Showing 51001 words to 51633 words out of 51633 words
Chapter 18 - NI DA GIDANA BOOK COMPLETE BY ZAINAB MAZAWAJE.pdf
nasan al'amari ma ya gama
lalacewa. Ga Khalifa ya hanani nayi bayani sosai har Momi ta shigo.K'arin d'imaucewar tawa
ma, da na kasa gane gaskiyar sirrin zuciyar Ancle Fa'iz na yarda ko rashin yarda, game da
mummunan sharrin da Khalifa ya k'ullamin, domin har Momi ta shigo ta soma magana baice
komai ba. Da alamu bayan rud'ani, kansa ya d'auki zafi, b'ararraka caji Kawai yake tayi. Momi ta
dubemu Mu duka tace
"Wai me yake faruwa a nan.? Ihu da surutai sun tsoratani da k'yar na iya fitowa, zatona ko
b'arayi suka shigo ma, Sai da na tabbatar da muryoyi."
Kafin ma ta rufe baki Muhibbat ta zayyano, Khalifa ya karb'a ya k'arashe har da k'ari. Mugun
Kallon da Momi tayi min banyi zaton zan tsira daga shan maruka ba, hagu da dama, ko kuma
saukar mahaukacin duka, irin na kawo wuk'a.
"Biri yayi kama da Mutum, kuma alamu a lamun somin hauka zub da miyau.Tuni na tsinke da
al'amarinki dama Sumayya, zaki iya fiye da haka. Wato bayan kin tarwatsamin Zaman lafiyar
yara, yanzu kuma kinzo kin gurb'atamin tarbiyyar yarona da na d'ebi shekaru Ina tarbiyya. To
Wallahi hukuncin da zan d'auka a kan'ki ba iya ke kad'ai zai tsaya ba, har iyayenki, ko da yake
baki ma dasu Sai kakanni, to har tsufansu bazan tausaya ba."
Cikin Kukan da da k'Yar yake fita saboda tashin hankali nace "Momi, Wallahi sharrin Khalifa ne,
shine......"
Ta dakamin tsawa."Rufemin baki Munafukar banza,mai bak'ar a niya, da mugun hali, da mugun
usuli."
Nan naga Ancle Fa'iz ya dubi Momi a har gitse, da alamun Furucinta ya Sosa masa rai sosai,
Kawai ta tsira ne, saboda itan maman sa ce, bansan me yasa shi jin zafin furucin ba dai, tun da
iya tunani na yanzu ni na gama tozarta, na gama bakin jinin da baza a tausaya min ba ko jin
zafin duk kalar mummunan furucin da za a jefeni da shi.
Babban tashin hankalina da har lokacin bansan cikin zuciyar Ancle Faiz ba, game da yarda ko
rashin yarda game da sharrin da khalifa ya kullamin, har zuwa in da Momi tace.
"Dole sai ka saki yarinyar nan Faiz, umarni ne ba shawara ba, in dai nina haifeka, na baka daga
nan zuwa safiya kawai, ni na rasa uwar dalilin da yasa har yanzu ka kasa sallamar ta ta ka ma
gabanta, daga taimako? to taimako mana domin ka samu sararin auren Salima, ne,kuma
bukata ta biya, to jiran me ka keyi?".
Dai dai nan cikin sheshshekar kuka na daga idanu na dubi Ancle, in da muka hada idanu,
idanun nan nasa suna nan jazur, kawai sai naga ya lumshe su a hankali ya sunkuyar da kai
kawai, da alamu yana cikin tsananin rudani, kuma kwakwalwarsa ta dauki mugun zafin shiga
tashin hankalin da bai taba shiga ba. Ni kam babu abinda nafiso irin yace ya sakenin yafiye min
komai, me zan tsinta a gidan, kuma da wani ido zan ci gaba da kallon kowa na gidan,
musamman Ancle Faiz game wannan mummunan sharrin da a ka kullamin.
*Bonanza*
_Tabbas page din baya da wannan duk na tsawaita domin page biyu ne duka a matsayin daya
kowanne, domin ni kaina na afu da kuzo kubawa idanunku a binci na hakika game da wannan
labari da har yau ba ku shiga birnin sa ba_
_Ga duk mai son ayi da ita to ga dama ta garabasa, cikin sauki da rahusa, saboda abubuwan
da mutum zai amfana da shi na karuwa da nishadi ya ninninka kimar abinda zai bayar babu ma
hadi_
mai bukatar hakan ga a count no
8025527956 Opay
_Zainab ilyas_
_Shaidar biya ta wannan number ta whatapp_
09096409711