Showing 21001 words to 24000 words out of 97462 words

Chapter 8 - REINA BOOK COMPLETE BY SALIHA A. NA'IBI -1.pdf

02 Aug 2025

10160

ta da na zuri'ar ta.

Haka suka ja rago har bakin titi suka ɗaura a ƙurƙurar da suka zo da ita sannan suka koma gidan Alhaji
Tahir.
Driver ne ya shiga ciki ya danna doorbell sannan Aina'u ta buɗe ta bashi daman shigewa parlour ya jira
Hajiya.

Ba'a fi mintuna goma ba Hajiya Fauziyya ta fito riƙe da Reina wanda yanzu rikicin tan da sauƙi.
"Malam Adamu kun kai aikan?" Ta buƙata bayan sun gaisa.

"Wallahi Hajiya wata tsohuwa tace sai dai mu dawo da shi, kalaman da tayi ma basu da daɗin
maimaitawa, harda kuɗi ta bayar wai kuɗin da Alhaji ya bawa Kamalu aro ne ta dawo da shi"

"Innalillahi wa inna ilaihiraji'un, yanzu ina ragon?"

"Yana mota a waje"

"Shikkenan barin turo wani ku koma"

"Sun ƙi karɓa fa Hajiya, harda maganar banza"

"Za'a basu haƙuri, har su karɓa in sha Allah".

Ta miƙe ta koma ƙaramin parlourn ta na ƙasa yanda ƴan uwan ta mata ke baje suna kallo, baki ɗayan su
yau suka zo mata wuni.

Tana shiga autar su Sajida ta karɓi Reina daman saboda za'a bada nono ta bada ita. "Yaya Aina don Allah
ki min wani taimako mana" nan ta zayyane mata halin da ake ciki.
"Dan Allah kada ku bar gidan sai sun haƙura sun karɓa, kice na ce idan suka sake juyo da ku zan fito in
kawo musu da kaina"

Taɓe baki Zeenat tayi tace "kema dai shiga ukun ki yana niman yafi ƙarfin ki, tunda sun ce basu so ba
shikkenan ba? Ko ana kyauta dole?"

"Ana yi mana, tun da muma anyi mana kuma mun karɓa"
Sake taɓe bakin tayi ta maida hankalin ta kan tv don bata da cewa.

Kafin Aina ta mayar da ɗankwali da gyalen ta Fauziyya ta shiga ɗaki ta fito hannun ta riƙe da bundle ɗin
sabbin naira dubu-dubu da babban laidar Diapers, wipes, sai set na kayan shafan yara ta bata. "Kice ga
nawa gudumawar don Allah suyi haƙuri su karɓa kuma ina basu haƙuri da abinda ya faru, ki danne mun
su yaya Aina"

"Toh Amma kuɗin nan baiyi yawa ba fauzee? Ina laifin dubu hamsin? Koma Ashirin tunda ga niƙi-niƙin
kaya?"

Murmushi Hajiya Fauziyya tayi tace "da na baki kaman haka na siyan jaka da takalmi ai da kin bani canji
tunda na san akwai sosai ma".

Kama bakin ta tayi ta miƙe haɗe da rataye jaka sannan tayi musu sallama ta fice.

Firr Aina tace ba zata shiga ƙurƙura ba don haka suka ɗauki motar Hajiya Fauziyya motar rago na biye da
su har unguwar su kamal. Da sallamar ta ta shiga gidan da ake ta faman hada-hada ta samu Huwaila da
amarya suka bata hankalin su.
"Don Allah mai jego nake nima"

Suka yi mata iso cikin uwar ɗakin Saudat aka bata bakin gado ta zauna sannan suma suka nemi wuri suka
zauna a maimakon su basu wuri sannan aka shiga gaisuwa.

"Amma ban wayi fuskar ba" Saudat tace cikin jin nauyi.

"Allah sarki. Yayar Fauziyya ce ni"

"Fauziyya Fauziyya?" Saudat tace tana son ɗago sunan.

"Hajiya Fauziyya matar Alhaji Tahir dai"

"Ayyah Aunty ba? Tana lafiya? Yaya jaririya?" Ita ba zata ma iya tuna inkiyar Reina ba, kuma tasan sunan
wata mai muhimmanci aka mayar mata balle tace Hafusatun.

"Suna nan Lafiya alhamdulillah. Daman shine ma suka turo ni bin sawu da bada haƙuri"

"Ni babu wanda yayi min komai Wallahi, daman goggo ne da abban su, bari a kira miki goggon kada mu
ari bakin ta aci mata albasa"

Huwaila da kanta ta fita kiran goggo kuma tun daga wajen ta fara mata bayanin abinda yake faruwa don
haka fuska a tamke ta shigo ɗakin ta zauna Aina ta gaida ta.

"Daga ina baiwar Allah?" Goggo ta sake tambaya don bata damar maimaita ƙudirin ta.

"Ƴar uwar Fauziyya ce ni matar Alhaji Tahir, saƙon ban haƙuri ta turo ni da shi Mama, don Allah kuyi
haƙuri kada ku maida hannun kyauta baya"

"Kuna ta zancen maida hannun kyauta, shin kun duba kyan shi hannun da ya miƙo kyautar? Kun duba
fuskar da ya bayar da ita?"

"Sai an san anyi wa mutum ba daidai ba ake bashi haƙuri mama, don haka anyi miki laifi amma kiyi
haƙuri, tace kuyi haƙuri da abinda ya faru " sannan ta luma hannu cikin jakar ta zaro bundle ɗin da ta
zare dubu goma a ciki tun a hanya ta miƙa mata "dan Allah ki karɓa goggo ba don halin mu ba, tace idan
baki karɓa ba da kanta zata fito ta kawo miki"

"Lalala raba ni da fito da mai ɗanyen jego haka kawai, kuma ma ita Fauziyya ai ko dan halinta tace in
karɓa zan karɓa amma ko Kamalu uban Tahir bai isa ya wulaƙanta ni ba balle shi ɗan ciki na, shi Tahir ɗin
ya san da haka"

"Kina da gaskiya Wallahi Mama, kuma shima ya gane kuskuren shi ya bada haƙuri, sunce ma ko kwana
zanyi a gidan nan idan baki karɓa ba kada in dawo, to ga ƴan marayu kuma a gidan suna zaman jira kada
a ɗauki hakkin su."

Hannu goggo ta saka ta karɓi kuɗin tana faɗin "toh shikkenan", na haƙura na karɓa zaki iya tafiya.
Godiya tayi ta miƙe tana faɗin "toh bari a shigo da sauran"

"A'a harda wasu saura?" Amarya ta washe baki jin zancen arziƙi.

"Eh akwai rago da kuma kaya a mota, zamu je da yara su ɗauko.

"Ai bama sai anje da yara ba muje in taya ki ƴar nan"

Suka fita suka bada izinin a shigo da ragon a ɗaure shi a cunkusasshen tsakar gidan sannan Aina ta miƙa
ma huwaila laidar pampers da wipes kayan shafar kuwa ta ɓoye su a ƙasan seat.

"Wannan ƙunzugu ai sai a shekara ma yaron bai gama sakawa ba" ta ɗaura da guɗa sannan ta shiga
gidan tana shelar abinda aka kawo din harda kudin.
"Yaro ya samu jibgegegen rago, ƙunzugun shekara da ɗori, abin goge kashi har pakiti biyu da kuma
gudmawar kudi Naira na dukan naira har dubu Ɗari, daga uban shi Alhaji Tahiru da Uwar gidan shi Hajiya
Fauziyya. Don Allah ku taya ni bani da hanci"

Kowa ta kame hanci suka ɗauki kuwwar "Ayyiririiii...."


......


*Wattpad users Please a taimaki Seemahwrites ta cika followers dubu guda🙈 ina godiya wa duk wacce
ta ɗauki lokacin ta wajen danna follow button💗*

*Masu karatun English Novels albishirin ku💃🏼💃🏼 Ayyiririiii ba guɗan haihuwa bane😂 Recent English
novel ɗina mai taken THE BLEEDING ROSE 🌹 ya samu kammaluwa an haɗe shi document full in full
kuma zaku same shi a kan Naira 500 kacal. Ga masu son ɗanɗano ku duba profile ɗina na wattpad zaku
sami free pages. Ina faɗa muku labarin akwai tsayawa a rai, sai wanda ya karanta yaji✨. Ga mai buƙata
ya tuntuɓe ni a wannan lambar 08021689184.*

*REINA �*

10.... Har driver sun ɗauki hanya ya tuna bai bada dubu Ashirin ɗin da goggo ta bashi ya maidawa Alhaji
Tahir ba. kaman zai riƙe yayi tafiyar shi tunda sun kawo musu abin da ya ninninka hakan sai yayi tunanin
Idan shi bai ƙara ma mutanen da suke rayuwa cikin irin wannan unguwan ba a kufayin gida toh bai
kamata ya rage su ba, sa'annan ko ba daɗe ko ba jima zance zai iya dawowa kunnen Hajiya Fauziyya ko
Alhaji Tahir.

Parking yayi ya zuge window sannan da hannu yayi alamu ma mai ƙurƙura da ya tafi kawai, kana ya juya
kan motar suka koma hanyar da suka baro.

"Lafiya Malam Adamu? Ina kuma zamu je?" Aina ta tambaya.

"Kiyi haƙuri nayi mantuwa ne, akwai kuɗin da tsohuwar ta bayar in maida wa alhaji shine hajiya tace in
dawo mata dashi." Yayi mata bayani yana ƙara gudun motar don suyi sauri ya samu komawa kafin Alhaji
Tahir ya dawo ya samu bayi nan on standby.

"Har Nawa ne kuɗin haka?"

"Dubu ashirin ne?"

"Shine zamu koma a kan dubu Ashirin bayan mun kai musu kaman shi sau biyar? Ka riƙe kawai mana ko
kuma ka raba mana mu koma muce mun kai"

Kallon ta yayi a kaikaice harma ya manta da tuƙi yake, sai a lokacin idanun shi ya kai kan saiti na kayan
wanka da shafa na yara dake boye a kasan seat ɗin shi. Murmushi ne ya ƙwace mishi yace "baki tunanin
asirin ki zai tonu idan baki basu abin nan ba?"

"Toh wa yace maka nasu ne?"

Dariyan kinma raina min hankali yayi yace "tunda haka kika ce shikkenan"

Da suka isa gidan ma ita ya bada kuɗin don ta shiga ta bawa goggo hannu da hannu. "Sauran kuma ki zari
wani abu a ciki, ta riga da ta san nawa ne, don ita ta ƙirga ta bani"

Baki ɗaya sai Aina taji ta muzanta, tunda har ya buɗe baki yake gaya mata magana haka bayan da
gaisuwar arziƙi ne kawai a tsakanin su ta tabbatar ta gama zubar da mutuncin ta a idanun shi. Saima ta
fara tunanin kodai ta haɗa da kayan shafar ne ta kai musu? Amma daga ganin packing ɗin ta san ba mai
arha bane, kuma komai akwai a ciki harda soson shafa powder na yara da su soson wanka. Idan siyarwa
zata yi zata samu abin da yafi dubu 50 wa'innan mutanen kuma ba sanin darajar kaya mai tsada suka yi
ba.
Babu ɓata lokaci ta shiga ta maida kuɗin ta fito, a ɗarare haka ta shiga motar suka tafi.

.....

Su goggo sun gama shiryawa tsaff da gari ya gama wayewa zasu wuce tasha su kama motar Jama'are.

Dunƙulawa amarya kuɗin Saudat ta sake yi bayan ta maido mata da shi, idanun ta da maiƙon hawayen
kewa tace. "Amarya don Allah ki karɓa ku rage kuɗin mota"

"Ke da'alla, ance miki don ki bamu kuɗin mota muka zo? Da ace bamu da kuɗin mota kinsan ba zaki ga
ƙafar mu ba don haka riƙe kayan ki" ta miƙe ta bar mata kuɗin a wurin sannan ta ci gaba da shirya jikokin
ta.

"Toh Saudatu, zamu koma inda muka fito, Zamu tafi mu barki da haƙurin ki. kina dashi amma ki ƙara,
kina ƙokarin tarbiyya ma yaran ki don mun shaida a kan Yaseer amma ki ƙara sannan kuma ki ƙara addu'a
sosai da sosai, duk macen da ta fara tara zuri'a cikakken bacci a ko wani dare ba nata bane, dole kina raba
wasu dararen kina kai kukan ki ma Allah idan kina son kiga daidai a rayuwar yaran ki"

goggo ta miƙo mata kuɗin da suka haɗa wanda ya tashi dubu sha shida sai kuma dubu cassa'in da Aina ta
kawo, ya tashi dubu ɗari da shida kenan.

Ta samu zannuwa ma wurin guda takwas duk da rabin su rubber ne ko mix cotton Amma goggo da
amarya da wani kawun su mai gold suka saka mata manya har biyu. Haka ma jariri ya samu kaya daidai
gwargwado ga kuma sauran kayan abinci da ya rage an jibge musu a ɗakin su Yaseer, lallai wannan
haihuwa yazo musu da alkhairi.

"Kina samun kanki ki ci gaba da ƴan sana'oin ki, ban yarda ki bawa Kamalu kuɗin nan ba kiyi jari dashi
kinji na faɗa miki."
Karɓan kuɗin tayi da godiya tana jujjuya shi a hannun ta, gani take yi sunyi mata yawa idan har aka ce ba
zata bashi ba, zata iya sana'a koda babu jari don har wankin kuɗi tayi nauyin ciki yasa ta bari. Amma shi
idan ta bashi kudin nan ko teburi zai kafa yana kasa wani abun idan ya dawo daga aiki, Yaseer kam tela
take so ya zama amma da ko shima zai iya taya shi idan ya dawo daga makaranta.

Shima kamal saida yasha tashi nasihar da bata gajiya da mishi a ko wani lokaci kafin ya raka su har tasha
har saida motar su ta tashi kafin ya dawo. Ya samu har Yaseer ya gama komai kaman yanda ya saba shi
da suhail sun wuce makaranta.

Zama yayi a gefen Saudat yana cire taɓani kasha hadisin dake kan shi, "Saudatu goggo ta tafi. Satin ta
guda a cikin gidan nan"

"Wallahi kuwa, bamu da abinda zamu ce sai Allah ya ƙara tsawon rai da albarkan rayuwa."

Ɗaura zancen shi yayi domin ta fahimci abinda ke ranshi. "A wannan sati gudan babu wanda ya leƙo ko
ya turo kai ko Ita su turo direba ya kai musu ita su gaisa idan gidan nawa ne ba zasu iya zuwa ba."

Zata iya rantsuwa wannan ne karo na farko da taji ya koka da su a kan duk wani abun da zasu yi mishi
kuwa, saboda a yanzu mahaifiyar shi suka taɓo.

Yaci gaba da cewa "kuma dukkan su babu wanda banje har ƙofar gida na shaida masa zancen haihuwar ki
ba har matan, da kuma zuwan goggon a karo na farko cikin shekaru 4. Bayan Alhaji Tahir ɗin da muka
samu matar shi babu mai tunanin ko aika ko saƙon gaisuwa."

Ba na gaya maka ba! Shine kalamin dake cikin ranta amma sai cewa tayi, " sai haƙuri, daman haka duniya
take, ba kowa zaka so da zuciya ɗaya shima ya so ka haka ba"

"Hmm, babu komai, Allah ya bamu ladan soyayyar da muka yi musu saboda Allah " da ameen ta amsa ya
miƙe shima ya shirya ya wuce wurin aiki aka bar Saudat a gidan daga ita sai baby suka sha barcin su
tunda ga wutan nepa kuma mai sawa a kashe fankan yanzu bata nan.

......

Da lokacin da kake ƙirga shi da wanda baka bashi hankalin ka ba wanne yafi saurin wucewa ne? Don tun
jiya Hajiya Fauziyya ke mamakin wai har kwanan abinda ta haifa 40 a duniya.

Kuma tun jiyan suke ta tiƙi-taƙa da Alhaji Tahir a kan yawon Arba'in. A karo na farko da zubar da
hawayen ta bai saka ya canza ra'ayin shi ba, ya mata iyaka kuma ya kafu a kan zancen shi, A dalilin Ƴar
shi Hafsatu Reina.

Ya jaddada mata yawan gidajen da ya amince taje daga fannin ƴan uwan ta, da wanda bai yarda ko
unguwar ta leƙa ba. Sannan su wanda ya amincewa ya bata adadin lokacin da zata ɗauka a can ɗin ciki
harda gidan nata iyayen kuwa. Maganan dubo ƴan uwa dake ƙauye kanma bata samu zarafin fara mishi
ita ba.
Ɓangaren da bai kafa mata sharuɗa ba kawai shine bangaren gidajen ƴan uwan shi, saboda matakin da
suke na rayuwa yazo ɗaya hakama tsarin su.

Taso ta fasa zuwan baki daya amma sai taga shi zaifi son hakan ma, kuma ita ce da asara. Haka ta shirya
ranan ta fita suka fara zagawa da driver yana zaman jiran ta a waje, da lokacin da Alhaji Tahir ya bata
kuwa ya cika haka zaiyi ta horn har sai ta fito, wasu gidajen ko ruwa bata samu ta saka a bakin ta. Kuma
haka zaiyi ta addaban ta da kira yana tambayar ta yaya lafiyar Reina idan bata ɗauka ba shima ba zai fasa
kiran ba har sai ta ɗauka.

Ƙarshe da abin ya ishe ta wajen gidaje 2 haka ta haƙura da zuwa tace driver ya kaita gidan su kawai tun
kafin la'asar ma tayi.

....
"Matar Alhaji yaya aka yi?" Mahaifiyarta ta tsokane ta cikin jin daɗin yanda ƴar tata ta murje ta canza a
cikin shekaru biyu, ga cikowar jego ya ƙara mata kyau, ba zaka ce Fauziyya ƙashi da rai bace kamar yanda
ƴan unguwa suka saka mata tsabar rama Saboda rashin cin abinci gata kuma tana da ɗan tsayi shiyasa
ramar yake nunawa sosai (kamar ƙawata Zahra😹)

"Ummi na kusa kamuwa da postpartum depression" tace tare da sauƙe ajiyar zuciya ganin wani kiran na
Alhaji Tahir na sake shigowa cikin wayar ta.

Rejecting kiran tayi cikin jin haushi, duka-duka ko minti talatin bata yi da shigowa ba, kuma tazo ta samu
umman da kanta a kitchen saboda shirin zuwan nasu, sai yanzu ta samu kanta aka zauna za'a gaisa.

"Subhanallahi, depression kuma? Me zai saka miki depression Fauziyya baki rasa komai ba, ko Tahir ɗin
ya daina kula da ke ne?"

Girgiza kai tayi ta saka yatsar ta manuniya ta ɗan zunguri goshin Reina tace "takwarar ki ne take son shiga
tsakanin mu" bata bawa Fauziyya kunya ba ta ɓare baki kaman yanda tayi tsammani kafin tace "kin gani
Ummi, gaba ɗaya ta rikita ni ta rikita shi, Idan kika jini da shi to a kanta ne, ni kawai zan bar miki ita a nan
in koma ni kaɗai idan ta gyara hali sai in dawo in ɗauke ta"

Dariya Ummi tayi kana ta karbi Reina daga hannun Fauziyyar, ta tabbatar tana iya kokarin ta. Daman Bata
da son yara bata da hayaniya, ga ƙananun shekaru, ba don matsawar Alhaji Tahir ba da sai a yanzu da ta
haura Ashirin da biyu zasu yi mata aure lokacin ta gama karatun ta amma ba haka Allah ya tsara mata ba.
"Idan bata gyara halin ba fa? Sai ki ci gaba da barin ta a nan? Mahaifin ta zai yarda?"

Wani kiran ne ya sake shigowa wayar ta bayan saƙon da saida kiran ya shigo ta lura da shi.

'kada ki kashe min waya Fauzah, ki dawo da Reina gida kafin wani ciwon ya kama ta, kinga jaririya ce bata
da ƙwari'

Taɓe baki tayi da gadara ta sake rejecting kiran ta saka shi a Do not disturb kafin ta maida hankalin ta
wurin Aina da ta shigo da abincin da Ummin ta bar mata ta ƙarasa.

"Yaya Aina irin wannan ai sai yunwa ya kashe mutum" tace lokacin da ta dire tray ɗin a gaban ta.

"Wani

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login