*JALLI JOGA*


NA

MAMAN AFRAH


FCW
Page 1️⃣7️⃣➡️1️⃣8️⃣



Ƴan kawo Uwani kuwa sashen Inna suka nufa, dan tamkar basu san da halittar Malam da Duduwa a cikin gidan ba haka suka watsa yinsu. Suna dab da shiga sashen na Inna Lami ta saka hannu ta gyarawa Inna robar da ta kwanta a gadon bayanta tamkar ƙadangare ya samu bango, har wani ƙara bazasu Lami ta yi ai hakan da ta yi sai Duduwa ta ji kamar ta haɗiyi zuciya ta mutu saboda ta tabbatar idan Malam ya kai hannunsa ya taɓa ɗaure-ɗauren nan sunanta soriye. Idanunta kafe a kanu har suka shige Inna kuwa har wani daɗa gyaran zaman rigar leshin nata take. Suna shigewa kewayen Inna Duduwa da ta saki wani kuka mai kama da na jakin dawa ra zube zaune a ƙasan ta yi zaman ƴan bori.


"Ni dama dan a ci mini mutunci aka auroni ko kazar amarci ba a siya mini ba son a jawo mini gori a gari" Wannan kalaman nata su suka dawo da Malam daga duniyar tunanin da ya lula dan shi gabaɗaya dawowar Inna ɗaga masa hankali ya yi tun da dai ya san ita ma yanzu sai ta ce sai ya basu kaza ita da jikarta dan ya san halinsu hatta Lami ya san taƙidarancinta sai dai sun sa shi a tsakiya bai ma san ya zai yi ba da wannan rikicin. Jin maganar Duduwa sai hankalinsa ya ƙara tashi dan ya san dai ko ƙuli-ƙulin kubura za a yi da shi ba san inda zai samu wata kaza ba gasasshiya ba.


"Mamaye luba ayya mamaye luba waya-waya. Mun kawo amaryarmu, mun kawota da langinta ta sha kwalliyar gashi waya-waya. Mun kawo amaryarmu mun ajiye ta a can ɗaki kai ango ka nemo kazar amaryar, mun fa faɗa da waƙenmu dan ma kar ka haɗa ta da jani talau wacce ko ƙafar kaza bata gani ba" Haka ƴan matan da suka rako Inna suke faɗa da waƙe dan Lami bayan ta sallamesu ta faɗa musu idan za su fita su fita da waƙar nan. Haka suka fice suna maimaitawa har wani ɗaga muryar suke ganin Duduwa ta yi zaman ƴan bori a cikin ƙasa har da masu mata dariya da gwalo dan kowa ya san auren cin amana ta yi dan kaf garin babu wanda bai san amintakarsu da Inna ba.




Suna fita ta saki wani marayan kukan da ya san hantar cikin Malam hautsinawa dan shi tun ba a zo mawar gumurzun ba har ya shiga tsoron abubuwan da ka iya zuwa su zo dan ya san dai tabbas akwai badaƙala.


"Wayyo shikenan an sani a bakin duniya, ashe kowa ma ya san ba a kawo mini kaza ba tun da ƴan waƙe suka fara waƙa da ni na san tuni zance zai bazama a gari shikenan ake nuna ni idan na fita wataran ma fitar ta gagareni" Ta faɗa tana kuka. Malam jin kukan nata yana ƙaruww sai ya fara matsawa kuda da ita dan ya bata baki dan idan ba bakin ba, ba ya jin akwai yadda zaa yi kazar nan ta samu. Lalume ya fara yana son ya taɓo ta Duduwa da ta zare idanu tana aikawa Malam wata harara ganin yana lalumenta aikuwa bata aikara ba sai jin yatsunsa ta yi luntsun a cikin idanunta dan shi har ga Allah so yake ya taɓo ta kuma da yake ba gani yake ba bai ma san ina yake shirin kai hannun ba sai da ya shi ta zunduma wani uban ihu tana kiran wayyo ya tsole mini ido zai nakasta mini idona mu zama ɗaya da shi" Sai sannan Malam ɗin ya farga da abinda ya yi.


"Ashsha Duduwa ba da sani na yi ba"


"Yo dama ina za ka sani kana baƙinciki ni ina gani kai baka gani shi ne ka sarƙama mini wannan kantoman hannun naka mai farata kamar na muzuru"


Ɗiiff Malam ya yi ya san dai duk tana abubuwan nan ne saboda ka shi kuwa sai dai in tsirensa za ta yi amma bashi da kaza bashi da dalilinta.


Inna da ke tsaye a kewayanta tana kallon duk abinda ke faruwa dariyar ƙeta kawai take har da riƙe ciki dan sosai suka mata kama da ƴan film ɗin Hausa. Lami da ke ta faman share ɗakin Innar ta ɗagawa Inna hannu alamar ya ake ciki. A hankali Innar ta faɗa mata tana zuwa bata gama ganin diramar ba.


Bayan Lami ta kammala gyaran ɗakin ta dawo suka haɗu da Inna suna leƙen su Malam lokacin Duduwa ta fito daga ɗakinta ɗauke da wani ƙullin himilin kaya wai tafiya gida za ta yi yaji a kan kazar amarci. Malam da ke riƙe gagam da mayafin Duduwa yana haɗa ta da Allah a kan ta yi haƙuri kar ta tafi yaji tana amaryar daren jiya. Banza ta masa tana cigaba da tafiya riƙe mayafin da ya yi ƙaƙam kuma da yake ta fishi ƙiba shi kuma ɗan tsololo ne tana cigaba da tafiya sai gashi ƙiiii tana jansa dan ta rinjayeshi amma dan ƙarfin hali ya ƙi ya sakata saboda ya san muddin ta kufce masa ba lallai ya kamata ba bare ya hanata tafiya tun da ba gani yake ba. Ko da a ce laɓewa ta yi a wajen haka zai wuce ya barta tun da makaho ne. Tun daga ƙofar ɗakinta take janyo shi dan gabaɗaya ma ya janye mata mayafin sai kaɗan ne a kafaɗarta wanda ta dafe da hannu. Malam sai gashi wacakar a ƙasa riƙe da mayafin aikuwa Duduwa ko ta kansa bata bi ba ta cigaba da tafiya haka take jansa ƙasa suna zuwa ƙarshen tudun barandar ƙofar ɗakin nata aikuwa Malam ya ci da ka, dan bai ma san ina suke ba duk ya rikice mayafinkwa yana riƙe a hannunsa ya ƙi saka wa dan ƙarfin hali ya riƙe ƙamƙam da hannu biyu tamkar wanda aka ce za a ƙwace masa sai faman haki yake tamkar wanda ya yi tseran gudu.




Yana tuntsurowa daga tudun barandar Duduwa ta dage iya ƙarfinta ta fisgi mayafinta aikuwa ya ƙara wuntsilawa ya ci da ka dan ita ko tausayinsa bata ji tun da tana ganin ya zubar mata da kima bai kawo mata kazar amarci ba tun da ga shi har maganar ta fita idan bashi ya faɗa ba wa ya saa ba a kawo kaza ba. Su Inna kuwa dariya har da hawaye dan su ma ko tausayin Malam ɗin basu ji ba dan dama duk tsuntsun da ya ja ruwa shi ruwa kan duka. Itama kuma Duduwar son banza ya sa ta aureshi dama kuma duk wanda ya ce zai hau motar kwaɗayi to kuwa a tashar wulaƙanci za ta sauke shi. Yana wuntsila wa cikin ƙarfin hali ya miƙe zinbet kamar ba shi ya niƙu da ƙasa ba ya hantsila. Raruma ya shiga kaiwa wajen dan burinsa kawai ya wawuro Duduwa ya hanata tafiya tana ƙoƙari shiga zauren fita daga gidan kuwa cikin ikon Allah ya ki mata cafka ya kamata, hannu biyu ya sa ya ruƙumƙumeta dan dan ko ana ha maza ha mata ba zai saka ta ba. Ƙiiii take jansa ƙafafun nan nasa suna tuzuwa a cikin ƙasa da yake zauren ruwa ba ya shiga akwai rairayi a ciki ƙafafun nan nasa suka yi butu-butu a cikin ƙasa tamkar wanda ya je ya wuni aikin siminti.


"Malam sakani"


"Haba Duduwa ya za a yi in saka ki, ki tafi ki tona mini asiri"


"Yo ba gwara in tona maka asirin ba ashe ba daɗi ni kuma ka tona mini"


"Ki mini afuwa yanzu zan fita na miki alaƙawarin da kaza zan dawo miki gidan nan duk runtsi duk wuya" Ya faɗa har lokacin yana riƙe da tsantsarta da ya yi wa kamun kazar kuka dan babu wanda zai sa shi ya barta ta tafi ko mai za a yi.




Haka ya lallaɓata ta yarda za ta koma amma da sharaɗin matsawar bai kawo kaza ba komin dare za ta tafi. Haka ta dawo da ƙullin kayanta duk abinda suka tattauna a kunnen Lami dan suna shiga zauren ta lallaɓo ta zo ta laɓe suna shirin fitowa kuwa fa koma kewayen Inna ta zayyane mata komai.


"Gashin yau nake so ba na son kwananniya, mai ɗumi wacce bara ƙone ba wajen gashin?" Ta faɗa lokacin da Malam ya tashi tsaye riƙe da hularsa yana daidaita ta.


"Yo ban da zaƙiya ko moshe kika samu ma in kawo mana amma har wani zaɓe kike" Ya faɗa a zuciyarsa a fili kuma ya ce


"Ayya amarya bakya laifi wa ya isa ya baki kwananniyar kaza ai ƙaryarsa ta sha ƙarya" Wani irin washe baki ta yi jin ana koɗata haka ta rako shi ƙofar ɗaki ta koma ciki.


Tahowa ya yi yana dogara sanda ransa in ya yi dubu ya ɓaci dan ya san ruwan dafa kansa ya ɗakko in dii ba wajen masu gashin zai je ya sato ba ina zai samu kuɗin siyan kaza a wannan halin da ake ciki na...


"Malam" Cewar Lami da ta zo wajen ta katse masa tunanin da yake idanunta kafe a kan hularsa da ya saka ta a baibai, kuma bayan a baibai ya saka hallaw ta kalli arewa maso gabas kallo ɗaya za ka masa sai ka yi da gaske in dariya bata ƙwace maka ba.


"Na'am Lami" Ya faɗa yana sakin murmushin yaƙe gabansa na wani irin bugawa dan ya san Lami tauraruwa ce mai wutsiya ganinta ba alkairi bane.


"Inna ce ta ce tana maka magana"


"Ƙulululuuuuuu" Cikin Malam ya bada wani sauti dan shi mugun jin nauyin Inna yake ji saboda auren cin amanar da ya yi da aminiyarta ga shi ta tafi yaji sati uku amma bai je biko ba ta dawo da kanta bai je ɗakin ba gudun kar ya ɓatawa amarya rai sai kuma gashi yanzu ta aiko masa saƙon

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login