Showing 36001 words to 39000 words out of 52878 words

Chapter 13 - WACECE NI BY Fateema Muhammad Suleiman-1.pdf

gidajen mutane kusan gida uku na buga
amma duk a rufe kuma babu wanda ya jini,abinka da rayuwar turai kowa mind your own
business ne.Allaah yabani sa'a a gida na hudun ina tura kofar sai na jita a bude da gudu na
shiga cikin gidan wani dan karamin daki na gani abude ina shiga na Kama kofar na kulleta.shi
kuwa wancen mutumin yana ta duba cikin gidan ne a zatonshi ina ciki kuma ganin ya yanke ni
da yawa bazan iya gudu ba saboda haka bai wani nemeni ba yatafi, ni kuwa daga shiga
wannan waje bankuma sanin inda kaina yake ba.










*share vote and comment*

���������������������������������


*WACECE NI*

�🏼by

*Fateema Muhammad Suleiman*
Email fmsuleiman743@gmail.com
Wattad teemacool2020



*🌈KAINUWA WRITERS�🏼 ASSOCIATION*�🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is ton entertain & motivate the mind of readers}```

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*page* 3⃣9⃣&4⃣0⃣




*Today's Hadith is about Acting When Seeing Wrong*

Abu Bakr As-Siddiq (RA) said: "O you people! You recite this Ayah: Take care of yourselves! If
you follow the guidance no harm shall come to you. I indeed heard the Messenger of Allah
(s.a.w) saying: 'When the people see the wrongdoer and they do not take him by the hand, then
soon Allah shall envelope you in a punishment from him.'"
(Jami`at-Tirmidhi, Book 33, Hadith 11)




Ina kwance cikin wannan dan karamin dakin bansan inda kaina yake ba, dukkan jinin jikina
kuma ya gama zuba da kanshi bleeding din ya tsaya su ko 'yan gidan basu san ma nashigo
gidan ba sai da gari ya yi haske,bayan sungama shiri zasu fita kenan suka fara karo da staining
na jini da shatin kafar mutum suna bin kafar mutum, har zuwa gunda shatin kafar yakare daidai
wannan dakin da nake ciki dukkansu sun tsorota da taba kofar dakin.wani a cikinsu mai suna
zaid ya yi ta maza ya turo kofar sai ganina sukayi kwance cikin jini dagani babu rai.musayar
kalmomi suka dinga yiwa junansu daga mai cewa mu kai report police station,zaid da tun da ya
ga halin da nake ciki yashiga taba dukkan fannin da yasan za'a gwada agane mutum ya mutu
ko yana raye,ya yi iyakan kokarinshi wajen gane ina numfashi daga karshe da ya duba pulse

dina,ya gane ina numfashi amma ina cikin critical condition da yake dukkansu medical doctors
suna kan yin internship na su ne,sun gane cewa ina da rai...
Duk da suna tsoron yanayin da nake ciki da wuya na rayu amma sunyi farin cikin jin ina da
rai,cikin gaggawa suka kira jimi 'an FBI,saboda basu damar taimakona ba tare da sahannun
hukuma ba kuma su kansu suna cikin fargaban meyene musabbabin faruwar hakan da zuwana
wannan daki? Cikin minti goma sai ga Jami'an tsaro kusan mota uku,wadansu suna cikin mota
sauran kuma suka shigo cikin gidan tun da kofar gidan kuma suka fara bin jinin dake kasa
hakan yana nufin Wanda akayiwa kisan daga waje ya shigo gidan don buye kanshi.har suka
gama binciken gidan gaba daya sannan zaid da tun da Jami'an suka shigo yake sanar da su
cewa ina da rai ayi sauri a bani taimakon gaggawa amma basu kulashi ba sai da suka gama
bunciken gidan sannan suka bada umarnin tafiya da ni asibiti.daga nan suka fara bin shatin
kafar daga waje har zuwa cikin gidanmu to a lokacin ne suka kuma shiga tashin hankali mara
misaltuwa ganin jinin da ke malale a kofar dakinmu suna cusa kai kuwa sukayi arba da gawan
Arrauda akan godon duk jini ya bata farin zanin gadon.bayan sungama buncika gidan babu abin
da suka samu na tuhuma itama asibitin aka wuce da ita.intensive care unit aka shigar da
ni.taimakon gaggawa aka shiga yimun dan ganin numfashi na ya dawo normal,jini leda shida
aka nema saboda dukkan jinin jikina ya kare.duk wannan abin da akeyimun zaid shi ne akan
gaba,jinin ma ya ce a debi nashi saboda yana group 0 negative ne universal donor.da kanshi
yaje lab aka gwada dukkan gwajin da sukeyi kafin daukar jini sannan aka debi leda daya,duk da
yasan ba'a daukar jini leda biyu a lokaci guda ajikin mutum amma sai da ya ce akara dibar wani
ledar, lab technician din ya yi murmushi ya ce haba Dr da kanka ai bama daukan jini leda biyu a
lokaci da sai bayan wata uku za ka iya bayar da jini.Dr zaid ya yi murmushi sannan ya ce
nasani kawai na tausayawa patient din da zan baiwa jinin ne tana bukatar taimako.lab
technician din ya jinjina kai ya ce Allaah ya bata lafiya matar ka ce? Ya yi mashi tambayar ne
saboda ganin irin damuwar da ya shiga gaba daya ya canja kamannishi.

Dr zaid ya juyo ya kuma kallon lab technician din,sannan ya shiga nazarina yadda ya ganni
kwance santaleliyar budurwa mai kammala sai kawai maganar lab technician din nan ya
burgeshi ya sanya a ranshi cewa gaskiya wannan baby Allaah yabaki lafiya kuma na kamawa
kaina ke a matsayin mata.sai ya ce wadda zan aurane.lab technician din ya kuma yi mashi add
u'ar Allaah yasa ayi aikin a cikin sa'a ya tashi kafadunta.
Ya ce Aameen .Sai da ya tabbatar ansamu dukkan jini leda shidan sannan ya komo dakin da
nake kwance.angama shiryani domin shiga dani dakin operation.da aka nema sanya hannun
taimakon gaggawa ma zaid din ne ya sanya hannunshi.
Wayoyinmu da suka dauko a gidane suka shiga neman iyayenmu.
Da farko iyayen Arrauda ne suka fara zuwa sannan sai ga su Mummy ma sun zo lokacin kusan
awa hudu ne kuma duk wannan awowi ana kan yimun aikine domin yayankani sosai dayake
ba'a yanka mutum ta gaba,makagoro baya yankuwa sai ta baya.fatan wuyana duk sun samu
damage. Bayan angama binciken irin wakar da yayi amfanin wajen kashemu aka gane nutumin da ya yi
kisar da wannan mutane hamsin kenan ya kashe kuma ba'asan dalilinshi na yin wannan kisar
ba,kuma babu wanda ya taba ganinshi tunda yake kisar sai dai a wayi gari aga anyi kisa amma
ba'a gane wanda ya yi kisar da musabbabin yinshi kusan shekara talatin ake nemanshi amma

har yau ba' a ganoshi ba.abu biyu yake amfani idan zaiyi kisar wuka ko silent pistol.haka iyayen
Arrauda suka dauki gawar 'yarsu suka tafi da shi.idan ka kallesu dole idanunka su kawo kwalla
duk rashin imanin mutum kuma dole yaji tausayinsu mahaifiyarta kuwa sumanta yafi a kirga.

Ta fannin mummy kam tashiga cikin kololuwar damuwa sai kuka da sumbatu takeyi daddy yana
ta bata baki amma taki shiru duk da shima daurewa yakeyi irin ta maza amma kallo daya zakayi
mashi kagane yana cikin matsanancin damuwa.

Sai ga khalid da Auntie Maryam ma sun samu labari sun zo,kowa yay I shiru suna jiran fitowata
daga dakin operation da yanzu kusan awa biyar ana abu daya.Humaira da idanuwanta suka
fada sun rine sunkoma jajir saboda kuka sai cewa take don Allah sis karki mutu ki barni idan ko
hakan ta faru wallahi rayuwata tana gargada domin nima zan biki ne bani da kowa bani da kawa
ko abokiyar shawara don Allaah kiyi hakuri kada ki mutu ya abar sona da tausayina.kukan da
Humaira keyi da sumbatunta kowa sai da yayi kwalla auntie Maryam ce ke rarrashinta ta daura
kanta bisa cinyarta tana share mata hawaye sannan ta ce kiyi hakuri sis in sha Allaah zaratun
za ta samu lafiya .

Khalid ma sai kaiwa da kawowa yake,da ganinshi shima yana cikin damuwa.
Ana cikin haka sai gashi amfito da ni daga dakin ciyatar shame shame kwance kamar babu rai
amma ansamu nadarar ceto rayuwata sun samu nasarar daidaita numfashina.duk suka mike
sukayo kan gadon sannan aka wuce da ni intensive Care unit din.kowa sai hamdala yake yi
ganin anyi aikin cikin nasara,zaid sai washe baki yake yana nuna farin cikinshi da kanshi ya zo
wajensu mummy,yake sanar musu cewa Ku kwantar da hankalinku tana farkawa komai zai
daidaita domin munyi nasara sosai awannan aiki.mummy sai kwarara mashi godiya take ganin
yadda ya tsaya akaina aka gama komai.
Ta bangaren yusuf kuwa tunda aka suka sauka a Germany yake ta kiran number ta amma bana
dagawa yayi mamaki sosai sai kawai ya turomun sako ko lafiya ina kiranki bakya
dagawa?saboda shi bashida masaniyar abin da ke faruwa.karfe biyu za'ashigar da ni aiki
saboda haka ina Neman addu'_arki..I missing you badly I love.
Dai dai lokacin magariba sannan Khalid yayi ma su mummy sallama ya tafi tareda jaddadawa
auntie Maryam cewa duk lokacin da na farka ta sanar da shi.

Ta ce toh in sha Allaah za kaga feedback at any time.

ya ce toh mu kwana lafiya...

Bayan sunyi sallah daddy ma ya dawo daga masallacin asibitin sai ga zaid niki niki da ledoji
abinci ne Kala Kala nasu mum daban da na daddy shima daban.mummy tayi ta koraro mashi
addu'a gaskiya ta yaba da wannan zaid din ganin irin hidimar da yake tunda suka zo shine
akan komai har ta kasa hakuri ta tambayi auntie Maryam akan wayeshi?
Auntie Maryam ta ce wallahi mummy nima sai yau na ganshi, da na tambayeshi yake sanarmun

cewa gidansu zaratun din ta buya lokacin da abin yafaru, shima kuma student doctor ne ya na
internship nashi ne Yanzu haka.mummy ta ce gaskiya na yaba da hidimarshi tun zuwanmu yana
tsaye akan komai, yana da tausayi.

Auntie Maryam ta jinjina kai ta ce gaskiya ya kyauta sosai.Allaah ya biyashi,mummy ta ce
Aameen.sai ga kanina yusuf da manya manyan ledoji a hannunshi,ya ce mun fita tare da uncle
Khalid ne yabani wannan ya ce na kawo.mummy ta ce ayyah wannan kaya haka ai da bai
wahalar da kanshi ba ga wannan ma bamusan gunda zamu sanya ba.....babu wanda ya ci da
bisket ne acikinsu mummy ce ma take basu umarnin su ci wani abu amma duk duka ki ci
saboda har yanzu suna cikin zullumin banfarka ba kusan awa hudu kenan da fitar da ni daga
dakin ciyatar.
Sai ga Dr zaid ya zo ya yi musu sallama ya ce muna sa ran nan da awa daya ko biyu zata farka
rashin farkawarta ba wani abin tashin hankali bane yanayin aikin ne haka basai na bata bakina
ba ga oga nan ai shi yasan komai daddy ya yi murmushi ya ce ,toh zaid muna godiya sosai da
wannan hidima gaskiya bamu da cikakkun kalmomi da zamuyi amfani wajen yi maka godiya sai
dai muce Allaah ya saka maka da alkhairi mungode sai da safe Allaah ya kaika gida lafiya zaid
ma cikin girmamawa ya ce Aameen dadi nima ina godiya sannan yabar asibitin....

Kasancewar Daddy likita ne ake barinshi yake dan dubani duk bayan awa daya saboda
intensive Care ba'a barin kowa ya shiga.....

Karfe daya na dare nafara jin kamar ana yawo da ni a sararin samaniya ,sannan na farajin
kamar lafiyar mutum sai kuma wannan hasken wukar da nagani yana walkiya,sai kawai na farka
da wani irin firgita ina kiran sunayen Allaah,Dr da yake lura da yanayin numfashi na yaga na'rar
da ke june da ni yana basu notification din na farka da gudu suka shigo dakin ganin karkarwa
da fizge fizge da nake sukayi saurin rirrikeni sannan suka kira daddy suke sanar mashi cewa na
farka amma mutum daya kawai suke bukata ya lura da ni kafin na dawo normal yanzu ina cikin
gigin alluran da akayimun general anesthetic.....

Daddy sai da ya sanar da su mummy cewa nan da wasu lokaci zasu samu ganina amma yanzu
shi zai zauna awajena.
Da hankali abubuwan da suka faru suka dinga zuwamun cikin kwakwalwata na fara turayosu
daya bayan daya sai gashi komai ya dawo sabo a idanuna sai kawai na tsinci kaina da kiran
sunan Arrauda shikenan ya kashemun kawata wayyo Allaah na Arrauda kitashi ki gudu kar ya
kasheki.hawaye suna ta zuba daga idanuna babu kakkautawa daddy ya rike ni sosai yana
tsoron kar na fizge na fado tun ina ganin daddy a nesa can sai gashi na fara ganinshi dishi
dish,ganin na bude idon kuma ina ganinshi kamar yau na fara ganinshi ya ce zaratun ki bude
idonki sosai nine daddy ki mai kaunarki sannu barka da dawowa cikinmu Allaah abin godiya.

Sai yanzu na Fara gani sosai kuma na gane daddy sai na ce daddy na nan ina ne ina Arrauda
da su Mummy?

Ya ce nan asibiti ne baki da lafiya ne su mummy kuma bara na kira maki su duk suna jiran

farkawanki ne....cikin jin dadi daddy ya kira su mummy har rige rige shiga dakin suke Humaira
ce ta riga kowa shiga dakin da sauri zata fada jikina mummy tayi saurin riketa ta ba cewa yi a
hankali kada ki fada jikinta aiko cikin sauri ta zauna a bakin gadon ta kamo hannayena duka
biyu bamu ce komai ba sai kukan da muke yi na farin cikin ganin juna.dukkanmu a wannan
lokaci muna kukan murnar.sai auntie Maryam ta mike da waya a hannunta ta shiga kiran Khalid
da Dr zaid ta sanar musu na farka...
Niko sai tambayarsu nake ina Arrauda daddy ya yi sauri ya ce itama tana dayan dakin ana bata
kulawa,sun boyemun mutuwarta saboda kar na shigo damuwa.......





_kuyi hakuri da typing errors saboda yau banyi editing ba_








*please share vote and comment*

���������������������������������


*WACECE NI*




�🏼by

*Fateema Muhammad Suleiman*
Email fmsuleiman743@gmail.com
Wattad teemacool2020



*🌈KAINUWA WRITERS�🏼 ASSOCIATION*�🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is ton entertain & motivate the mind of readers}```

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*page* 4⃣0⃣&4⃣1⃣



*DAILY DAHWA*
[7, ROBIU THANI 1441]

```Allaah is sufficient for us, Truth are the words Allaah ï·»`

*QURAN*
*If you obey and fear Allah, He will grant you Furqan [(a criterion to judge between right and
wrong), or (Makhraj, i.e., a way for you to get out from every difficulty)], and will expiate for you
your sins, and forgive you; and Allah is the Owner of the great bounty* (8:29)

*HADITH*
Narrated Abu Umamah (يضر الله هنع ) said: I heard Messenger of Allah (ىلص الله هيلع مالسو ) during the
sermon of the Farewell Pilgrimage saying, *Be mindful of your duty to Allah; perform your five
daily Salat, observe Saum during the month (of Ramadan) , pay the Zakat on your properties
and obey your leaders; (if you do so) you will enter the Jannah of your Rubb* [At-Tirmidhi].

*DUA*
Oh Allah (لج هلالج) *Protect us from known and unknown enemies*

*AAMIIN*


Duk da muryata bata fitowa sosai saboda nadewa da akayi da bandage,amma suna fahimtar
duk abin da nake fada.koda da daddy ya nutsar da ni cewa Arrauda tana dayan dakin kawai
nayi shiru ne amma bangasta maganar ba saboda da idona naga wannan mutumin ya caka
mata wuka,kuma naji magagin fitan ranta.kukan zuci na Dinga yi, sai hawayen da suke
zubomun masu dumi,muna cikin hakan sai ga Doctors kusan hudu da jami'an tsaro masu farin
kaya,sai da suka kuma duddubani sannan suka shiga yima jami'an tsaron bayanin cewa zuwa
nan da kwana uku zansamu damar yin magana sosai amma yanzu kada abarni tayi yawan
magana saboda aikin da akayimun a wuya,dan ma Allaah ya taimaka yankewar bai shafi
makogorona ba.dan yankewar da nasamu akan fatan wuyanne.


Jami'an tsoron suka matso kusa da daddy suka ce toh yallabai mu zamu tafi sai nan da kwana
ukun zamu dawo saboda muna da tambayoyi da muke son zamu mata.

daddy ya gyada kai ya ce toh Allaah yakaimu lokacin.

Bayan tafiyarsu ne daddy ya umarci su mummy su fita suje su kwanta,ganin nima na koma
baccin,kasancewar dakin ba mai jinyar da zai kwana tare da marar lafiya sai na 'ura da kuma
nurses dinsu ke lura da marar lafiyar.haka suka bar dakin ba dan sun so ba,Humaira kam sai
turjewa take wai ita za ta kwana da ni sai da daddy ya tsawata mata ta yarda ta bi su mum
dakin da aka tadanar musamman saboda hutu.

Tunda Khalid yaji na farka yake Allaah Allaah y gari yawaye yataho asibitin,shima Dr zaid din
haka ya sanar da sauran 'yan uwanshi na gidan cewa na farka kuma normal babu wata
matsala,sun nuna murnarsu sosai.

Kashe gari da asubah bayan sun idarda sallah,daddy ya shigo dakin da nake ya iske na farka
daga bacci ya yi sauri ya zo kusa da ni ya sunkuyo kanshi sosai ya ce daughter sunnu da jiki,
bara na kira maki mum,ya yi sauri ya fito ya kira mum tare suka shigo dakin mum ta matso ta
dafa hannayena,sannan ta dan zuba ruwa a saviet ta gogemun fuska.nidai sai ido bakin nawa
ma yarufo tun bayan na farka daga bacci, duk maganar da sukeyimun da kai nake bada amsa
a haka har ruwan dake hannuna ya kare,tun kafin daddy ya yi magana sai ga nurse ta shigo ta
kuma chanjamun wani sabon ruwan sai da ta zuba metronizol da sauran magunguna sannan ta
fita,bayan fitanta Mummy ta dinga shafamun gashin kaina dake kwance duk sun bazu ta ce
wannan gashin naki kullum a tsefe bakyason kitso na kura mata idanu tsantsar sonta ne fal
cikin zuciyata cikin kwana daya amma duk ta fada kamar mai jinya nida kaina nasan cewa tafi
sona fiye da sauran 'ya'yanta bansani ba ko dan ita kadai ke gareni.

Karfe takwas dai dai sai ga Dr zaid bai samu wata damuwa ba kai tsaye ya shigo dakin da
nake,mummy ce ta amsa mashi sallamarshi,sai da ya gaisheta sannan ya wuce kan gadon da
nake ya yimun sannu da jiki ta kai nake amsawa sai yaduba bandaging wayana ya
gyaggyarshi.ya juya ga mum ya ce munyi magana da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login