Showing 36001 words to 39000 words out of 97462 words

Chapter 13 - REINA BOOK COMPLETE BY SALIHA A. NA'IBI -1.pdf

02 Aug 2025

10162

yanayin ta ya gwada.

Zagawa tayi ta ƙarasa ta zaro tsintsiyan kwakwa guda biyu ta nufo ta da shi.

Abun ya ishe ta, duka kan sai ta daki Reina idan yaso Tahir ya dawo yayi farfesun ta ya shanye.

Kuka ta saka tun kafin tsintsiyar kwakwan ya kai jikin ta tana tsalle cike da tsananin tsoro "Wayyo Aunty!
na tiga uku!"
Sai ga fitsari tsirrr ta sake shi na tsoro daidai lokacin da aka yi sallama a ƙofar kitchen ɗin dake buɗe
Saudat ta shigo ɗauke da murmushi, Reina kuwa tayi wurin ta da gudu domin ta san duk kitchen ɗin
babu mai iya ceton ta.

Da wani ne yace mishi hancin yarinyar nan zai taɓa tasowa da sai yayi rantsuwa kafin ya musa.




*Saliha Ahmad Na'ibi (seemahwrites)✨*

*REINA �*







16....da sauri Saudat ta maida ta bayan ta, ya kasance ta mata shamaki tsakanin ta da Hajiya Fauziyya.

"Dan Allah ki barni in kewaya yarinyar nan Umman Yaseer" tace tana ƙoƙarin janyo Reina daga bayan
Saudat.

Ganin zata iya cin mata daga wurin yasa da gudu ta kauce ta koma bayan Yaseer dake biye da Saudat ta
ɓuya, ta riƙe wandon jikin sa gamm jikin ta na kyarma.

Da wani ne yace masa hancin yarinyar nan zai taɓa tasowa da sai yayi rantsuwa kafin ya musa.

Sai dai ɗan hancin caɓa-caɓa yake da majina saboda kukan da ta sha na tsoro.

"Haba Aunty, kiyi haƙuri mana, wanda ake wa murnan badday kuma ita ake duka?" Saudat tayi ƙoƙarin
tausar ta.

"Idan ba zane ta nayi ba bana jin zata dawo cikin hayyacin ta. Haba! Yarinya kamar wanda ifiritai kewa
fitsari a tsakar ka? Bata ji ko kaɗan? Kiga ta'adin da tayi min fa!" Ta karɓi carpet ɗin tana gwada ma
Saudat.

Karɓan tsintsiyan kwakwar tayi daga hannun ta "yanzu kam ta ji tsoro, ba zata sake ba."

Ta watsa mata harara daga yanda take ɓoye. "Zaki zo a ɗauraye miki jiki ne ko sai na ƙaraso wurin?"

Sai ta ƙara ƙanƙame Yaseer domin ta san idan taje wurin ko da hannun ne sai ta dake ta tunda tayi niyya.

"Kije ba za ta miki komai ba"

Ɗaga kai tayi ta kalle shi, idanun ta sun sake cika da ƙwalla.

"Wayyayi duka na za ta yi"

"Ba zata miki komai ba" ya jaddada mata.

"Toh ka ce wayyayi" ta buƙata don idan ya rantse ta san da gaske yake.

Sauƙe Sabir yayi a ƙasa sannan ya kama hannun ta suka ƙarasa wurin Auntyn, da yanzu aka saka mata
stool ta zauna tana fitar da numfashin ɓacin rai, daman ƙiris take jira.

"Kiyi haƙuri aunty, don Allah"

Harara ta watsa ma Reina sannan tace wa ɗaya daga cikin masu aikin wurin su ɗauke ta suyi mata wanka.

Sai da taga sun bar kitchen ɗin kafin hankalin ta ya kwanta.

"Ki daina barin karamin abu yana ɓata miki rai a yanayin da kike ciki. Kada ki saka jinin ki ya hau" Saudat
tace tana zuba ruwan da aka miƙo mata a jiki da da kuma ƙafafun ta da suka shiga fitsarin Reina.

Hawan jini na nawa kuma,Tace a ranta. kana ta saki fuska kaɗan tace.

"Ku yi haƙuri kun zo kun same mu kaca-kaca amma yanzu zamu ƙarasa tattarawa. bari a kai ku falon
sama ku sha ruwa kafin a gama kimtsa nan ɗin"

"Kada ki damu wallahi , yaran zasu jira ko a waje ni sai in taya ki da wani abun"

Da faɗar haka, Yaseer ya kama hannun yaran suka fice ita kuma ta ajiye jakar ta da laidar hannun ta a
ƙasa alamun ta shirya ma aiki.

Yanzu kam sosai Hajiya Fauziyya ta saki fuska don ɓacin ranta ya fara washewa.
"Gamu da yawa umman Yaseer sai kin wahalar da kan ki?"

Ƙarasawa jikin cake ɗin Saudat tayi tana kallo "da kan ki kike yin cake ɗin kuma?"

"Eh, amma fa ba na kyauta nake musu ba, biyana suke yi" ta murmusa sannan ta ɗauƙi robar whipped
cream zata mayar da shi fridge don ya ƙara kama jikin sa kafin ta ƙarasa.

Saudat ta hango wasu guda biyu da tayi su tun jiya a cikin fridge ɗin.

"Ah ashe fa kin iya aunty!"

"Ƙaraso ki gani" tace da ita tana wangale mata ƙofofin fridge ɗin, Saudat ta matsa kusa tana kallo cikin
burgewa. Harda wasu doli aka yi masu kyau a kan dogon, guntun kuma an cika saman shi da wafer da
chocolate.

"Ina yin sana'ar gashe-gashe ai sosai tun kafin in yi aure, kuma anyi min ciniki lokacin da ake neman
soyayya ta" tace tana murmushin da ta kwana biyu bata yi wanda ya fito daga ƙasan zuciyar ta kaman shi
ba.

Ita shaida ne a kan soyayyar da Alhaji Tahir yayi mata, irin son da ke saka ta kokwanton ko yana cikin
cikakken hankalin shi.
Amma me yasa auren shi ya fara fita a kanta cikin shekaru biyar kawai duk da irin wannan soyayyar da
yake mata?.

"Ahh kice kin ja ajin ki Aunty"

Gira ɗaya ta ɗaga tana jin kanta tace "sosai ma. Tausayin sa na ji a lokacin na sauƙe farashi" 

Ba yi son talaka da talauci ta sani. Ba yi iya ɓoye son zuciyar shi ta sani. Soyayyar shi ya jawo mata baƙin
jini a wurin dangin sa ta sani.

Amma me yasa duka wa'innan basu zamo mata matsala a zaman ta da shi ba sai Reina? Ƴar ta na cikin
ta, ba wai ƴar riƙo ko ƴar kishiya ba?.

......

A hankali yake takawa idanun shi na yaba kyau da tsaruwa irin na garden ɗin. Ga hadari da ya haɗu a
sama yana bada iska mai sanyi wanda ke kaɗa ciyayi, fulawowi da bishiyoyin dake wurin suna bada wani
sauti shuuu mai sanya nutsuwa a cikin kunnuwa.

Jikin lilon dake kafe a tsakiyar wurin yaje ya zauna. Ya ja kanshi baya sosai kafin ya raba ƙafar shi da ƙasa
shi kuwa lilon ya fara yawo da shi a hankali, ya lumshe idanu yana jin daɗin yanayin har cikin gaɓoɓin shi.

Ihun Sabir ya riski kunnen shi kaman daga sama sai kuka kuma ya biyo baya.

Miƙewa yayi sannan ya nufi yanda yake jiyo sautin kukan da gudu, ya kai shi har ƙofar shiga main parlour
na gidan, yanda ya hango Reina tsaye sanye da riga da wando kalar ruwan ɗorawa ga ƙaton cikin ta da ya
bulluƙo ta cikin rigar, tana fuskantar Sabir dake zunduma ihu ga wani abu kalan kashi a fuskar shi, rigan
shi kuma a jiƙe.

"Sabir! Reina! Lafiya?"

Bata firgita da ganin shi ba ko kaɗan, soyayyun idanun ta a kan Sabir ta gwada shi da ɗan tsintsiyar yatsar
ta.

"Gobe ka shake taka ni shai na mammaye ka, dirty boy!"

"Reina!"

Ɗagowa tayi tana kallon shi babu ko digon tsoron da ya gani ɗazu a idanun ta.

"Me kika mishi?"

Water bottle da laidan chocolate dake hannunta ta ɗaga mishi.

"Ina wasa ne ban ssani ba na..."


"Yi shiyu!!" Ta zungure shi tana zazzare idanu. Shi kuwa ba ma iya ganin ta yake yi ba kasancewar
chocolate ɗin ya fara shiga mishi idanu don haka ya rintse idanun gamm.

"Yashin kunya yayi min" ta bada amsa kai tsaye.

"Don yayi miki rashin kunya sai ki jiƙa mishi jiki ki saka mishi abu a ido?" Yace yana rage tsayin shi sannan
ya cire handkerchief daga aljihun wandon shi ya shiga share ma Sabir ido.

Fauce handkerchief ɗin tayi idon ta na kawo ruwa. Sai Yaseer kawai ya tsaya kallon ƙarfin hali, ya dai
samu idon Sabir ɗin ya buɗe.

Da gudu Suhail ya ƙaraso wurin su, daman tare suke a wajen ya bar shi ya shiga ciki da ya ji an saka kiɗa
sai yanzu da aka sake kashewa shine ya dawo.

"Kuje jikin famfo ka wanke mishi fuska" Yaseer ya umarci Suhail da bai san mai ya faru ba tukunna amma
da tuni ya kai wa Reina hannu.

Sai da suka bar wurin kafin shima Yaseer ɗin ya juya zai barta a wurin tayi saurin riƙo ƙafar wandon shi.

"Ai gidan mu yajo"

"Okay, haka kike yi ma duk wanda ya zo gidan ku? Shikkenan, ba zamu sake zuwa ba balle idan Aunty zata
zane ki in ƙwace ki"

"A'a kai kajo amma ban da shi"

"Shi ba abokin ki bane? Yazo miki Birthday ne fah"

"Ni dirty boy ba aboki na bane. Umma ta ce duk dirty boy talakawa ne"

Bai san waye umman ba amma numfashi kawai ya ja tausayin ta na kama shi, saboda mutanen da ke
zagaye da ita basu da hankali.

Ya sauƙa a kan guiwar shi ɗaya don ya daidaita tsayin su duk da a hakan ma yayi mata rata sosai amma ta
fi Sabir tsayi.
Kafaɗun ta ya riƙe duka biyu ga hawayen rashin gaskiya dake bin fuskar ta.

"Kina so in sake dawowa?"

Gyaɗa kai tayi.

"To ki bawa abokin ki haƙuri kuma kada ki sake cewa kowa talakawa"

Maƙe kafaɗa tayi. "O'o ban bashi akuyi ba"

"To shikkenan babu ruwana da ke" zai miƙe tayi saurin riƙo hannun shi.

"Kai ka fa'a wa Aunty pleash"

"Toh idan kika bashi haƙuri ba zan faɗa mata ba."

Hannun riganta ta saka ta share idanun ta sannan cikin dakiya tace.

"Ni ban bashi akuyi ba, ai shi ya faya taka ni"

Laɓɓan bakin shi na ƙasa ya ciza kafin ya kira sunan ta "Reina. Idan aka yi miki laifi ƙara zaki na kaiwa
wurin babba kin ji ko?"

Ta gyaɗa kai.

"Toh muje ki bashi haƙuri"

Ta maƙe kafaɗa.

Girgiza kai yayi cikin rasa abun yi.

Zai sake magana ta ƙwala kiran "Daddyyy" kana ta kwace jikin ta daga riƙon shi ta ruga a guje ta faɗa jikin
Alhaji Tahir wanda ya buɗe mata hannayen shi.

"Sarauniya tah!" Ya shiga juyi da ita a wurin yana bin fuskar ta da sumba ita kuma sai ƙyalƙyala dariya
take yi.

Sauƙe ta yayi ya buɗe bayan motar da ya dawo a cikin ta sannan ya fito mata da farin teddy bear mai riƙe
da jan heart a cikin shi, a jiki an rubuta Reina @3. Ta karɓa cike da murna sannan ta rungume a ƙirjin ta
tana tsalle.

"Thank you Daddy"

"You're welcome my queen"

Ya ɗauke ta da dolin da suke tsayi ɗaya yana faɗin "muje ciki kiga sauran gifts ɗin ki ko?"

"Yayyy" ta fara zillon daɗi a jikin shi kamar wacce take kan doki.

Sai lokacin hankalin shi ya dawo kan Yaseer dake tsaye a wurin yana bin su da idanu.
Lokaci ɗaya Alhaji Tahir ya haɗe fuska ya watsa mishi wani kallo kafin ya wuce ciki da sarauniyar shi.

......

"Ina yi don in samu kuɗi na amma ba ra'ayin wannan kalolin bidi'ar nake ba. Haba ace abu duk shekara
babu fashi? Har na wata shida sai da ya saka aka yi mata fa."

Ta san akwai ne ya saka ake yi amma ko da ace tana da shi, da zata iya ɗin, ita kam abun yayi yawa kuma,
bai bata sha'awa ba. "Amma da sadaka kuke mata kawai a ranar badday ɗin. Ko idan aka yi biki wannan
shekarar a wani sai ku kai kuɗin yanda za'a yi mata addu'ar albarka ma rayuwar ta"

"Ina ƙoƙarin yin hakan tunda duk abinda nace ba fasawa zasu yi ba. Kayan ta ma idan aka cire akwai wani
gidan marayu da nake kai musu sai in haɗa musu da wani abun."

"Toh hakan yayi. Allah yayi mata albarka ya ƙara shirya mana zuri'a. Tarbiyya ne a wannan zamani ba abu
ne mai sauƙi ba"

Matse baki tayi tana ajiye piping bag ɗin hannun ta wanda yanzu ta gama frosting ɗin cake ɗin, sprinkles
kawai ya rage ta zuba mishi ya ƙara haskawa.

Ta kalli Saudat, tana son ta buɗe mata cikin ta ko zata samu mafita, ko zata samu shawara, ko da rage
damuwar ta ne ta samu tayi, amma bata san ta ina zata fara ba.

"Umman Yaseer" ta kira ta da wani irin muryar da ya sanya ta raba hankalin ta daga jikin cake ɗin da ta
gagara gaskata cewa a kan idanun ta aka yi adon shi tun daga farko har zuwa ƙarshe, ta ɗora su a kan
Fauziyya.

"Na'am"

Ajiyar numfashi tayi kana tace. "Abban Reina Ya..."

"Mai kuma na yi?"

Yace yana shigowa cikin kitchen ɗin ɗauke da ƴar gudaliyar shi.

Miƙewa tayi. "Babu komai, Sannu da dawowa"

"Yauwa matar aljannah" ya ƙaraso ya sumbaci goshin ta ya matso da Reina ma da nufin itama ta
sumbace ta amma mugun kallon da Fauziyya ta watsa mata ya saka ta juyar da kanta daga kallon ta
bakiɗaya.

"Daddy mu je a yanka cake" tace don su bar kitchen ɗin.

"Shikkenan, bari in canza kaya ko?"

Yayi ƙorarin sauƙe ta amma firr ta maƙe shi.

Sai a sannan Saudat tayi ƙoƙarin gaida shi sai dai ko jin ta ma baiyi ba don hankalin shi bayi kan ta.


"Fauzah me kika yi ma yarinyar nan a bayan ido na?" Ya bita da kallon tuhuma ganin tsoron da ke tattare
da Reina.

"Ni babu abin da nayi mata, amma Allah ya ƙi ki kishiga hannu na Reina"

Ya ware idanu "Oh a gaban idanu na kike faɗan haka Fauziyya?"

"Ka tambaye ta abin da tayi tukunna, me ya haɗa ta da iyami? Ai gashi da ta san bata da gaskiya ai ɓuya
take yi a jikin ka"

Ba wai don yaji laifin tan ya tambaya ba, sai dai kawai don ya san me ya haɗa ta da wacce aka kira da
iyamin tunda yana da tabbacin mai aiki ne. Masu aikin da ya kafa musu sharaɗi a kan ta, kuma duk wacce
ta tsallake wannan sharadin toh a bakin aikin ta ne.

"Me ya haɗa ki da ita Reina?"

Shiru tayi tana cin farcen hannun ta cikin fargaba kada Daddyn tan ma yace hukunta ta zai yi.

"Ta yi min yashin kunya ne shine nace Uwar ki!"

A tare Saudat da hajiya Fauziyya suka riƙe baki cikin kaɗuwa don basu san da wannan zancen ba, sai dai
zasu iya cewa tambayar da Alhaji Tahir yayi ma Reina shine abin da yafi kaɗa su fiye da wannan
nannauyar ashariya.

"Wani irin rashin kunya tayi miki?" Shine abin da ya tambaye ta.

"T!!!. Fisabillilahi baka ji abinda tace bane? Ni na koya wa Reina ashar ko kai da ba zaka tambaye ta a ina
ta koyo ba?."

Ya buɗe baki zai yi magana, ya dubi Saudat da ta kafe idanun ta a kan kantar kitchen ɗin tana jin dama ta
dawo tsuntsuwa tayi filfili ta bar musu wurin.

Sai kawai ya fasa, suka juya da Reina suka bar mata kitchen ɗin, yayin da ƙafafuwan Fauziyya suka gagara
ɗaukan ta ta koma jikin kujerarta ta zuba a kai idanun ta a jikin ƙofar kamar sun fita sun bar tabon zagin
ne a wurin.

"Na shiga uku!"

......

Bakin ta da na mahaifin ta har kunne, hannun Reina cikin na Fauziyya, nata kuma cikin na Tahir suka
yanka cake ɗin bayan an ƙirga musu daga ɗaya zuwa uku. Nan kuwa wuri ya ɗauki tafi da suwwa Dj ya
cigaba da aikin shi.

Dukkan su uku suna cikin shiga ta alfarma musamman ita celebrant dake cikin wata buɗaɗɗiyar riga mai
walwali iya guiwa kalan emerald green. Kanta da tiara kalar rigar, sai kuma fairy wand da ta riƙe irin dai
na fairy ɗin cikin cartoon ɗin da take son gani mai suna tinkerbell.

Cake ɗin ya fara yanka ya kai bakin Reina ta gutsura sannn itama ta karɓa ta kai bakin mahaifin ta, ya ci
ya goge hannun ta saboda kada ta ɓata jikin ta kafin aka shiga haska su da kyamarori. sun ma manta da
duniyar Fauziyya a wurin, wanda itama a nata ɓangaren ta manta da tasu duniyar.

Cikin gidan da haske sosai amma gari ya gama baƙiƙƙirin hadari sai ƙugi yake, kiɗan da ya cika falon ya
hana su jin buƙatuwar da ruwan sama yake da shi don ya sauƙar da Ni'ima.

Ji take yi duk girman gidan kaman so yake yi ya matse ta, numfashi yana niman kasa mata, ga zufa dake
yanko mata a cikin sanyin Ac da kuma ruwan da ya kece yanzun kaman da bakin ƙwarya.

Daman yanayin damina ya saka su yin hidimar a ciki, ta fara takawa a hankali saidai tana jin ƙafar ta
kaman ba a kan ƙasa yake tafiya ba.

Su Hajiya Farida da suka gama kashe hoto yanzu suka nufo ta suna maganganu sai dai ba zata iya fayyace
me suke faɗa ba. Ba ma zata iya gane su waye a kan ta ba.

Ita dai kawai ta san ganin ta yana dishashewa a hankali har ta daina ganin komai, ta daina jin komai,
sannan ta daina tunanin komai na wani lokaci.


Baki ɗaya mutanen parlourn kowa yayi kanta, Alhaji Tahir bai san lokacin da ya dire Reina a wurin ba, ya
shiga tutture mutanen da suke tsaye a hanyar shi na ƙarasawa gare ta sannan ya zuba a kan guiwowin shi
yana bubbuga fuskar ta cikin tsananin tashin hankali da firgici.

Goran ruwan da ɗaya daga cikin mutanen tayi hankalin miƙowa ya karɓa ya shiga shafa mata amma inaa
babu numfashi. Ganin ɓata lokacin shi kawai yake yi yasa ya ciccibeta da zungureren cikin ta suka yi
hanyar waje da gudu

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login