Showing 27001 words to 30000 words out of 97462 words
Chapter 10 - REINA BOOK COMPLETE BY SALIHA A. NA'IBI -1.pdf
min, amma ka bar kofin ya shiga cikin randar sosai"
Da fara'ar shi na yayi abun arziƙi ya karɓa ya sake rugawa jikin randan ƙasar kana ya tsumbula kofin silver
a ciki, saidai bai ɗibo wani abun arziƙi ba yanzun ma saboda an ɗaura randar a kan daron ƙasa yayi masa
sama.
Ganin zaiyi ta wahalar da Abban ne yasa Yaseer sake ɗauraye hannun shi ya miƙe ya wafce kofin a
hannun shi ya ciko kofin har baki sannan ya tunkari Kamal da shi. Zubewa Suhail yayi a ƙasa ya riƙo ƙafar
shi yana kuka suran kaɗan Yaseer ya zubar da ruwan amma sai ya cigaba da jan ƙafar da Suhail ɗin ke
riƙe dashi kayan jikin shi na daɗa tumurmusuwa a ɓaɓɓakakken simintin tsakar gidan har suka isa gaban
Kamal a haka sannan ya ajiye mishi ruwan "gashi Abbah"
Ɗagowar da zaiyi idanun shi suka sauƙa a kan Suhail ze kai masa cizo a sha raɓar sa yayi saurin buge
masa bakin ai kuwa ya fasa ihu.
"A'a me yayi maka zaka buge shi Yaseer? Bani son zalunci fah!" Kamal yace bayan ya shanye ruwan.
"Ai daman ba'a cizon mumini sau biyu a rami ɗaya. Madallah, shine maganin ka tunda baka ji" Saudat ta
gwada Suhail dake riƙe da baki da yatsa. "Kuma kazo min nan wallahi sai na ƙara maka. Ka ga yanda kayi
da kayan jikin ka! Jiƙa maka su zanyi sai ka wanke"
Yana tsoron zuwa jikin Abban sun ma ta riƙo shi don haka ya juya ya faɗa jikin Yaseer ɗin yana kuka.
Dariya ne ya kama shi yace "toh muje a siyo kayan daɗi, amma sai kayi min alƙawarin ka bar cizo"
"Wallahi na bari" yace yana murza idanu.
Cewa yayi ya jira shi ya ɗauko kuɗi amma kafan shi ƙafar Suhail suka shige ɗakin ya ɗauko Naira hamsin a
cikin jakar makarantar shi, sannan suka fice daga gidan.
"Alhamdulillah, Allah ya ƙara shirya mana yaran nan, Allah kasa su zama madafan jinginar juna a lokacin
da bamu tare da su" Kamal yace yana bin su da kallon sha'awar shakuwar dake tsakanin su duk da ratar
da suke dashi a shekaru.
"Ameen, amma ka sani don Yaseer yana da haƙuri ne, ba don haka ba ko ni bani iyawa da babana"
"Haka ne, Allah ya ƙara mishi haƙuri toh"
Kuɗin da ta ciro a cikin jakar ta miƙo mishi. "Bani son tafiya da kuɗin nan wallahi don zanje nayi ta kashe
su a banza ne koma su ƙare a tsakanin ziyara, kuma kaga goggo sana'a tace in fara da shi".
Murmushi yayi ganin wayo wai take son mishi yace "Saudatu nace ba zan karɓi kuɗin nan ba, ke da kanki
kika ce goggo tace kada ki kuskura ki bani Amma shine zaki saka ni saɓawa umarnin mahaifiyata ko?"
"Toh ko aron rabi ka karɓa ka fara wani abun, zan yarje maka har lokacin da Allah ya baka sai ka biya ni,
dubu tamanin ne a nan kaga koma wani irin sana'a zan fara dubu 40 zai yi."
Ya girgiza kai. " Ni yunwa nake ji a taimaka a bani abinci" ya ce haka ne don kawar da zancen.
Babu musu ta miƙe ta shiga kitchen sannan ta ɗauko kular dake ɗauke da abincin nashi tare da ruwan
wanke hannu.
Hannun ya fara wankewa ta kawar da ruwan kafin ya shiga cin jollof ɗin shinkafa na manja da wake.
Komawa tayi ta zauna kana ta ɗaura zancen daga inda suka tsaya. "Toh ko buhun gawayi ka siya ka fara
kasawa da ɗan kayan miya, kaga Yaseer ma sai yana taya ka zaman wani lokaci, duk da akwai masu
siyarwa da yawa a layin amma kowa kasuwan shi yake ci ko?"
A zafafe ya ɗago yace "Yaseer dai naji kika ce? Toh kada na ƙara ji! Kada na ƙaaara ji Saudatu!. Yaron da
ya maida hankalin shi a kan karatu kike son a rabawa hankali? Ribar nawa ne zai samu a wani saida
gawayi ko kayan miya da har zai fi mishi karatun shi mutunci?"
"Hmm, Abban Yaseer naga karatu babu a inda ba'a yin shi, ba sai yaje can ɗin yayi ta karatun shi ba? Wai
gani nayi asirin mu ne zai rufu don abin da aka bamu ba tabbata zaiyi ba har abada. Kuma buƙatu kullum
ƙaruwa suke yi, zuri'a tana ta ƙara faɗi yara suna ƙara girma"
"Rufin asiri? Akwai nufin asirin da yafi mishi karatun ne? Kina gani da yanzu ni na jure nayi karatun mai
zurfi kuma ba a ƙurarren lokaci ba da yanzu muna cikin wannan wahalar ne?" Bata barshi ya dire ba ta
cafe da faɗin.
"Naga dai ko karatun ne sai da kuɗi ake yinsa, Idan karatun zai yi dame zamu biya kuɗin makarantar
matakin gaba? Ko shima komawa zamu yi mu sake roƙa a wurin wa'inda suka ajiye mu??"
Jan numfashi yayi yana ƙoƙarin daidaita fushin sa ganin itama ta haura. Ba zai biye mata yau maƙwafta
su fara jiyo abinda ba'a taɓa ji ba a tsawon zaman su a gidan na tsawon shekaru 4, ko zasu yi rikici bata
bari a jiyo muryar su don haƙura take yi bata jaa shiyasa wannan karon yayi mata uzuri.
"Ni dai na faɗa miki Yaseer sai yayi karatu har matakin PHD in dai inada rai da lafiya ta. Aikace-aikacen
gidan nan ma da yake faman yi kamar mace daga yau na soke shi." Ya bangaje kwanon abincin ya faɗi
tare da miƙewa tsaye, juyawar da zai yi idanun shi ya sauƙa a kan Yaseer ɗin riƙe da kunnuwan Suhail
duk sun kafe su da idanu.
Ƙaramin tsaki kawai yayi ya ratsa su ya wuce ya bar gidan, su kuma jiki a saɓule suka ƙaraso ciki.
Abincin da Kamal ya zubar Yaseer ya sunkuya ya fara tattarawa kafin ya rufe kulan ya mayar kitchen. Bai
cewa Saudat komai ba ya ci gaba da wankin sa yana bitar hadda ƙasa-ƙasa don ya samu Alkur'ani ya
kawar mishi da damuwar da yake son shiga ciki.
Kafin dare kuwa sai ga yunwa ta sake koro Kamal ya dawo, siɗin-siɗin ya shiga kitchen ɗin ya ɗauki kular
abincin da ya zubar ɗin ɗazu da ƙasa da komai haka ya zauna ya ci.
Har washegari da ta gama shirin tafiyar ta ya raka ta tasha tare da yaran yana wani ciccin magani don ta
fahimci zancen da ya faɗa mata babu wasa a cikin sa.
"Muma zamu zo muyi sati guda da yaran kafin su fara jarabawar Islamiyya in yaso sai mu dawo tare"
"Toh Allah ya kawo ku lafiya" tace kafin ta faɗa bayan motar, saida ya gama cika aka mishi lodin kayayyaki
kafin Yaseer yana ɗaga mata hannu Suhail na kuka har motan ta tashi.
.....
Hajiya Fauziyya ke faman kai komo tsakanin babban falourn ta da kitchen. Tana shirye cikin sabuwar
maroon ɗin abayar ta ƴar egypyt wanda kalar ya dace da hasken fatar ta matuƙa.
Baki daya yau yanayin gidan daban yake, hada-hadan da ake yi a cikin ta ya ninka na kullum, kalolin abinci
ake faman girkawa ana shake saman dogon dining table ɗin da shi, an share ko ina an daɗa goge shi,
ƙamshin da yau yake tashi a gidan yafi na kullum.
Agogon hannunta ta duba bayan ta ajiye tray ɗin coleslaw, a kowani lokaci baƙin zasu Iya shigowa, don
an ɗauki fiye da awa guda da Alhaji Tahir yaje ɗauko su daga airport da kanshi. ta daɗa gyara zaman
kwanukan da masu aiki suka jera sannan ta tabbatar sun tanadar da duk wani abun buƙata cikin tsari da
ɗaukan ido.
Kiran shi da ya shigo wayar ta ya sanya annurin fuskar ta bayyana domin sun ƙaraso a daidai komi ya
gama kammala, ɗaki ta koma ta ɗauko mayafin kayan ta yane kanta tare da dan gyara fuskar ta da soson
powder kafin ta fito cikin takun ta na manyan mata zuwa farfajiyar gidan a lokacin da baƙi da farin motoci
suka yi parking a ƙofar shiga.
Alhaji Tahir ne ya fara fitowa daga cikin baƙar bayan an bude mishi, Fauziyya ta ƙarasa kusa da faran
lokacin da aka buɗe ƴar yarinya ta fito sanye da riga da wando kanta da kitson da aka zubo da na gaban a
kan fuskar ta.
Suna haɗa idanu da Fauziyya tayi kanta da gudu tana "Oyoyo Aunty" lokacin da dattijuwar mata ta ƙarasa
fitowa daga motar tare da mai gidan ta.
Da mamaki amma cike da jin daɗi Hajiya Fauziyya ta rungume yarinyar don ba wai sun taɓa haɗuwa bane
kwata-kwata tun da aka haife ta sai a wannan karon mahaifin ta ya yarda aka zo da ita Nigeria amma
yanda ta sake da ita yayi mata daɗi.
A hankali ta sauƙe ta tana gyara mata kitson dake rufe mata idanu gashi yasha beads masu kyau.
"My daughter yaya sunan ki?"
"My name is Aicha Abdou Hamissou" tace tana duban mahaifiyar ta domin ta tabbatar mata daidai tayi,
itama cikin jin daɗi ta ɗaga mata kai alamun tayi daidai, sannan ta maido da duban ta wurin Fauziyyar.
"Aunty ance kin haifa mana baby. Ina yake?" Tace tana leƙa bayan Fauziyyar kaman babyn takowa zaiyi
da ƙafar shi ya fito.
"Ina taje dai ko Aisha?"
Girgiza kai tayi beads ɗinta na ƙara "uhm- uhm. Aicha ba Aisha ba"
Mahaifiyar ta tayi dariya kana tace "Ai duk abu ɗaya ne Darling"
"Toh ina babyn? Where is my brother?" Wannan karon bata jira amsar ta ba tayi cikin gidan a guje.
A kunyace Hajiya Fauziyya tace "kuyi haƙuri Ina ta fama da ɗiya ta na barku a tsaye, Bismillah mu shiga"
Alhaji Tahir da mijin matar ne suka fara shigewa ciki kafin ita kuma ta ƙaraso ta rungume Hajiya Fauziyya
ba tare da tayi tsammani ba. "Sai yau Allah ya haɗa fuskokin mu my dear. Mun sha ganin wace irin mace
Alaji Tahir zai dirje ya zaɓo ashe baiyi rawan ido a banza ba"
Ta sake rungume Hajiya Fauziyya dake murmushin jin daɗi lokaci ɗaya matar da ƴarta sun shige cikin
ranta. Ba a banza Alhaji Tahir ke yabon mijin ta ba baki daya familyn su abin sha'awa ne.
Hannun su cikin na juna suka shiga ciki mazajen har sun riga da sun sama wa kansu matsuguni sun shiga
gaisawa da hirar duniya. Sai ga Aicha ta fito daga kitchen tana bin duk wani ƙofa ɗaya bayan ɗaya tana
dubawa.
"Me kike nima please?" Mahaifiyarta ta ƙarasa ta riƙo ta.
"Aunty Ina babyn ban ganshi ba?" Tace idanun ta na kawo ruwa.
Upstairs Fauziyya ta haura zuwa ainihin bedroom ɗinta da jego ya saka ta barin shi, babu daɗewa ta
sauƙo riƙe da Reina cikin purple baby towel mai laushi ta ƙaraso wurin da su Aicha yanzu suke zaune tare
da iyayen ta, kana ta zauna itama tace "gashi zo ki karbe ta"
Cike da zumuɗi ta ƙarasa jikin babyn tana leƙa fuskar ta saidai ganin ɗan kunnen dake kunnen ta da
kuma kalar kayan jikin ta yasa ta fara baya-baya a hankali sannan ta saka kuka.
......
*A wannan gaɓa bayan uban Sarauniya wa ke sonta don Allah Please? Har ta kaiga idan an kalli fuskar ta
ayi kuka? í ½í¸‚*
*So far labarin wani gida yafi muku daɗi? Na su Saudatu ko Fauzah ko kuma duka?.*
*Saliha Ahmad Na'ibi ✨*
*REINA í ½í²�*
Saliha Ahmad Na'ibi.
13...... Da mamaki Fauziyya ke kallon yarinyar da ke kuka har da bubbuga ƙafa ta koma wurin mahaifiyar
ta.
"mummy ce na ki kai baby boy ne?"
Gwada kanta tayi tana mamakin lokacin da suka yi hakan "Kada ki min ƙazafi Please. Ce na nai an haifi
baby amma ban ce boy ne ba"
"Toh a mayar da ita a karɓo min boy please, baby brother ina so" tace tana share hawayen sakalcin da ya
fara bin kuncin ta.
Riƙo ta Hajiya Fauziyya tayi ta jawo ta a hankali ta dawo kusa da su sannan tace "wannan sister ɗin ki ce,
zata kula da ke idan ta girma idan kina mata kirki"
Fuskar ta dai a haɗe tana yiwa Reina dake barci kallon tara saura kwata.
"Haba Nana, yaya kike mata kallo kamar kishiyar ki na?"
Bata san me kalmar kishiyar ke nufi ba amman sai ta samu kanta da daɗa yamutse fuska, wannan karon
wurin mahaifinta ta nufa tana ƙunƙunin "Ni dai bani son ta"
Haka har aka sake sabunta gaisuwa, aka gabatar da kai ma Fauziyya da bata gama sanin su ba, da
tambayar gajiyar hanya, Aicha na maƙale jikin ubanta.
Da aka zo cin abinci ma sai wurin nanny Fauziyya ta mayar da Reina don firr Aicha ta ƙi zuwa kusa da
dining table ɗin.
Daga mahaifin ta Alaji Abdou har Alhaji Tahir abun baiyi musu daɗi ba amma kuma mai ƴa ɗaya ce da
mai ƴar fari. Kowa a cikin su na ji da nashi kaman kifi guda a cikin teku musamman ma Alaji Abdou da
auren shi kusan shekaru goma kafin Allah ya azurta shi da samun haihuwa, kuma bayan Aicha har yanzu
da take niman shekaru huɗu a duniya shiru babu labari. Ga mahaifiyar tata ma sickler ce yau fari gobe
tsumma shiyasa koda yaso ƙara aure ya sanar da ita ciwon ta ya tashi kaman ba zata yi rai ba ya haƙura
ya aje zancen a gefe suka ci gaba da manejin abinda Allah ya basu.
Hajiya Fauziyya kam ko a jikin ta don ta san fidda fice ne kawai irin na yara, don haka ta ɗauki Aicha ta
ɗaura bisa cinyar ta tana bata abincin a baki suna yi dukkan su suna taɓa hira sama-sama.
Suna gamawa ana kiran La'asar, saida suka yi Sallah sannan Hajiya Fauziyya ta shiga da matan ɗakin baƙin
ta, mazan kuma suka wuce study room ɗin Alhaji Tahir.
"Aunty kin san SpongeBob?"
Gyaɗa kai Fauziyya tayi idanun ta a cikin na Aicha da ta ɗale mata cinya ta tsaya sannan ta riƙo fuskar ta
cikin ɗan tafin hannunta tana kallon ta ido cikin ido domin ta samu hankalin ta hundred percent.
"Na san shi"
"Ina da ƙaton SpongeBob a gidan mu. Babba ya kai haka" ta ware hannun ta don ta gwada girman
teddyn, kana ta sake riƙo fuskar Fauziyya kafin hankalin ta ya bar kanta zuwa ga mahaifiyar ta da suke
hirar arziƙi.
"Masha fah?"
Ta sake gyaɗa kai "Reina tana da teddyn ta itama" Fauziyyar ta biya mata.
"Idan naje gida zan saka nawa a dustbin" tace tare da ɓata fuska, abun har ya basu mamaki ganin fa da
gaske take yi zancen bata son Reina amma ta liƙe wa mahaifiyar ta.
"Kin san Omar and Hana, da paw patrol?"
"Aicha, sauƙo!" Malika tace cikin dakakkiyar muryar da ya saka ta sauƙowa babu musu amma kuma bata
bar hirar ba, sai ma ta shiga bata shirmen labarin duk cartoon ɗin da take kallo.
Mayar da hankalin ta Wurin Malika Fauziyya tayi bata bar gyaɗa ma Aicha kai ga duk abinda tace ba.
"..Toh yaya Nijar? Ina sha'awar ziyartar ƙasar kuwa"
"Nijar alhamdulillah, muna miki maraba, sai kice Tahir ya ɗauko ki kuzo mana ziyara"
"In sha Allah da Reina ta ƙara ƙwari muma zamu zo"
Malika ta kama baki "Toh! Kema halin ku ɗaya da Daddyn Nana. Ina Nigeria ina Nijar da za'a ce sai jariri
yayi ƙwari? Tafiyar jirgi saboda daɗi yayi muku yawa ko?"
Fauziyya ta jinjina kai "nima ba ra'ayi na bane wannan, na nata Daddyn ne. Unguwa a cikin garin Bauchi
ma yace ba yanzu ba sai ta daɗa ƙwari"
"Idan yayi wasa ko sace ta zanyi in gudu saidai ya tsinto ta a maradi" suka saka dariya dukkan su Fauziyya
har tana imagining irin rikicewar da Alhaji Tahir ɗin zai yi.
"Yauwa Fauziyya, faɗa mini wani tanadi kinka yi wa baby Reina?" Cewar Malika bayan ta haɗa Aicha da
huruful hija'iyya a waya ko zata barsu su zanta ta daina damun Fauziyya da surutun da tana da tabbacin
ba ganewa take yi ba.
Dariya tayi "wani irin tanadi kuma? Na aure?"
Itama saida ta dara kafin tace "kina da abin dariya idan kinka so. Ina nufin tanadin raino, tanadin tarbiyya
da kuma tanadin rayuwa irin ta ƴa mace mai buƙatar matuƙar kulawa"
Ajiyar zuciya tayi "akwai wani tanadi ne bayan Allah ya raya mana su da imani?"
Jinjina kai Malika tayi ganin kaman bata da ra'ayi a zancen tace "gaskiya ne, Allah ya kare mana su daga
dukkan sharri kuma ya raya mana su da imani"
Sai ta kaikaita hirar ya koma na duniya, Malika tana bata labarin Nijar haka ma Fauziyya na bata na
Nigeria sannan suka koma na ƙasa mai tsarki da kuma ƴan yawace-yawacen da suka yi na honeymoon
lokacin tana amarya.
Ƙarfe takwas na dare aka sake jere musu dinner suka ci.
Duk yanda Fauziyya da Alhaji tahir suka kaɗa suka rawa firr suka ƙi yarda su kwana a gidan.
"Da gida na da iyali na ka saka ni kwana nan gidan ka Tahir kaman gauro? Lallai ka raina ni" shine abinda
Alaji Abdou yace yana ɗaukar Aicha a hannu kana ya riƙo hannun Malika.
"Gobe da sassafe zani Sabon warehouse ɗinnan in duba tare da masu ƙiyasi sai mu kimanta kayan da zai
iya ɗauka. In yaso daga baya kuma idan na samu hutawa sai mu zauna muyi maganar shigo da kayan da
kuma ɗiban ma'aikata"
Fauziyya na jin maganar ɗiban ma'aikata bata bar shi ya dire ba tace "Yauwa Daddyn Aisha Idan an zo
ɗiban ma'aikatan akwai wanda nake so ayi min alfarma a ɗauka"
Maido da hankalin shi gare ta yayi fuska a sake yace "Babu damuwa amarya