Showing 45001 words to 48000 words out of 52878 words

Chapter 16 - WACECE NI BY Fateema Muhammad Suleiman-1.pdf

cewa yusuf zan kasance tare da kai a duk halin da kake ciki amma
daga ni har kai dole mukai zukantanmu nesa saboda akwai matsaloli da zamu fuskanta.....

Ya ce nasani my wify ,kina tsoron iyayenki ne akan bazasu yarda su aura maki masaki mara
kafa ba....

Na nisa, bankuma cewa komai ba, gaba daya nashiga cikin tunanin yadda zamu bullowa
Lamain......

Kusan minti biyar babu wanda ya yi magana na dauka ma ya katse wayar, sai da naji ya ja
numfashi, na gane yana kan wayar. daga bisani ya yimun sallama tare da cewa my wify ki koma
baccinki in sha Allaah,
Allaah zai kawo mana mafita good night..

Nima na mayar mashi martani da good night too bye.....




_masoyan yusuf next page zakusan waye yusuf😜_








*wayan comment yawan typing please kuyimun share,vote* _teemacool2020_ _wattpad_



���������������������������������

*WACECE NI*




�🏼by

*Fateema Muhammad Suleiman*
Email fmsuleiman743@gmail.com
Wattad teemacool2020



*🌈KAINUWA WRITERS�🏼 ASSOCIATION*�🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is ton entertain & motivate the mind of readers}```

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*page* 4⃣6⃣&4⃣7⃣






*DAILY DAHWA*
[14, ROBIU THANI 1441]

```Allaah is sufficient for us, Truth are the words Allaah ï·»`

*QURAN*
*Therefore remember Me, I will remember you. Give thanks to Me, and reject not Me* (2:152)

*HADITH*
Umar ibn. Khattab (يضر الله هنع ) asked " Messenger of Allah what kind of wealth should we
acquire?" The Prophet (ï·º) replied: *Let one of you acquire a thankful heart.A tongue that
remembers Allah.A believing wife who will help him with regard to the Hereafter*
-(Ibn Majah)

*DUA*

Oh Allah (لج هلالج) *You know my situations better than I do, please forgive me and grant me
what is best for me*

*AAMIIN*



Ana kiraye kirayen asatu na farka da sauri na sauko daga kan gadon,saboda banason nayi latti
ina da lecture 7am.komai cikin sauri nayishi cup daya ba tea na sha sannan na kama hanyar
makaranta cikin sauri nake driving saboda na fara hawa motar da Khalid ya bani bayan samun
umarni daga daddy.da farko bai yarda ba,sai bayan faruwar al'amarin da ya yaba da Khalid
din,da yanzu suka zama kamar da da mahaifi saboda shakuwa.

Mun fito daga lecture kenan sai ga khalid,cikin murmushi yake gaba toni idonshi sanye da bakin
space shigan kananan kaya yayi,sun mashi kyau sosai.

Tashi nayi daga wajen da nake na zo kusa da shi ganin bashi da niyar zuwa dai dai wajen da
nake zaune cikin colleagues dina yawancinsu kuma maza ne yayi kicin kicin da ido wai shi yana
kishin ganin muna zama acikin maza,yana kuma yimun kashedin hakan a koda yaushe cikin
zuciyata kuwa cewa take kajimun mutum fa kai ba aure kake ba amma kana tsaramun yanda
zan gudanar da rayuwata duk da nasan kaina ba kula wasu samari nake ba wadannan kam
yawancinsu ma age mates dinane,sannan kuma abikanan karatuna ne so what is wrong da har
zai dinga takuramun.

Kamar yasan abinda nake fada azuciyata,sai ya yi murmushi ya ce,yes gaskiya na ne dole nayi
kishin ki,ni da son samune ma babu wanda zan yarda ko kallo ya yi maki ,bazaki sani
bane,amma duk lokacin da na samu sa'ar aura Mani ke zaki ga real love nake maki.don Allah ji
bani chance na turo maganata na wallahi ina cikin matsala fa yarinya ki tausayamun tun da su
daddy kam nasan basu da wata matsala akai.

Sai da naga yayi shiru,sannan na dago kaina sosai na kuma kare mashi kallo shima kuma
kallon nawa yake,sai ya ciro space din dake sanya akan idonshi ya ce ki dubi idanuna tsantsar
sonki da son kasance tare da ke acikinsu.

Sai da na dube idanun nashi sun rine sunyi jajir,tsananin so na ne shimfide acikinsu,nifa gaba
daya wadannan guys din sun jefani cikin tsaka mai wuya,wannan irin yanayi fa gaskiya ko a
exams ne aka baka karubuta assay akanshi to ba karamin matsala bane zaka sha na fiddoda
hakikanin amsar da zai gamsar da malaminka, to ni kuma gashi practically ina
fuskantarshi.bangama wattsake daga maganar yusuf ba,sai ga na Khalid .a gefe daya kuma Dr
zayd da shi ko sauraron maganata bayayi idan na ce ya yi hakuri ya bani lokaci sai fura wutar
cewa cikin satinnan zai gabatar da magabatanshi,saboda yafara tsorota da ni kar yayi sanya
akasashi.cikin zuciyata kuma duk ba ta su nake ba.ina son ganin yusuf dina yasamu lafiya naji
dadin gabatar dashi da hujjar cewa,shine farkon wanda yafara furta yana sona kafinsu.

Sai da na sauke kallona daga kanshi sannan cikin sanyin murya na ce,
Khalid kamar kullum babu abin da zan iya cewa sai dai kayi hakuri,ka bani dan lokaci kadan
kamar yadda kasani tun farko na fada maka akwai Wanda muke fita dashi to bashi da lafiya
ne,ina tsoron kar ya zargeni da na yaudareshi idan yaji maganar ka agidanmu,dama inason na
lallabashi ne har ya hakura da ni, sai na baka damar katuro nagabatan naka.tsawon lokaci
yakuramun idanunshi,gani yake kamar ya daukeni ya hadiye..

Sai yadan nisa yaja dogon numfashi ya ce,
Gaskiya yarinya na fara tsorota da wannan man da kike magana akanshi wane irin so ne kike
mashi haka?
A sanina fa duk wannan jinyar da kika sha banganshi ya zo wajenki ko sau daya ba,amma ki
duba ni akanki wallahi da zan fada maki irin abubuwan da na fuskanta zaki daura hannu aka
kiyi ta iho amma duk na share na mantasu saboda ina ganin wata kila zan iya samun wani gurbi
daga zuciyarki .amma kuma abin da na fuskanta zuciyarki ko gizau batayi ba wajen sona.ki
duba ki gani fa cewa kike bakyason ya zargeki da yaudara ni kuwa oho. kenan baki damu da
halin da zan shiga ba...sai da ya girgiza kai ya fada a fili this love,u can't escape for fate....

Kasa bashi amsa nayi ganin yadda zuciyarshi ta baci banta ba ganin Khalid ya shiga cikin irin
wannan hali ba gaba daya ya canjamun.sai kawai nayi shiru ina kallonshi har ya dan sauko
daga fushin da yake.

Da kanshi yadan murmusa ganin yadda nayi kicin kicin da ni kamar mai son yin kuka,Allaah
yayine mai jin tausayin mutum da karaya a duk lokacin da naga abin tausayi bana iyayin
resisting hawayena,sanadin wannan tausayin ne ya jefani cikin wannan tsaka mai wuya,ko
kadan bani da jarumtar fadawa duk Wanda ya ce,yana sona bana sonshi,sai dai nayi ta yi maka
kame kame da hanya hanya,har mutum ya gane da kansa ya fita hanyata.shi kuma Khalid ya
katse ya tsare har muka shaku da shi har zuwa wannan lokacin.

Nima na saki raina muka ci gabada hirarmu cikin kwanciyar hankali,sai da yaga lokacin lecture
mu yagabato ya yimun sallama tare da jaddamun cewa sati biyu ya bani,idan suka cika to ba
makawa cewa kawo iyayenshi wurin daddy su gama maganar aure har da cewa,na gaji da
ciwon mara nan yarinya kisan yadda zakiyi da ni.....sai kawai naga ya kamo hannuna ina,da
sauri na dubeshi ya dake baidamu da kama hannunnawa da yayi ba,sai ga dan karamin box
zobe yaciro na what gold mai matukar kyau sai da ya sanya a yatsana na tsakiya das yayimun
kyau kuwa sosai,sai da ya tsumbaci hannun nawa ya ce I love you, ki adanamun kanki,take
care ki koma gida lafiya.

Wani irin kallo nayi mishi mai rikuta duk Wanda akayi mashi sannan na ce thanks so much my
man,Allaah yakara budi ya tsaremun kai.thanks once again.har wurin motarshi na rakoshi
sannan na bi haryar hall naga har amfara shiga....

***************



Haka rayuwa tayi ta tafiya,yayinda nake zuwa makaranta na cikin kwanciyar hankali da walwala
,duk da kowane banagre na masoyan nawa suna ta damuna da neman iznin gabatar da su wa
daddy hakuri nake ta basu har ta kai ga cewa shi daddy da kansa ya ce mun my princes yanzu
lokaci yayi da ki zabi daya daga cikin wadannan yara saboda gaskiya nima na gaji da yadda
suka rige rigen kamun kafa a wajena,yanzu ni kaina kasa ganin waye ya dace acikinsu nayi
saboda dukkansu ba kanwar lasa bane mudai addu'armu Allaah ya zabar maki magi alkahairi
acikinsu,na ce Aameen daddy,a dan bani lokaci saboda yanzu ina dab da fuskantar council
exams dina,ya ce toh amma kiyi tunani ki cire daya daga cikinsu musan abinda ya dace.

Muna zaune ni da Latifa
Yau tsawon daren na kasa bacci sai kawai na tashe ta daga baccinda take gaskiya ni kaina
abubuwa sun fara rikicemun yanzu,kasa yanda zanyi da rayuwata nayi maganganu sun fara
isata,na ce, sounty na please ina tsaka mai wuya fa yau ina son ki bani shawara ne I mean
goyon bayanki nake nema,kawai mafita zaki nemomin,kuma duk abin da na ce shi da shi zaki
nemomun mafitan na kura mata idanuna ina jiran abin da zata ce.

Sai da ta dan harareni da gangan,sannan ta ce badai Neman shawara kike nema ba kawai ki ce
commanding dina kike.

Ya ce koma meye zaki ce,let me talk my issues first. Kinga akansu Khalid ya Fara matsamun da
na cire daya daga cikinsu ina ganin suna zuwa wurin daddy suna damunshi kinga ni kuma
bazan so hakan ba,at long last kuma ni suke jawowa ruwa.saboda ni gaskiya zuciyata,yusuf
take so take so ta karasa rayuwarta tare da shi....yanzu muka gama waya da yusuf,cewa
kudaden da suke cikin account dina zan bayar ayi mushi final operation da za'ayi amma
wannan zamu canja country.toh shi ne na ce ki zana witness dina saboda yaki yarda da karban
kudin ba sai da sa hannun dan uwana ,kuma kinsan bazan sanar da su mummy ba sai bayan
yusuf ya warke.sai da nagama maganata itako Latifa ta kuramun idanu daga ni mamakin
maganganuna take.

Sai da ta dan nisa sannan kamar tayi kuka ta fara magana da cewa,
Lallai *zaratun* Sai yau nagane cewa you are insane,how could you let such a thought enter
your mind?at the first place ma toh ni Wai waye ne Yusuf? Menene asalinshi da hakikanin inda
ya dosa akan sonki?
Let me predict, ace ma inda da gaske sonki yake toh ko da bashi da lafiya dole ya nuna kanshi
agaban kowa idan har soyayyar gaskiya yake maki kenan amma ki duba fa a koda yaushe yana
cikin boye maki kanshi da zuriyarshi.duk jinyar da kikayi ya kasa turo ko da kaninshi ko

kanwarshi,su dubaki idan shi bazai iya zuwa ba amma baiyi ko daya ba.
Ke kuma da yake giyar sonshi ke dibarki yasanya kika sanya kafa Kika shure.toh nikam gaskiya
bazan sanya hannu cikin wannan gangancin da rashin sanin tudun madafa ba.
Kuma gaskiya idan baki janye wannan shawarar bashi kudaden nan ba zan sanar da su daddy
hakikanin gaskiyar lamarin...

Aikuwa bansan lokacin da kuka ya kubcemun ba da jin kalamenta masu zafi ne akan yusuf
dina,wallahi da tasan yanda nake ji da shi,baza tayi garajen furta wadannan maganganun ba.
Sai da nadan samu relief daga zafafan kalamunta sannan na dubeta ido cikin ido na ce,sosai
nagade da kalamenki amma don Allaah ina rokonki da cewa keep it to yourself wannan
maganar banason kifitar munshi,hakan da zakiyi shi zai kawo zaman lafiya a tsakaninmu kamar
yadda kishiyar hakan zai kawo gagarumin matsala sakaninmu,ina fatan kin fahimce abin da
nake nufi? Yusuf kuma zuciyata ce ta yardada shi,so babu abin da zai sa nadaina sonshi duk
halin da yake ciki.so be careful with your word against yusuf duk wannan maganganun ina yinsu
cikin bacin rai wanda ita kanta Latifa sai da ta tsorata da ni.daga haka bankuma cewa Kala ba
na juya nayi kwanciyata.

Itama ta kwanta duk jikinta yayi sanyi da maganganuna,bata taba kawo a ka cewa har haka
nakeson yusuf lallai wannan abu azimun ne....


Da safe misalin karfe goma na safe,kasancewar yau lahadi ne duk muna gida full house kenan
kowa kuma harkar gabanshi yake,sai na dauko wayata na kira Humaira akan maganar liyafar
da ake kan shirin shiryamun na musamman daga gidan gomnati Nobel price,akan taimako da
na bayar wajen kama wannan gagarumin dan ta'adda da ya gagaresu shekara da shekaru.shiri
sosai da zai samu halartar manya manyan jigagen gomnati.

Muma kuma muna kan shirin ne duk wani nawa sai da muka gayyata kama daga dangi,har da
kawayena.Yau ya kama saura kwana uku kenan.
duk wani shiri da nake bukata kuma Khalid shine akan gaba.ga zayd da yadinga zirga zirgan
bin government official don raba musu nvitation card. Bayan tayimun bayanin abubuwan da
suke gudanarwa a gida na gamsu sosai da bayananta sannan na katse wayar,na juyo na
fuskanci Latifa na bayyana mata abubuwan da ke Lafiya ta jinjina kai sannan ta ce Allaah yasa
muyi wannan taro mu gamashi lafiya.

Na ce Aameen Allaah dai yakaimu lokacin.


Bayan mun idarda sallar isha'imuna shirin fara cin abinci, sai ga kiran Khalid
Bayan mun gaisa ina yimashi bangaji ,yashiga yimun bayanin abubuwan da ya gabatar sannan
ya ce ki duba WhatsApp na turo maki da PDF na bayanan abubuwa da ya dace kiyi maganarsu
a wajen taron,kuma kin tun yanzu ki bi ta kansu saboda tsayuwa agaban dinbin jama'a akwai
wahala sai kin hada da kokari da juriyar kallon idon mutane....

Na gamsu da duk bayananka kuma zanbisu nagode da kulawarka gareni inajin dadin
kasancewarka cikin rayuwata.

Stop it abin da ya ce kenan,bana son kina godemun a duk lokacin da nayi maki wani abu.
bayan mun gama cin abincinmu banida niyar yin kallo saboda haka bedroom na wace nayi
shirin kwanciyata,sai ga kiran zayd shima yayi ta yimun bayanan abubuwan da ya gabatar da
duk gunda yakai katin yafadamun shima nayi ta yi mashi gidiya,da yake shi dan love ne sai da
yayi ta kasheni da kalmomin soyayyarshi sannan yabarni na kwanta.
Kamar kullum karfe biyu da rabi sai ga kiran Yusuf don sabawa har na saba da kiran da
yakemun tskiyar dare,munsha hirarmu na love sannan na kuma tuna mashi cewa liyafar da
za'agabatarmun saura kwana uku,ko da bazai samu damar zuwa ba ya turo wani nashi da zan
gani kuma na nunawa su daddy,saboda sun fara kunnomun kai da maganar aure cikin damuwa
ya ce toh my wify tunda haka kike so toh zan sanya kanwata ta halarci taron in sha Allaah..

Naji dan sanyi a raina ko ba komai dole a wannan rana su Mummy su san da maganar yusuf.




Yau Alkamis yayi dai dai da ranar zagayowar Haihuwa da kuma gagarumin taron da aka
gabatar musamman saboda ni wajen ya tsaru matuka ta yadda tsayawa ina bayyana maku shi
kauyencine .manya manyan jigagen gomnati da masoya da abokan arziki duk sun hallara a
wannan taro. Ko ina ana haskawa da camera kala daban daban na tashoshin TV na kasan da
ma ba na kasan ba.sai da aka dinga gabatar da zuwan manya baki da gabatar da su ga
taron,bayan wadanda ya dace suyi magana sun ciki kuwa har da ni da na gabatar da dan ta
kaitaccen bayani,tun da na mike cikin taku dai dai na amshi mic din,sai da nayi nazarin cikin
dakin taron da mutanen daya bayan daya duk zaratan samarin nawa sunsha kamshi da shigan
da sukayi kamar Wanda zasu je gasar African idol.daga zayd har Khalid din sun zauna a waje
ma banbanta.amma dukkaninsu sun kuramun idanuwashi cikin sha'awa,bangama kare musu
kallo ba sai kawai idona ya hangomun Yusuf zaune akan wheelchair,kamar gizo idona kemun
na kuma murza su sosai na kuma kallon wajen babu tantama shidin ne zuciyata ta ba dam
ganin da yayina kura mashi idanu babu kakkautawa,ya sanya yimun nuni da hannu cewa bai
samu wanda zai zo taron ba,sai kawai ya zo da kanshi saboda ya farantamun jinjina kaina
nayi,na kuma bayar da hankali na ga dimbin jama'ar dake gabana suna jiran jin bayanai na.
Cikin bayani mai kayatarwa da gamsar da mai saurarona nake bayani a tsanake cikin nutsuwa,
Sannan na koma ma zaunina na zauna.sai da kowa ya gama bayaninshi,sannan aka bude
kofar bayar da kyaututtuka....
Sai ga sanarwa cewa prince Khalid zai gabatar da kyautar soyayya ga masoyiyarshi da suka
shafe kusan shekaru biyu suna soyayya wato uwar buki *Zaratun Hameed* da dam dam
zuciyata tabada lallai ko yau Khalid ya gama da ni dama dan abin da yakeson shiryamun ne
yadinga zumudin zuwan ranan nan tab,yau za'ayita kenan ta kurum kus.bangama dawowa

daga tunani na ba sai ganin Khalid nayi ya fito da wani irin gift duk an nannadeshi da wani abu
mai walkiya kamar diamond, sai aka kuma kiran mai girma gomna shi ne Wanda zai gabatar da
kyautar Khalid a hannunshi.ganin bani da niyar fitowa aka kuma Kira na da cewa masoyiyar
prince dinmu mai girma ki fito maraba da isowarki ya mai girma.babu yanda na iya sai kawai na
mike na fito kan step kafin na karaso kuwa sai ga zayd shima shima yafito dauke da gift
dinshi,kaka tsara kaka sai ga uban gaiya yusuf ya ja wheelchair dinshi yadinga kokarin hawa
kan step din da ya kasa wani dake kusa da shi ya taimaka mashi shima yahau kan step
din.shima kuma da dan karamin kwalinshi na gift suka ja suka tsaya kallon kallo aka tsaya yi da
juna kowa kuma yanason sanin wannan cakwakiyar MC da tun faruwar lamarin ya kare musu
kallo don shi baisan abin da su zayd ke nufi,ya kuma cewa to princess zaratun ke prince dinmu
ke jira don mika maki zoben alkawarin aurenshi taka da hankali ki amshi wannan gagarumin
kyauta.daya bayan daya na tsaya kallonsu dukkan ukun kuma yana mikamun abin da ke
hannunshi nuna alamun na karbi nashi.
Sai da nagama yin nazari akansu hankalina gaba daya ya koma kan yusuf da ya zama abin
tausayi..da na juya shima

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login