Showing 21001 words to 24000 words out of 24634 words
kira.
"To, to, to Lamisa shalelen Innarta" Ya faɗa yana daddogara sandarsa ya nufi hanyar kewayen Innar.
"Salama alekum, uwar gida ran gida, uwar gida shalele an buga an barki gaba salamu baya salamun barka da dawowa ta hannun damar Malam kowacce mace bayan Uwani take bi" Ya kai ƙarshen kirarin nasa yana wani jinjina hannu.
"Shege sama wai kura ta hangi biri, lallai namiji barkono ne sai an tauna za a san yajinsa, a gabana fa jiya kake yabon amaryarka kana kusheni baka san da ni kake tare ba amma kuma yanzu ka zo kana yabona kana cewa ni ce sama da kowace mace lallai Ashirulle ka zama munafikin mata" Inna ta faɗa a zuciyarta a fili kuma sai ta ce
"Wayyo Malam na ji daɗin kirarin nan naka Allah barmu tare" Ta faɗa tana danne zuciyarta dan haushinsa take ji amma kuma ba za ta ba wa marar ɗa kunya ba
"Ai matsayinki ya kai dole a yaba miki" Ya faɗa yana washe baki.
"To godiya nake, na ce kuma sai ka ji dawowata banbarakwai"
"Kai Uwaniyo ke da gidanki wane irin banbarakwai kuma ai kin birgeni har da su guɗa da waƙe irin na yaran amare kika dawo a kan jaki abin ya birgeni"
"Ai sai ka ji yadda na sha gyara ma taɓa kaina ka ji" Inna ta kama hannun Malam ta ɗora a gadon bayanta ɗaya hannun nasa kuma ta ɗora daga gaban goshinta inda robar ta zuba yaraf-yaraf.
"Uwani waiiiii wai-wai-wai in ji ciroki, wai Uwanin ce ko kuma indiya na je ziyara" Ya faɗa yana taƙarƙarewa yana ta murza robar har neman wareta yake, ya kamo wajen tsakiya ya shiga jijjijgawa suna ƙara kacaf-kacaf.
"Ni ce mana kuma hannayen nan zanen fulawa ni Tsigi-tsila ce ma ta mini ga sarƙa da sabon leshi" Ya faɗa tana ɗora hannunsa kan sarƙar aikuwa ya shiga santi yana cewa
"Kuma aradun Allah Uwani har wani ƙamshi na ji kina yi tamkar na kai ziyara garin shuwa arab"
Wani daɗi ya cika Inna jin an zo kan gaɓa.
"Ai duk dan kai na yi shi ne na ce sai ka biya tukuici"
"Yo faɗi mana Allah na tuba ko shi tukuicin ya ganni ai guduwa zai yi mai aka yi aka yi wani tukuici wanne daga ciki kike so bado zan siyo miki a kasuwa ko kanya ko magarya? Ke idan ma aduwa kika ce kina so kwano guda zan auno miki Uwaniyota" Ya faɗa yana washe baki yana kuma jiran Inna ta zaɓi ɗaya daga cikin abubuwan da ya lissafo.
"Babu ko ɗaya"
"To zaɓi da kan ki ko a ina yake sai an nemo" Ya faɗa yana wani bada faɗi dan shi tunaninsa abin da Innar za ta zaɓa ba zai wuce kayan naira ɗari ba zuwa da hamsin kuma ya ga dai ita ma kuɗi ta kashe ta masa gayu ga kuma daɗin da yake ji ganin ta saki jiki da shi bata masa jidali ba a kan auren nasa.
"Cewa na yi dama...
"Haba ki faɗa mana ai kawai ki bar wani kame-kame"
"Na ce tun da ni ma amarya ce to ina so ka kawo mini gasasshiyar...
"Masara ko Uwani" Malam da yake tsoron abinda za ta ce ya yi saurin cewa gasasshiyar masara dan kar ta ɓallo masa ruwa dan in ta ce kaza ai ta kashe shi.
"Kaza dai ko"
"Ka???"
"Za" Ta ƙarasa masa ji ya yi kamar ta doka masa guduma lokaci guda ya ɗauke wuta kitsan robar ma ya daina shafawa.
"Malam ya ka daina taɓa ɗaure-ɗauren.
"Haba Uwani ɗarme-ɗarmen me(Ɗaure-ɗaure) Haka kawai z ki tada zaune tsaye in lalifin ma ki ce gashin masara zan kawo"
"Wato banda cin amanar da ka mini har kazar ma tafi ƙarfin in ci amma ai jiya an ce manyan zabbi ka kawo wa amarya har guda biyu amma ni saboda kuka ce mai daɗin hawa ka nuna ba zan samu ba"
"A'a abin bai kai nan ba bari in fita in ga yadda za a yi" Ya faɗa kamar zai yi kuka.
"Yawwa masoyina Malamina abin ƙau...
"Bari in je in dawo" Ya faɗa yana ɗaukan sandarsa ya dogaro ya fito daga ɗakin yana jin kamar an tsoma shi a ruwan zafi yau ake yinta ashe mata biyu matsala ne yanzu kowacce ta murza kambunta ya ma rasa wane kalar tunani zai yi ina zai samo kaji har biyu gasassu a wannan zamani da masarar tuwo ma wahalar samu take yi wa talaka.
Yana fita Lami ta shigo suka tafa ita da Inna tare da fashewa da dariya.
Yana cikin tafiya ya kusa kaiwa zaure ya ji motsin Duduwa tana ƙoƙarin fitowa daga ɗakinta da sauri ya tura sandarsa har yana neman ha tsilawa Allah ya taimakeshi bata gan shi ba da yanzu sai yadda hali ya yi.
*JALLI JOGA*
NA
MAMAN AFRAH
FCW
Page1️⃣9️⃣➡️2️⃣0️⃣
Duk damuwa da da na sani sun baibayeshi ganin wai yau shi ne yake gujewa Duduwa saboda gudun bala'inta ya san idan ta san daga ɗaki Inna yake to sai ta yi kamar ta haɗiye shi ɗanye. Wasu hawayen tausayin kansa ne suka gangaro masa ya saka hannu ya share, yana ji ina ma bai auri Duduwa ba, gashi ba a je ko ina ba har sun fara haɗa masa kitumurmura.
"Ni dai wanan mata sun zame mini JALLI JOGA" Ya faɗa a zuciyarsa yana tunano lokacin da yana da idanu ya san fuskar Duduwar ba wani kyau ne da ita ba haka ma Uwanin amma kuma sai shegen iyayi da baƙin jidali. Haka dai ya yanke shawarar fita daga gidan dan har lokacin yana cikin zauren gidan, dan ya je ya samarwa kansa mafita dan lokaci tafiya yake. Tura sandar ya fara ya buɗe ƙofar ya shiga shi dai ya ji shi kamar bai fito ƙofar gidan ba amma haka ya bi sandar tasa tana masa jagoranci sai lokacin ya ji ya shaƙi iskar waje alamar ya fita kenan. Tuntuɓen da ya yi da wani dutse har ya kusa faɗuwa shi ne abin da ya bashi mamaki dan ya san dai a bakin ƙofar gidansa babu wani dutse kuma ma abinda ya ɗaure masa kai bai wuce yadda ya ji bai ji hayaniyar mutane ba da ya fito.
"Malam dama baka tafi ba" Muryar Lami ta katse masa tunani. Da sauri ya sunkuya ya taɓa dutsen da ya yi tuntuɓe aikuwa zarginsa ya zama gaskiya domin dutse ƙofar ɗakinsa ne wanda yake daga can gefen ƙofar ɗakin da yake zama a ka ya yi alwala. Wani tausayin kansa ne ya kama shi jin wai tsabar damuwar da tashin hankalin JALLI JOGAR matansa da suka saka ya nemo gasassun kaji har biyu a wannan zamani na Tinubuyya (Mulkin Tinubu) Abin har ya kai ya shiga ɗakinsa ya ƙofar zaure da aka yi dan shigar baƙin turakar tasa ya fito ta ƙofar tsakar gida amma bai gane a ina yake ba.
"Yanzu zan tafi Lami" Ya faɗa kamar zai yi kuka yana saurin juyawa ya koma cikin ɗakin nasa da sauri-sauri gudun kar ta je ta faɗa wa Inna cewar yana nan ta tada masa zaune tsaye ko kuma ita Duduwa ta fito ta ganshi ta sako shi a gaba da jarabar za ta tafi gida.
"Wata shari'ar sai a lahira" Ya faɗa a zuciyarsa tunowa da ya yi duk abubuwan nan mutanen ɓoye ne suka janyo masa da suka haɗa shi da matar da ta cinye kazar tas da yanzu lamarin aljannu bai shigo sabgar ba ai da ina yana cikin matsala ma kaɗan ce bata wuce matsalar Inna.
"Barka da fitowa Malam, ina wuni Malam" Su ne abubuwan da suka yi wa kunnuwansa tsinke lokacin da ya fito daga gida da almajiransa ke gaishe da shi kai kawai ya shiga gyaɗa musu dan shi yanzu ba gaisuwarsu bace a gabansa dan haka sai ya shiga cewa.
"Garzali, Garzali"
"Na'am Malam gani" Cewar wani matashin almajiri da ya zo ya tsugunna a gaban Malam da yake tsaye.
"Garzali ka je akurkin kaji, ka kamo ɗan tsako guda biyu, na wannan kazar da ta haihu, ka yanka su ka gyara tas ka soka a tinken gashinku da kuke gashi da sallar layya idan kun samu sadakar nama, ka haɗa wuta maza -maza ka musu gashi ga fam goma, murtala(20) Ka siyo mandan 10 (Gishiri) Barkono dakakke na goma ka barbaɗa ka yi sauri ka gasa" Malam ya kai ƙarshen maganar yana jin wani ɗaci a ransa na yan tsakin da za a kama masa har biyu inda barsu za a yi ai za su girma ya siyar ya samu kuɗi amma yanzu tun da Inna ta matsa a kan tana son kaza dole a a kama a gasa ba dan ransa ya so ba ita kuma Duduwa ya fita ya ga yadda hali zai yi.
"Malam ƴan tsaki kuma? Ko dai talo-talo?"
Dammm Gaban Malam ya buga jin Garzali ya ambaci talo-talo yo shi idan har ya ce a kamo talo-talo biyu a yanka to ai tabbatar ranar cutar ajali ce ta kama shi dan kar ya mutu ya bari zai je a yanka masa ya ci.
"Talo-talo Garzali ashe baka da hankali ina maka ganin mai tunani ashe kallon kitse nake wa rogo yanzu talo-talo zan ce a kamo har biyu a yanka? Sai ka ce wanda nake gargarar mutuwa to ai sai dai gani na yi ina dab da barin duniya zan ce a yanka ko ba zan iya taunawa ba saboda cutar ajali sai in ce a soye raƙas a nuƙo a inji a jiƙa da ruwa ake mini ɗura in san dai na ci amma ina nan da raina kaima da gangan kake to da ka ji na ambaci keji? Akurki fa na ce" Ya kai ƙarshen maganar yana ɗaga sandarsa dan haushi zai ƙwaɗawa Garzali da sauri Garzalin ya goce ya koma ɗaga gefen ya tsugunna ya ce
"Malam ni tunanina ko sabo da sabbin amare za a kamo talo-talon a yanka shi ya sa na tambaya"
"A ina sabbin amaren?"
"Iya Duduwa da Inna Uwani mana, jiya an kawo Iya Duduwa ɗazu kuma muna nan aka wuce da Inna Uwani a kan jaki ana waƙa ana rafka guɗa tana langi to duk tunanina wata ƴar ƙwarya-ƙwaryar walima za a shirya musu"
"Garzali na bi sabbin amaren da gudu babu takalmi haka kawai dan ka jaza mini yo a kan me ma"
"A mini afuwa Malam, dana ƴab tsakin da ka yi magana ne na ga ko isa yanka basu yi ba jairirai ne fa tun da yaushe ma uwarsu ta tashi daga kwancinsu ko yayesu ba a yi ba bana ji ma sun cika sati biyu da haihuwa fa"
"Ma,aifa ce (Mahaifa) Ƙarewa jarirai to ko a cikin ma'aifar kazar na ce a fito da su a yanka ina ruwanka, ƴan tsakin da har suna iya faɗin iya-iya(Ciyat-ciyat da ƴan tsakin ke yi) mutane bakwa mutuwar tsakar ɗakinku"
"Allah huci zuciyar Malam bari na je na aiwatar yanzu" Ya faɗa yana kallon ashirin ɗin da Malam ya bashi ta gishiri da yaji.
"Yawwa ko kai fa suyar ta yi daɗi"
"To Malam"
Juyawa Malam ɗin ya yi yana sauke wata ajiyar zuciya jin ya samu mafita ɗaya saura ɗaya tun da ya san dai Inna ba sani za ta yi ya siyowa Duduwa kazar ba in ya samo kenan bare har ta ji haushin ƴan sakin da za a gasa mata duk da ya san ƴan tsakin cinyarsu ma vata fi yatsan jariri ɗan mutum ba dan yara ne.
Tun da ya tafi yake jin faɗuwar gaba dan ya san dai ɗan Garki ba zai taɓa bashi ko da kai da ƙafa bane idan bai bashi kuɗi ba bare kuma kaza haka ya tafi yana ta taraddadin yanda abin zai kasance. A haka ya je wurin ɗan Garki mai gashin kaza ya samu wuri ya zauna sai da mutane suka ɗan watse ya shiga gabatarwa da ɗan Garki bayanin abin da ya kawo shi wato ya bashi bashin kaza idan aka gama amfanin gona zai kawo asa kuɗinsa amma fir ya ce wallahi ba zai bayar ba Malam ya yi ta magiya ya hana shi ƙarshe dai ya ce sai Malam ya kawo masa wani abu wanda zai riƙe a wajensa matsayin jingina duk ranar da Malam ya kawo asa kuɗi sai ya bashi abin. Haka Malam ya baro wajen ɗan Garki yana ta saƙe-saƙe dan shi bai san ma mai zai kai masa a matsayin jingina ba dan ba a bada ɗan mutum jingina da ɗaya zai ɗauka cikin almajiransa ya bashi yake masa aiki idan ya kai kuɗin sai almajirin ya dawo wajensa.
Gida ya koma ko cikin gidan bai shiga ba gudun matsala ta ƙofar zaure ya shiga ɗakinsa kayansa ya ɗakko sabbi wanda yake saka wa idan za shi ɗaurin aure ko dai wani taro nasu na Malamai idan an gayyaceshi. Haka ya ɗakko shaddodin nan yana ji kamar ya yi kuka ya saka a kedar biba ya fito ya koma wajen ɗan Garki ko da ya je suna masallacin magriba haka ya zauna riƙe da ledar dan shi ko alwala bai samu ya yi ba bare a yi zancen sallah. Ɗan Garki ganin kaya masu kyau sun sha gugar almajiran Malam sai ya karɓa ya saka wa Malam kaza a leda da ɗuminta ta sha mai shanak sai ƙashi take, a kan idanun Lami aka saka wa Malam kaza a leda kuma ganin idanunta guda ɗaya aka saka masa dama daga siyen rogo take Inna ta aiketa wajan ta siyo rogo mai ƴar dama da zafinsa. Tana kallon Malam ya karɓi ledar kaza ya ƙanƙame yana ta faman godiya. Ta kama hanya ta tafi gida ba tare da ta yi wa Malam magana ba.
Malam kuwa hanya ya kamo yana ta murna ransa fari ƙal zai kwashi garar amarci yau dan ya huta da jarabar Duduwa da ta ce za ta bar gidan a kan kaza. Yana zuwa ya karɓi ƴan tsakin da ya saka Garzali ya gasa, dan Garzali ya gasa har ya saka a baƙar leda dan shi kansa Garzali idan ya kalli ƴan tsakin dariya ce take kama shi dan ko girman tsuntsuwa basu yi ba ko da ya je akurkin ma dakyar kazar ta bari ya kama ƴaƴan nata tana ta cakon hannunsa. Malam yana karɓar ledar ƴan tsakin sai ya ji ta shafal bbu nauyi kamar ma ba a saka komai a ciki ba.
"Garzali ledar ƴan tsakin da na ce ka gasa fa na ce ja bani ba ledar ƙosai ba"
"Malam su ne dai a ciki"
"Kuma guda biyun ne ko dai ɗaya ne ai na ji ledar shafal kamar babu komai a ciki"
"Biyu ne Malam"
"To, to, to, ina sauran mandan (Gishirin da yajin?)"
"Duk suna cikin ledar Malam"
"Ikon Allah duk a cikin ledar amma bata yi ɗan nauyi ba to ai shikenan da babu ai gwara ba daɗi sa maida mugun yawu" Ya faɗa yana saka kai zai shiga cikin gidan dai dai nan Lami da ta gama jin komai ta sawo kai za ta fito.
"Sannu da dawowa Malam"
"Yauwa sannu Lami, ungo wannan ledar ki kaiwa Innarki ki ce har sauran manda da yajin ta riƙe gasu nan da zafinsu ni sallah zan yi ne shi ya sa" Ya faɗa yana miƙa mata ledar ƴan tsakin yana kuma ɓoye ledar kaza dan kar ta gani ta faɗa ya san Lami da shegen gulma bai san cewa ba a gabanta aka saka masa kazar a leda.
Karɓa ta yi ta koma cikin gidan amma bata shiga ba tana ganinsa ya shige ɗakinsa ta ƙofar soro, yana shigewa ta fito waje ta faki idanun mutane ta saka ledar ƴan tsakin a cikin kwata.
"Wato ga mayu, yo in ba maita ba waye zai ci naman jinjirin ɗan tsako dan bamu da galihu ita kuma ishashshiya da mai za a kai mata kaza" Cewar Lami a ranta cikin tsiwa ta koma cikin gidan ta je ta ɗakko ledar zazzafan rogon da ta siyo musu yana turiri, lokacin Inna tana bayi bata san ma mai ake yi ba zauren ta dawo tana kallon Malam ya fita ya yi alwala a tsakar gida amma ledar kazae tana hannunsa da zai yi alwala ma a cinya ya ɗora ta matse ƙafafunsa. Malam kuwa duk gudun kar aljannu su ɗauke kazar ya shiga uku shi ya sa ya ƙi ajiyeta kuma abinda ya sa bai kai wa Duduwa ba ba ya so ya kai mata ya fito yin sallah ta je ta ci ƙarfin naman shi bai ci ba. Dan haka da ya gama alwala ya zo ya lalumi dardumarsa ya shimfiɗa har lokacin ledar tana maƙale a hannunsa.
"Allah ka yafe mini ban yi sallah a sahu ba ban yi ta a kan lokaci dama haka yau da safe ma na yi sallah ban je masallaci ba" Ya faɗa a fili.
Lami da ke tsaye ta ga Malam ya janyo wani wandonsa ya nemi waje ya zauna ita da take tunanin sallah zai tada kallonsa take cikin mamaki, lawurjen wandon(Tazuge) Ya shiga zarewa daga jikin wandon sai da ya ciro sai ta ga ya ƙulla tazugen a ƙafarsa, bayan ya ƙulla ya janyo ledar kazar ya ƙulla a jikin tazugen ƙafarrasa. Sai da ya nannaga ƙullin ya ji ya ƙulli taminjau a fili ya ce
"Wallahi sai ko a haɗa da ni da kazar a ɗauke" Ya faɗa yana saka hannu ya rufe bakinsa saboda tunawa da ya yi da ɓaran-ɓararmar da ya yi ashe fa aljannu yake cewa su haɗa har da shi a kan su ɗauki kazar. Gabas ya fuskanta ya fara tada iƙama har ya kammala iƙamar zai tada sallah sai kuma ya sunkuya ya ƙara taɓo ledar kazar ya ji tana nan sannan sai ya juya ya tada sallaar ya shiga karatun sallah.
Sai da ta ga ya yi ruku'u ta lallaɓo ta shigo ɗakin riƙe da ledar rogon abinka da ba gani yake ba bare ya ganta idan ya sunkuya haka ta lallaɓa ta kama tazugen jikin ledar kazar ta since ta ɗauki ledar rogon ta ƙulla a jikin tazugen ta tashi saɗaf-saɗaf ta bar ɗakin ta tafi ta kai musu