Showing 42001 words to 45000 words out of 51633 words
Chapter 15 - NI DA GIDANA BOOK COMPLETE BY ZAINAB MAZAWAJE.pdf
a kan'sa. Ya cire ya ajiye. Na sake d'auka na rik'e nace.
"Wallahi hula ba k'aramin kyau take yi Maka ba, my Ancle."
Yace. "Ko?".
Na sake saka masa a kan'sa, ya kuwa cire da sauri yace.
"Wai yaya haka ne, ina cirewa kina samin?".
Nace. "To, ni nafi son ganin ka da hular, kafi kyau Allah".
Wannan Karon wani murmushi naga yayi Maimakon hasala da nafi zato, yace.
"Sumayya, kina fa takuramin, kina fa sani surutun da ban shirya ba, Allah kina ma cin darajar
maraicinki ne nake sassauta miki, domin ina tausayinki wani lokacin, amma a kiyayi dai zuwa
rafi kullum, wataran sai an fasa tulu".
"Nayi murmushi. "In dai bukatar da a kaje na debo ruwan ya samu to ai ba damuwa, Ancle
kasan ranar biyan bukata rai ma ba a bakin komai yake ba".
Ya dan daga min bakar girar sa gami da dan fito da ido. "I see".
Iya a binda yace kenan, da alamu ya dan shiga duhu da furucina, ko kuma ya fahimta ya maze,
saboda na fahimci yana da saurin karantar mutum sosai, amma sai ya waske yayi kamar baisan
me kake ciki ba, ni kuwa da gayya na furta.
Kwana biyu na sake samun Ancle a daki ya na bubbude sababbin wasu unders da ya sayo
daga leda ya na dubawa, bai dago kai ba gareni duk da ya amsa sallama ta. Na zauna gefen sa
kan kafet din dakin, shi kuma yana gefen gado.
"Sannu da aiki my Ancle".
Nace ina murmushi.
Yace " Yauwa sannunki".
Na mika hannu zan amshi singilet din dake hannun sa, ya janye.
"Ancle gani fa zanyi".
Yace "Ahaka ba kina gani ba, look karfa kizo ki matsamin, bana son takura".
Na sake yin murmushi.
"Ni ba takura maka zanyi ba Ancle, kawo to na ninnin ke nasa maka a ward robe".
" Barshi nayi".
Nace "Kai my Ancle bai kyau tu ba ina zaune kayi aiki ba gaskiya kawo please".
Yace " Hmmm!! " Kawai.
Kamar bazai bani ba sai ya miko min kayan duka ya mike yana mai fadin.
Yarinyar nan duk kin bi, kin hanani sakat? nasan idan ban baki ba baza ki barni ba, bansan wa
kika gada ba wurin kafiya a dangi".
Nayi 'yar dariya nace.
"A dai laluba za a samu, domin ruwa baya tsami banza"
"Bulala kawai Allah zan a jiye kusa dani. Surutun da ki
ke Sani banyi niyya ba, yayi yawa fa".
Nace "Barewa fa a dawa ance da d'anta take wasa Ancle Fa'iz. Kaman ta bani da kowa Sai kai?
Kaine uwa, kaine uba, kaine Kawu, kaine Yayana kaine....."
Ya da katar dani da hannu.
"Ya isa !. Ke kin fiye Surutu, Sai kace aku kuturu."
In da sabo na saba da irin wad'an nan lafazai nasa. Kuma a hakan muke ci gaba da hirar bana
fushi kamar kullum.
Ranar dai na ganshi cikin walwala dai, Bansan dalilin ba. Ya nutsu ya soma cemin.
"Ki ta yani murna, na samu shigowar wasu kud'ad'e masu yawa na wasu wasanni da muka yi a
state uku, Sai jiya aka turomin nawa cikin a count. Ban tab'a Samun kud'i masu yawa a wasa ba
irin wannan. Nayi kasafin su ma. Na wari wanda zan ba Momi da Baba, na wari Wanda zan Sai
mota, da wanda zan sake jefawa a harkar ginina da yake taci min kudi, da na samu da ya
handame".
Naji dad'i sosai da na samu matsayin da ya fad'amin sirrin ci gaban'sa. Na kuma yi ta
surfamasa godiya da addu'a na kyautar kud'in da zai ba iyayen'sa, Sai a zaci nawa iyayen zai
bawa.
"Wallahi ka kyauta Ancle Fa'iz, musamman alkhairi na kyautatawa ga iyaye yafi kowanne. Allah
ya saka da alkhairi, ya k'ara bud'i"
Ya gyara zama daga kishin gid'ar da yayi gefena da nake ninke masa kaya.
"Kema za'a baki Lada na ganin ido, kamar 'yar dubu goma, tayi?".
Nayi masa murmushi
"Wanda za'a ba kyauta har yana da zab'i? aiko naira goma ka bani godiya zan yi tayi,
ballantana har dubu goma Ancle?".
Ya kanne ido guda cikin dubana yace.
"Na lura, kina da Yakanah! Saboda haka bari a k'ara miki dubu goma su zama twenty thausand.
Godiya nayi ta surfawa da addu'a."
Yace. "Ya isa haka Sumayya, Sai kace kyautar rai na baki?".
"Ancle wai kuwa wacece Anti Husna da naji su Khairat suna yawan fad'e?".
Yace"k'Anwar Momi ce, ita ce autar su.
"To, Ancle Jamil fa?".
Yace. "Yayan Momi ne"
Na sake cewa "Maman fahad fa?"
Cikin nuna 'yar k'osawa yace.
"K'anwar Babar Momi ce, Kenan uwa take a wurin Momi. Na gaji Sumayya, tashi Kije ki kwanta,
bacci zanyi karfe goma na dare ta gota, ina son yin sammako".
Nace"Abin har da kora my Ancle?".
Yace"Wanzami dama ba yason jarfa, ni me yasa jiya kika koroni daga d'akinki?".
Cikin 'yar dariya nace. "Au, daga kayi bacci na tasheka nace kaje ka Mik'e a gado?".
Yayi doguwar hamma kafin yace. "Wannan a bu duk mai sauki ne, idan baki son tafiya, nan
d'akin yayi miki, Sai na kawo miki guzurin filo, ba Shike nan ba?"
Na kuwa ce "Kawo min".
Sai kuwa naga ya tashi, ya na kokarin jawo filon, nan nasan da gaske yake. Kafin ya dauko
kuwa na mike da sauri na fice, in da nace masa
" Sai da safe Ancle".
A tsukin cikin wata hudu da aure na da Ancle Fa'iz, a bubuwa sun soma zuwa min yarda nake
so. A lokacin ne kuma na sake shiga tsangwama da takura da fitintunu a cikin gidan, saboda
sun fuskanci muna d'an d'asawa da Mijina, yana nunamin kulawa fiye da da.
Kwana ne kawai Ancle bayayi a d'akina, amma har a binci tare muke ci, idan ya shigo d'akina.
Kuma ni na gadar masa da hakan, domin ko shi kad'ai ya soma ci, Sai na zo na sashi a
gaba,nima na soma ci, muci gaba da ci tare. Ko a bincin Momi ne kuwa, domin naci na yasa
kullum Sai yaci nawa. Shi yasa baya cika cikin'sa ma da a bincin Momi, saboda yasan nawa
d'an k'a'ida yana jiran'sa.
Wulak'anci da cin mutunci muraran a ka Shiga yi min a gidan, da kare ma ba zai ci ba.
Duk wani laifi idan a kayi a gidan, Momi ni take cewa. Babban a bin takaici har Sata a ka
kallafamin. A zatona babu wani abu da ake sacewa, domin a d'oramin laifin sata ne kawai. sai
Momi yau tace an sace mata a bu kaza, gobe ma haka, kuma tace nice ware, nice lallai zan
d'auka, domin cikin 'ya'yan ta babu b'arawo. Momi ta kirani cikin 'ya,'yan ta, ban da Ancle, taci
min mutunci a matsayin ni b'arauniya nayi mata Sata. Khalifa ma da Muhibbat su zageni son
ran'su. Khairat ce Kawai bata tofawa, zanga ta b'ata rai sosai. Na lura bayan kirkinta, hak'uri ne
da ita ainun.
Muhibbat ta matsamin lamba sosai a tsukin. Idan nayi wanki, nayi shanya ta zubar a k'as. Da
yake Ina wanke ma na Ancle marasa nauyi, amma bata zubar da na yayan'ta. Kunji son zuciya.
Ni ke sharar gidan, amma randa Muhibbat ta so tsiya, Sai ta fizge tsintsiyar daga hannu na, ta
share ko'Ina. Sharar idan ta kwashe Sai ta watso falona. Na rink'a dauriya, Saboda Kawai bana
so K'orafi ya fara b'ulla daga bakina wurin Ancle ko wani nawa. Sannan Zuciyata tayi nisa a son
Ancle Fa'iz, banason a binda zai haifar da sa'in sa tsakanina da kowa nasa . Zaman aure na
mutu ka raba na k'uduri yi da shi, iya yina.
Komai nawa na Kayan kichean, ni da Muhibbat muke amfana, musamman idan tayi bak'in
k'awayen'ta, komai na kichean d'ina za'tayi facaka da shi. Filet filet da kofuna na k'arau ta yi
amfani da su, ta zubemin a waje babu wankewa, ta kuma fasa na fasawa da gayya, duk dai Sai
an cuzgunamin nayi magana, an zagi ubana. To, ni kuma Sai nayi lub, kamar banji ciwo ba.
Kayan kichean d'ina duk ta farfashe k'arau d'in, ban dai tanka ba, na k'yale. Sun Sani a kwana
sosai Muhibbat da Khalifa. Wulak'anci salo salo, zagi da Habaici. Hannune kawai basa sawa su
dakeni. Sau d'aya nayi wa muhibbat magana da ta fasamun fulas d'in shayi, da shi kad'ai ya
ragemin, ta kuma kwashemin drink's na Friedge da nake tanada saboda Ancle.da tayi bak'i.
A binda ya fito daga bakin'ta shine.
"Ai naga, ba' daga gidan uba, akazo da drink's ba, yayan mu ya saya, aikin banza shishshigi
babu kwarjini, diyar matsiyata ke har wani kaya ne ma dake na kichean da zakiyi fariya a kai,
kuma komai na ci ko sha ai yayan mu ke sayowa ba daga gidan tsoho a ka kawo ba".
Raina ya sosu, tamkar na fallamata mari, amma na daure zuciya, saboda ubana da baya raye
da ta tsomo a ciki".
Tabbas yayanta na sayo komai, amma wanda duk ta kwashe ni na Saya. Kawu Sulaiman yana
aiko min da kud'i a kai a kai, kuma yawanci, wurin yiwa Yayan su d'awainiyar sa kai na, suke
tafiya. Sauk'inta bana yini a gidan,saboda makaranta, ba domin haka ba, a bin yawa zai min,
wai shege da hauka.
Ranar a sabar bani da lacture, banje school ba. A kayi dace nayi bak'i kuma.'yan uwan ummata
da suke uba d'aya, baba Maryam, da baba Hasana. Tare na had'a mana a binci mukaci, Sai
yaran su, dana ware musu a faranti guda.
Ancle Fa'iz ne ya shigo da a zahar da ba sabon'sa ba. Ina hangen sa ta taga, saman Momi ya
haye rik'e da poly bag k'arama, irin ta take a way.
Muna hira da bak'ina ya shigo falon da sallama, baisan da bak'in ba, Sai da ya shigo. Bayan
sun gaisa, na gabatar masa da su suka gaisa a mutunce kuwa. Sai yace nazo yana son ganina
dama tsintsiya ce a hannuna, zan share a bincin da yaran suka watsar, sai baba Maryam tace
naje Kiran mijina ta share. Nabi bayan Ancle
Yana tsaye a d'akin nasa ya rungume hannu a k'irji, ya jingina da bango, kamar wani a bu yana
damunsa na fuskanta.
Nace "Ancle yau ka dawo da wuri Amma "
Fuskar'sa babu walwala yace "Eh!" Yayi shiru. Sai daga baya Yaci gaba.
"Momi ta dawo dani,saboda waya tayi min wai na taho mata da take a way yunwa take ji. Nace
mata yanzu Momi a binci Sai ya gagareki a gidan bayan da a kwai komai? Saboda bana son
dawowa, Ina kan wani a bu mai muhimmanci, amma Sai da na barshi, saboda tace min su
Khairat dama ke dafa binci su bata, kuma duk sun tafi unguwa tun safe . Kuma gashi likita yace
lallai Sai taci a binci sosai kafin tasha magungunan ta, na larurar rashin lafiyar da take ciki."
Nan na dubeshi nace, Dama Momi bata da lafiya?".
Ya dubeni galala. "Wace irin tambaya kike min? Waye baisan MomI bata da lafiya ba, kwana
biyu? duk da tace kikan jima bakije kin gaisheta bama, amma ai za'kiga ta fad'a kwana biyu".
Wannan abu ya Sosa min rai, shi yasa kika ga na kasa juriyar a jiyewa zuwa wani lokaci. Domin
da nace Momi tayi miki magana ki bata a binci, tun da kina gida, Sai tace bata buk'atar a bincin
ki, tun da baki damu da ita ba. Tunda ta kwanta jiyya baki tab'a yi mata sannu da jiki ba, ba kya
gaishe ta ma. Kuma da kina bata a binci, kika daina, Sai dai kiba almajiri. A binda ciwo a ce
Momina ta rasa a binci a gidan nan Sai da na dawo, amma ga bak'inan su sunci, har sun
zubar".
Tun da nazo gidan raina baitab'a b'aci ba irin ranar. Duk a binda suke yi min, ni banyi k'orafi ba
Sai Sai su? Kuma gashi ya Shiga cikin su, ya yarda tun da yake tuhumata.
Na had'iyi yawu da k'yar .
"Nifa ban fahimci zargin nan da ake so a lik'amin ba. Sam ni bansan Momi bata da lafiya ba.
Waya fad'amin? Kuma Ina gaisheta, ni banga alamun wani rashin lafiya ba. A binci Ina bata ta
dai naci tace bataso, to yaya zan yi.
Na sake daukar zafi saboda na fuskanci Ancle yana bayan su, yarda ya daure fuska yana yimin
wani kallo a sangarce.
Kuma a binci ma ai cewa a kayi nayi iya cikina, nifa a ka ware. Kuma ai ba'a bani umarnin ma
bawa Momi a binci ba, iya kaina a kace na dinga dafawa, ina dalilin da zaa dawo a na zargina
kuma. Ni fa nasa kaina nake bawa Momi a binci".
Take naga ya fusata ga rashin zato na.
"Har wani alfahari kike na wai ke kika sa kanki kika ga damar bawa Momi a binci? Sai da kika
ga dama? to kiga kuma hagu. Kar ki sake bawa Momina a binci, umarni na baki Shima. Ki dafa
iya cikin ki na sake fad'a. Ki Sani, ko zan iya hak'uri a kan wani a bu, banda a tab'amin uwa. ko
wanene bai isa ba wallahi."
Take zuciya tazo min iya wuya. A fusace nace.
"Girkin ma ai ba dole bane. Domin iya cikina zan wahala? nama daina dafa komai, kome na
samu ya fad'o bakina ya wadatar. Kuma Allah shine Sha'hidi a kan kome nene gaskiya. K'arya
ta shekara k'arya. Gaskiya na makwafinta".
Ina fad'in haka na mik'e nayi ficewata.
Na fusatashi sosai na gani kan fuskar sa, amma Sai naga ya gaza cemin komai, face bina da
kallon Mamaki, har na fice.Tun daga ranar na rufe kichean ruf, ko ruwan tea bana dafawa. Sam
bana karyawa da safe, ko ina gida. Abinci Sai a bu mai ruwa ruwa,Sai ciye ciye Sama Sama.
Amma banacin gaskiya a bincin kirki a cikina. Ga damuwa da na d'orawa zuciyata. Kuma na
d'au fushi da Ancle Fa'iz ko falonsa bana zuwa. Da safe yana shigowa wurina Bayan sallar a
suba. Bayan na gaisheshi, bana sake ko kallon sa ballantana na tsinka masa. Shima ganin
babu fuska, Sai ya ajiyemin kud'in da yake bani, batare da sake kulani ba. To dai banga ya d'au
fushi kamar ni ba, yarda na fuskanta. Komai ya sayo zai kawomin nawa d'aki ya a jiye. baya
cewa komai, Sai ya fita.
Ni kaina banyi zaton Ina da zuciya ba, Sai da aka kaini bango. Dama wasu sunce, mai hak'uri
bai iya fushi ba.
Ba iya Ancle Fa'iz ba na d'au fushi da shi ba, duk gidan ne. Ji nayi an kai ni gargarar da bazan
kuma d'aukar raini da wulak'anci ba. Momi Kawai zan iya d'agawa k'afa, albarkacin Ancle Fa'iz
da kuma darajar haihuwa, tun da ta haifeni. Amma ita kan'ta Momi taga canji a wurina. Kullum
zan je na gaisheta, Amma fuskata babu walwala, da rawar jiki na biyayya da nake yi mata.
Domin da kullum naje gaishe ta, Sai na tambayi ko da wani aiki da zan yi mata. Bayan fa
Kusan aikin gidan gaba d'aya da na kallafawa kaina, kamar mai aikatau.
Momi ta ban Mamaki da tace wai bana zuwa gaishe ta, da bata a binci, da dubiyar rashin lafiyar
da ban San da ita ba. Gaba d'aya zuciya ta ta karkata wurin yarda da cewa Momi yak'i take
yiwa Salima bayan idonta.
Domin Khairat ce ta sameni rannan da babu kowa a gidan bayan sallar magariba, tazo d'akina
tace min.
"Matar Yaya, wallahI ki k'ara rik'e mijinki da kyau, domin Kusan kullum Sai Salima ta yiwa Momi
waya. Rannan hands free Momi ta manta tasa, naji Salima tana yiwa Momi magiya kamar zata
yi kuka, Wai tana bala'in Son Yayan mu, shi yasa baza ta iya zama da kishiya ba, Wai Momi ta
taimaka mata. Saboda Salimar ta cewa Yaya, ya sakeki tun da saboda ya sameta ya aureki,
kuma tun da Momin ta ta sauko ma tace ko yaushe yazo a yi aure. Amma Sai Yaya yace mata
babu ruwanta da zancen auren sa dake, tayi gefe da shi. Kawai tasa himma a kan tsara musu
zaman farin ciki da Soyayyar da za'su shimfid'a, kafin isowar auren. Ita burin Salima fa Kawai
Yaya ya sakeki kafin auren ta da shi. Shi kuma yak'i bata amsar yiyuwar hakan. Momi hak'uri ta
bata dai, tace tabar komai a hannun'ta zatasan yarda za'ta b'ullowa komai, saboda yanzu binsa
take yi a sannu, saboda har yau bai gama hucewa ba, da a binda maman'ta tayi masa. Kuma
Khairat ta ce min, taji Momi tana fad'awa Ancle Fa'iz wai ya d'auki matakin plannig, wato tsarin
iyali a auren ku, saboda batason ya haihu da ke kafin zuwan Salima. In so samu ne ma ya
sallameki yanzu, tun da kwalliya ta biya kud'in sabulu. Amma Sai cewa Momi yayi. Momi nasan
a binda nake yi nima name ya kamata nayi a lokacin kuma da ya dace, kusamin ido".
Momi bataja musu da shi ba, duk da bata fahimce shi sosai ba. Haka za'lika nima ban fahimta
ba. Amma fatana kar burin su ya cika a kanki Anti Sumayya. Wallahi ni nafisonki da Anti
Salima."
Wani irin k'aunar Khairat ya k'ara mamayeni. Rungumeta