Showing 15001 words to 18000 words out of 32509 words
Chapter 6 - DUTSEN CIKIN RUWA Part 1 Complete Hausa Novels by Haleema G Khaleel.pdf
"Cin lokacin duk tabi tarame ga ciwan Inna yatashi jikin ya matsa mata, hakan yak'ara
sanyayarwa da Naja'atu jiki.
"Duk dare kafin su kwanta bacci se Innar tai amfani da wanna damar taita musu nasiha gameda
rayuwa. Tak'ara had'awa da bata makamai na addu'a yadda zata bi da arun dazasu taimaketa a
sabuwar rayuwar dazata shiga.
"Ba abinda takeyi se kuka dazarar Innar tafara, gani take kaman wasiyya Innar take basu.
"To ganin Innar tafara warwarewa yasa hankalin Naja'atu kwantawa tad'an fara walwala har
take samun damar karanta wasu daka cikin littattafan da Innar tabata:
*ZINAREN MA'AURATA*(MY ANEE)
*WASIYYATUL-UMMI*
*ZAMANTAKEWAR MA'AURATA*(DIDIN-ANEE)
Dawasu sauran littattafai dasuka shafi Rayuwar Aure da Tarbiyar Yara a Musulunci. Uwa tagari
kenan.
"Gyaran jiki da akema Amarya kuwa Innar ce da kanta take mata tun tana jin nauyi har tasaki
jiki take gyara 'yarta duk abinda yadace takemata.
Ana cikin turareta da Dukhan Usman yabugo mata waya, gata a lullu6e badaman
d'aga wayan, dole samiha ta d'aga tasa mata a kunne, wata sassanyar dariya tasaki, meya
gaya mata tace "nide baruwana a shagwa6ance, tama manta da Inna tana gurin, "mezan
fad'ama to? Usman yace kina ina yanzu?
"Ina gida Allah yasa lafiya? Naja'atu tafadi.
"Yace to mekikeyi, kinmaci abinci kuwa?
"Naci mana mikagan?
"Nikam kinganni dangatan Mamata gyara miki ni take tayi. Tahad'an wani abu mai dad'i konazo
nakamaki?
"La la! nids banceba baruwana. Hhhhhh
"Kinji ai ke kita kunya abundama kinkusa zama tawa, itadai shiru tamai yanatayi. Da abun ya
ishetane tace ana kiranta.
Bawani kiranki da ake zaki kashen waya dai? Usman yafad'a yana murmushi abinsa.
Kinga nama san komi ai da akeyi inma kin 6oyen. Sema na fad'o miki basu .......
"Ai bata yadda yakai k'arshen zancenba takashe wayan tanata murmusawa. Inna kuwa tabita
da kallo tana me addu'ar Allah yasa Farincikinsu yad'ore a zaman dazasiyi.
Sunkuyar da kanta tayi ganin irin kallon da Innar kebinta dashi.
"Hada-hadar biki ta kankama, danma Amaryar tace it ba bidi'ar daza ai. Komi bisa tafarki za
ayishi.
Ana saura kwana uku afara biki dangi na nesa suka fara zuwa mutan getso da Gusauma
ba abarsu abayaba. Anty husna itada Ummi farin zuwa, suka cigaba da shirye,shiryen biki. Ita
dai Amarya duk tak'ara sanyayewa abincima se Inna ta matsa mata takeci, setakoma dama
Kunun Alkama da Madara. Dukdan kada tai rama dayawa. Bayan daffaffiyar Madarar shanu
safe da yamma, tun bata iya shanyewa harta hak'ura shiyasa jikinta yai lumi, fatarta tak'ara
santsi da taushi. Se shek'i take irin na Amaren da suka sha gyara.
"Ana i jibi d'aurin auren laraba dasassafe suka tafi k'unshi k'awatenta biyu Sady da Hafsa dan
Nafisa a lokacin tayi nauyi. Juwairiyya Samiha harda Anty Husna suka tafi. Sun babbaje anata
hira agidan lallen itakuwa seda taga anfara mata Jan lalle jikinta yakuma mutuwa ya tabbata
takusa barin Inna da 'yan k'annanta jita hawaye masu d'umi sunabin kuncinta. Ganin haka itama
Samiha tafara hawayen, Anty Husna kuwa mezatai inba dariyaba.
Tahau yimada fad'an ai Aure shine DARAJAR MACE. Kumashi Katangane babu wani
mahaluk'i dazai kamiki wargi matuk'ar girman nan ya hauki, Rigar mutunci tamiki lullu6i duk inda
kika samu kanki za abaki girma da MARTABARKI(Ummi-Aishha) ta D'IYA MACE(Khadija Sidi).
Taita mata ita kuwa tak'ara rushewa da kuka. Sauran kuwa sukai ta tsokanarta. " ```Ke kikacw
kinaso Amarya dabaki so da ba abaki shiba``` sukaitayi suna dariya.
"Meyi mata k'unshi kuwa dakatawa tai, tanata ganin ikon Allah. Wannan shagwa6a ta Amarya
har ina.lalla6ata sukai tai shiru akagama mata lallen sannan suma akayiyyi musu.
"Bayan la'asar suka dawo mutane dayawa sun zazzo anata aikace-aikace, shigowarsu tasa aka
kaure da hayaniya masu gud'a nayi abokanan wasanta suna tsokananta, kowa da abinda zaice
aikuwa meneman kuka anjefishi da kashin awaki(inji hausawa) aikuwa tasa kuka. Seda wata
k'anwar Babansu tazo tajanyeta, suka k'yeleta.
"Alhamis akaimata kamu irin na Al'ada, dayamma kuwa Walima akashirya Matan aure zallah se
Ango da abokanansa. Kuzo kutayani ganin Amarya cikin shiga ta alfarma wata had'dd'iyar gown
ce ajikinta gold colour da veil inta and'ora shi akan Top Knot inda akaimata jikinta rufe ruff light
make-up aka mata ba k'aramin kyau taiba. Malam Auwal Muhamnad da Malam Nazifi sunyi fad'akarwa sosai akan Aure. Da matakan
daza subi subi su mallake junansu. Ba Boka ba Malam musamman ga ita Amarya da sauran
mata. Walima cikim tsari ba hayaniya akai lectures sosai kan Addini. Kafin magriba akai addu'o i
da neman Albarka acikin Auren. Akatashi itade Amarya Murmushi kawai take. Sunda gida taga se had'a mata kayanta ake jikinta yak'ara mutuwa kamar anzare mata
laka.
Ranar jumu'a Takama 24 ga watan 10 dubban jama'a suka shaida d'aurin Auren *USMAN
BELLO GALADIMA* da Matarshi *NAJA'ATU ABDUL-MU'IZ AUWAL* bayan Sallar Jumu'a bisa
rangwamen sadaki.
"Yinin biki aka zarce dayi bayan angwaye sunzo gaisuwar dangi akayiyyi hotuna. Amarya
masha Allah kamar kasace ka gudu. Nikaina Didi ba k'aramin burgeni Amarya dashi kansa bikin
yaiba. Lek'e nake tayi chan na hango su Haleema da Maman Ansar ansha anko. Sukuwa su
Ukty yadda zasu Amshi take away suke. Nakallesu nace daga Take kuma se Away mukasa
dariya dukanmu.
"Kuka take kaman ranta zai fice, anata shiryata wankanma dak'yar tayi.wankan turaruka Anty
Husna da yar Babansu suka mata nakaima dabanne Aka nad'eta da yalwataccen Mayafi, gurin
Babansu aka kaita yaimata iya tashi Nasihar yahad'a mata da Al-Qur'an charbi da babbar
Dadduma, shima jiyake kaman yasa kukan. Zagayawa da ita akai gurin sauran matan gidan suma sukasa Albarkacin bakinsu. Masu
yada maganganu nayi kowa da abinda yadameshi.
"Itadai Inna k'arfin hali kawai take, "Allah yasa kishiga a sa'a abinda ta iya furtawa kenan. Tai
musu alamada hannu aka wuce da Amarya. Deedat ya k'ank'ameta shi bazata tafi tabashahiba
dayawa cikin mutan gurin saida sukai k'walla. Aka tafi da Amarya gidanta dake Sharad'a. Gidan
ya k'ayatar da mutane danba k'aramin dukiya dangi suka narka mataba. Kowa yataho akabar ta
daga ita sai halinta.
Semuce Allah ka d'anbaba mai k'uli-k'uli
Am so sry makaranta Abubuwan dayawa shiyasa baku ganin postn akai2. Inkomi ya gyaru
zakunajina koda yaushe inasanku nima aduk inda kuke. Allah bar zuminci da k'aunar juna
Luv u all
© *Aneesa_Didi*í ¼í½¼í ¼í½‰
[2/18, 10:48 AM] +234 703 962 5239: [25/11, 2:50PM] Didin Anee
♡ *DUTSEN CIKIN RUWA.....*♡
*Na*
*Haleema G Khaleel*
*41-45*
Abokanan Ango sukayo masa rakiya suka wuce bayan sunyi Addu'o i danemanmusu farinciki
dazama lafiya mai d'orewa. Suka d'anyi ciye-ciyensu itadai akunyace tasha Ruwa shima danya
matsamata ne.
Usman ya Umarci Naja'atu data sake alwala, cikin toilet in d'akin tai Alwala. Sallar isha
suka fara sannan suka d'ora da nafila yai musu Addu'a mai tsaho sannan yai mata tambayoyi
gameda Addini, yak'ara mata haske har Wankan Janaba yakuma mata bayani dayadda take
samuwa. Kanta a sunkuye yake tamata bayani, wani tai magana wani tai shiru.
"Hannunta duka yakama, yajanyota jikinshi janye mayafin duka yayi yarungumeta tsam ajikinsa,
dukda hakan bak'on abune agurinta jinta tai she is safe, zippin rigarta yasoma yana kuma cusa
kanshi ajikinta cikin wani salo na soyayya dabata ta6a tunanin haka abin yakeba, nikam danaga
lamarin yajuye abin yafi k'arfin ganina. Najuya nabasu guri. Kunsandai bakyau bincike balle su wannan daya zama sirrinsu. Asuba tagari couples.
"Wayewar asabar, komi shiyayi mata, Addu'a kuwa tashata ba adadi takuma narkewa soyayya
yake gwada mata wadda ba algus acikinta. Har sukai karin kumallan safe. nok'ewar da takene
adan fusace yace "ai aikin gama yagama, abunda take kunyanma yagani tomiyai saura? Itadai
murmushi kawai take tana k'ara sunkuyar dakai. Kujerar da take kai yadawo ganin ta mik'e
yasashi janyota tafad'a kanshi. K'ok'arin zamewa take yak'ara k'ankamota.
Zauna ma kiji abinda zaki fara ma shine indai ina gida bakida gurin zama daya wuce nan,
yanuna mata jikinshi. Kinsan body contact yanada tasiri wurin shak'uwa da mararin juna ga
ma'aurata.
"Bugun k'ofar da akeyine yadakatar dasu, saurin mik'ewa tai daka jikinshi tayafa mayafi akan
kayanta tanufi k'ofa danta bud'e, Abdullah ne da Shukra k'annan Usman mama ta aiko suka
mata abincin Rana.
Guri tabasu suka shiga falon gaisar da Yayan nasu sukai, itama suka gaidata tacikasu da
kayan mak'ulashe. Shukra Autar mama dasaurin sabo duk inda Najan tayi tana biye da ita. Har
Usman ke tsokanarta tayi 'yar zaman d'aki, murmushi tai tace " aikam danaji dad'i daza abarta
ta zauna. Hararar wasa yabita da ita tareda fad'in "bakowa ma kink'i sakin jiki musha Luv inmu bare anka
miki wannan mai surutun. Tace " aida Mama zata ban ita danaji dad'i.
"Hmm! Bakisan yadda Mama da Shukra suke bane bame rabasu se makarantar data shiga
amma da ko ina suna tare, har yanzunma. Bata yadda tazauna agidan kowa se Mama. Dakwai
sanda mama suka tafi Dabinai aka kaisu gidan Sisto, har yamma basu dawoba data fara kuka,
kowa seda yaji haushinta Sadiq da Anas sukai zamansu harsun kwanta amma Shukra seda
akada da ita gida k'arfe 10 nadare. Tana ganin Mama shiru kikeji.
Wai lallai kuwa naga ranar rabuwarsu da Mama. Allah sarki aikam dolene rabuwar ta fad'a
tana rau-rau da ido.
Laah! Nibance kiman kuka ba kingama natafi. Yafice daka kitchen in yana dariya.
"Bak'i sukai tayi danginsa da nata danma ankakkamata abinci taita zuba musu faranfaran
takar6i jama'ar. Tacikasu da kayan arziki.
Washe garima haka sauran danginsu dabasu tafiba sukazo ganin idan amarya.
"Anty Husna dasu Samiha se yamma suka tafi bayan sun gyaramata ko ina dasauran
kayayyakin ta nagida, takuma ware wasu kayayyakin daza a rarraba harda wasu daka cikin
kayan lefanta. suka turare mata gidan bayan anty Husna tasata tai wanka kwalliya sosai tasa
tayi, dan yanzu bada bace dole sekina gyara ladabi da biyayya sannan zaki mallake mijinki
atafin hannunki. Kud'an bamu guri tace dasu Samiha. Suka fita suna k'us-k'us batasan yaran
zamani wasu sunmafi masu Auren sanin abubuwa ba.
Tacigaba dabata tip da dabarun zama da miji. Da sirrikan dazasu k'aramata Ni'ima batareda tayi
amfani da abunda zasu cutarda itaba wanda batasan dame akaiba.
" *Sirrri na daya*:- kisamu kankana kiyayyanka kisa madara kinasha.
" *Sirri na biyu*:- kisamu zogale ganyansa da cocomber kiyi blending insu sekisa zuma da
madara zakisha mamaki.
" *Sirri na uku*:- kwakwa dabino dankalin,hausa(kadan) farar shinkafa cukwi. Ki markada shiima
kinashan ruwan. Inkinso kuma zaki iyayin na gari kina damawa da madara kinasha.
" *Sirri na Hudu*:-kihadasu gero mazankwaila dabino farar shinkafa kwakwa busasshiya
busasshen muruci kida kasu siyi gari. Seki zuba man habbatussauda kihadesu guri daya.
Yazama gumba.
" *Sirri na biyar*:-Man zaitun Man tafarnuwa Man Habbatussauda Miski kihadesu kina
shafawa/insert.har maganin sanyi yikeyi.
"Taita gayamata abubuwa tana rubutawa wanima intayi harshi zasuna sha kaman inzata dafa
shayi tazuba Minannas da kirfa aciki kunasha tare tsafta dayadda zata tsaftace gida da jikinta
turaren bayan kunne daban nagashi, na matse-matsi cibiya. Shikansa mijin tadinga tsaftaceshi
da kayansa yadda bazai taba zamada daud'a ba balle ajiwani unwanted odour yana tashi daga
jikinsu.
Seda Anty Husna tacikata da abubuwan Alheri sannan suka tafi tanata kewarsu.
"Alwala tai tazauna kan akira sallah tanata lazimi abinta. Alamun bud'a k'ofa taji da sallama
yashigo cikin husky voice insa, sansanyan k'amshin turare yaji yabigi hancinsa wanda bazai
tantance ainayi wasu iri bane. Tun alokacin tafara aiki da hud'bobin Anty Husna.
Tasowa tai zuwa inda yake ganin kaya da ledoji fal a hannunsa tarusuna tamai sannu da
zuwa takar6i kayan hannunsa janyota jikinsa yai yakuma jin wani k'amshi na musamman
natashi. Eye ball to Eye ball suke kallan junansu yana mata wani sassanyan kallo da murmushi
dashi kad'ai yasan ma'anarsu.
"Kinyi kyau yace da ita. Tallafota tai tagefansa suka k'arasa cikin falon, takai kayan inda yadace
shikuma yai Alwala yatafi Masallaci.
"Cikin kwanakin Amarcinsu kawai sukeyi, seda tai sati sannan yakaita gidansu tagaida Mama
da Abbansu. Dabinai kuma seta k'ara kwana biyu zaikaita taga danginsu nacan. Yanata rawar
kai agaban Maman itakuma duk yasa tatakure, Maman bata k'ara ganin rashin kunyaba saida
suka gama abinci tazubamai waishi da Matarsa zaici. Taitamai tsiya kuwa, itadai Naja sai
murmushi kawai take ta duk'ar sa kanta. Da Maman tagaji da shak'iyancin nasa tace itama tatafi
gano nata Mijin. Bak'aramin burgeta sukaiba yadda suke abunsu faran-faran kamar ba
Mahaifiyarshiba. Komansu a kammale ba raini in social life. Taji sunk'ara shiga ranta.
Musamman mijinnata. Habeeb injita da fad'a dukdan karta ambaci sunanshi. Yayi-yayi da ita
amma taki, irin abubuwan dasuke k'aramata Martaba da Daraja agurinsa Allah yai yawa dasu,
banda zazzafar Soyayyar dayake mata wadda bazata misaltuba. Agidan suka wuni se dare
sannan suka tafi tinda bawani nisa garesuba duk Unguwa d'aya ce.
Kubiyo *Didin anee* danjin ya rayuwar Naja'atu zata kasance bayan Aurenta???
© *Aneesa_Didi*í ¼í½¼í ¼í½‰
[2/18, 10:49 AM] +234 703 962 5239: Didin_Anee
♡ *DUTSEN CIKIN RUWA.....*♡
*Na*
*Haleema G Khaleel*
*46-50*
Da k'afa suka k'arasa gidan, shi yabud'e musu get in gidan tunda ba maigadi garesuba. Seda
yakunna hasken gidan, Masallaci ya wuce dangabatar da Sallar Isha, ita kuma tashiga ciki,
wanka tafarayi tagabatar da tata sallar, shafa tazaunayi rigar bacci tasa silk light blue, turare
tafeshe jikinta dashi, kowana sak'o seda ta mulkeshi da nashi kalan turaren. Tahad'e gashin
kanta da ribbon tareda d'ora hula aka. Jin shiru beshigoba yasata dawowa falon kallo takunna,
Eternal Love take kalla a Ztv.
Bata dad'e da zamaba taji Karan rufe k'ofa Alamun yadawo kenan, da d'an saurinta tataroshi,
kayan hannunsa ta kar6a tai kitchen, tana wawwarewa yashigo kitchen in. Yatayata aje kowane
abu agurinsa ita kuma tayayyanka fruits in dayashigo dashi, tin a kitchen in yahau shan
kankanar datake yankawa, dataga haka ta d'auke plate in kankanar ta ajemai na lemo dasauran
kayan fruits in.
"Abun ma hakane? Yafad'a ashagwa6e kaman shine matar, ganin tayi blending in ragowar
Kankanar, ido kawai yabita dashi tamarkad' kankanar tasa madara da zuma amemakon Sugar.
A fridge tasa tagyara gurin suka fito atare daka kitchen in se murmusawa take ai kuwa ya hau
fad'in. "Shifa beyadda da wannan murmushin da take ba, tafad'a masa metake shiryawa.
Murmushin takumayi sannan tace "bakom muje nahad'ama ruwan wanka tinda ba abinci
zamuciba. Tashige cikin d'akin tana dariya ganin yadda yabita da idanu kaman baisantaba.
"Ruwan wanka ta had'a masa wankanma seda ta lalla6ashi yashiga. Wai yayi fushi tinda tak'i
gayamasa metake shiryawa. Kayan bacci tafito mai dashi tafeshesu da turare, tak'ara kintsa
d'akin dukda bawani datti yaiba se bada k'amshin freshner yake.
Kallonta tacigaba dayi tanata farin ciki itama da Allah yabata miji irin Usman. Ganin yadda
Sahiba da Ranveer suke zuba salon tasu soyayyan.
"Kitchen tashiga, ta d'auko kankanar datai blending tayi sanyi, bame yawaba tazauna tanasha,
d'an sanyi dayai yanabin jikinta harwani lumshe ido take, k'anshin turarensa kawai taji tabud'e
manyan idanunta duka akansa, k'arasowa kujerar datake yayi yazauna jikinsa na gogar nata.
D'ebowa tai zata kai bakinta yai saurin kai nasa bakin, "irin dad'in dakike sha kenan ashe,
yafad'a yana lumshe narkakkun idanunsa.
Sunkuyar dakai kawai tai murmushin de takuma, hannu yasa ya d'ago fuskar yahad'ata da
tashi kowa nashak'ar numfashin d'an uwansa, yana mata wani sassanyan kallo dashi kad'ai
yasan ma'anarsa. Cup in hannunta ya kar6a yana bata yanasha har suka shanye, seda yakalli
News sukai brush yasunkuceta sukai d'akinsu. Tareda rufo k'ofa. Safiyar alkairi.
"Kwance yake kaman bazai tashiba tinda yai bacci dagari yafara haske, bayan yagama
yamutsa Naja atun Queen injishi da fad'a.
Wayan tak'ara ringin akaro na uku, jin vivration in yayi yawa yasashi bud'a ido da kyar.
Ganin a sch inda sukai ne yai saurin ansa wayar, "ok godiya nake prop, Allah yak'ara girma.
Yamike yashiga band'aki already yasan tahad'a masa ruwan wanka ilai kuwa tarufe mai ruwan
yasamu yayi daidai wanka.
Wajen k'arfe goma yafuto, se kamshi gidan yake, yaduba ko ina batanan yai d'akinta.
Sark'a take k'okarin sanyawa, ya kar6a yasa mata har d'ankunnen yak'arasa shiryata, tana
tabinsa da kallo ire-iren abubuwannan dayake mata nakulawa da soyayya su suk'e k'ara mata
k'aimi wajen yin duk wani abu datasan zai farantamai yasashi nishad'i da farinciki cikin d'an
zaman dasukayi tare. So da K'aunarsa kuwa sun mamaye jini da jijiyoyinta, duk wani motsi da
zatai da k'aunarsa take, Addu'arta kullum suzama cikin so da k'aunar junansu da farinciki mai
yawa a rayuwarsu.
"Rungumeta yai tabaya yad'ora ha6arshi a kafad'arta, suna