Showing 33001 words to 36000 words out of 51633 words
Chapter 12 - NI DA GIDANA BOOK COMPLETE BY ZAINAB MAZAWAJE.pdf
ya cire da nufin wankewa ko ba a lokacin ba. Na
zauna a falo. Ya fito yace. "Zan fita, ki rufemin d'akina an jima, mukullan suna kan tebur d'in
ward robe."
"Nace"To, Ancle".
Sai da ya lek'a tsakar gidan, yaga babu kowa Sannan yay wuf ya arce.
Nayi masa a dawo Lfy, Bayan ya Fice, bai amsa ba, shi yasa nasan bai ji bane.
Bansan me yake faruwa ba, amma Ina ta jiyo hayaniya a Saman Momi, da a lamu bak'ine.
K'arfe takwas na dare, Ancle Fa'iz ya dawo. Dama yakan lek'oni, kafin ya wuce wurin Momi,
idan ya dawo.
Karfe takwas na dare Ancle , ya shigo falona da sallama na amsa, nayi masa sannu da zuwa.
Yace. "Bari naje wurin Momi naga yarda za mu kwashe da ita
Sai nazo na fad'a Miki kome ya faru, nasan kin zak'u. "
Yafi a wa d'ya, kafin ya dawo. Na d'ebo turare cikin show glass ya shigo. Kan kujera two seater
ya zauna. Nima Sai nazo kusa da shi dab, na zauna.
Nace. "Nayi zaton kamanta fa"
Yace.
"Yaya zan manta, bayan ninace zan fad'a Miki. Ya kwantar da kan'sa jikin tudun kujera ta baya,
cikin galabaitacciyar murya yace. "Don Allah Sumayya ki daina saka wannan turaren d'akin mai
k'arfi. Wanda kike sawa ma na jiki sent d'insa is high. Turare mai k'arfi har kaina yake hawa."
Na danne, ba dad'in da naji nace.
"To my Ancle, zan daina sawa na samu air freshner Kawai mai sanyin k'amshi na d'aki. Na jiki
kuma zan saka iya body spray mai sanyi, sansanya".
Yace. "Koma wani iri kiyi amfani da shi, amma d'an kad'an zaki sa. Yayi a jiyar zuciya ya zarce.
Dazun Salima ce tazo gidan nan. Ina wanka naji sallamarta. Shi yasa Ina jin ta hau benen
Momi, ni kuma da na fito daga wanka shine nayi sauri na shigo d'akinki. Saboda nasan Momi
zata tilastani da cewa,na bita Muje
wurin mamanta, saboda ta turo kirana har sau uku nak'i zuwa. Tayi laushi tayi nadama sosai, ni
take ta zabarin nema nazo ta bani hakuri na auri 'yarta, batasan ta makaro ba. In dai nine to
Wallahi ba ta ma soma nadama ba.
Sai jiyan Salima da yamma ta samu labarin aure na dake, domin mamanta b'oye mata tayi a
she a son samunta Sai an nemoni an dai daita komai, Sai Salima ta Sani, saboda tasan taga
katin auren ma ba k'aramin hauka zata yi musu ba. To jiya ta samu labari, ta tashi hankalin su.
Ta nemeni a waya na fad'a mata a binda mamanta tayi min. Kuka ta rink'ayi min sosai, Wai
banyi mata a dalci ba da tun farko na rufeta. Wai ai babanta yana raye ai shi Sai ya d'aura mana
aure.
Amma Yaya zanyi aure? Ina nake ta tsoma rayuwarta. Ko ina zaton zata iya rayuwa babu ni.
Ke surutai kala kala. Jiya ma cikin dare ta kirani a waya tana kuka da surutai. Gaba d'aya daren
jiya ban samu bacci ba fa. Kiran waya, babu hutu. Lallashin duniya nayi domin ta fahimci bawai
na barta Kenan ba, Ina sonta, kuma Ina da burin auren ta, amma da sauran lokaci. Kuma auren
da nayi duk Saboda ita ne, domin idan ban tauna tsakuwa a ya taji tsoro ba, al'amari Bazai
gyaru ba.
Amma Salima fafur ta kasa fahimtata. Da na gaji na kashe waya ta, naki kunnata kuma har
yau. Shine fa kika ga tazo da safen nan, Wai mamanta tace tazo ta tafi dani, saboda ta gigita
nutsuwar su."
Duk da fargaba ta rufeni da jin a binda ya faru, da nima zance ya shafeni dole. Cikin taushin
murya nace.
"Ancle, Kayi hakuri mana kai ma. Tayi nadama fa maman nata. Kuma naga burinka kenan."
Ai gani nayi, ya mik'e zaune sosai ya dubeni.
"What? Nayi me? Wai nayu hakuri yanzu? Lallai yarinya baki sanni ba, labarina kike ji."
A raina nace. Ban dai gama sanin ka ba.
"Wa'adin da na yankar mata wallahi Sai ya cika. Ina son Salima. Ina son 'yarta fiye da zaton su.
Amma wallahi ban shirya auren'ta yanzu ba, ko da kuwa za'a tattaromin kud'in masu arzik'in
k'asan nan a bani a matsayin gudun mawar aurenta. Wallahi bazan aure ta ba sai wa'adin da na
d'ibar musu ya cika".
Nan nasan lallai Ancle Fa'iz ya wuce sanina da karatuna. Zuciyar da Kawu Sulaiman yace yana
da ita, ta wuce zatona. Amma a hakan kullum zuciyta k'ara zarmewa take a son sa, duk da
zahirin halayan'sa masu wuyar Sha'ani da juriya, suna dad'a tallata kan su da kan su. Wannan
bai hana Soyayyarsa k'araci gaba da hab'aka a raina ba. Wuyarta mu kwana Mu tashi, nayi ido
hud'u da shi, naji muryarsa kuma.
Zan iya cewa, tun da daga ranar nan, gaba d'aya naga gidan sun sauyamin fuska, idan a ka cire
Khairat, da Ancle Fa'iz. Amma Khairat ta d'an ja baya dani kad'an a kan da. Ta yiyu kashedi a
kayi mata, saboda ko magana zata yi min zan ga bata da nutsuwa. A kan matsalar Ancle fa da
Salima na zurma wannan rigima. Saboda Momi tayi iya yinta Ancle yak'i saukowa a yi sulhu
shida maman Salima. Domin burinta Kawai yazo ta bashi hak'uri ya auri Salima. Shi kuma yace
ba yanzu ba, bashi da ra'ayi Sai lokacin da yayi ra'ayi. Momi da kan'ta tasan halin d'an ta, idan
ya kafe a hak'ura, idan ba haka ba, to lamari b'aci zai yi. K'arshe ma a yi uwar watsi, yace auren
ma baza'ayi ba ya hak'ura da ita.
Da wannan dalili Momi ta danne zuciya tasa masa na mujiya. Wato ido.
Amma a damuwa take game da lamarin, saboda a wurinta a ke kamun k'afa, ita kuma ta kasa
yin yadda suke so ga Ancle. Shi yasa Sai a Kayi haushin kaza huce kan dami, ni fushin a ka
juyeshi a kaina, saboda su so suka yi ya sakeni ya auri Salima a lokacin, tun da sun zo neman
sulhu. Shi kuma Ancle sun ga bashi da niyyar, hakan. Sun fahimci baya nunamin wata
kulawa,ko ta aure. Domin kowa ya Sani, baya zaman minti biyar a d'akina, ballanta na wai ya
kwana ciki, bayacin a binci na ko da wasa.
Amma kuma babu wani fitintunu na rikici tsakani na da shi, duk da borar da na zama. Ina
girmamashi, da yi masa biyayya dai dai gwargwado. K'alau muke zaune ba'ajin ko tari na na wai
muna ko da da musu. Wannan shi ya zamo k'arin umda da ya had'u da na bijurewar sa ga
auran sa da a ke so yanzu da Salima, a kace Ina wuta a jefani.
Alhakin komai kamar gani suke a wuya na yake, nice sila.
A tunani na inda a dalci basa yi min haka ba. Matsalar Auren Salima da Ancle tun kafin a San
Ancle zai aure nine. Ya kuma fad'i hujjar bijirewar sa ga Momi. To don me zan zama a bar
juyewa haushi? nima a barni naji da kashe wutar gabana Mana, da suma sun San da ruruwar
ta. Zaman aure na da Ancle ko a suna ma bashi da takwara, ko mahad'i.
Ban ware girki na ba, har lokacin tare muke yi da Khairat na gidan duka. Wani zubun ni keyi,
amma Ancle bayaci momi ke yi masa nasa shi kad'ai kullum.
Momi ta kirani har saman ta, naje na gurfana cikin sababben ladabi da nake mata, ko uwata
albarka, domin jiki na har rawa yake, saboda tsabar biyayyar da nakewa Momi idan ta Sani a
bu. Idan nasan tana son a bu ma, bana jira, Sai ta sani, yi nake.
Cikin d'aure fuska Momi ta dubeni."Sumayya daga yau, bana son ki sake saka hannunki cikin
girkin gidan nan, ki rink'ayin naki.Dama Fa'iz nike yi masa, Kinga iya cikinki zaki dafa. Na
fad'awa Fa'iz ma zaki soma girkin ki."
Nace"To, Momi".
Naci gaba da tsuguno, koda sauran umarni, da naga tayi banza dani, na mik'e na janyo
sanyayyun k'afafuna nayi waje.
Ancle bai min zancen girki ba, momin ce ta sake kirana tace"Nayi magana da Fa'iz ya
ce. Ko me kike so, ki tambaye ni, na baki, kudin girkin cefane da abin da kike so ki dafa".
Abinda na fahimta, so a ke a kara nisantani da shi, yarda komai babu ruwansa dani, sai dai na
tambayi momi, kuma dama ce da za a rinka samu da za a rinka gasa mini magana, son rai.
Tun yanzu kenan na soma haduwa da matsaloli, kafin ma na soma samun kofar da zan dana
tarko na ga Ancle Fa'iz yarda zan soma janyo raayin sa gareni ya ma soma saurarata ko a hira
ne, wanda wannan aiki ne na sani ja mai zaman kansa, to ban kzi ga wannan ba ma ga wata
gwaramar ta tunkaro ni, ta mutan gidan, idan a ka cire khairat kowa ma ba kauna ta da son
zama na yake a gidan ba, musamman khalifa da kallon kiyayyarsa gareni yafi na kowa, to ta ina
zan fara, abinda yawa wai kura ta shiga kasuwa, kwace goriba kuma hannun kuturu ai bazai yi
wuya ba. Abin nufi banje koina a zuciyar Ancle ba, ballantana a sha wuya wurin rabani da shi.
_Taku_
_Zainab ilyas mazawaje_
Follow this link to join my WhatsApp group:
https://chat.whatsapp.com/JhPLFkgTb4U0Y3wVj6YRQe
*NI DA GIDANA*
_Zainab ilyas mazawaje_
_Best brilliant interlligent writer_.... ️
_Page 15_
Saboda Momi ta kula ban fiye zuwa wurinta na karbi abun bukatar da tace ba, ta sake kirana
washe gari. Na durkushe a gabanta kamar mai neman gafara.
Sai da ta shari lokaci kafin ta waiwayeni tana kallon wayarta, da latse latse kamar ba ita ta kirani
ba, kamar yarda ta saba yimin, sai can a dakile ta waigeni.
"Um, kina sane da cewa nace kome kike bukata ki na girki da bukatun yau da kullum kizo
wurina, domin Faiz ni yake ba kudi duk sati na bukatun gidan nan, har kayan a binci da komai".
Nace.
"Momi, ai ba sai na karb'a ba, tun da ina da kayan garata da aka kawo ni ita, da komai na girki."
Ta zabgomin wani kallo na baki isa ba.
"Na Sani d'iyar tajiri, 'yar na gada. To, hak'k'in mune ciyar dake. Babu ruwan mu, da wanda aka
kawo daga gidan tsoho. namu za'kiyi amfani dashi."
Ni kam mamaki ya kamani ma, na menene a bin zafin a ciki. Ai duk domin a amfana dashi aka
kawo garar.
Na sanyaya murya nace.
"Allah ya huci zuciya, Momi, ayi a fuwa, tuba nake. Zan rink'a karb'a.Duk da haka komai na
aikin gidan nike yi. Wanke wanke Shara, wanke band'akuna da kayan k"amshi. Amma fa banyi
fari ba, bata hanani ba dai. Khairat girki ne nata. Muhibbat Sai taga dama take sa mata hannu,
kuma Momi bata yi musu gyara ba.
Daga nan damuwa ta soma samun gurbi a Zuciyata. Gani da yalwar kud'i, ga Kayan binci a
store, da a ka kawomin komai a kwai, amma wai kullum Sai naje wurin Momi karb'ar komai,
kuma idan naje, Sai an min wulak'anci kafin a bani, musamman idan Khalifa da Muhibbat, suna
wurin. Habaici, da zambo da tsaki, nafi shansu ma.
Gaba d'aya Momi ta canza min. K'iyayya muraran ta fito min da ita. Ko kirana tayi, ban ji ba, ko
na kuskure wani a bu, to zagine. Banza ,shashasha, sauna, d'iyar matsiyata, wannan sunaye
nane,da Momi ta rad'amin daga baya. Sam bata Kiran Sunana ma. Kullum a mai laifi nake,da
nayi da banyi ba, Sai an k'irk'irar min.
Khalifa da Muhibbat sun fi takuramin. Bani da 'yancin fitowa tsakar gida Sai habaici, harara da
tsaki. Amma Khalifa idan shi kad'ai ne, kulani ne kawai bayayi, sai harara da tsaki, sai dai idan
Muhibbat tana kusa, ya samu 'yar uwa Sai suyi min taron gayya. Khairat idan tana kusa, a fuska
zanga ta nuna damuwa sosai a kan a binda suke min.
To sai dai bata da yarda zata yi da su, sun girmeta. A Kwai Sanda tayi magana a kan bai dace
ba a binda suke, suka hayayyak'o mata. Khalifa ma saura k'iris ya kai mata duka Muhibbat ta
Kare.
Yace mata a gabana.
"Wallahi, kika sake yi mana shishshigi jikinki Sai ya fad'a Miki.
Kuma Sai na fad'awa Momi, zagon k'asa kike mana."
Tun daga lokacin, Sai take jan jiki, da taga sun soma yi min iya shege.
Sunan da suke kirana da shi, wai 'Yar jiran k'ofa. A bin nufi, ni Salima nake yiwa gadon wuri,
kafin tazo. Wato bani da wani amfani face kula da muhalli suke nufi. Jin sunan ya zamemin jiki,
domin suma shi suka rad'amin ko kirana za'suyi, bayan na Momi da nake ji da shi kuma.
Duk da naga gabar suke dani ta sosai, ni har gaishesu nake, idan basu kulani ba, amma babu
sauk'i wai ciwon Arne. Ko sallama nayi musu basa amsawa ma.
Rannan Khalifa ya biyo Muhibbat a guje suna wasan banza, ni kuma zan wuce rik'e da fulas da
kofunan tea biyu na glass, na fito daga kichean zanje na wanke su, Muhibbat da gayya ta
bangajeni da k'arfi na kife, fulas ya fashe da kofuna, ni kuma bakina ya d'an fashe na k'ume da
garu, kafin na kife amma Muhibbat ko ta d'aga kai ta dubeni ballantana tace sannu.
A gaban Momi, aka yi, domin ta lek'o ta Sama tana yiwa Khalifa magana, amma bata yi
magana ba, kuma ko sannu. Hak'urin dai da nayi ban tanka
saboda naga kullum k'ara d'aukar zafi a ke yi dani. Ta yiyu, so a ke na tanka a yi b'atacciya.
Domin ko washe gari da naje gaishe da Momi, bayan ta amsa da k'yar, na mik'e Sai Muhibbat
da take kusa da ita taja tsaki tace. "Aikin banza, isar ba'a isa ba. Mace Sai nacin jarraba, ba'a
sonki, amma kin manne."
Ban d'aga kai na dubeta ba, na fito. Momi naji.
Sati na biyu Kenan da aure na da Ancle Fa'iz. Ji nayi komai yayi min zafi. Baki d'aya naji gwara
nayi komawa ta makaranta, duk da hutun da na dauka da saura kwana biyar ya cika.
Babu wani a bu da yake d'ebemin kewa a gidan. Ga kuma damuwar wulak'ancin da a ke yimin.
Ni kuma bazan iya fad'awa kowa ba nawa, ballantana Ancle Fa'iz da dangin sa ne kemin.
Nasan bai Sani ba, tun da komai Sai bayanan a ke min, duk da ba wani sona yake ba,
ballantana nace suna shakkar ya Sani ya d'au mataki, Sai dai kawai sun San shi mai zafi ne da
baya d'aukar wargi ko wani iri, ko yaga anyi wani a bu da bai da ce ba, batare da ya taka
zazzafan burki ba.
Sam hutun ma da na d'auka na aure ma nayi da na Sani, domin bai min rana ba, Sam. Sannan
babbar damuwa ta kawu Sulaiman yak'i zuwa ballantana naji sanyi. Domin ganin sa da hirar sa
mai kwantar min da hankali, kan mantar dani damuwa ta, da maraici na.
Ancle Fa'iz ya kasa bani lokaci, ko yaya da zan jarraba salo ma na soma jan hankalin sa gareni,
ko da daga hira ma gajeriya a bin ya faskara. Kullum cikin uzuri yake, idan na nemi hakan.
Banyi zaton zai yi tsaurin samuwa haka ba gareni.
Amma kuma duk Sanda zai fita, ya kan ce me nake so ya sayo min, nace babu komai.Abinda
nake son ya gaza.Komai ya sayo d'aurina dabam. Kuma komai ya sayowa su Khairat sai ya
sayo min. Wannan ya, tabbatar min rukuni guda ya a jiye mu.
Randa na hak'k'ak'e zan fad'a masa komawata makaranta, ranar ya shigo da robar madarar
roba biyu a hannunsa, ya mik'omin d'aya. Daga tsaye bai zauna ba, Sai yace.
"Bari naje na nemi Ado coach d'in mu, naji ance yanzu yazo bana nan, ba domin shiba
kwanciya zan yi na gaji".
Ban yi mamakin gajiyar da yake yawan cewa yayi ba, saboda nasan Boll ya buga, ko training.
Amma uzurin sa na kullum da baya yankewa, shi yafi ban mamaki.
Har ya juya, Sai ya dawo yace min.
"Ki rink'a rufe k'ofarki da daddare Sumayya. Naga har na kwanta a bud'e take, me yasa?".
Nayi masa wani salon kallo nace. "Bacci ne, yake kwasheni ban Sani ba."
Yace"Yace "Saboda me?".
Nace.
"Saboda bani da a bokin hira"
Ya gyad'a kai."Kin raina a bokan hirar takine. Gaki da book's na gani, ga kayan kallo ai sun
isheki."
Nasan jahiltar manufata yayi, yana sane. Nace cikin narai narai da ido.
"Wad'an nan ba'a bokan hira bane face d'ebe kewa. My Ancle kaifa kace na rink'a kallonka
kamar Ancle Sulaiman, amma Sam baka bani lokaci irin nasa. Baka hira dani irin sa. Anya za'ka
maye gurbinsa?
Kullum Sai kace kana da uzuri. Na Shiga d'an Kukan shagwab'a kamar na gaske. Ni Wallahi
bazan iya wannan rayuwar ba. Kullum ni kad'ai kamar mayya.Karabani da Ancle d'in dake yi
min hira yana sani dariya da wasan nishad'i, kai kuma kak'i hira dani. Ni gida zan tafi yau ma".
Yarda nayi zaton zai d'an lallasheni ko yaya, ai sai ya bud'emin wuta.
"Maza maza tashi, ki tafi, karki bari k'uda ma ya rigaki. Ni zaki fad'awa wai damuwar