Showing 30001 words to 32509 words out of 32509 words
Chapter 11 - DUTSEN CIKIN RUWA Part 1 Complete Hausa Novels by Haleema G Khaleel.pdf
*96-97*
~~~Da ikon Allah, aka fara shagulgulan biki. Hausawa sukace Rana bata k'arya.....!
Asabar 12 gawatan Goma dubban jama'a suka shaida d'aurin Auren 'ya'ya hud'u na Alh
Abdul-Muiz Auwal, Namiji d'aya da Mata Uku. D'aurin Auren yaya Hafiz akafara d'aurowa Tudun
maliki, da Amaryassa Maryam.
Juwairiyya da Angonta Aminu. Samiha da Mukhtar, wanda silar had'uwarsu Allah yamasa
shiriya kamar dawasa suka fara Soyayya da Samiha kuma Allah yai matarshice takaisu gayin
Aure ayau.
Akaro nabiyu aka kuma d'aurawa Naja'atu Aure da Angonta Arc Sulaiman Kazaurw.
Yana daka cikin Al-adun bahaushe nawannan lokacin yayin Aure. Bayan and'aura Aure,
Angwaye da abokanansu, sukan shiga gidansu Amarya domin gaisawa da Iyaye Maza da Mata.
Hakance takasance gidan Alh Abdul-Muiz A yacika fal da Jama'a masu Hotuna, da Marok'a seyi
suke.
Mazajen Samiha da Juwairyya se hotuna ake musu haka Yaya Hafiz ma anatayi dawasu 'yan
uwan. Sa6anin Sulaiman dayakasa ganin tasa Amaryar se washe baki yake kaman gonon
Auduga. Abokansa kam se tsiya suke masa.
"Yanzuke hakan dakike yayi dai-dai kenan? Inma bazaki shiruba yaci kin kammala shiryawa"
Inna data shigo tatsaya akan Naja'atu datake ta shar6an kuka, tunda akakusa bikin tazama
sukuku da ita duk tasusuce banda ramar data kumayi. Dayawa sunmata magana tak'i shiru
sega Innartasu takuma dawowa. Anty Husna ganin datai kamar Inna zata rufe Naja'atu da duka tai saurin matsawa kusada ita,
Lalla6ata tashigayi ahankali tana mata Nasiha "Haba Daughter na kedama bayau ko gobe zaki
tafi gidan mijinba. Ko Samiha kiduba daza akaita gobe batai wannan kukanba ammake anrasa
Kukan mekike ko Aurenne bakyaso?" Tana kallanta ta girgirza kai "To maza kishiru kinji Aure ai
Ni'ima ne da Daraja. Shine Cikar Zati Kamala da Mutuncin duk wata 'YA MACE muddin tarik'e
mutuncinta tobamai kyetamataahi. Kuma kowace Uwa dakikagani Burinta ta Aurar da 'YA'YA
MATAn dake gabanta shine samun nutsuwa da kwanciyar hankalinta. Kowa kuma da haka
tasaba. Maza k'arasa shiryawa kar Mijinnaki yazo yaganki haka, kinji 'yar albarka". Shiru tai duk
tasaurari metace k'awarta Jidda da Mino dake fama da ciki sukai tamata iya-ege, ahaka suka
k'arasa gyaramata kwalliyarta data 6ata da kuka suka Shirya fes da french less coffee colour
damayafi milk&coffee har kanta se k'amshi take Amarya tafito fess da ita se ajiyar zuciya datake
saki.
Gud'ar dasuka jiyoce, taji wata mata dabata gane waceba tanata Kabbara, sekirari takewa
Inna da 'Ya'yanta. Sulaiman suka shigo har falon Inna gaisawa sukai tayi da 'yan uwa dake
falon. Anty Husna tajata suka fito falon, kanta asunkuye. K'walla tataru a idanunta. Masu hoto
da masu d'auka da waya sukai tayi hasken Flash kawai kake gami.
Kukan datake 6oyewa ahankali take shashshek'a, Sulaiman datun shigowarsu seda yaganta
farincikinsa yak'aru. Bayan mutane sund'an ragu a falon, duk'addakai Sulaiman yai yad'an
tallafo Naja'atun sesuka bada wani Style masu Cemara kam mezasiyi ba hotoba akaita
_Snaping_ insu. Ni Aneesa_Didi Duk k'ok'arina na injiyo muku meya cemata akunnenta
banjiyoba murmushi nikaina nasa ganin kowa yana darawa.
Itakam ganin Sulaiman naneman bata kunya yasata sakin murmushi tareda janyewa daka
jikinsa nikuwa nace kaga Masoya. _Gud Moment_ kenan "Tears & Smile".
© *Aneesa_Didi*í ¼í½¼í ¼í½‰
[2/18, 10:50 AM] +234 703 962 5239: ♡ *DUTSEN CIKIN RUWA.....*♡
*Na*
*Haleema G Khaleel*
*98-99*
~~~Haka akai biki aka gama cikin farin ciki da Annushuwa, su Husna da Hassan shigar
sababbin kaya akai tamusu. Yara masu kyau dashiga rai, kowa sansu yake duk inda suka shiga
kamar kasace kagudu abin gwanin ban sha'awa.
Inna nasa k'afa suma suna sauke tasu ko ina suna biye da ita sabida Mamynsu Hauahin kowa
takeji jin ance "bazata tafidasuba kosu koma gidan Kakanninsu, duk dashi a 6angarensa
bashida matsala Sulaiman ya amince zai Rik'esu koba komai Rik'on Maraya Ladane kuma D'A
NAKOWANE. Amma iyaye sunce sesun duba labarin. Hakan yasata 6acin rai.
Sharar hawaye take akai-akai yaranma ko kallansu batayi.
Washegarin ranar lahadi. Daga cikin yayunsu mata Anty Husna ma tabi wanda zasu gidan
Samiha suka tafi gidan Amaren dan k'ara gyagygyarawa kafin akai Amaren.
K'arfe uku na yamma agogon Nigeria Niger da Chad. Shirye shiryen kai Amare Juwairiyya da
Samiha ake ana la'asar za akai kowacce gidan Mijinta.
Inna dai bata tankaba ganin ita Naja'atu se shirye, shiryen fita take da alama 'yan kai amarya
zatabi. K'anwar Babansu Gwagwgwo ta Getso tashigo ganin Naja'atu tana fesa Turare yasata
cewa "Hala kai Amarya zaki kema?" Sunkuyar dakai tayi "Ah Gwaggwo dan Allah kuje dani"
cike da shagwa6a tai maganar hadda langa6ar dakai. Dariya sukayi 'yan d'akin. Gwagwgon takuma fad'in "Ai tafiya dake babu matsala mutuk'ar
dayaddar Mijinki maizai hana mutafi dake, tunda ke tariyar ba yanzuba." Ai jitai kamar tasa ihu!
Matar wansu dasuke mutunci da ita tace "Maida wuk'ar yanzu da Aure akanki, inda zaki fita dole
saida izinin ma'ana kin tambaya komai kinma sani ai, sedai k'arin bayani. Ki kirashi kisanarmai
inya amince muje mudawo ko Gwaggwo?".
Naja tai shiru tamkar bazatai maganaba. Ganin anata shirin tafiya kai amaren har anshiryasu
ankaisu gurin Baban dasauran Matan Gidan sekuka suke. Yatsuna fiska tai kamar tahak'ura ma
dazuwa, tai tunani to aikuma batada ranar zuwa k'ara taje yanzu ayama.
Kiran layinsa tayi seda tai Ringin Hud'u yad'aga "Ran Gimbiyata kuma Amaryata yadad'e!"
Rasa maizatace tayi dabara tafad'o mata tace "Tare dakai fatan kana lafiya?"
"Alhandulillah, muna lafiya dani har Matata dakowama."
"Uncle mai Zane"
"Na'am Mamyn uncle mai zane"
Shiru bawanda yakuma magana sai numfashinsu dake shiga kunnuwan junansu.
"Dama wai zanbisu kai Amarya shine wai Gwaggwo tace sena tambayeka" tafad'a harda cuno
baki kamar anmata dole.
Dariya Sulaiman yai sosai lallai Matar tasa 'yar daruce ko rigima zaice. Jin yana dariya taji
inama bata kiraba, kamar takashe wayan taji sedai koma takashe abanza kiranta zaikumayi.
Taji yace "Tajirashi yazo yakaita dakansa danba mai kallrmasa kayansa"
"Haba Uncle ga Jama'anan muna zuwa zamu dawo damafa Gwaggwo zamu."
Duk yadda tabi k'iyayi dole shid'in yazo yakaisu. Samiha ita banisa cikin Unguwarsune.
Juwairiyya itakuma aka kaita Hausawa.
Semuce Allah bada zaman lafiy da k'azantar d'aki amma bata sharaba.
Exams in su Naja tazo shikansa Angonnata Sulaiman sarara mata yai dayin Waya.
Dantasamu tai karatun final Exams inta. Dataimakon Allah suka kammala exam inau da
makarantarma duka sejiran sakamako.
© *Aneesa_Didi*í ¼í½¼í ¼í½‰
[2/18, 10:52 AM] +234 703 962 5239: ♡ *DUTSEN CIKIN RUWA.....*♡
*Na*
® *Haleema G Khaleel*
10 jan 2017
*100*
í ½í´š
*_But if they intend to deceive you. Then sufficient for you is ALLAH. It is he who Supported you
with his help and with the believers._*
~~~Tunda tafara exams Sulaiman ke kaita yadawo da ita harta kammala.
Watarana yad'aukota daka sch suntsaya a _Go slow_ a junction mutane se hada-hada, suke.
Un expected taji anrik'o hannunta abinda Sulaiman beta6a mataba, dagashi har ita wani
_Haptonasty Reaction_ sukaji sosai yakuma rik'o hannunta ganin abinnasa nakuma k'aruwa
cike da shagwa6a ta turo baki "Allah kaban tsoro kuma sena rama" dariya sosai tabashi yadda
bakinta ke motsi da shagwa6anta ya birgeshi yace "to ai nariga nabiya dan wannan kawai,
barikiga kad'an daka ciki..." Gaba d'aya ya janyota jikinsa yafara Sumbatar bakinta cikin
nutsuwa k'amashin Air freshner motar da Turarensu suka had'u suka bada wani Sanyayyan
k'amshi mai Sanyaya zuk'ata. Hakan yakuma ingizashi yakuma rik'ota tako ina aikamata
zazzafan sak'o yake yanakuma shafota.
K'arar horn d'in da ake yimusu yayi yawa, dole yahak'ura. Saurin komawa mazaininta Naja
tayi d'ankwalinta dayazame tagyara had'eda mayafinta. Allah yasa Motar da Tinted, nawaje
bazega nacikiba amma naciki naganin nawaje.
Sunkuyar dakai tai tana wasa da abin mayafinta, tafiya suka cigaba dayi. Jefi-jefi yana
dubanta yana sakin wani k'ayataccen murmushi dake k'aramasa kyau da kwarjini.
Sunkusa kaiwa gidansu Naja'atu yai Parking dai-dai gurin wasu masu nama wanda anan suke
siyan Nama kowane iri kakeso zakasamu agurin "Haleema Suya Spot" fita yai daga motan yace
"yana zuwa."
Binsa tai da idanu aranta tana tunanin dama haka Sulaima yake shima d'an soyayyane,
murmushi tai tana kuma tuna abinda yawakana mintina kad'an dasuka wuce.
Bedad'eba yadawo da ledoji a hannunsa. D'aya yasa abayan motar, leda biyun kuma ya
d'oramata akan cinya yad'ora dacewa "Ga Tsiran Tsira da Soyayyanan da Kilish, dukda ni
nasan tawa a Safe content take."
"Kai Uncle wannan Confidence haka"
Dariya sukai duka yaja motar yak'arasa da ita gida sukai sallama yawuce dan cigaba da shirin
taryan Amaryassa.
Kwana biyu da gama Exam inta, Babansu yasa dole tatare asatin fad'a sosai yamata. Hassan
da Husna karma susata kuka aka kaisu gidan kakanninsu. Maman aranta taso datana dawani
babban d'a Namiji ya auri Naja'atun takasance cikinsu. Yanzuma addua da fatan Alkairy suka
mata. Daga canma gidan Yaya Yusra aka kaisu yar Usman Mahaifinsu.
Ranar Jumu'a k'arfe Hudu da rabi, kamar yadda akakai sauran 'yan uwanta. 'Yan uwa da
abokan arzuk'a nakusa suka rakata gidan Mijinta akaro nabiyu dake d'an Agundi G.R.A. kuzo
kuga wani _Mension_ da Arch Sulaiman yazana Tasweerar Gidan dakansa. Tundaga wajen
gidan abin kallone, ido nabud'e harda hanci da baki ina kallon Aljannar duniya. Varender ce dazata sadaka da Falo mai Girma d'auke da Kitchen, Dining Area Toilet sewani
D'aki da toilet ahad'e. Daga gefe nagano Stairs dabasu dayawa duk cikin falon zubin ginin
Indiawa. Inka haura Saman d'akunane manya guda uku da aka k'awatasu kowanne d'auke da
Toilet aciki launi daban-daban se Varender tasama itama. Gidan gaba d'aya abin kallone 'yan kai amarya se san barka suke dasa albarka. Amaryan
nagano cikin wata Gown zubin Qatar anrufeta sinkif se walainiya take da tashin k'amashi. Wani
_Purple bedroom_ aka ajeta akan gadon da Fulalluka suka yawaita akai. Nikaina nadad'e ina
santin d'aki (Lol).
Kafin Maghriba kowa yatafi akabrta se wasu daga cikin dangin Sulaiman, kukan dataitayi
hartagaji tabari har ango yazo yasameta. Nafila suka gabatar tareda 'yan Tand'e-tand'e da
lashe-lashe Nakaji da lemuka harda Tsiran Tsira da Soyayya, nima Uncle mai Zane yaban
K'unshi d'aya yace nasanwa Miss xoxo da besty miss Fais ceeda, danyaga abimnamu iri
d'ayane.
Tsayawa nai abakin k'ofa gan Sulaiman yafara Rud'a Naja'atu da sak'on Soyayyarsa mai
girma, fuskarsa yake kuma cusawa jikinta yana k'ok'arin rabata da kayan jikinta azafafe yake
shafarta har tausayi sukaban, se numfashi suke saukewa suka Lula Kogin Soyayya mai Sanyi
da Wahalar Nink'aya. Bashiri nai waje. Tsiran Tsira da soyayyan da akabam nawarware nafara
ci. Kuma Makaranta ganaku. Hhhhhh.
************
BAYAN WASU LOKUTA
~~~Soyayya suke gwadawa Junansu mai tsafta. Dukda ZAMAN TARE zomu zaunane zomu
sa6a. Yaransu masu kyau. Namiji tafara haifa maisuna Sufyan, Zuwa lokacin Hassan da Husna
sunk'ara girm. Babu tayadda zakace ba 'yan gida bane, kowa sansu yake adangin Sulaima.
Suntaso da soyayyar dangi da gata.
Haihuwar Safiyya takumayi 'yar Babynta gwanin sha'awa mai gashi da ita ba inda tabaro
Umman Sulaiman.
Zama suke maitarin Aminci K'auna da Soyayya dakuma Hak'uri da Juriya akomi na Rayuwa
dayasamesu medad'i ko akasin haka.
Girki tagama takuma salla wanka wata Fitted Riga da Zani tasa na Atamfar Vilisco launin sky
blue da maroon ahad'e tasha _Makeup_ sek'amshi take takuma cika sabida jegon datake 'yar
Chafai da ita. Bazakace tayi yara Hud'u ba. Hutawa take ita kad'ai se Baby Safiyya(yadda su
Hassan ke gayamata) sauran yaran duk taturasu gurin Umman, tagyare gidan dataimakon
Sulaimam kafin sufita. K'amshin turaren data sa a electric burner ketashi cikin gidan. Safiyyan
tana kan jikinta anmata gayu itama tasha hoda b'angala dariya take, dahaka tasamu talalla6ata
tai bacci. Kusada ita takwantar da ita.
Wani Novel take karantawa maisuna JANAN na (CHUCHUNA AYEESH) sallamar
Maul'ainain(Ruwan idonta) taji Sulaiman nagano yakuma girma, Sumar kanashi se k'yalli take
gawani Zagayayyen gemu daya ajiye wanda yakuma k'awata fuskar tashi da 'yan mata kerubibi,
basusan Naja takafa ta tsare kuma taraka.
Sama da ita yai sukaita zagaye falo sannan yadireta. Tabaya yarungumota tsam har tanajin
bugun zuciyarsa. Farar takadda yafito da ita yace tarik'e, akunne yarad'a mata "nagode Allah
matata mai sa'ace gashinan and'aukeki aiki a General Hospital, so get ready nanda 1-2month
zaki fara attend" wani juyi tai takuma rungumo mijinnata "Alhamdulillah Nureena, Wht a Suprise
Habibi" nagode sosai mijina na har abada hak'ik'a KAINE GATANA kuma FARIN CIKINA. Allah
yabiyaka da d'umbin alkairy yafarantama ka kamar yadda kakemana. Nakuma Godewa Allah
yadda mukazama DUTSEN CIKIN RUWA DABAI SAN ANA RANA BA. Dagamu har
Mahaifiyarmu tayi hak'uri muma tad'oramu akai. Tabbas Hak'uri Ribar Rayuwane. Ba irin nacin
dabanyiba kabarni nai Aikin kak'i yanzu kaga nasamu amincewarka 100% nagode Allah
dasamun miji irinka. In sha Allah zanyi aiki sabida Allah zantaimakawa Al umar musulmi kuma
zankare DARAJA DA MARTABAR AURENA. Allah yak'aramana lafiya dazama Lafiya.
_Deep french kiss_ tashiga aikamasa sak'on kuwa yashigeshi yafara fita hayyacinsa yana ba
Amsa danasa salon Sak'onnin. Cak yad'auketa sukai samansu d'aki sukai tareda rufo k'ofa.
Dole najuyo nace asha soyayya lafiya.
_Soyayya gaskiyace Allah yabarmu da masoyanmu ako ina suke_
Alhamdulillah!!!
Anan nakawo k'arshen wannan labari. Kurakuran ciki Allah kayafemana kazama jigonmu.
*$adarkrwa garekune*
Hafsat GL (Miss xoxo)
Masoyiwa kuma 'yar uwa
Aneesa A Rimi (Mamyn swty Ayman)
Haleematu Bukar Saje
Kinfi kowa san littafinnan. Allah yabar k'auna da zuminci.
'Yan uwa marubuta inamuku fatan alkairy. Allah bar zuminci.
Duk wanda ya isa gareshi nagode sosai da tarin sak'onne da soyayyarku. Inbabu ku babumu.
Allah yahad'amu da rahmarsa.
K'arshe.
Semun had'u asabon labari.......
Taku maik'aunarku
Haleema Sadiya g Khaleel.
© *Aneesa_Didi*í ¼í½¼í ¼í½‰
Copied By
HAYATU BABA ZUBAIRU
(admin
Arewa hausa novels
Novels villa
Duniyan novels
Hayat hausa novels
Hausa novels and fashion
And
Cool novel, makeup and cooking)
WHATSAPP NO:
+2347039625239