Showing 39001 words to 42000 words out of 51633 words
Chapter 14 - NI DA GIDANA BOOK COMPLETE BY ZAINAB MAZAWAJE.pdf
kafin kiyi min kora da kara."
Dariya ta cikamin ciki fal! amma ina bari ta fito zai d'ago komai, shi yasa na gintse a bata. Nan
ma tun yana mita har ya zame masa jiki, ya rabu dani, ko nayin baya tankamin, kuma baya
janye jikinsa, Sai ya mai da idon sa kan kallo Kawai, domin kallon ke sawa ya jima sosai ma a
falona. Domin ni nake samo irin film d'in da yake so, har na boll masu tashe. Duk domin na ja
hankalin sa ya rink'a jimawa sosai. Shi yasa har k'arfe d'ayan dare yana kaiwa. Wani lokacin ma
bacci zan yi, shi zai tasheni idan ya gama kallon. Wani zubin shi zai yi bacci, ni zan tashe shi.
randa ya gaji kenan idan ya buga boll. Kuma duk dare, Sai ya koma d'akin sa, bai tab'a kwana a
wurina ba.
Tun daga ranar da nayi wa Ancle Fa'iz gyaran d'aki ya zame min jiki. Kullum Sai na Shiga nayi
masa gyara,domin bai karb'i mukullin d'akin ba da na cira, yana wurina.
A bu d'aya yafi damuna, nake gwagwagwar juriya. Shine na yarda Ancle yake yawan yin waya
da Salima, kuma a gabana. Sautari ita ke bugo masa, kuma ya amsa ya biye mata a falona suyi
ta hira. Ko Ancle baisan ina son,sa ba, bai kamata yayi min haka ba a zatona, tun da yasan
aure mu kayi, dole zanji babu dad'i. A binda Zuciyata ta bani kawai, Ancle Fa'uz bai d'auki auren
mu a bakin komai ba, face aure ne kawai na wata manufa, mai wa'adin k'arewa.
Sai dai na lura, Salima tana cikin damuwa ainun na aure na da Ancle Fa'izu. Domin Kusan
kullum idan suna waya, a lallashi da ban hakuri yake k'arewa.
Sababbun kalmomin da yake fad'a mata har na haddace sune.
"Kinfi kowa sanin matsayinki a zuciya ta Salima. Wallahi sonki da k'aunarki babu a binda ya
gutsiresu, suna nan. Kiyi hakuri lokacin zai zo, kamar yanzu ne. Aure na dake babu fashi,
za'ayi in Sha'Allah. Ki soma kiran kanki ma matar Fa'iz." Idan hirar tayi tsayi
tashi yake ya fice da wayar suna hirar soyayya, bazan sake ganin sa ba, Sai safiya.
Kishi sosai nake ji, amma danne zuciya ta nake yi, kar nayi wa kaina gurun gund'uma. Domin
sautari, nuna matsanancin Kishi, kan sa mace, tayi a sarar wanda take kishi a kan'sa. Ina ga ni
kuma da har yau ban mallaki zuciyar sa ba?.
Ancle Fa'iz, har yau bai je Kiran da maman Salima ke aiko masa ba da sak'on yaje ba. Na lura
kuma bashi da niyyar zuwan ma a kusa Sam. Tayi aike har ta gaji. Nasan kuma ko da kanta
tazo bazai saurare ta ba. Kuma ko kunya bai ji ba, ga 'yarta suna tare kullum a na shek'a
soyayya a waya. Ancle Fa'iz da bam yake.
Na gama shirina tsab na makaranta. Na rufo k'ofa, na nufi d'akin Ancle Fa'iz a karo na uku
yana ciki tun da na aure shi. Da safen da na Shiga d'akin Ancle Fa'iz, haka kwance yake kamar
mai bacci, amma da nayi sallama Sai naji ya amsa.
Na zauna kan wardrobe gajera dake jikin gadon, na, fara da gaisheshi.
Nace kuma."Ancle, zan tafi makaranta." Ya bud'e idanu a hankali, ya mik'e ya tashi. Ya nufi
sib,ya bud'e ya k'irgo kud'i jikin kyauro sabbi fil, ya zara ciki ya mik'omin.
"Ga kud'in mota dana kashewa."
Nace"Wallahi, kabarshi Ina da kud'i da yawa."
Zan masa gaddama, a karo na farko, ya lalubi tafin hannu na, ya mannamin kud'in ciki, ya
dunk'ule. Yace. "Ungo nan malama, hak'k'inki wuyana yake, I don't care, a bout, you have
money or not."
"Na gode, Ancle. " Na fad'a a ladafce.
Lokacin na kula da irin iskar da ya sakarwa kan'sa. Ga fankar tsaye, kusa da kan'sa ga fankar
Sama, Sai kad'awa take. Kuma ya saki k'arfin'ta.
Nace"Ancle Fa'iz iskar nan fa tayi maka yawa."
Bayan ya koma kwance ya bani amsa da cewa.
"Tayi min kad'an ma."
Nayi dariya a hankali nace.
"Shikenan,Kawai Sai a huda bango a k'ara Maka da A C."
Ya rungume fulon da yake kwance sosai kafin yace. "Wannan a bune sassauk'a tun da Ina da
Hajiya kamarki, Sai kisa a yimin a kusurwoyi hud'u ko?."
Murmushi nayi, cike da jin dad'in zolayar da yayi min, ban taga ba kuma saboda sauri nace.
"Na tafi Ancle."
Yace. "A dawo lafiya."
Momi kuwa da nayi mata sallamar zan tafi makaranta bayan gaisheta, bata cemin ko cikan ki
ba. khairat ce tayi min a dawo lafiya, a tsakar gida. Muhibbat tsarabar harara na samu. Khalifa
baya nan shi. Abban su Fa'iz ma a waje na sameshi na gaisheshi har k'as nace na tafi
makaranta Abba. Addu'a mai kyau yayi min.Mutum ne mai kirki da kyautatawa na lura.
Ga shi da sanyin zuciya sam ban tab'ajin ya d'aga hak'ark'ari ga kowa ba, Sai dai na jiyo
muryar Momi. Ina yawan jin hargowar fad'anta ga Muhibbat. Ita ma Kenan.
Komawata makaranta, na samu sauk'in damuwa. K'awayena suka yi ta murna dayi min
shak'iyanci kuma. Abubuwan da suka wuceni tuni na mai dasu, saboda a minai, gashi ni kuma
akwai himma da fikira wacce baiwace daga ubangiji.
_Tabbas Sumayya ta soma samo bakin zaren sakarta, amma bamu sani ba, zai tsinke ko zai
tafi dodar ga irin sakar da take so tayi_
*Taku*
_Zainab mazawaje_
Follow this link to join my WhatsApp group:
https://chat.whatsapp.com/JhPLFkgTb4U0Y3wVj6YRQe.
*NI DA GIDANA*
*Zainab ilyas mazawaje*
__Best brilliant interlligent writer_ ........ ✍️
*Page 17*
Ranar litinin sai yamma Lis ni da gida. Sai naji na sarara a raina a kanda.
Sanda na dawo daga makaranta, Kichean nake shiga na dafa a binda ya samu, nayi shigewata
d'aki, idan ba alwala ba bana sake fitowa. Amma duk a binda na dafa, ina kaiwa Momi. Bata
tsinkamin, amma sai na a jiye gefe. Bansan yaya take da shi ba. A lokacin babbar damuwata na
samu kulawa koyaya daga Mijina, kar abin yayi min yawa wai shege da hauka.
Cikin nasara na soma samun kuwa.
Domin Ancle yana d'an zama a falo na fiye da da, muyi 'yar hira kad'an, da sai dai mu zauna
kawai muyi jugum jugum, ko shi naga yana ta chat a waya, kuma nasan da Salima ne, sai yayi
kamar ma ya manta da ni a wurin. Da abin yana da muna daga baya sai na dai na sawa kaina
damuwar, domin naga ba mafita bace.
Ancle baya jimawa dai sosai ma a falona idan ba wani kallo na kunna da yake so ba. Kuma bai
fiya yi min hira ba, Sai dai ni. idan kuma na cika jan shi da hira, Sai yayi min shiru, nayi ta zuba
kamar kun nan niyar rediyo baya tagamin. Idan hirar ma tayi tsayi, Sai kawai naga ya tashi ya
fice.
Hakan na nufin na dameshi da Surutu kenan.
Da na fuskanceshi, sai nake binsa da salon halinsa. Da naga yayi shiru ya daina tayani, ko bani
amsa, Sai nima nayi shiru. A hankali a hankali na soma sanin Ancle Fa'iz. Me yake so, menene
bayaso. Kuma hakuri da kwantar da kai yasa na soma fahimtar.
Ancle yana da wani irin hali da raayoyi da ya bam bamta da na wasu mazan, baison turare mai
tashi, sai mai sanyi can kasa, baison turaren wuta na daki sam, ko za asa sai dan kadan sosai
da baaji sai sama sama, haka ma air freshner nunawa yayi baiso ta yi yawa sai kadan.
Sannan baya son k'unshin zamani da ake yayi, yanzun. Bansani ba, Sai bayan nasa an zo har
gida an rangad'amin.hannu da k'afa, marun da bak'i na fulawoyi, yayi kyau ya zanu. Amma
yana arba dashi yace.
"Wannan ai b'ata jiki ne,menene a bin Sha'awa game da wannan shirmen."
Nace"Kwalliya cefa ta mata Ancle."
Yace"b'ata kwalliya dai, Ina a bin burgewa a ciki?".
To kwalliyar fuska ma ta mata, baya so Ancle Fa'iz. Ranar wata lahadi banje makaranta ba,
bayan kwalliya ta situru nasha make up.powder eye liner, da eye shadow ,lipstic da white lips da
jagira tsararriya, da tasha shape. Wallahi kuma nayi kyau har ga Allah. Amma Ancle yana
shigowa da ya kalli fuskata ai sai naga ya kwashe da dariya. Dariya sosai da ban tab'a ganin
yayi ba. Zatona daga can wurin su Momi ya taho da a bar'sa, ai sai na ta yashi, ina yi ina
tambayar ba'asi.
Abin gwanin bandariya wai yaro ya tsinci hak'ori.
Yace"Kema dariyar kikewa yi wa kan ki?".
Nayi harr da ido, Nace.
"Kamar yayafa?'".
Ya sake duban fuskata, ya tintsire da dariya.
"Kinga fuskarki kuwa? Sai kace wata sabuwar aljana?".
Tabbas furucin'sa ya sosa min rai, amma na daure zuciya ban nuna ba, ko furtawa ba.
Cikin salo ma na kamar shagwab'a nace.
"Kai Ancle, me fuskata tayi?".
Yace"Kin cikata da shafe shafe da yawa. Ga na fuska, gana ido gana leb'e gana gira, gana
zagayen ido. Is too much, Sumayya. Don Allah karki sake yi."
Tun daga lokacin kuwa ban sake yi ba. Iya kacina powder kad'an, kwalli. Sai white lips idan tayi
hali. Domin ragowar basa burgeshi, baya so. A bubuwa da yawa basa burge Ancle Fa'iz.
Lokacin da ka Tak'ark'are Sai kayi masa bajinta, to lokacin zai kushe. Shi yasa daga baya na
sanyawa Zuciyata salama, bana fushi sam idan nayi abu ya kushe bana fushi, sai dai nayi
k'ok'arin gyarawa irin yadda ya nuna yana so, ko bana so kuwa.
A cikin 'yar hira dana ke Samun albarkacin ta a tsukin, nake bincikar sa irin ra'ayoyin sa da a
binda yake so da wanda baya so. Ya kan fad'a min, wani zubin. Wani lokacin kuma ya bijire
yace wai menene dalilin da nake damunsa da tambayoyi da bincike?.
Nan saduda na rabu jdashi, na tara gaba kuma. Har lokacin babu ka lamun somi somin Sona
dana fuskanta daga gareshi.
Har lokacin girkin Momi kawai yake cI. Cikin hikima nake yi masa magiya nace ya rink'a
ragomin, nima ina Sha'awar girkin Momi. To wani zubin ma nan falona yakan zo da shi yaci,
saboda naci na. Nima daga nan Sai na turo masa nawa da magiya nace yasa albarka. To dai
nawan ma kushewa yake a gabana. Ya kance gishiri ya zarta. Ko kuma magi. Ya dai ficewa na
cika attaruhu. To Sai na rage sa attaruhu, na rage magin ma da gishiri, nayi iya iya wata wurin
kyautata komai. To amma me.? ya daina k'orafin, amma ba yabo.
Na lura girkin Momi kawai ya fiso. Kuma naci, na yaba Kam. Yabon gwani tilas. Momi ta iya girki
sosai kuwa. nafi zaton fannin girki ma ta karanta.
Na dai zamewa Ancle Faiz dan kadafi, na manne na nace, cikin shiga al'a muransa, duk furucin
da zai jefamin mara dadi ba na yin fushi ko zuciya, zuciyar tuni ta horu da haka har ta bushe.
Ni keyin zaraf cikin al'amuran sa, kafin ya buk'aci a bu nayi. Sam. baya so na yi masa
d'awainiyar komai. Rufe dakin sa yake yi da mukulli idan zai fita. Idan yana ciki, kuma bayaso
nace zan Shiga ballantana nayi masa gyara ko Shara kamar yarda na k'wallafa rai, Sai ya
hanani fir!.
Baisani ba rannan na zari d'aya daga cikin 'ya'yan mukullin sa da yake jikin key holder na
b'oye.
Da yamma Lis, na taso daga makaranta da wuri saboda lacture ta ranar gajeriya ce na bud'e
d'akin nasa. Gaban su Muhibbat da Khairat suna hira, suka bini da kallo. Gyara nayi masa
sosai. Dakin a share yake tas, amma a kwai 'yar k'ura jikin sib da wardrobe. Na k'alk'ale komai .
Na cire zanin gadon nasa masa sabo gau, nawa duk da nasan ma baiyi wani datti ba, saboda
ba laifi Ancle yana da tsafta. Haka ma labule na cire nasa masa nawa sabbi masu kyau, domin
biyu aka yi min. Nasan ma mai kyau ne, amma nawa sabone ful, domin kala biyu ne dani masu
tsada. Zanin gado kuma kala uku. Na tsara masa Kayan cikin kwabar sa, na jera, saboda yana
yawan hautsinawa ya barsu garin binciken kaya. Nayi masa gyaran da bazai rinka hautsina
komai ba, komai dalla dalla. Na ware under's d'insa da singlet da gajerun wanduna, har da
Kayan boll da babu wanki na kai d'akina na a jiye da niyyar gobe na wanke.
Na fesa masa air freshner Sama Sama, kar yayi min k'orafin turare ya hau masa kai. Shi yasa
ma ban k'ara da turaren wuta ba. Dakin nasa yayi kyau sosai kamar ba shi ba. Da yake falon
ma babu tarkace, kujera guda ce sai TV dake jikin bango da risiba.
Wata laptop d'in Ancle na gani madaidaiciya ta d'au hankalina na bud'e.
Tabbas da nasan me zan yi tozali da shi, da ban bud'e ba. Hoton Salima ne da Ancle Fa'iz ya
cika fuskar laptop d'in. Suna jikin juna, Salima ta kwanto a jikinsa ya tallafota da hannayensa ya
mannata gam a jikinsa. Tamkar mata da Miji. Abin ya d'aure min kai, dama Ancle Fa'iz zai iya
haka? Ko kuwa soyayyarce duk ta zautar da shi, ya biyewa hud'ubar shaid'an?. Sai da na daure
zuciya na sake kallon hoton. Su duka murmushi suke yi a hoton. Sai da nayi tasbihi ga
mahaliccin surorin'su. Ita da shi d'in babu kanwar lasa wurin kyau. Sun dace da juna Kam in dai
wurin duba ne.idan kuwa suka tashi haihuwa,wad'anne irin kyawawan yara za'su haifa. Za'a
Sha kallo.
Ko shakka Ancle Fa'iz yana son Salima sosai. Kusan duk wani abu nasa mai muhimmanci
hotonta ne a kai. Wayoyin sa biyu ne banason gani ma, Saboda duk hoton
Salima ne. Da dai da key holder dinsa na d'aki hoton Salima ne, k'arami a ciki anyi masa siffar
zuciya. Lallai Ina da gagarimin aiki a gabana, tun da ko makami na yak'i daya ban mallakaba,
na satar zuciyar mijin da muka kusa tarayya da Salima.
Ko ince ni zaman wucin gadi nake yi a wurin Ancle, waadi nake jira.
Tayi min fintin kau Salima na k'wace Miji tuni. Tun da familyn sa ma duk mayak'anta ne na
fagen daga. Gashi kullum kuma k'ara zarmewa nake cikin Soyayyar Ancle Fa'iz. Shi yasa
kullum kishin sa ma k'aruwa yake a raina, duk da bai a jiyeni a rukunin mata ba ma. Ba domin
na tabbatar Sai mun d'ebi 'yan kallo da shi ba, da Sai na rotsa laptop d'in nan. To laifi kan laifi
ma zanyi. Na shigo masa muhalli bai Sani ba, kuma nayi masa tsadadden ta'adi. Nan ma cewa
zai yi lek'en a Siri ya kaini. Wannan hoton, ko ba'ace ba, nasan yana ji dashi.
Da na fito daga d'akin Ina rufe komai, Momi da Muhibbat na gani daga saman bene sun kafa
min idanu, nayi kamar bangan su ba. Nasan Muhibbat ta kai mata tsurku.
Fuskar'sa d'auke da alamomin Mamaki ya shigomin. Hannun sa ya dafe kujera yana daga tsaye
ya ce.
"Wa ki ka ga ya shigar min d'akina?"
Kamar da gaske na dake
"Anya an Shiga d'akinka kuwa yau Ancle? Wani a bune ya faru?".
Yaja dogon numfashi.
"Tabbas an Shiga an jima, domin komai na d'akin ya canza. An canzamin tsarin komai na wurin.
Wanene mai wannan aiki, ko nace wacece?".
Na kanne cikin b'oye dariyar dake son k'wacemin.
"Ta'adi a kayi maka Ancle?".
Yace. "Gyara a kayi, tun da wurin ya k'ara haskaka yayi kyau".
Naji dad'i sosai na yabon da yayi. Ancle Fa'iz kafin ya yaba abu a ya'ra.
Saboda Jan zare, na zolayeshi da cewa.
"Ancle, Ina Jifa aljanun cikin d'akinka ke sonka, suka yi maka gyara."
Yayi min k'uri da idanu, har Sai da naji wani abu mai hargitsa yanayi kafin ya nisa tukun yace.
"In dai haka ne, to kece shugabar aljanun, ke kika jagorance su."
Dariya nasa ta burgewa. Wato ya fahimci ni nayi masa dai gyaran.
"Ina kika samu mukullin d'akina? Yace.
Nace.
"Jikin mukullayenka na cira."
Nayi zaton zai min fad'a, amma Sai naji yayi shiru.Na fahimci yaji dad'in gyaran da nayi masa a
fuska. Duk da kullum nunawa yake yi baya so nayi.
Tamkar kaska haka na Mak'alewa Ancle Fa'iz, saboda ya rage kyarata da yawan yi min fada,a
kan da. Domin takai ko bai shigo d'akina ba, ni zan bishi nasa d'akin, bana kuma shayi, ko
fargabar mutanen gidan. Tuni na soma yin sabo da shan zagi, harara, habaici da zund'e. Shi
yasa idan ma anyi min, bana d'aukar'su a bak'on al'amari da zai yi ta damuna. Wannan yasa
zuciya ta ma ta kangare ta bushe, domin idanuna sun rufe da Soyayyar Ancle da bin hanyoyin
da zan janyo ra'ayin'sa gareni. Duk da Shima Ancle Fa'iz d'in ina shan wuyar sarrafashi wurin
shishshige masan da nake yi. Yakan nunamin ma k'arara cewa na ta kuramasa, wani lokacin,
amma Sai na shanye.
Bayan Ancle Fa'iz ya sauko daga saman Momi, ya sameni zaune a d'akin'sa Ina dakon'sa.
Ya samu wuri ya zauna, ya fara da cire hular kan'sa. Nayi zaraf na d'auka, nasa a kaina na
dubeshi nace.
"Ancle tayi min kyau?".
Ya jefeni da kallo d'aya na gefen ido yace.
"Ke namiji ce da hula za'ta yi miki kyau?".
Sai na cire daga kaina nasa masa