Showing 48001 words to 51000 words out of 52878 words

Chapter 17 - WACECE NI BY Fateema Muhammad Suleiman-1.pdf

Khalid din yau yabani tausayi,ga Dr zayd uban love shikam tun ba'aje
ko ina ba ya fara raurau da idanuwanshi.dukkan dakin taron kuma sai yanzu suka farga da
cewa wadannan masoya na ne kuma ko wannensu kuma yana Neman na zabeshi ne a
matsayin gonina...su mummy da suka ganin abin kamar a film sai pointing da hannu suke na
zabi Khalid.

na yi kamar bangane abin da suke nufi ba na rufe idanuna nayi nazari sosai da zuciyata abinda
ta zabarmun shi zan dauka,sai ko ta zabamun Khalid ne ya cancanci na zaba tunda bani da
tabbas akan warkewar Yusuf,da sauri na nufi wajensu Khalid dake tsaye da gomnna,kamar zan
sanya hannu na karbi kyautar sai na kuma juyowa na kalli gunda yusuf da ke zaune rike da dan
Karamin gift dinshi take wani irin tausayinshi da sonshi ya ziyarci zuciyata habawa da sauri na
koma wajen yusuf na karbi kyautar da ya kawomun,jikina sai bari yake kaina kuma sai juyowa
take saboda fargabar abin da na aikata sai kawaici na tsinci Kai na da fadin wallhai kai ne kai
ne yusuf ta amince ta zauna da kai ina sonka ina kaunarka don Allaah kuyimun uziri bisa abin
da na yanke a yanzu sai ga hawaye daga idanuwan yusuf shar shar ,take kuma wani irin sautin
wakar Celine Dion,cikin wakarta na

For all stand you stood for me
For all joy you brought to my life
you are the one who help my life,never let me go,your the show me truth,truth enough

.sai kuma tafi raf raf raf duk dakin ya dauka,sai wadansu abubuwa masu kyalli da suke ta zuba
akanmu.sai da na dawo da kallona sai naga har da su Khalid ake wannan tafi suna murna aiko
bangama mamakin su ba sai da naga Yusuf ya mike tsaya yana taku dai dai yana zuwa gunda
nake furkarshi cike da annuri da murmushi,ai bansan lokacin da ya tafi kasa lu ba sai gani
sumammiya...

_kuyi hakuri da typing errors da zakuyi encountering,saboda banyi editing ba_












*comment*
*share*
*vote*
_Wattpad teemacool2020_


���������������������������������


*WACECE NI*




�🏼by

*Fateema Muhammad Suleiman*

Wattpadteemacool2020



*🌈KAINUWA WRITERS�🏼 ASSOCIATION*�🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is ton entertain & motivate the mind of readers}```

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*page* 4⃣8⃣4⃣9⃣


*Dedicated this pages to my real fans I thanks u all*


_"It's really an opportunity and privilege been in 500 level, after cruising helter skelter to every
nook and cranny of this University and other course related Ministries, finally we are here for our
Final Year Project, we all need to thank God for his blessings, by then we have to work harder,
let's keep pillows with the zeal of sleeping aside, and start the Final Battle, 500 level deserves
only As and hardly Bs for better Class of Degree, and as a Project where everyone belongs to a
group of 10 or 20 or 30 fellow course mates, Team work is of great significance and most
importantly prayers at all times."_



Ina farfadowa daga suman naganni kwance akan lallausan darduma da aka shimfida akan step
din,da hankali na bude idanuwana,duk sunyi cirko cirko a kaina,yusuf nagani da first Aid box,ya
gama dubani sannan ya ce bawani abu bane kawai shocked ne tasamu na sadden
surprise,amma yanzu komai ya zama normal.
Tunda yake maganganunshi jira nake acemun ki tashi daga mafarkin da kike saboda kwata
kwata ban gaskata wannan al'amarin ba gani nake mafarki nake,sai na juya ga Humaira da take
kusa da ni dagani tasha kuka.
Na ce sister don Allaah ina mafarkine ko kuma na zauce please fadamun gaskiya saboda ke ba
za kiyimun wasa ba?

Humaira cikin girgiza kai ta ce sister duk da ni ban fahimci komai ba,amma kina cikin haiyacinki
ba mafarki kike ba.sai a sannan ne na juyo da kaina na Fara duba mutanen da suke
kaina.Khalid,Dr zayd,mummy,dad,da gefe daya kuma Auntie Maryam ce, sai daidaikun mutane
da bangane ko su waye ba,na kuma juyowa da mummy na ce,da gaskene mummy ba mafarki
nake ba?

Cikin takaici ta ce haba my angel ki nutsu ki dawo haiyacinki,taso ki dawo kusa dani,ta
nunamun gefenta na taso da sauri na zauna.sai da aka nutsu kowa ya koma
mazauninsa,sannan MC ,yafara bayani da cewa hakika yau mun riski gagarumin al'amari kamar
almara,lallai wannn al'amari zan iya cewaToday, tomorrow and forever there will be one heart
that would always beat for you.

a wannan rana,a wannan lokaci zamu so musan wannan cakwakiya da yasanya wadannan
dimbin jama'a da suka taru musamman,saboda princess zaratun Hameed tauraruwa acikin
tauraru.wannan taro anshirya shine musamman saboda wannan ranar,hakika gimbiyarmu kin
cancanci numbar yabo,saboda dimbin 'yan mata sun fadi a wannan jarrabawar, tun kafin aje ko'

ina amma ke sai da kika tsallake wannan keshi,muna tayaki murna,kuma muna maki fatan
alkhairi,ke ta dabance kowa kuma ya tabbatar da hakan,mungode.Without much wasting of time
zanso na gabatar maku da kanin yusuf,prince Khalid don ya warware mana wannan cakwakiya
,daganin idanunku nasan cewa kun kagu da son jin wannan al'amarin.
Duk wannan bayanai da MC ke yi ni kuwa tunanin abubuwan da suka faru da yanda naga yusuf
tsaye da kafafuwanshi what a surprised,dama Ashe haka yusuf dina yake,duk da dimbin mazan
dake wajen,duk tauraronshi sai da ya haska wajen,jarumine, a mike yake dogone.gashi da irin
lallausar farar fata da ko mace take dashi zatayiwa maza yanga.duk hankalina ma baya cikin
hall din sai da naji muryar Khalid cikin lafiyayyen turancinshi.sai da yayiwa taron gaisuwa
sannan yafara bada tarihin Yusuf kamar haka

An haifi yusuf Abduljalil a Canada shine da na uku a cikin jerin yara goma da mahaifinmu sarki
Abdujalil ya haifa,mahaifinmu Sarki ne na anarbour Muslim community,kasancewarshi shine
founder na wannan community da ya tara dimbin musulumai dake fadin Canada.asalinmu
larabawane daga Syria.ya yi karatunshi daga primary har zuwa jami'a a nan Canada,ya karanci
aikin likitanci fannin mata wato gynecologist.
da yafara bautar kasarshi na shekara daya akan aikin soja sai yaci gaba da karatun koyon aikin
soja shidin yanzu sojane mai mukamin Major,ya samu mukamai masu dimbin yawa daga gida
har waje ,yanzu haka shine security intelligent to the president of united states of
America.Allaah yayi mashi baiwa sosai.kasancewarshi ba asalin dan kasar ba. Sai da yadan tsaya yaja numbashi sannan ya ci gaba.

amma kuma yasamu mukamai masu dimbin yawa da yayiwa 'yan asalin kasar fintinkau hakan
yasanya ya dinga haduwa da makiya masu yawa.
yashiga neman wata yarinya Sophia 'yar prime minister ta ce,sai daga baya yagane asalin
munafurci aka hada don kasheshi ta hanyar hadin bakinta.

saboda sunyi iyakan kokarin ganin sun kasheshi amma Allaah baibasu dama,toh tun daga
wancan lokaci ya watsar da maganar neman aurenta.sai ya kuma neman wata acikin
unguwarmu,itama daga baya yagane, yaudararshi take saboda haka ya hakura da ita.haka
yayita Neman aure amma daga baya sai yaga akwai munafurci da ake hada mashi. ahaka dai
ya tattara maganar Neman aurenma ya hakura.


Tun daga wannan lokaci na shiga nema mashi mafita sai wani tunani ya fadomun akan cewa ya
nemi friend mata a social media yayi testing dinsu idan ya dace zai samu mace ta gari idan
kuma ba'a daceba za'a iya samun kishiyar haka.

Sai da ya ce mun yasamu wata da yake so amma yayi basaja bai nuna mata ko shi waye
ba,saboda ya tsorata da halin mata.duk da ance ,cewa never lose hope.hope is rope that
swings you through life.
To a hakane na taimaka mashi,

Bana manta wata rana
da yayana Yusuf ya kirani a waya,yabasu kabarin yadda muka hadu da duk hidima da yayi
akaina da motar da yabani duk daga yusuf kaf ya kwasha labari yafada musu,sannan yadan ja
numfashi yayi murmushi ya ce kutayane jinjinawa wannan jarumin aboki kuma aminina wato
zayd ,ya ce lokacin da wancan killer yayi attempting din kashe zaratun da akayi na buya a
gidansu coincidence ne,lokacin da naji labari naje asibiti ne muka hadu da shi yake sanarmun
cewa a gidansu na buya .

Ni kuma na bashi labarin komai sannan na ce ya tayani campaign har lokacin da zamu kai ga
gaci.ahaka har muka kawo matakin da Yusuf yakasa jurewa yayi insisting zai bayyanawa
zaratun hakikanin wayeshi. saboda taci,
wannan jarrabawar dari bisa dari.saboda tun lokacin faruwar kisancan yaso ya bayyana kanshi.

amma na ce yabani dan lokaci kadan nayi hakane saboda yasamu fully support akan zaratun
din.
lamarin ni kaina yana bani mamaki ace,a wannan zamani kasamu Wanda zai soka saboda
Allaah gaskiya sai an bincika.Kada Ku manta duk irin soyayya da kulawa da nake yiwa zaratun
bantaba jin ta furtamun kalmar ina sonka ba,haka yake agun zayd saboda dukkanmu muna
amfani da CCTV camera duk lokacin da zamuje wurinta hira,Wannan halin natane yake ingiza
Yusuf son baiyana kanshi tun ba'ayi nisa a gwajinba,sai da yadanyi murmushi,kafin yaci gaba
dakin kuma duk sun maida hankalinsu sunajin wannan labari mai ban mamaki da ban sha'awa.
Ya kuma yin murmushi ya ce Dan Allaah Ku tafawa wannan dadaddiyar soyayya da tashirinshi
ya taramu anan,na tabbatar muku cewa yusuf irin mutane ne da ake cewa born with a silver
spoon in their mouth.ya so aikin likitanci, shidin likitane,sannan kuma hamshakin soja ne mai
mukamin major.
yanason zaratun kamar kamar son ranshi gashi yau zaratun ta tabbatar maku cewa soyayya su
acikin jini take.sai ko aka dau tafi raf,raf,raf.tunda Khalid ke bayani tsananin mamaki ne fal
acikin zuciyata,sai kallon yusuf din nake da ya dake zaune kusa da gomna,shima kuma kallon
nawa yake cikin tsananin so ko kunyar mutanen wajen ba yayi. Sai da Khalid yaje kusa da zayd suka jeru dukkansu uku naga suna maganganunsu cikin
walwala.yayinda ni kuma hankalina yayi mugun kwanciya ganin yanzu bani da sauran fargaban
cewa na yaudaresu.ina cikin wannan tunanin,MC ya kuma Neman yusuf da yadan bayar da
takaitaccen bayani, sannan a rufe taro.
Cikin kasaita da taku daidai na irin jinin sarauta ya mike sai gashi dakin taron ya dauki kananan
maganganu kasa kasa,sai yanzu kuma nagama karewa yusuf din kallo gaskiya ina cikin matan
da sukayi sa'ar samun mijin nunawa sa'a.
Sai da yayi hamdala ya godewa ubangiji,sannan yafara bayani cikin dense voice dinshi,duk
tsayuwar da yayi ni yake facing,ya zubamun lumsassun idanuwanshi,duk maganganun da yayi
abin da yashafeni ne da abubuwa alkhairi da na nuna mashi daga karshe ya ce to the extend
abin da yarinya ta munyi Wanda bazan iya mantawa da shiba,ya ce we all know what is money
is all about but my wify ta sadaukarmun duk abin da ta mallaka saboda kawai ta ganni ina

takawa da kafafuna.gaskiya wannan wane irin so ne? meye nayi maki har hakada yasanya kika
soni haka?sai ga hawaye shar daga idanuwanshi.
Abubuwa da nake tambayar zuciyata kenan
Sai daga baya nagane Allaah baya zaluntar bawanshi matukar bawan yana bin dokokinsa.

Nima kuma sai hawayen ke zubomun shar,ji nake kamar naje na rungumi yusuf saboda
tsananin sonshi ne ya rufeni a take. Ko ban fada ba
shima ya nuna kamar yazo ya dauke ni ya hadiye yake ji.duk wani masoyanmu awajen sai da
ya jinjina mana,sai sanya albarka suke mana.

Sai yadan ja numfashi sannan ya ce,there are no enough word to describe what I went through
in my mind,when I set my eyes on you.how very precious this is?
Thank you Allaah,for making this possible.....
I love you and I will always love you to the rest of my life.

Sannan ya godewa mahalarta taro da su koma gidajansu lafiya.kyautukka sosai aka raba
awurin wanda naga su Humaira da sauran kawaye nane suke rabarwa.sai yanzu na tuno da
Auntie Maryam juyawan da zanyi sai banganta a wurin da take zaune ba nayi mamaki da alama
nayi nuni da Humaira take wucewa kusa da ni tazo. A hankali ta dawo kusa da ni ta sunkuya kusa daidai kunnena
.na tambayeta ina Auntie Maryam?

May be ta tafi gidane naga tana kuka da na
tambayeta, take sanarmun ciwon ciki ke damunta.
Na tabe baki na ce, ayyah Allaah yabata lafiya.cikin zuciyata kuma fadi nake rigiji rigab,yau ga
Auntie maryam da yusuf ido cikin ido wannan yaya kenan?

Sai da aka watse sannan nagane ashe dai yusuf da yawancin danginshi ne suka zo wajen
taron.farin ciki awajensu mummy ba'a magana 'yan jarida kuwa sun samu hanya sai jefa musu
tambayoyi suke.
A hankali yusuf yazo kusa da ni ya radamun akunnena yarinya wallahi kintaka babbar sa'a ba
aure aka daura mana ba.da yau sai na sauke dimbin kasalan da Kika dauramun yau.

Na zungura bakina cikin shagwava na ce ni ka kyaleni babu abin da nayi maka,bacin kaine ma
ka kacuceni ka tsoratani da salonka why all this game? Wallahi am serious kun sanya
kwakwalwata ta daina aiki for some minutes. Muna cikin haka sai ga Khalid da zayd sunzo
wurin dariya sosai suke,niko na sadda kaina don nafara jin kunyarsu ,sai dai da na tuna duk
kalmomin soyayya da suke furtamun na bogine?
Oh oh oo garin dadi na nesa!
Masu photo kuwa sunyi ta haskamu da camera.sai ga daddy acikinsu suna ta murna shima yayi
ta yiwa Yusuf godiya da tayashi murnar cikan burinshi.

Da 'yan wan yusuf da nawa kuwa anhadu Ana ta raha ahaka muka fito wajen parking lot........

Juyawar da zanyi sai ganin Auntie Maryam nayi cikin korkosa da girgiza jikinta ta nufomu dama
gashi tana da duka biyu daga sama har babu kunya balle tsoron Allaah tayi fari da ido ko gunda
nake bata kallaba balle na sanya ran zatamun murna,cikin salon jan hankali ta fara gaishe da
yusuf............




_kudinga hakuri da typing errors coz bana iyayin editing cikin kwanakin nan_








*comment*
*share*
*vote*
_teemacool2020_
Wattpad

���������������������������������


*WACECE NI*




�🏼by

*Fateema Muhammad Suleiman*

Wattpad teemacool2020



*🌈KAINUWA WRITERS�🏼 ASSOCIATION*�🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is ton entertain & motivate the mind of readers}```

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*page* 5⃣0⃣&5⃣1⃣






*wannan page nakune masoya Yusuf da zaratun ina jin dadin comment dinku sosai my real fans
bazan iya ambatonku ba saboda kuna da yawa I love you wujiga wujiga*
_sai mutanena na fikrah writters Especially shalele, Hassan & Hussain 80k,Maryam
Obam,Hassana Danlarabawa gaskiya kuna sanyani nishadi lots of love💋💋💋_




*Today's Beautiful Hadith is about Ablution*

It was narrated from Ibn Abi Sa'eed Al-Khudri (RA) that his father said: "I passed by the Prophet
(peace be upon him) when he was performing Wudu' from the well of Buda'ah. I said: 'Are you
performing Wudu' from it when garbage is thrown into it?' He said: 'Water is not made impure by
anything.'"
(Sunan an-Nasa'i, Book 2, Hadith 3)

*_We take water for granted as a purifying and purified source. We feel thirsty, it can be
quenched by this natural blessing from Allah. Alhamdulillah for water which we use to wash
ourselves and prepare for Salah._*






Yusuf dake hankalinshi duk da yake kaina da na shagwabe mashi,sai riritani yake duk da
dimbin taron 'yan uwa da abokan arzikin da suke tsaye.Auntie maryam sai kara matsowa take
cikin fadin Yusuf da kai nake fa wai baka ganeni bane?
Ko kallo bata ishashi ba ya yi banza da ita duk maganganu da take da salonta bai ma san tana
yi ba.sai yanzu nagane,Yusuf irin mazan nanne masu wuyan gane hakikanin halinsu zan iya
cewa miskiline.amma kuma yana da karamci.abin da yayiwa Auntie Maryam kawai zai sanya
duk wani mai tunani jin kunya.silent is the best anawer to a pool. Kai su Yusuf akwai dakiya

kowa a wajen sai da tajawo hankalinshi gareta saboda wani irin roko ta tsaya yi mashi wallahi
nima so nake na gwada ka ne a wancen lokacin.sai wannan munafukar ta nunoni da dan yatsa
sannan ta ce ta dauki number wayanka bayan ta goge number ka a cikin wayata.to tun daga
wancen lokaci na daina jin duriyarka,Ashe munafuka yaudarata tayi, tamun snatching dinka. ta
karasa maganar ta cikin kukan munafurci.

Ikon Allaah kaji wata sabuwa inji dan caca,Auntie Maryam lallai batajin tsoron Allaah kazafi Kiri
Kiri agaban idona.mutum kenan kaji tsoronshi.

Gogan naku Yusuf ko gizau baice ba asalima duk hankalinshi akaina da nayi raurau da idanuna
jin maganar Auntie Maryam ganin bashi da niyar mayar mata da martani, ya ja hannuna da
niyar barin wajen sanya Khalid yin magana da cewa Adeel wayece wannan? kuma zaka
barmana ita ba tare da ka saurareta ba.ba bakuwarka ba ce?duk da shima Khalid sarai yasan
kwanar zancen da komai sannan yasan auntie maryam farar sani. amma yanzu gashi, ga ita ya
take, kamar baitaba ganinta ba.

Yusuf cikin kasaita ya ce no I have never set my eyes on this frame,zaka iya tambayar ta ko
kamanni na ta sani, koko tana dauke da ciwon haukane. anyway non of my business my wify
tana bukatar hutu zanyi dropping dinta then naga Ku har yanzu tsayiwar bata isheku ba so idan
kungama ma hadu a gida.daga haka bai kuma cewa komai ba sai da muka je kusa da motarshi
kirar Lamborghini, wannan motor karshene wajen kyau da tsari.
sai da yabude gaban motar ya zaunar da ni ahankali kamar wata jaririya sannan ya zagayo
yashiga ya tayar muka fita daga harabar wajen.

Komai na Yusuf dabanne tukin motor ma cikin kasaita yakeyinshi,sai da muka danyi nisa da
tafiya ya rage gudun motor ya tsayar a gefen hanya ranshi in yayi dubu ya baci sosai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login