Showing 1 words to 3000 words out of 97462 words
Chapter 1 - REINA BOOK COMPLETE BY SALIHA A. NA'IBI -1.pdf
*REINA í ˝í˛Ť*
_Book 1_
  *By Saliha A. Na'ibi (Seemahwrites)*
*Women of words writers*
*Sadaukarwa ga my dear Hanifah shamaki da addaririya ta Ramlat abdulrahman manga(mai dambu). Ina
godiya da sahihiyar ƙauna, Allah ya barmu tare❤️.*
*Disclaimer: Ban amince a sauya min littafi ta ko wace irin siga ko a É—aura min a wata channel na
youtube ba tare da izini na ba, yin hakan babban kuskure ne kuma zai sanya mu saka ƙafar matsatstsen
wando É—aya da mutum*
_Any resemblance to any figure or event, deceased or living is purely coincidental_
مسب الله نامŘرلا Ů…ŮŠŘرلا
01...shi zumunci a wannan zamanin na mai shi ne, ga masu hannu da maiƙo ake sada zumunta mai
bushashshiyar hannu kuwa saidai shi ya sada ta"
Taɓe baki Saudat tayi tana gyara kwanciyar Suhail a jikin ta wanda tunda iskar napep ta kaɗa shi barci
yayi awon gaba da shi
"Amma abin yayi yawa Abban Yaseer. Ko wani hidima nasu muna kan zirya a hanya amma ko sau É—aya!
Ko sau ɗaya fa ban taɓa haihuwa mutanen nan suka ɗago ɗaya daga cikin su yazo mana barka ko suna ba
saidai mu ko yaushe muna kan faman kashe kuÉ—in adaidaita zuwa gidajen su.
Yamutsa fuska yayi alamun baiji daÉ—in zancen ta ba, ga Yaseer É—in dake zaune a tsakanin su ya kafe shi da
idanu yana dakon amsar da mahaifin nasu zai bayar don da gaske ko shi mai shekaru 12 ya fahimci cewa
yawan zirya da suke ma ƴan uwan mahaifin nashi ba buƙata ko appreciating suke yi ba balle kuma
mahaifiyar da ta haife su.
"Ćłan uwana ne fa Saudatu. Ki taya ni son su mana"
Girgiza kai tayi "nifa ba son Ć´an uwan ka bane bana yi, kawai yanda suke treating É—inmu ne bani jin daÉ—i
gaskiya. Su basu É—auke mu a matsayin Ć´an uwa ba sai kaman masu aikin su kuma ba don basu da isassun
masu musu hidima bane A'a! Don kawai a gwada mana matsayin mu ne"
"Nima idan na shiga wasan su Jamal kora ta suke yi wai wasan su ba na ƴan ƙauye bane" cewar Yaseer .
Kama baki Saudat tayi. "Kaji marasa kunyan yara, duk baka girme musu bane don sun samu ma kai ke
binsu har zasu na maka rashin kunya?"
Kamal ya É—aura hannu saman cinyar Yaseer É—in gudun kada ya biye wa mahaifiyar shi su mulmula
ƙaramin zance zuwa babba.
"Kuɗi shi ke bada matsayi ba shekaru ba. Ku lura mana cikin su Alhaji Tahir ne ƙarami Amma shine gaba a
komi na hidimar family, ko family meeting za'a yi ba mai fara magana sai yayi, kuma idan ya bada
shawara a take zai rikiÉ—e ya koma umarni, ba mai ja dashi a kan adalci ko rashin adalcin sa ba don komai
ba sai don Allah ya wadata shi fiye da sauran. don haka kada kaji komai don ka girme su tunda nasu gidan
kazo sai ka lallaɓa su har su barka ka shiga wasan ko?".
"Oh shima koya mishi jurar wulaƙanci kenan zaka yi?" Saudat tayi kicin-kicin da fuska.
Bai samu damar bata amsa ba kasancewar sun iso. Motoci ne kala-kala jere har kusan ƙarshen layin, shi
yasa a tsallake mai napep yayi parking yana jiran su fita su sallame shi.
Kamal ya ɗauki Suhail dake barci saudat kuma ta janyo ƙaton cikin ta da ƙyar ta fito tana gyara zaman
wuyan hijab ɗinta da baƙar jakar ta ƴar kullum wanda kwance ne Hajiya Fauziyya ta bata shine ya zamo
mata na shiga taro.
Ta riƙo hannun yaseer yayin da Kamal ya biya mai adaidaita ya tafi sannan suka nufi gate ɗin
tamfatsetsen gidan suna gaisawa da masu gadi don an riga an san su aka buɗe musu ƙofa suka shige.
Saida suka É—an taka suka sake shigewa gate na biyu kafin girman gidan ya daÉ—a bayyana da kuma
mutanen dake hada² a cikin ta.
Saudat bata san me yasa jikin ta yayi sanyi ba ganin ta kusa saduwa da su sai dai shima kamal É—in haka
take a gurin sa, taya su murnar biki suka zo yi amma ba lallai a basu muhimmanci ba domin jiya da
shekaran jiya ma haka ta kasance idan suka gama musu ayyukan da suke buƙata toh har su tafi ma babu
wanda yake lura, kuma ko sallamar kayan biki ba'a musu tunda su ba komai suke kawowa ba. Saudat da
tayi musu gudumawar kayan su muciya, bulogari, ƙoƙo, mara, tsintsiyar kwakwa dana laushi harma dasu
kuka, busasshen kuɓewa, daddawa, barkono da kanwa daga ƙauye ce mata sukayi sun gode ba'a buƙata
don an daina amfani da irin wannan tarukucen yanzu, shara da injin vacuum cleaner ake yi kaÉ—a miya
kuma ga whisker. Shine tace musu har sharar harabar gida ma da injin ake yinta? To ai sai ayi mata da
tsintsiyar sauran tarukucen kuma tayi kyauta da su ga masu buƙata. Haka dai ba daraja suka amsa
ballantana ta saka ran samun godiya, bata bar gidan ba tana ji tana gani aka yi rabon kayan ma sauran
Ć´an aiki.
"Ke da Suhail ku shiga ɓangaren matan, zan tafi da Yaseer mu gaisa da masu gidan" Kamal ne ya dawo da
ita daga duniyar tunanin da ta lula.
Gyaɗa kai tayi ya ɗan bubbuga Suhail ɗin ya buɗe ido kafin ya sauƙe shi a ƙasa Saudat ta kama hannun
shi sukayi cikin gidan yana mutstsuka idanu. Da duk wanda suka ci karo a hanya Saudat sai ta ɗan duƙa ta
gaida su haka ma Suhail har suka isa babban falon da manyan hajiyoyi ke manne a kujera ƙafa ɗaya kan
ɗaya kowa tana faman kaɗa warwarayen gold ɗinta don yafi na ƴar uwarta ƙara, wa'inda basu kai su
matsayi ba kuma ke kai komo na hidimar biki.
Samun wuri a ƙasa Saudat tayi ta zauna tana gaida su Suhail ma ya zauna gefen ta, wa'inda suka ga dama
suka amsa gaisuwar sauran kuma suka yi kaman basu san da halittar ta a wurin ba.
Hajiya Hauwa da fitowar ta kenan daga uwar É—aka bayanta biye da Hajiya Fauziyya ta kalli Saudat, ko
damar gaida ta bata bayar ma Saudat ba tace "yauwa Saudatu sai yanzu kika iso? Dama ana niman masu
wankin waken yin alalar yamma wajen Inna larai, kije ki same su a can".
Bata amsa ta ba sai cewa tayi "ina wuni Hajiya yaya hidima?"
Ɗan ƙaramin tsaki tayi sannan ta amsa da "lafiya lau"
"Toh Allah ya bada zaman lafiya, Allah yasa gidan zamanta ne"
Cikin ƙosawa tace "ameen ba zaki iya taimakon bane in samu wata?"
Nan ma bata amsa ta ba ta gaida Hajiya Fauziyya wanda ta amsa da murmushi saman fuskarta itama tana
É—auke da zungureren ciki aihuwa yau ko gobe tace "ina Yaseer ko ba'a zo mana dashi bane?"
"A'a yana waje tare da Abban shi."
"Toh yayi kyau" ta juya wurin Hajiya Hauwa "Umman Jamal barin je in shigo da su aunty Zeenat"
"A'a da dai kin bari an tura a shigo dasu, ke da kike fama da tsohon ciki amma sai É—awainiya kike tun
Safiya "
Kallon cikin jikin ta Saudat tayi, girman shi ɗaya da na Fauziyya ko ma ya fishi girma tunda ita ƙibar hutu
dama cikin yasa jikin ta ya shanye shi, amma na Saudat gashi a ƙasa ranƙwalele shine kuma ake saka ta
surfen wake bama yanka salad ko irin haɗa su zoɓo ba. Ko ita ba ɗan adam bane a cikin nata?.
Murmushi Hajiya Fauziyya tayi tace "zan iya, yanzu idan na shigo dasu zan samu in zauna"
"toh shikkenan a kula dai kar a wahalar mana da É—a"
Nanma murmushi Hajiya Fauziyya tayi ba tare da ta sake cewa komai ba ta nufi hanyar barin parlourn.
Itama Saudat tashi tayi kafin Hajiya Hauwan ta sake cewa wani abu tace "barin je toh"
"Yauwa da yafi" cewar Hajiya Hauwa sannan ta shiga gaisawa da sauran hajiyoyin da zuwan su kenan
cikin fara'a da annashuwa.
Haka Saudat ta ƙarasa ta bayan gidan wurin da ake faman haɗa kalolin abinci cikin manya manyan
tukwane wanda zai ciyar da ɗaruruwan mutane. A cikin dandazon masu aikin ta tsinto Inna larai ta riƙo
hannun ta don ta samu hankalin ta suka gaisa sannan tace. "Inna ance ana buƙatar ƙarin masu surfen
waken alala, shine nazo"
"Lalala Ć´ar nan! Da wannan tsohon cikin zakiyi surfe kalan ki haihu a gidan biki ace ni na takalo miki
naƙuda!"
Saudat tayi murmushi kawai "toh kije can ga su Rabi suna haÉ—a salad sai ki kama musu yanka kabeji ko
kankare karas"
taji daÉ—in sauyin aikin da Inna larai ta bata duba da yanayin ta wanda wancan makauniyar ta kasa, haka
kuwa tayi mata godiya sannan taje ta fara aikin ta cikin azama suna taɓa hira dasu rabi don sun ɗan saba.
...
Kamal da ya duba bai samu ko ɗaya daga cikin mazajen bane ya koma wurin masu gadi suna ɗan taɓa
hira shima don zaman cikin gida ba nashi bane. Suna nan zaune motar yankakku kuma feÉ—aÉ—É—un shanu
har guda 3 ya iso nan suka tashi ya shiga cikin su don taya mahautan sauƙewa sannan suka ɗunguma
yanka naman gunduwa² da kuma faskaren ƙashi, don haka kafin a gama farar shaddar shi ta Sallah wanda
sawa ta 3 zuwa 4 kenan da yayi mata tayi caɓa² da jini.
...
Wuraren ƙarfe 4:30 na yamma an gama cike motocin kai amarya da suka ƙaraso, saboda girman cikin ta
Alhaji Tahir ya gargaÉ—i Hajiya Fauziyya da kar ta bisu. Hakan yasa ta yanke shawarar yin zaman ta har
masu kai amaryar suje su dawo in yaso aka zo tafiya dinner da daddare sai taje, gashi dama bata wani jin
É—aÉ—i tun da rana ta fara yin sanyi.
Dagewa suka yi saidai ta kai musu amarya mota tunda ba zata bi ayari ba, haka kuwa akayi, ta rungume
amarya Sakina tana faman turawa har jikin danƙareren farar jeep ɗin da aka kawo don ɗaukar ta suka
amshe ta daga nan sannan ita ta koma ciki.
A hanyar ta na komawa Yaseer yayi saurin shan gaban ta. Ta É—an firgita da gudun da ya É—ibo ganin sauran
kaÉ—an ya mangare mata ciki amma tana gane shi sai itama ta saki fuska. "Yaseer yaya school" ta tambaya
hannun ta a kan cikin tana fitar da numfashi.
"Ina wuni aunty" ya rusuna har ƙasa don gaida ta.
"Lafiy..." Amsar ta ya katse ganin Yaseer ɗin ya miƙe hannun shi riƙe da ɓawon ayaba da aka ci aka yasar
akan interlocking É—in wanda ba don Yaseer É—in yayi saurin tsare ta ba, toh da tabbas ta taka shi zamewa
zata yi ta faÉ—i.
"Wayyo Allah yarona na gode. Ka ceci rayuwar ƙanwar ka" ta shafa cikin tare da faɗaɗa murmushi.
Shima murmushin ya mayar mata don shi dai matar tana birge shi ba don komai ba ko dan yawan fara'ar
ta. Bata da yawan magana sai murmushi kuma ita kaÉ—ai ce idan ya gaishe ta ko iyayen shi suka gaida ta
take amsawa cikin mutuntawa.
"Kaci abinci?" Ta tambaya cikin kulawa.
Girgiza kai Yaseer yayi alaman A'a.
"Muje ciki a saka maka kaci" ta fada cikin dakakkiyar murya sanin cewa zai iya mata musu don yana da
kawaici, yana buƙatar abu amma idan ka bashi sai yace maka 'A'a na gode' ko kuma 'ki barshi kawai'.
Babu musu ya bita a baya har cikin babban parlourn Hajiya Lubabatu uwar amarya. Sannan tace a saka
mata abinci.
Babu ɓata lokaci aka kawo mata plate ɗauke da fried rice, gefe ga stir fried spaghetti mai ɗauke da
veggies yasha nama sai kuma kwatan kaza a saman shikafar da coleslaw a gefe ga alalen laida da aka riga
aka ɓare mata aka saka wuƙa aka yanka gida hudu sannan aka zuba onion sauce a kai don a tunanin su
ita ce zata ci. Sai kuma disposable cup dake É—auke da kunun aya an rufe da murfin shi an zura straw a ciki
don sauƙin sha.
Kiran Yaseer tayi ta ajiye mishi plate É—in a kan dining table sannan tace ya ja kujera ya zauna ya ci.
Ya haɗiyi miyau ganin kayan daɗin da aka shaƙe plate ɗin dashi sannan a maimakon ya zauna sai ya ɗauki
plate É—in a hannun shi.
"Zan kai muci da Umma na Aunty" haka kowa yake ce mata Aunty tunda bata taɓa haihuwa ba tukuna
ballantana a lanƙaya mata sunan abinda ta haifa.
"Umman kan itama bata ci abincin ba?" Fauziyya ta tambaya cike da mamaki.
Sanin cewa Saudat ba zata iya samun abinci taci ita kaÉ—ai ba tare da ta kira shi, shi da Suhail ba yasa ya
girgiza mata kai kawai.
"Indo kawo wani plate É—in abincin" ta umarta.
"Ma waye ne aunty?" Indon ta tambaya gudun kada ta sake zuba bajintan ta a sake kyautarwa.
"Ma nice, ki saka min tuwo da zobo kuma ya ji nama"
"Toh Aunty" bata da zaɓin da ya wuce tayi yanda aka ce da ita.
Saida aka gama zubawa aka ajiye a saman dining sannan tace da Yaseer "kaje ka kira umman ka da ƙanin
ka kuzo ku ci a nan" ta faÉ—a don itama bata kiyaye sunan Suhail ba. Shima da "Toh Aunty". Ya amsa, Ya
fita da gudu don kiran umman tashi".
Mrs Imran ✨
*REINAí ˝í˛Ť*
BookNest, arewabooks and Wattpad @ Seemahwrites
 Â
مسب الله نامŘرلا Ů…ŮŠŘرلا
02...... "Toh aunty" ya amsa mata sannan ya fita kiran Saudat. Hajiya Fauziyya bata bar wurin ba har saida
Yaseer ya dawo tare da umman shi da ma Suhail wanda yake ta mata mitan yana jin yunwa shine Inna
larai tace bari taje ta karɓo masa tuwo, kafin ta dawo ne Yaseer yazo yace Aunty na kiran Saudat amma
bai faÉ—a mata dalilin kiran ba.
"Gani Aunty" Saudat ta faÉ—a tana shirin kai duka ma Suhail wanda yanzu ya fara kuka saboda yin arba da
abincin dake kan dining a gaban Hajiya Fauziyyan. Miƙewa tayi da ƙyar sannan ta nuna ma Saudat ɗin
kujeran da ta tashi.
"Ki samu ki bawa yaran abinci. Ni barin shiga ciki in É—an watsa ruwa ko zan ji daÉ—in jiki na" da faÉ—ar haka
tayi shigewar ta ɗakin dake kusa da dining area wanda na musamman aka bar mata ta tare a cikin sa har
a gama hidimar biki duk da kuwa ba a gidan take kwana ba, da kanshi Alhaji Tahir yake maida ta gida duk
dare saboda kiyaye abinda ke cikin ta.
Tana ƙulewa ciki Saudat tayi saurin zama don itama yunwar take ji. Anyi rabon abinci bayan sun gama aiki
amma ba'a bata ba ganin itama Ć´ar cikin gida ne tana da damar shiga ciki ta ci, Itama kuma sai bata yi
magana ba har saida Suhail ya fara mita kafin Inna larai ta fahimci halin da suke ciki.
A nutse Yaseer ya fara cin tuwon domin ya bar musu shinkafar su ci. Saudat tasa cokali ta fara baiwa
Suhail a baki amma sai ya janyo plate ɗin saboda ƙaguwa ya luma yatsun shi ciki yana dunƙulo manyan
loma yana jefawa a baki. Cikin ƙanƙanin lokaci ya ɓata wurin ya kuma ɓata kayan shi da maiƙo.
....
Hajiya Fauziyya na shiga ciki ta sanya wa ƙofar sakata kafin ta shiga rage kayan jikin ta ta ɗaura
madaidaicin towel. Har ta isa ƙofar bathroom Amma murɗin da taji cikin ta yayi wanda saida ya saka ta
saki ƙaramin ƙara yasa ta dawo a hankali ta cire sakatar sannan ta shiga ban ɗakin, haka shima tura ƙofa
kawai tayi ta daidaita temperature na ruwan da É—an zafi sannan ta sake ma kanta shower.
A daddafe ta ƙarasa wankan ta kashe shower, taso ta tsane jikinta tun a cikin bathroom amma abin da
take ji yana niman wuce tunanin ta hakan yasa ta tako a hankali ta fito tana kama garu. Niman wayan ta
ta shiga yi saidai ta manto shi wurin da ta zauna a kan dining.
Fara jero 'hasbunallahu wa niimal wakeel' tayi tana addu'ar Allah ya bata ƙarfin sanya sutura a jikin ta
kafin wani ya shigo ya same ta cikin wannan yanayi.
Ta samu nasarar maida undies ɗinta da ƙyar, amma kafin tayi aune ruwan ta ya fashe!.
Wai-wai ta fara tana yarfa hannuwa, sai dai ganin zata iya kwana a haka babu wanda ya jita gashi abu sai
gaba-gaba yake yi yasa ta ƙwalla ƙara, tana buga jikin gadon da iya ƙarfin ta tana matsar ƙwolla.
....
Sun kusan tada abincin dake plates ɗin duka suka fara jiyo sautin bugun da Hajiya Fauziyya take yi amma
sai Saudat ta basar ganin ba abinda ya shafe ta bane.
"Umma kinji kamar ana bugun ƙofar can" Yaseer ya nuna ƙofar ɗakin da Hajiya Fauziyya take.
"Anya kuwa? Wataƙil wani abun dai take bugawa a ciki". Saudat tayi ƙoƙarin kawar da ko wace irin
mummunan tunani a ranta suka ci gaba da cin abincin su.
Wayar dake gefen plate ɗin tuwon Yaseer ne ya fara ruri, ya jawo ta sannan ya miƙa ma Saudat.
"Umma wannan kamar wayan aunty"
Serviette É—in da ke tsakiyar dining Saudat ta ciri É—aya ta goge hannun ta da na Suhail don kada shi ma ya
damƙi wayar ya ɓata musu sannan ta karɓa wayar yayin da kiran ya yanke a take kuma wani ya sake
shigowa ta duba sunan mai kiran don tabbatar da wayar wacece.
'Habeeby Da'eeman' ta gani as caller ID sai kuma hoton bikin Alhaji Tahir É—in tare da hajiya Fauziyya da
aka yi shi shekaru 2 da suka wuce ya bayyana a ɗan ƙaramin zagayayyen akwati.
Saurin miƙewa tayi ta ƙarasa jikin ɗakin sai a sannan ta fara jiyo kukan Hajiya Fauziyya tare da ihun niman
taimako, ai ko da azama ta bankaɗe ƙofar