Showing 18001 words to 21000 words out of 32509 words

Chapter 7 - DUTSEN CIKIN RUWA Part 1 Complete Hausa Novels by Haleema G Khaleel.pdf

kallon junansu ta madubin.
"Queen Tunanin mekike kina tare dani? Idan muna tare bakida sauran damuwa a
rayuwanki. Am always there for you. *Ina tare dake*(Meemee bea ta) cikin kowana yanayi
*Komai Rintsi*(Hama Gee). Kikasace dani kowana hali samu da rashi, cuta da lafiya yafad'a
yana k'ara rungumota kaman za a k'wace masa ita.
"Hannayenta duka tasa tana shafo kansa, tahau rattabomai tsadaddun kalamai "kazama ni
nazama kai mijina komai inzanyi dole saidakai. A kullum ina godiya ga Allah daya bani kai mai
hak'uri da kawaici mijina takuma narkewa ajikinsa. Sund'au lokaci suna kallan junansu kowa na
Sakar zuci sukasa dariya gaba d'ayansu yabata kiss a fore head inta, dak'yar yabari ta d'aura
d'ankwalin suka fito dansuyi break fast.
Agurguje yaci abincin, shima saida tai kaman zata masa kuka yazauna dakanta tabashi Oat
ne yaji madara da Omylet, tanad'e mai Pan cake a foil da ginger drink aroba yatafi dasu. Dan
idan yai irin fitar wurinnan baya dawowa da wuri, takanyi k'ok'arin yimai dabarun dabazai sa yaji
yunwa dawuriba. Tinda ba abincin ko ina yake ciba.
"A ranar ma kuwa se yamma yada gidan. Tana zaune itakad'ai se Radio data kunna, wak'an
Nayi gamo ake tana tabin wak'ar dan tana santa(Miss zo6o�) kawai ganin mutum tai jitai anyi
sama da ita tai saurin rintse ido, yai juyi sosai sannan ya ajeta. Neman kujera tai tai saurin
zama gudun fad'uwa, seda ta maida numfashi ta iya cemai sannu da zuwa, kusada k'afarta
yazauna yana "Addu'ar dakuke min a kullum ta k'ar6u anza6eni cikin wanda akai sponsoring
inmu miyi masters a sch in damuka baro, dan haka kihau shiri dake za atafi. Dirowa kansa tai
tarungumeshi tanata murna itama, jin bakinsa tai cikin nata tin tana tirjewa harta soma
maidamai da martani ganin yana neman zarcewa yasata janye jikinta tai gefe sunata ajiye
nannauyan numfashi.

"Ruwa takamai yasha suk'a k'arasa maganar nanda wata biyu zasu tafi, kannan itama zata
zaga dangi har gida zata tinda yau wata4 da zuwanta gidan bataje gidaba. Shiko yajajje
gaidasu. Kafin magriba yatafi gida yagayawa Mamansu da Abbansu. Suji zancen suma. Sula
kuwa samai Albarka dafatan samun Nasara arayuwarsu gaba d'aya.

*Bayan Wata biyu*

"Kafin lokacin seda tazazzaga dangi, dasukaje gida kuwa Inna kamar tacinyeta dan farin ciki
ganin yadda 'yarta takuma cika da murjewa fata se shek'i take alamun hutu da kwanciyar
hankali. Tawuni cir agida har mak'ota tazazzagaya.
Gidan Yayarsa Yusra ma takar6esu hannu biyu-biyu sukai ta hira kamar sun saba. Tahado
mata abubuwa dangin kayan k'amshi tinda su take siyarwa.

"Daga getso suka ziyarci dangin mahaifinta, yacikasu da shatara ta arzik'i wanda basu
sanshibama duk suka ganshi. Gusau suka wuce kwanansu biyu Anty husna kam tafi kowa farin
cikin zuwansu. Tak'ara mata dabaru da sirrika irin na Mata masu aji.

"Seda sukai kwana biyar dadawowa daga Gusau sukai shirin tafiya Dabinai. Suka k'ara kwanaki
acan yadda dasunda se shirin tafiya. Taga karamci da mutuntaka irinnasu, taita godewa Allah
daya had'ata da miji da danginsa masu so da k'aunarta da mutuntata. Tsaraba iri daban2 suka
had'o su dashi taita kunya ganin ita bawani abun azo agani takai musuba. Turaruka sai
k'ananun turamen atamfofi takai aka rarraba. Sukai ta farinciki dasa Albarka.

"Tun ana sauran kwana5 sutafi kayansu sukai gaba a motar haya, se d'an abunda ba a rasaba,
sunata shirin tafiya. Agidansu Usman ne Mama taita musu Nasiha musamman ma shi tinda ita
bak'on guri zata shi bayau yafara zuwaba. Tajamai kunne yarik'e mata 'yarta Amana. Yaita
dariya yana "ya kar6a to shi wazai rik'eshi? Allah mana inji Maman sukaita abunsu. Itadai Naja
kanta a sunkuye. Tana k'ara san sirikar tata da irin d'abi'unta.

"Dayawa daga cikin dangi sunmusu rakiya, haka sauran likitocin da aka za6esu suma yawanci
'yan uwa sun musu rakiya. Akaita sallama da 'yan uwa da abokan arzuk'a. Se alokacin jikinta
yai sanyi. Dan tasam zatai kewar gida da dangi gaba d'aya. Taita Addu'ar Allah yahad'ata da
abokan zama nagari. Hawaye kawai yagani a fuskarta. Yasa handkchf yasharemata tareda
kamo hannunta suka shiga jirgi, tak'ara narkewa ajikinshi tana kewar ahalinsu.


Kowa yabar gida.... Gida yabarshi inji hausa people..!!

Semuce asauka lafiya!
Team Naja'atu suna rakiya..�


Am realy sory makaranta. Zaku naji yanzu in sha Allah akai akai. Tnx 4 ur luv and prays. Luv u
all��


© *Aneesa_Didi*🍼🍉�

[2/18, 10:49 AM] +234 703 962 5239: {5/12, 9:35AM} Didin_Anee�
♡ *DUTSEN CIKIN RUWA.....*♡
*Na*
*Haleema G Khaleel*


*51-55*



``` EDO STATE```

Saukarsu keda wuya babbar mota lexirius ta makarantar ita tazo d'aukansu, takwashesu
dukansu masu mata da singles in d'alibai.
To tun amota Naja'atu ta lura da wani abokin karatun su Usman d'in ya kafeta da ido duk
wani motsin dazatai a idansa yake koya ta d'ago ido sesun had'a ido dashi. Har aka saukesu a
Staff Quaters, yawancin masu Aure 2 room apartment aka basu, sukuma marasa matan wasu
suna Hostel wasu kuma su 4 gida d'aya aka basu.
"Gida ne matsakaici, babban falone da toilet ahad'e mai d'auke da d'akunan bacci kowanne da
band'aki aciki, kitchen matsakaici se varenda.
Tinda suka sauka agidan ruwa kawai ta iya sha suka hau gyara ko ina, sauran kayansu
ta aje kowanne a inda yadace. Ruwan wanka tahad'a masa yayi, itama tashiga tai.

"Ranar dai bai barta tayi girkiba. Darana abubuwan dasuka taho dashi sukaci da yammaci kuma
yayo musu take away.

"Rayuwarsu a garin tai musu dad'i, rayuwa suke cike da so da kulawa ga junansu. Baya ta6ayin
nesa da ita saidai in makaranta yashiga ko Teaching Hospital in da aka turasu. Dayawa
mak'otan datayi ba hausawa bane, ita da Fatima matar abokin Usman d'ince sune kad'ai
Hausawa itama ganin yadda Fatyn take fiffik'a da d'aga kai yasa tarage shiga sabgarta.
Yawanci in yafuta gidan Maman Benue take shiga sita hirarsu takoyamata abubuwa dayawa irin
na yaransu da abincikansu. Ba bak'inciki ko hassada zama suke na amana da mutunta juna.
Kafin itama yanemarmata gurbi ta d'ora karatunta a Jami'ar tasu. Matsalarta guda ta wani
abokin karatunsa maisuna Salis amma amfi kiransa da Baby. Yadda ko kallanta yakeyi seyai
wani k'asa da idanu kamar d'an maye.

"Sallar walha ta idar tanata addu'a yau batajin fitar ma, bugun k'ofa take taji, tinaninta Usman ne
to amma in shine a yanada key bud'ewa kawai zai inya k'wank'wasa sau d'aya, bata cire hijabin
jilkinta tai hanyar k'ofar ko mak'otane. Salis(Baby) tagani yabita da Shu'umin kallansa, yace
"Minyi waya da Usee in yanzu zai dawo yace najirashi" Jin haka yasa tabashi hanya yawuce, kamar wani gidansa yazauna a inda suke zama
tareda d'ora k'afa d'aya kan d'aya yana chanja tasoshi, sa6anin da datakai saudi Qur'an tana

sauraran K'ira'a, tinda taji yace Habibintane yace yajira shi, kitchen tashiga takamai dambun
naman datai jiya tahad'o da lemu, ruwa da cup a tray. Ganin ta ajemai yasakar mata murmushi
tareda cewa "godiya nake Sarauniya. Itadai jitai wani banbarakwai wai sarauniya. Saurin
d'auke tunanin maganar tai aranta.
"Tin wajen 11:30 yazo gidan, tanata 'yan aikace-aikacenta, dukda a d'ar-d'ar take dan basan
zamansa takeba. Kitchen ta shiga ta d'ora girki Tuwan Semovita tai da Miyan Kuka tabirge kaza
aciki, tuwan kuwa ta mulmuleshi a leda tasa a warmers. Kafin biyu ta kammala tashiga wanka.
Ta had'o da alwala seda tashirya cikin riga da skirt na atamfa tai sallah, tana cikin d'aura
dankwali taji sallamarshi, kafin tafito har Usman ya shiga toilet, tai sauri ta kammala kintsawa
cikin sassauk'ar kwalliyarta tad'ora babban mayafi akan kayan.
Kafin yafito tafito mai da k'ananun kayan dazai chanja. Tak'ara tattare d'akin tai kitchen.

"Babbar leda da ake cin abinci akai ta shimfid'a tajere wermers guda biyu na Tuwo dana Miya
ga roban manshanu da yajin daudawa agefe, tasamusu plates masu zirfi biyu da cokula ga
roban wanke hannu agefe komi dazasu buk'ata ta ajiye. Usman Yana fitowa kuwa suka hau cin
abinci. Salis(Baby) yanata zuba surutu Usman sede yai murmushi ko "Ah, A'A" danba
d'abi'arshi ceba magana inyana cin abinci. Naja'atu tana gefe taji yak'ara bata haushi kaman ta
bubbugeshi kawai sotake yatafi amma ba alama.

A kwanakin da suka biyo baya Salis(Baby) yamaida gidan gurin zuwansa inbezo daranaba zezo
da dare tinda dasafe suna asibiti ko makaranta. Ko Usman d'in nanan kobayanan haka zaizo.
Yabi yashiga jikin Usman sose komai tare suke. Abun yafara damunta tarasa yazatai da lamari
irinnasa. Rufe k'ofa tafarayi, koyazo tanaji bazata bud'eba, hakan kuwa ba k'aramin rigima yasa
sukayiba. Ranar tasha mamakin Usman din akan wani aboki zenemi yatada musu da hankali.
Yak'ara jaddada mata indai yazo ta bud'e masa ai arzik'i nema anuna anayi dakai.
'Yar rama tafara dalilin sa damuwa datai aranta. Ganin zata jawa kanta ciwo yasata cire
komai daka ranta ta fauwalawa Allah lamuranta da duk wata damuwarta. Allah yabayyana
gaskiya kowa yaganta.

"Fuskarta d'auke da farin ciki tagama waya da Mamansu Usman takira Innarsu, bayan sun
gaisa take sanarmata da kud'in auren su Samiha za a kawo, dan babansu yace duk aure zai
musu kowacce tacigaba da karatunta a d'akin mijinta, murna kaman tarufe ido taganta agaban
Innar tasa albarka suka gaggaisa da 'yan k'annanta tai hanging wayan. Gama wayanta keda wuya Maman Benua tashigo. Ganinta yasata fad'in "kinji shiru ko
mama(wani lokacin haka take kiranta tunda tagirmemata) kika biyo bayana, ainace nadena
zuwa tunda bakyasan shigowa. Maman benua kuwa cikin rikitacciyar hausarta tace "baniso
nazo mijinka yadawo yaganni nahanaku sakewa bare masoya irinku "to mezaimiki kai Mama
made yanzude mekika kamun? Sukai tahira abunsu secan tatafi nata 6angaren.


*Six Month letter*

Seda sukai rabin shekara sukaje ganin gida, Naja semunna take dantayi kewarsu bakad'anba.
Nagaya miki ba inda zaki ga gidanki shima yana buk'atarki, kawai de ko ina kyaje ki wunan
musu. Turo baki tai had'e da muryar shagwa6a tana "haba nawan dan Allah ko kwana biyu
kabarni nayi yaushe rabona dasu.
Nafa gama magana nagaya miki yaja bargo yakwanta. Itama kwantawa tai tajuya baya sa6anin
da dasetajita manne ajikinshi suke bacci, sabo dolenta tajingina dashi tahau baccin.

"Duk inda yadace seda sukaje, cikin sati biyu damin sati uku zasiyi, duk tabi takasa gane kanta,
barin hakan tai dalilin zaman dabasayi.
Randa taje gidansu kuwa Inna duk tagano komai dake tattare da 'yartata, tak'ara cika da
murjewa abin gwanin birgewa taita k'ara addu'a aranta. Naja kuwa sawatai akai mata
d'anbagalaje taitaci kamar an aikota. tofi azam-zam innar taimata tasha, haka taitayi tana
aikamata kansutafi. Dazasu koma kuwa taimata tofin dayawa tahad'a mata da kayan kad'i yaji K'uli-k'uli har
garin rogo seda tahad'a mata. Amota kuwa warin fetur yahau kanta taita kwara amai.
Agalabaice dai suka dawo seda ya d'aura mata drip tada hayyacinta.

"Wani abu data futo dashi kuma cin k'uli-k'uli, taitace wataranma hadda lemu take had'awa.
Idantasa daru dolensa yanemo ko a inane, ganin haka yasashi d'aukar jininta yaje lab in cikin
sch dashi bayan yayi Spinig in Blood in yai Pragnency test, anan yaga positive result. Godiya ga
Allah yafarayi, no wonder abubuwan da Queen keyi kaman shigan ciki ashe shid'inne. Lallai
ubangiji yanasanshi tinda yaza6eshi cikin wan'yanda zasiga k'wansu a duniya. Yak'ara godewa
Allah. Jiyai soyayyar Naja'atu da abinda ke cikinta tunkanma yaga meza a haifa tak'aru. Bejira
komaiba yakoma gida.

"Tana tsaye tana gugan inner wears insa, jitai an d'agata juuu anjuyata, abinka dame jiri jitai
tana neman fad'uwa, saurin tarota yai a jikinsh taruntse ido tareda k'ara k'ankameshi tanasake
saka kanta ajikinsa.

"Kujera ya ajiyeta, yasamo ruwa yabata tasha.seda ta da nutsuwarta yatambayeta meke
damunta?
"Itadai ba abinda kedamunta se nauyin da jikinta yayi, kuma taita kwad'ayi wasu lokatan,
tace tana yamutse fuska.

"Lakuce mata hanci yai yace to k'aruwa muka samu. Babynane acikinki shike saki komi kikeji.
Aibata bari yak'arasaba ta sadda kanta jikinshi cike da kunya. Add'ua yaita mata yana
gaggayamata abubuwan dazata kiyaye da irin wanda zatana ci. Sekuma zuwa asibiti yakuma
dubata acan.

"Naja'atu tak'ara kyau takuma murjewa abinka dame matashin ciki.
Zaune take tanacin Teba da miyar Ogun da Maman Benua taka mata. Tanaci d'an tsamin
teban namata dad'i, har wani lumshe idanu take. Daka ita sai wando three quater iya gwiya
yamatseta da 'yar ficilar rigarta me fad'i cikinta d'an wata hud'u yataso sosai kaman wata

takwas. Jitai kawai anbud'e k'ofan, tajuya ma k'ofan baya. Tasande bame shigowa se Usman,
maidakai tai tacigaba dacin abincinta.
Hannu kawai taga ansaka a kwanon. Yadda kuwa takeji dad'in abincin kowaye bazata
bashi yaciba. Janye kwanan tayi tace gaskiya Habeeb bazakaciba a shagwa6ance tai maganar.
Haba Sarauniya nid'in?
Jin haka yasata dubansa dan bahaka yasaba gayamata ba.

"Caraf idanunta cikin nashi, Innalillahi kawai tahau ambata cikin razani tanemi tashi amma
takasa dan suman zaune tayi...

Nima zaro idanu nai👀 nai duba garesu duka!!!


Kubiyo didi. Danjin yazata kaya!


© *Aneesa_Didi*🍼🍉�
[2/18, 10:49 AM] +234 703 962 5239: {12/12, 5:00PM} Didin Anee�
♡ *DUTSEN CIKIN RUWA.....*♡
*Na*
*Haleema G Khaleel*

*56-60*

Zafafan hawaye taji suna bin kuncinta, ita tarasa wannan wace irin rayuwa ce sam mutum
baida sakewa acikin gidan, kawai wani k'ato yashigo batare da ambashi iziniba, kome gidan
aiyana nuna alamun dawowarshi bare wani daban.

Tana daka zaune take jada baya, ganin haka yasashi mik'ewa.
Batasan sanda tafara gaya masa maganganu marasa dad'i ba. Ta inda tashiga batanan
take fita ba. Tanayi tana kuka. Fita kawai yayi batareda yace komaiba.

Ranar kasa gane kanta Usman yayi, daya matsa mata da magana tasa mai kuka, badan
yasoba ya hak'ura da tambayarta yajanyota jikinsa yana shafar bayanta.

To cikin kwanakin sam yakasa fahimtarta, abincima dak'yar takeci duk tabi ta ruruce masa
banda ramar datayi se tulin ciki datake fama dashi fuskarta tai fayau. Hawaye kawai taga
yanabin kuncinsa ad'an firgice ta d'ago tana kallansa, yahau fad'in "Queen yakikeso nayi? Nayi
nayi kifad'amin damuwarki kink'ki, ko gida kikeso namaidaki? "Ah ah" tace tana girgiza kai "to mikikeso kowani abun namiki plss Queen kifad'amin.
Banasan duk wani abu dazai takura rayuwarki akullum banida addu'ar data wuce murayu cikin
aminci da k'aunar junanmu da tattali har tudun tsira. Yaita gayamata kalamai masu shigarai da
kwantar da hankali.

Hawaye tashare yabata tausayi bakad'anba, tashiga yimasa bayani duk irin abubuwan da
Salis(Baby) yake mata tun randa suka zo garin har k'arshen zuwansa gidan. Yadad'e yana
jimamin abun idanunsa sukai jajir yana fidda wani gauran numfashi, ya hasala sosai, ganin yai
haka tashiga bashi baki. Har zuciyarsa ta sauka. Abinka da mata da miji sai Allah (Maganar
gaskiyace) suka shirya kansu kamar ba abinda yadamesu.

Washegari tun safe yatafi da ita asibitinsu. Inda yake kaita Antinatal. Sabida complain in datai
na nauyin jikin datakeji dole aka mata Scanning. Murmushi kawai yake dayaga hoton 'ya'ya
kwance acikin mahaifarta dakoni Didi bebarni nagano muku guda nawa bane. yaita tasbihi da
godiya ga Allah. Ranar kaman yamaidata ciki. Ko suraba cikin yakeji. Seda yakaita gida danufin
zeda dayamma sud'an zagaya. Tana shiga kayan jikinta tarage ta watsa ruwa tazauna daka ita
sawata riga iya gwiwa me fad'i. Bacci tahauyi harseda yunwa tatasheta. Sallah tai tashiga
kitchen.

Tana tsaka da jajjaga attaruhu yashigo gidan, kai tsaye yayo kitchen in jin k'amshi yacika gidan.
Da sallamarsa yace "Queen mikike dafama unborn babys ina kuma?
" Babys kuma? Tafad'a tana kallansa.
Bagarar da zancen yayi yahau bud'e tukunya.
Karka k'one Habibi Taliya nake dafawa me daudawa, murmushi yayi baice komaiba yak'arasa
mata jajjagen yayankamata albasa harta kammala suka gyara gurun. D'aki yanufa dan yawatsa
ruwa. Itakuwa kafin yafito tabaje ak'asan carfet tahaucin abincin kaman tashige kwanon.
Futowa yai kawaiy gani yai tanata zuba loma duk ta had'a zufa, fanka yayo saitinta da ita
yazauna tareda nad'e k'afafu, sa6anin itada ta ware k'afafu cokali yagani agefe dawani plate in.
Bismillah yayi yahaucin abincin adaddafe yai spoon biyar yakur6i lemon dake gefe. Ita kuwa
seda taji dam cikinta ya d'auka taja gefe, kallanta yake kawai cike da tausayi dan duk tafara
kunbura tunkamin cikin yatsufa ma kenan inaga yatsufa. Dakansa yad'auke kwanunkan
yamaida kitchen. Yazauna sukaita hira abunsu.

Wajajen bayan la'asar suka fita, sun d'anyi nisa damakarantar ganin tafara gajiya
yasamammusu taxi. Kasuwa yakaita taga abubuwa iri-iri na al'adun yaroba da Igbo awani
6angaren kuma hausawa ne. Siyayya yamata sosai mother care haka kayan baby komai setaga
ba guda yad'aukaba itadai binsa kawai take ta idanu inya d'au wani abun seya saka ajikin
cikinta itadai sede tai murmushi takalleshi kawai. Kaya fall suka siya. Wani gurin hutawa yabiya
da ita tasha kayan sanyi. Tayi enjoying futar sosai, ranar ko girkin dare bataiba da gajiya
dakansa yamata wanka yasa mata rigar baccinta me fad'i dan yanzu sutafi sawa dan tafi
sakewa cikinsu. Komi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login