Showing 39001 words to 42000 words out of 52878 words
Chapter 14 - WACECE NI BY Fateema Muhammad Suleiman-1.pdf
Dr da yayi conducting aikin cewa idan
kwana ukun yayi za'a fara bata abubuwa masu ruwa ruwa,da dimi, kafin zuwa lokacin, ko ta
bukaci wani abu kada Ku bata.
Mummy ta ce toh zamu kiyaye sannu likita muna godiya sosai.
Sa Ai da takuma dawowa kusada ni yayimun sllama ya tafi.
Nabi bayanshi da kallo saboda bansan ko wayeshi ba sai da mummy take yimushi godiya ne
nagane likitane.
Bayan fitanshi da kamar minti goma sai ga Khalid ma yau shigan larabawa yayi saboda juma'a
ne,cikin girmamawa ya gaishe da mum ta amsa cikin Fara'a,niko tunda na ganshi hawaye suka
fara fitomun babu kakkautawa domin ganinshi ya kuma tunamun da Yusuf Dina,cikin damuwa
ya matso kusa da ni sosai sannan ya fara yimun magana a hankali sorry my dear ya isa haka ki
daina kuka akwai abin da ke damunki ne na kira likita?
kai na girgiza mashi nuna alamun A'a.
Ya danyi murmushi ya fada kamar rada I love you,wish you quick recovery.Allaah ya tona asirin
wannan azzalumi yakuma kara maki lafiya.
Sai da ya zo kusa da mummy ya ce ko akwai abin da kuke bukata ne?
Mummy ta ce Aa babu abin da muke bukata Wanda kakawo jiya ma suna nan Allaah yayi maka
albarka mungode sosai da hidimarku.
Ya ce Aameen bara naje wurin daddy.mummy ta ce toh,ka kiramun Humaira,ya ce toh.
Sai bayan ya fita ta matso da kujeran kusa da ni,ta ce akwai abin da kike bukata ne?
Na gyada kaina nuna alamun eeh kafin takaramun wata tambayar sai ga Humaira ta shigo da
sauri ta nufo gadon ganin mum da tayi ta bada dukkan hankalinta gareni,ya juya hankalina ga
Humaira sannan na nuna alamun ina son takawomun wayata da sauri ta mukamun shi,sai
mummy ta ce meye zakiyi da waya keda ba magana zakiyi ba? Da ido nabita bance komai ba ganin na Fara daddanne wayata sai dukkan su ,suka matsa ajikin
gadon.
Inbox dina na bude ganin yawan notification da na gani bisa saman wayar.
Duk kuma sakonnin yusuf ne sukafi yawa,sai kuma na 'yan makarantarmu da suke turomun
jimaminsu sunzo dubani amma anhanasu shiga da dai sauransu.
Sakonnin da yusuf ya turomun nabi daya bayan daya.na karshen da na karanta,yana sanar da
ni cewa yanzu za'a shiga da ni aiki my soulmate..
To daga wannan sako bai kuma turo wani sako ba,ina kyautata zato shima yana kwance kamar
nine.....
Nima sai na shiga rubuta mashi sako kamar haka
_Abin sona,da badan hikimar ubangiji wannan sakon da na turo yanzu wadansune za su turo
maka sakon mutuwata.amma Allah cikin ikonsa ya nufeni da rubuta maka da kaina,wani
azzalumi ne yayi nufin rabani da duniya, sai dai adadin kwanakin ne basu kare ba. yanzu da
nake wannan sakon ina kan gadon asibiti ne yin magana ma anyi restricting dina sai bayan
kwana uku.ina yimaka fatan samun waraka daga mahaliccinmu nayi kyawarka sosai da sosai_
Sai da na turo sakon na ajiya wayar kusa da ni sannan na lumshe idona duk abin da nake kuma
daga mum har Humaira hankalinsu na Kai na .
Sai ga nurses umarni aka basu akan a canja mun daki tunda yanzu nayi 48 hours a ICU din
wani babban daki suka mayar da ni dakin ya tsaru sosai komai na bukata kuma akwai aciki,sai
da suka ciremun kayan jikina suka gogemun jikin da towel sannan suka kwantar da ni bisa
makeken gadon dake dakin kasan dakin Chinese carpet ne a shimfide,bayan nurses din sun fita
sai ga surgeon da Dr zaid sun shigo, wajen da sukayi aikin ne suka duba ina jinsu suna cewa
ina da jiki mai kyau kuma yana responding treatment.. Gaskiya naga so da kulawa ta
mussamman daga iyayena da kawayena sun nunamun gata,Daddy kam babu abin da zance
saboda tun asali son da yake nunamun baya yiwa Humaira ko yusuf su da kansu suka radamun
daddy's girl.saboda shakuwaya da daddy din.
beep beep sako yashigomun waya ina dubawa kuwa number yusuf ne da Sauri na bude ga
abin da nagani...
_Masoyiyata hakika jikina ya bani cewa akwai abin da ya faru da ke, nayi kuka sosai da na kasa
jin muryarki nayi ta sake sake sai dag karshe na fauwala lamrin ga Allaah,bayan na rokeshi da
ya tsaremun ke a duk halin da kuka shiga.lallai da na rasaki nima kuwa zan rayune cikin abu
biyu imma mutuwar ko kuma rayuwata zata kasance cikin kunci da wahala ni Allaah yaji tausayi
ya tsaremun ke nagode mashi bisa wannan taimako ina ji kamar nayi tsuntsu naje na kalleki
amma hakan ba abu ne mai samuwa ba.nima kuma anyi conducting operation din,toh yadda Dr
suka fada wannan na biyune,bayan wata uku ma za'a kuma yin wani operation din.to gashi anyi
na biyu saura daya kenan amma yanzu Alhamdulillah ansamu improvement a aikin..ina maki
fatan samun lafiya cikin sauri ina sonki so irin wanda bantaba yiwa wani mahaluki ba rokona dai
kullum ki rikemun amanarmu_
Sai da nagama karanta sakon tausayin Yusuf yakamani sosai,sanin da nayi cewa ya kwallafa
ranshi sosai akaina kuma ya yarda da ni .......
******************
Wasa wasa yau har kwana na bakwai a kwance a asibiti,cikin wannan kwanakin kuwa jami'an
tsoro kuwa sai zirga zurga suke suna jiran umarnin likita ne domin yimun tambayoyi,tun a
kwana ukun suke zuwa da Neman magana da ni sai dai Dr zaid ne ya hana ya ce sai ankunce
stitch din sannan zasu samu daman magana da ni hakan kuwa akayi yau kam ankunce stitch
din wajen ya warke sosai.sai da nayi wanka na shirya sannan jami'an tsoron aka basu umarnin
shigowa.
Tambayar farko da suka jefomun shine sunana
Na fada musu sunan
Sannan suka ce toh mrs zaratun ko za ki iya bamu cikekken bayani game da wannan abin da
yafaru?
Sai da na dan nisa na ja dogon numfashi,sannan na kwashe duk abin da yafaru da yadda akayi
na samu na gudu na buya a gidansu Dr zaid,
Duk abin da nake fada suna rubutawa sai da nagama,sannan suka kara cewa ko za ki iya gane
mutumin idan Kika kuma ganinshi?
Na ce kwarai zan ina ganeshi saboda kafin ya farga da ni a dakin na karemashi kallo.
Suka kuma jefomun tambaya toh mrs zaratun yanzu ace muka baki takarda da pencil zaki iya
zana mana yanayin mutumin?
Na ce zan iya zana maku shi.....
Sai gashi sun mikamun farar takarda plain sheet da pencil,kowa a dakin yayi shiru an nutsu ana
jin tambayoyi da bayanan da nake bayarwa.duk daga kai na da zanyi kuwa,sai munyi ido hudu
da zaid din ya kuramun na mujiyarshi.a gefe daya shima khakid ba'a barshi a baya ba,shikam
suna tare da daddy da yanzu suka zama kamar da da mahaifinshi.
Na zane mutumin dai dai kamar yadda na ganshi da kayan da yake sanye ranar black suit ne
da hukar car boy sanye a kanshi,sai fuskarshi cike yake da kasumba .bayan nagama zanawa
namika musu kowannensu sai da ya girgiza kai hasashensu ya fara zama gaskiya.sai da
sukayimun godiya sannan sukabar dakin.
_ga wannan kuyi manage yau am kinda busy_
*vote share and comment*
â�â�â�â�â�â�â�â�â�â�â�â�â�â�â�â�â�â�â�â�â�â�â�â�â�â�â�â�â�â�â�â�â�
*WACECE NI*
âœ�í ¼í¿¼by
*Fateema Muhammad Suleiman*
Email fmsuleiman743@gmail.com
Wattad teemacool2020
*í ¼í¼ˆKAINUWA WRITERSâœ�í ¼í¿¼ ASSOCIATION*í ¾í´�í ¼í¿»
```{United we stand and succeed;Our ambition is ton entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*page* 4⃣2⃣&4⃣3⃣
*Dedicated this page to WACECE NI Fans lots of love*
*Today's Beautiful Hadith is about Dajjal*
Narrated Anas bin Malik (RA): The Prophet (peace be upon him) said, "There will be no town
which Ad-Dajjal will not enter except Mecca and Medina, and there will be no entrance (road) (of
both Mecca and Medina) but the angels will be standing in rows guarding it against him, and
then Medina will shake with its inhabitants thrice (i.e. three earthquakes will take place) and
Allah will expel all the non-believers and the hypocrites from it."
(Sahih al-Bukhari, Vol. 3, Book 29, Hadith 15)
_What an awesome reminder of how blessed Makkah and Madinah are! Full of serenity, worship
and protected from the Dajjal. May Allah allow us all to visit there insha'Allah._
Musamman uncle Anas da uncle Mustapha suka zo daga Nigeria saboda yin dubiya,duk da
mummy ta sanar musu cewa jikin nawa akwai sauki har video call take yi musu su ganni amma
ran kakata Hajja Bintu bai kwanta ba sai da ta sanya yaranta suka zo dubiya.
Sai Vaishali da Muhammad Ameen da yaran duk sunzo sunyi dubiya,najmi ita ce 'yar Vaishali
na biyu tunda sukazo tana tare da Humaira naga kamar jininsu ya hadu da ita,da suka tashi
tafiya fafur taki binsu ta ce ita sai ta huta za ta koma haka suka barta duk da Vaishali ta ce ki
bari idan ansallamosu kije gida taki saboda muma muna sa ran sallamar cikin kwanakin nan.
Suna zuwa office dinsu zanen da nayi sai da suka gama binciken da ya kamata suyi sannan
suka sanyashi cikin system sukayi scanning dinshi sannan sukayi comparing dinshi da asalin
hoton mutumin da suke zarginshi shekaru masu yawa amma basu da evidence da zasu
kamashi sai gashi yau kuru kuru hoton da na zana da Wanda suke da shi ya zama abu daya
mutumin da suke zargine yanzu yazama red handed......sai da suka tabbatar da zarginsu,gaba
daya u.s a maganar akeyi antabatar da wanda ake zargi da kashe mutane sama hamsin. nan
da nan kuma aka kamashi yana kokarin guduwa yabar kasar kenan.
Ni kuwa tun da FBI din suka fita na koma baccina,sai kusan sallar azahar na farka daga baccin
mummy da Humaira naga sun idar da sallah suna kan rug na sallah suna lazimi.
Ganin na farkane Humaira ta yi sauri ta zo kusa dani,ta na tambayata ko da abin da nake
bukata?
Kai na gurgiza mata nuna alamun Aa.duk da na fara magana amma jifi jifi naje nake yi saboda
dama ni asalina ba mai yawan magana bane.tsawon sati biyu kenan ina asibiti,a wannan
kwanakin kuma naga gata daga kowane bangare na friends dina na school,daga colleagues
dina na department har da sauran dama bama department daya da su,sai uban gayya Khalid
gaskiya shima babu abin da zance akanshi.uwa uba kuma ga Dr zaid da har kunya yake bani
idan naga yadda yake azarbabi da nuna kulawa ta musamman,it seem to me,kamar neman
shiga yake a wajena kuma kamar yana competition ne da khalid.saboda ko ba'a fada masa
yasan akwai wani muhimmin abu tsakani na da khalid.nasha kamashi da wani irin harsh kallo
da yake yiwa khalid alamun yana kishi da shi ne,idon yaga na kalleshi saurin dauke
idanuwanshi yake daga Khalid din.cikin zuciyata kuwa tana mamakin halin maza,ni ina ta kaina
ina naga wata soyayya..
cikin zuciyata kam dukkansu suna da darajar da bazan iya hada su da kowa ba especially Dr
zaid kam da jininshi ke gudana ajikina, sai khalid da yadau nawin yimun aikin gyaran wuyan da
za su yi kamar dai plastic surgery,saboda tabon da ke wuyana din za su gyara ya koma normal
kamar dai yadda jikina yake da,toh gaskiya kudaden suna da yawa,har munfasa yin aikin
bamusan wanda ya fada mashi ba sai kawai ya ce ayi aikin shi zai bada kudaden duka.
ranar dagani har su mummy mun rasa bakin yin godiya lallai a al'amarin khalid akwai abin
mamaki wannan ta shi wane irin kudi yake da shi ne?kuma duk wani abu da akayimun shine
duk ya biya kudadensu da daddy yaje biya ne management na asibitin ya ce khalid ya riga ya
biya wancen ma dadi yayi ta mashi fada akan meyesa ya biya sannan yayi mashi godiya.
toh bamu gama yin godiyan wancen ma ba sai ga wani taimakon daga gareshi.gaskiya
wadannan guys din bani da abin da zan saka musu dashi, sai dai addu'a.
Yusuf kam babu abin da yake dashi da zai taimakamun fa ce addu'o'in da yake ta yimun,kullum
kuma maganarshi kenan abin sona hakika nayi bakin ciki da wannan abu da yasameki gashi
bani da abin da zan taimaka maki da shi sai dai addu'a,wannan aikin da za'ayi maki Allaah yasa
ayishi cikin nasara.sai dai hankalina ya tashi da kika ce wani ne daban ya dauki nawin wannan
makuden kudaden nan.ina tsoron ya kwacemun ke wallahi this time around kam,na karaya
sosai.duk lokacin da yusuf ya yi mun irin wannan magana tausayinshi ne ke kara ruruwa acikin
zuciyata saboda sanin da nayi cewa yusuf jarumine tsayayye mai tausayi sannan nasanshi
sosai rashin babu ne toh babu yadda ya iya shima kuma ya na fama da nashi darurar.nutsar da
shi nake da kalamen masu karfafa gwiwa har ya hakura da maganar.saboda nima yanzu na
karaya da wannan lamarin.
Idan zanyi maganar so na hakika Wanda zuciyata ta amince da shi ta zauna har karshen
rayuwa ne toh yusuf ne,amma kuma Khalid da zaid,kam gaskiya sun Riga sun sace zuciyar
mummy da daddy da dukkan makusantana.ni kam dukkansu suna da daraja a wajena amma
maganar so kam yusuf dina nake so,saboda ni tun farko ba abin hanun wanda zai sace
soyayya ta amma yanzu sai dai nayi musu kawaici.
Sanin da nayi cewa addu'ar Mara lafiya karbebbene toh addu'ar na gukufa da yi Allaah ya
zabamun mafi alkhairi.
Tsakanin wannan lokaci kuma nidin na zama abin kwatance a duka ilahirin kasar saboda nayi
abin bajinta wajen taimakon zanen wannan azzalumi da ya gagari kasar kusan shekara talatin
kenan cases nayi death da aka tabbatar shi ne yayi a record mutane hamsin kuma da kanshi ya
amsa cewa shine yayi duka wadannan kisan. Da aka tambayeshi meyene dalilinshi na yin duk wadannan kisan sannan ana sanyashi ne
yakeyi ko kuma wata gaba ne tsakaninshi da wadanda ya kashe?
Amsar da ya bayar ne kowa ya daure mashi kai.
Ya ce ko daya duk Wanda na kashe babu wanda yake sanyani kawai kashe mutum din ya
zama,hobby nane.tun daga ranar da na kashe wani da mukayi musayar magana na kasheshi
toh sai kisan ya zama addicted a gareni wallahi duk ranar da na sanya raina zanyi kisa toh idan
bansamu nayi ba bazan iya yin bacci ba sai na kashe mutum sannan zan samu nayi
bacci.saboda haka ne ma na zama mai farautar daukan ranta duk Wanda na kyalla ido akanshi
idan har ranar yakasance ina da mode din kashe rai.musamman nake da Master keys dina na
yin ammafani da shi lokacin da zanyi kisa.bayan nayi kisan sai na saje da mutane ta yanda ba'a
gane ni ba.duk kisan da zanyi sai na tabbatar wanda zan kashe shi kadaine a gidan ko dakin da
yake kwana saboda ina tsoron kar a ganeni.
Wannan bayani live ake nunowa a TV kowa yayi mamakin wannan lamari ace mutum yayi ta
kashe mutane basu ci ba,basu sha ba.kamar wani kwaro duk tsawon lokacin nan sannan daga
bisani aka kamashi ta dalilina wannan abu ya matukar farantawa gomnatin America sosai ko ta
ina sunana ne ake ta yadawa mutane kowa sai zuwa sukeyi sukalleni daga.gomna da
tawagarshi ma musamman suka zo suka dubani sannan ya jinjinamun namijin kokarin da
nayi.abinka da turawa sai kyautukka suke ta kawomun na cewa ta sanadiyata sun samu
kwanciyar hankali,saboda kullum suna cikin taraddine da zullumin yaushe za'a kuma yin wata
kisa....yanzu kam wannan batu yakau tunda ankama boyeyyen mutumin da yake aikata
laifin.gomnatin ta mayar da duk wani expenses da aka kashe zuwa account dina sannan ya
kuma daukar nawin yin karatuna daga digree har zuwa gunda naga dama na tsaya a
karatu,sannan da wani makeken gida na gani na fada da aka bani saboda wannan abin da
nayi...
Farin cikin da muke ciki ba sai na tsaya na kashe ku da surutu ba,kuma kunsan recognition a
bainar jama'a abin alfaharine balle abu ya hadu da har presidency sun san da maganar.
'Yan uwa da abokan arziki sai tayani murna suke...Khalid dad yakira ya ce mashi tunda gomnati
ta mayar da kudaden da aka bata awajen jinyata toh ya karbi kudinshi.girgiza kai ya yi har
idanuwanshi sun kada sunyi jajir sannan ya ce, haba daddy aiko duk dukiyata ne na kashe akan
zaratun bazan iya karban wannan kudaden ba ni na batane duniya da lahira wannan da ta
samu yanzu arzikintane Allaah ne ya arzurtata,saboda haka kabar zancen wadancen kudin.ni a
tsarina bana kyauta kuma na sake karba.
Daddy ya jinjina maganganun Khalid sannan ya sanya mashi albarka sosai,sai gashi sunbar
zancen sunkama wata hirarsu.
Shi ma Dr zaid sai da daddy ya sanar da shi cewa ko zai dan karbi wadansu kudade acikin
kudaden da gomnati tabayar,shima kamar Khalid fafur yaki amsar ko da sisin kobo ne.shima ya
ce matsayina awajenshi yafi kudi..
Toh haka dai daddy da Mummy sukayi ta jujjuya maganar Khalid da Dr zaid,sun kasa sanin
yaya zasu bullowa wadannan jaruman samarin..mummy ta ce ni gaba daya kaina ya kulle bisa
dukkan alamu shi ma zaid din son zaratun yake Khalid kam nadanji labarinshi a wajen Maryam
cewa yana son zaratun din,duk da Maryam din take bani labarin duk da dawainiya da Khalid ke
yi mata akwai wani da ita kuma take so,bansani ba ko zaid dinne,tunda mukam bamuga wani
ya zo ba tun faruwar wannan al'amarin.
duk abinda suke fada inajinsu nayi lamo ne wato auntie Maryam sai da ta fadawa mummy
maganar Khalid da yusuf amma ina ganin bata ce Yusuf din bashi da lafiya ba,ita kuma mummy
da taga Dr zaid ta zata shine dayan da auntie Maryam ta ce nafi sonshi.
Dam zuciyata ta buga da naji daddy ya ce ai ita yanzu bata da