Showing 9001 words to 12000 words out of 32509 words
Chapter 4 - DUTSEN CIKIN RUWA Part 1 Complete Hausa Novels by Haleema G Khaleel.pdf
biyar tai shirin tafiya, sukai bankwana dukda sunso tak'arasa sati, ita kua taki
yadda tunda hutun nata bawani yawane dashi ba. Suka cikata da kayan Arziki. Anty khadija
kuwa kayan shafa da makeup tabata. Dakyar Hinduwy ta amsa sallamarta, (se kuma wani jik'on
my Hinduí ½í¸‚)
*Dabinai kano*
Bayan Alh Bello galadima yasamu sauk'i, da k'warin jiki, dakansa yaje Dabinai yasamu
kannansa, Baba Saminu da Baba Sani, wanda yake kulada gidan idan bayanan.
Yasanar musu gameda abinda ketafe dashi. Duk da shi Baba saminu yaso anhada Auren
zuminci da Maryama 'yarsa da Usman 'din. Amma haka yaja bakinsa yaishiru. Sukai fatan
Alkairy da nufin wani satin zasuje cikin garin, gidansu yarinyar da Usman in yakeso. Domin ai
zancen manya. Se muce Allah yanuna mana.
**********
Kawu Sa'ud ne ya'dakkota daka gidan Kawu Harunan. Dukda taso yakaita unguwar Gada-Biyu,
gidan 'yar Autar su Innar tasu mace, Anty Husna ganin yamma tayi yace: "tabari gobe taje setai
mata kwana biyu" tinda sati biyu zatai.
Da shigarsu gidan ummi tana tsakar gida tana Alwala, tai masu sannu da zuwa, itama ta aje
kayanta tashiga bayi kama ruwa. Shima kawu Sa'ud yai waje
Alwala tayi tashige 'dakin Ummin suka zauna kan atada sallar subi Jam'i.
Bayan sallar isha sungama cin abinci itada ummin, Tuwan shinkafa ne da Kawu Sa'ud in yayi
kamin yaje 'daukota, yabarma Ummi Miyar Shuwaka da taji Nama zuk'u-zuk'u tak'arasa.
Kwashe kayan tayi tamaida kitchen. Tadawo tazauna suna kallo, Sallama sukaji ta amsa
tareda rage volume in tv.
Kawu Sa'ud ne tareda Yunus abokinsa.
Suka k'arasa shigowa falon Ummin. Har k'asa ya duk'a yagaida Ummin. Malam Yunusa ne yau
a gidannamu?
Ya amsa da fara'arshi. Belura da su biyu ke zauneba. Seda yaji Sassanyar muryar Naja'atu
har cikin kansa tana gaidashi. Amsawa yai a kasalance tareda kai idanunsa kanta.
Wata kyakkyawar bak'ar yarinya idanunsa suka ganemai. Tamkar Sa'ud, sedai shi yafita
Haske da tsayi. duk yadda akai *Jininsu 'daya*(My Anee_luv).
Amma ya akai baisantaba. Kuma bai ta6a ganin taba.??
Wanga Samrayi Kodai shima yayi Gamo neí ½í¸‚??? Wayaga Rk&Madhubala
*Didi_Aneesa*í ¼í½¼í ¼í½‰
Anisadidi.pun.bz
[2/18, 10:47 AM] +234 703 962 5239: ♡ *DUTSEN CIKIN RUWA....* ♡
*Na*
*Haleema G Khaleel*
2⃣5⃣-2⃣6⃣
Harararsa tai tareda sunkwi dakai, ganin irin kallon dayake mata,
'Dakin Ummi tai nufin shiga, Kawu Sa'ud yace taka musu Abinci. Bayadda ta iya haka ta'dauko
flask guda biyu ha'de da plate da chokula. Taka ta ajiye seda yasata zuba musu. Sannan
tashige ciki, dan duk tatakure da kallan da Yunus in yake binta dashi.
A wayewar garin, tashirya tsaf. Tazauna zaman jiran Kawu Sa'ud in zai kaita Gada-Biyu gidan
Anty Husna, yaje 'dauko motan gidan dasuke ajewa.
Tsiya Ummin take tamata dantace mata ita batada Saurayi. "An daiyi Budurwar banza" kamarke
ace bakida Saurayi kode korarsu kike? "Hmm habade Ummi kawai baruwana dasu".
Gashi nikuma banda miji bare najona masa ke. "Allah ma yakiyaye na auri tsoho".
Aikuwade maga irin mijin naki. "Zakuwa kiganshi zanka'de'de"
Allah de ya nuna mana wannan rana dazanga Auranki 'yar jikalle.
"Assalamu Alaikum"
Sallamar Yunus ta katsesu,
Wa alaikumus salam.
Ummi tace "shigo mana Malam Yunus".
Ummi barka da safiya ya gida? Alhamdulillah. Ya mutan gidan?
Lafiya lau suna gaidaki.
"To madallah"
Sa'udun yaje 'dauko mota anan baya. Kajirashi. Gidan Husna ma zaikai Naja'atu.
Se asannan Najan tagaisheshi. Ya amsa cikeda fara'a.
Ummi nadawo Sa'ud yace. "Au 'dan halak yak'i ambato kajishima ya dawo"
A ah! Abokina yaushe kashigo? Yamik'a mai hannu suka chafke. Futama zanyi bara in'dan zuba
ruwa. Daughter kina ina sry kinji bari nai wanka.
Kai kawu danAllah kabari inka dawo kayi. Aibawanda zai ganka, "toke haka zaki tafi baki
wankaba" salon budurwata taganni ba wanka" kaga shikinanma sainaga antyn tawa, tafa'da
tana murmushi. Aikam ba ayi hakaba Yunus yasako baki shima, "kidaiyi hakuri k'anwarmu yayi
wankan seya kaiki ko? Nima nayi rakiya".
Shikinan karka da'de kawu. Suka fice yana fa'din "yanzu zaifito suje".
Tak'ara tattarewa Ummi gidan dukda bawani datti yaiba.
Basu sukaje gidan Husnanba saiwajen 12 na rana, Anty Husna tai matuk'ar farin cikin zuwanta,
Naja ta tausaya mata ganin Tsohon cikin dake jikinta Haihuwa yau ko gobe, dasuka gaisa Kawu
Sa'ud yaimata Sallama yatafi yana mamakin girman ciki irin na Husna.
Wasa takeda Khaleefa 'dan Anty Husnan, yaro 'dan shekara biyu da 'doriya, cikin kwana biyun
datai sukai sabo sosai, abinka dame san yara da juriya da dabdalarsu.
Bayan tagama duk ayyukan gidan, ta 'dora musu girki. Shiru-shiru taji bata fito ba, seta bari
cewa Bacci Antyn tata tasamu. Ganin har tagama girkin ranar, lokacin Sallah yayi bata fitoba,
shiga 'dakin tayi da Sallama, ganin Antyn tata tayi durk'ushe, abakin gado. "Subhanallah" Anty
lafia. Hmm kawai tace da ita. Ganin tarasa yaza tayi yasa tabugawa kawu Sa'ud waya
yagayama Ummi Anty husna ba lafiya.
Cikin mintunan dabasu fi Arba'in na, saigasu shida Ummi, tanata mata addu'a, taha'da mata duk
kayayyakin Sa'ud yakaisu asibitin datake zuwa. Dan mijinta baya gari. Ita kanta Ummin batai
tunanin watan haihuwar Autar tata yatsayaba.
Naja'atu kuwa sai kuka take rungume da Khaleefa, dama haka haihuwar take, lallai iyayenmu
sunyi k'ok'ari. Taji tasake san Innarsu ha'de da jinjina mata.
(Luv u my Innarmu. Mom like no other).
Tasha wuya sosai, sannan tahaifi 'diyarta mace, akai tawaya anagayawa 'yan uwa da abokan
arziki. Kansu dawo gidan har mahaifiyar mijinta da k'annansa sunzo gidan, seganinsu kawai
sukayi.
saboda haihuwar Naja'atu tazauna se bayan suna.
*Kano*
Kamar yadda suka zartar, sati na zagayowa, Baba Sani da Baba Saminu, sukaje gidan Alh
Abdul-mu'iz, Usman 'din dakansa yai musu rakiyar. Baban nasu kuwa yakar6esu da karamci irin
na Kanawa, suka rattabo meke tafe dasu, "'Dansu yaga 'yarsa kuma yanaso". Domin subi
k'a'idar musulunci yasa suka zo k'afa da k'afa, nemar masa izinin zaifara zuwa gurin ita yarinyar.
Alh kuwa yai farinciki, tareda yarda da nagartar yaron, sawa yai akira Usman in yaganshi. Baba
Sani yakirashi awaya, yazo yarisuna yagaida Alh Abdul-mu'iz cikeda girmamawa dajin nauyi.
Yamasa 'yan tambayoyi, duk ya amsa, yasanar musu da Najan ma batanan taje ziyarar dangin
Mahaifiyarta a Gusau.
Yamasu sallama yai waje. Basu tafiba saida suka bada ku'din zance. Tinda bawani lokaci
sukeso a 'diba ba. Gaisuwa suka k'ara irinta manya, sannan suka rabu sunata zuba godia. Shi
kuma Alh yashiga cikin gidan yasanar musu, kowa saida yai mamaki, bama Inna da bata ta'ba ji
koda wasa Najan tai maganar Usman dinba. Amma wai gashi harda ka ku'din zance. Addua
tashiga yi Allah yatabbatar da alkairi koma menene.
(Topha ita amaryar bama tasaniba maji magani dai).
*************
Ana i gobe suna duk taha'da komatsanta waje guda, ranar Suna kuwa, suna akai irin namasu
rufin asiri ba alamun k'arya aciki, yarinya taci sunan Raheena.
Aranar sunan da daddare tatafi gidan Ummi dan gobe zatai sammakon tafia kano, anriga
ankoma Sch shiyasa zata tafi. Kawu Sa'ud shi yamaidasu gida ita da Goggo, dan Ummi k'in
zuwa sunan tayi. Jitai kamar kada surabu dasu Anty Husnan, barema Khaleefa boy inta hadda
guntun hawayenta.
K'arfe 9 na safe, bayan sunyi karin kumallan safe, Ummi taita mata Nasiha akan rayuwa da
kukanta sukai sallama da Ummin, tareda fatan Alkairy gaba 'dayansu. Suka ha'da mata tsaraba
fal.
kawu Sa'ud yakaita tasha yabiya mata ku'din motar sai kano ta dabo timbin giwa.
*Aneesa_didi*í ¼í½¼í ¼í½‰
[2/18, 10:47 AM] +234 703 962 5239: ♡ *DUTSEN CIKIN RUWA.....*♡
*Na*
*Haleema G Khaleel*
2⃣7⃣-2⃣8⃣
Sassanyar iskar data chanja ce ta tabbatar da sun shigo Kano, a tashar mota ta Kano,line aka
sauk'esu.
Drop in Taxi tayi har gida, yasauk'eta abakin Get insu, kayanta tafara shigarwa ciki, sannan ta
mik'a masa ku'din yatafi.
Bakowa a harabar gidan, yaran duk suna makaranta, manyan kuma yawanci suna gurin
sana'arsu. Da sallama tashiga cikin gidan, Deedat da wasu yara dabata gane suwaye ba
sunata wasa, muryarta da Deedat yajice yasashi tahowa da gudunsa ya 'dafeta "oyoyo yaya
Najata". Oyoyo autan Inna Deedat 'dina, suka sa dariya, ajeshi tai yai 'dakin Innar da gudu.
'Dakunan sauran matan gidan ta shishshiga, suka gaisa sannan tai 'dakin Inna. Tanata mamaki
jin Gwaggwo Safiya, takirata da Amarya hadda Allah yasa akairy, yasa ayi dasu. To yaushe
tazama Amaryar? Kowani abun yafaru batanan? Duk wa'dannan tambayoyin bata da me bata
amsa sai Inna, jiki salu6e tashiga falon Inna, a kujera ta zube, tanata maida numfashi kamar
wadda tai gudun shekara.
Inna ta futo daka 'daki tana "lafiyarki kuwa yayar Salim naganki haka?".
Seda ta rusuna tagaida Innar, tace lafiya lau kawai gajiyar hanyace. Sannu to yakika
barosu? Ina masu jego? Ah tagayamin munje kasuwane lokacin da k'annan Abban Khaleefa,
sunanan lafiya duka. Duk suna gaidaku har matansu Kawu Haruna da Kawu Bashir, Ummi ma
tace gawani magani nan wai kitafasa mana dukanmu muna sha. Allah sarki Ummi, yajikin nata
kuwa? "Alhamdulillah Inna dan taji sauk'i sosai" kawu Sa'ud wankane kawai baya mata. "Ina
ruwan Sa'ud, nagadai yazasu rabu da Ummi, wannan shak'uwa tasu."
Ai Inna nagayamasa kawai inyatashi auren yai zamansa a gidan, yasa dariya yaga kamar
wasa nake masa. Yacede zai duba. Allah dai yai mana jagora Innar tafa'da tafita zuwa 'dakin
Babannasu.
Sallah kawai tayi tahau bacci, k'arar da Samiha tasane yasata farkawa agigice, ganin Samiha
tai tanata tsalle ha'de da "ki'da da jikin wardrobb insu tana Wellcome back Amaryarmu, mata
agidan Ya,Usman". Tanatayi. Binta kawai Naja take da ido, se yanxun tafara ```Tuna
baya```{Anty sumy takori} tatuno duk irin yadda sukayi da Usman 'din, tanan ya 6ullo kenan.
Jitai hawaye yana bin kumatunta dabata tantance namenene ba. Bak'in-ciki ne ko Farin-ciki??.
Ganin tafara hawaye yasa Samiha daidaita kanta, zamatai akusada ita tafara bata hak'uri, Naja
kuwa murya na rawa tahau tambayar Samiha meya faru dabatanan? Zayyano mata komai tayi,
bata 6oyeba. Murmushi tai wanda dakajinsa na yak'e ne. Allah yashige gaba shikinan, tai
ban'daki tabar Samihan hangame da baki.
Da maghriba, suna zaune a falon, Inna ta wawwarewa kowa tsarabarsa, aka kaimusu.
Sungama cin abinci Inna takira Naja'atu, alokacin suka warwarewa juna duk abinda ake ciki.
Naja bata musaba ta amsa. ```Tunda dama iyaye keda right dazasu za6awa 'yarsu budurwa
mijin Aure.``` iyayen iyayansuma da akaimusu auren basusan mazajenba sun zauna maiya
samesu, gashi kuma har akasami wa'danda suka kasu duniya. Balle ita tasan wayema dazata
Aura.
Albarka Innar taita sakamata ha'de da fatan Alkairy a rayuwarsu duka. Sukaita hira
abinsu, hakan ba k'aramin kwantarmata da hankali yaiba.
Bayan isha, dasuka ci Abinci suka gyara gurin, da taimakon Samiha suka gyara kayanta,
taha'da duk abinda zata buk'ata, dan gobe dawuri zata shiga sch tanemi time table, sun shiga
final semester se sun dage. Kowa yanemi makwancinsa ya kwanta.
Wannan kenan.
Usman bek'ara kiranta a wayaba tunda akace batanan, koda aka koma sch dayaga bata
dawoba, ya kar6an mata time table, Lectures in datai missing yasamammata Hand-out da
manual, wasu har jotting yayiyyimata ajiki. Duk yaha'da yasa a leda yabawa su meenoh da
Jidda Ja'o subata watak'ila kozata shigo shi bayanan. Suma sunyi mamaki daganin haka. Seda
yace musu ma shi Visitin lec ne suka k'ara mamakantuwa.
Da safe duk suka shirya suna Karin,kumallon safe suka fice, har Deedat ansashi awata
Islamiyya tasafe. Inna ka'dai suka bari a 'dakin.
Su biyar duka suka tafi a Napep aka sauk'esu a Kuntau, itama aka sauketa aka wuce da Fawad
Al-Azhar shi acan yake.
Kamar sun ha'da baki suka ha'du da Meenoh. Seda sukaje class suka ha'du da Jidda
Ja'o sannan su Meeno suka gaggaya mata abubuwan da akai batanan. Suka mik'a mata sak'on
da Usman yabadar subata. Amsa tai taimusu godiya dukda tasha mamakin zak'ewa irin tasa.
Lectures sukai tayi babu wani interval sosai, saboda semester ta chanja.
K'arfe biyar suka tashi, sunzo fita abakin get taganshi se asannanma tasan yana cikin
Makarantar dan sam bata ganshiba se yanzu.
Matafiya kuma tafiya ba sallama? Shiru tai kamar bada ita yake ba. Har suka fita wajen
makarantar. Ba abinda yadameshi. Yanata janta da hira.
Seda taga idanu zasi musu yawa tasakammai wani mischevious smile, jiyai kamar yarungumota
ajikinsa, amma babu halin haka.
"Kayi hak'uri ka tafi"
Babu halin sauraranka anan.
Badan yasoba yajuya yatafi. Yana mai farin cikin yau Queen of Heart inshi tamasa magana.
*Didi_Aneesa*í ¼í½¼í ¼í½‰
Anisadidi.pun.bz
[2/18, 10:47 AM] +234 703 962 5239: 11/11, 3:47PM Didisco
♡ *DUTSEN CIKIN RUWA.....* ♡
*Na*
*Haleema G Khaleel*
2⃣9⃣-3⃣0⃣
Dawowarta kenan tazo wucewa ta k'ofar part in Babansu, Alh yayo kiranta dayaga wucewarta,
Sallama taimasa tarusuna tagaidashi cikin ladabi da girmamawa daya kamata duk wani 'da
nagari yayiwa Iyayensa.
Suka gaisa ha'de da raha kamar ba 'diyarsaba. Dan yana tsananin san Naja'atu sabida
biyayyarta agaresh da hak'urinta.
Naja'atu yakira sunanta. Kiyi hak'uri namiki laifi, "Subhanallah" Baba dan Allah kadena fa'din
haka, kana da damar dazaka bani kowana umarnine nabi, in dai ba sa6awa mahalicci neba,
matuk'ar inaso inga Haske a rayuwata.
Alhamdulillah! Alh yace "Abinda yasa kenan banji 'dar ba na amshi ku'dinsu nasan
bazakiban kunya ba".
Amma dole innemi amincewarki inkin yadda Alhamdulillah. Inkuma bakyasanshi, se amaida
musu da ku'dinsu. Yace "kin amince naja'atu koba kyaso?
Sunkuyar dakai tayi ta'dan saki gajeren murmushi, abinka da manya kuma dama
*(```Amincewar Budurwa shine Shurunta, Bazawara kuma Maganarta```)*.
Alhamdulillah Alh yace, "Allah yayi miki albarka yasa alkairy arayuwarki yasa kigama lafiya".
Ameen Baba. Yayiy yimata nasiha ha'de da yaba Nagartar yaron. Yauwa tashi kije, kituran Innar
taki. To Baba nagode.
Sanyi taji zuciyarta tana mata, dukda dai ba sansa takeba, amma zatai ta addu'ar neman za6in
Allah tai sallama tashiga 'dakin Innar.
Inna Baba yana kiranki, har kindawo, ah daka gurin baban nake to ina zuwa, tanufi 'dakin Alh.
Zamatai da nufin tahuta, kafin lokacin Sallah yayi, wayarta tashiga k'arar *Antudd kilani
Rabbil janna...*, kaman bazata 'dagaba taji da'din kwanciyar datai, mik'a hannu tai tajanyo
jakarta, wayan tazaro tai Reciev batare da ta duba wayeba.
Nannauyar ajiyar zuciya taji a kunnanta, "Amincin Allah yatabbata agareki Sanyin idaniya
tauraruwa mai haske acikin taurari"
Tare dakai amma dukni ka'dai wanna kirarin, tasamu kanta da fa'da. "Aikinfi hakama words
can express how spcl you are" murmushi tayi, tamasa godia, balaife ta 'dan saki jiki sukai hira,
dukda rabi hirannasu akan karatune.
Seda zasi hang up yace dole tai fixing date da time dazaizo har gida, kunya ta lullu6eta
kaman yana ganinta. Wai yau aganta da namiji tana zance a gida yazatai? "Kinyi shiru kobaki
so nazo? A a kawai dai kaban time zan fiddama randa zakazo, "ok tom no prob amma fa kada
ki waladdani". Allah bazan wahalar kaba, but sekamin uzri kaga sch yanzu ta'dau zafi last semester innan.
"Hakane kada kidamu, kita Addu'a dai akuma dage, Allah yabaku sa'a".
Ameen nagode Allah yai jagora yace Ameen sukai hang up wayan yanata farinciki. Hadda
```Sujudu shshukur/sujjadar godia```. Dan tsantsan farincikim daya samu kanshi aciki.
Seda yai sallah Isha sannan yashiga gidan, Yanata bu'da hak'ora, Ah A "ko tallan maclean
kafarane?" Maman tasu tace tana k'aremai kallo, kokuma Aikinne yasamu?
Adai tayamu da Addua Mama komai yakusa kammaluwa in Allah yayarda, "Allah ya yarda
yatabbatar da alkairy, ai haka akeso.
Jiyai yana jin nauyinta, be iya gayamata komaiba akan Naja'atun 'daukar Abincinsa yai kawai
yanufi 'dakinsa.
Shirin Duniya tumbin giya takeji agidan Radio, tana zaune akan sallaya gefanta kayan
karatuntane, Tirrrrr taji 'yar Nokia tata tayi, message ne ya shigo.
"Nasamu kaina dajin kunyar Mama, nakasa gayamata komi dangane dake, dukda a 'dokance
take taji harma gani daka kyakykyawar Surukartata."
Tamaidamasa da
"Hmm topha inni cema ai bazan iya gayaba."
"Kema kenan dannasan bakece 'diya tafarkoba?"
"Marabarmu dasu sutafara haifa amma dani ake kunyan 'yar farin hmm.".
"Hakane amma kinsan ya za ai?
"Ah ah saika fa'da"
"Kawai zangayawa Matata wato uwargidanki ta fa'da mata."
"Mata kuma??