Showing 15001 words to 18000 words out of 97462 words
Chapter 6 - REINA BOOK COMPLETE BY SALIHA A. NA'IBI -1.pdf
mata Wai Raina ne ko menene? Abun ki dai da matsiyaci bai iya samun wuri ba"
"Reina aka cewa ku kuma ƙauyawa, ƴan gayu suna abu kuna ɓata musu" saboda dariya har hawayen da
ya kwanta a idanun ta ya fara saka ta ganin hanya duru-duru dama ga duhun maghriba, don haka ta zari
tissue daga cikin kwali ta goge hawayen ba tare da ta bar ƙyaƙyatawa ba.
"Wallahi Farida zan mari bakin ki idan baki ƙyale mu munji da abu ɗaya ba." Hajiya lubabatu wacce ta
gama ƙufula ta harare ta "Ah-ah, asiri hauka ne? Don kawai mun zuba mata idanu sai ta maida mana ƙani
boyi-boyin ta? Ki kalli fa yanda Tahir yake rawar ƙafa a kan haihuwar nan fisabilillahi, Haihuwar ƴa mace
wanda ba zata amfane shi da komai ba saidai ya gama gina ta ya bawa wani ya aura."
"Shi yasa muke so abun ya dawo gida ai, ta ginu ta auri ɗan dangi ko ba komai munci ƙarfin dangin
matsiyata" Hajiya Hauwa ta ƙarashe tare da murguɗa baki kaman Fauziyyar ce a gaban ta, Wanda idan ita
ɗin ce a tare da ita yanda take nan-nan da ita zaka ɗau ciki ɗaya suka fito.
Ƙanƙance idanu cike da bala'i Hajiya jummai tayi tana fuskantar Hajiya Hauwa "Ke a tunanin ki zata bari
ne? Ko dan ba a gaban ki yazo ya tsuguna yana kuka da hawayen shi shar-shar na aje a roƙa mishi Hafsatu
da Ahmadu su amince su bashi Fauziyya ba?! Kwanar uwar mu 9 fa a cikin ƙasa lokacin, shine yaya
Zuwairah ta tsinke shi da mari don ya dawo cikin hayyacin sa toh tun daga lokacin suka ɗaura gaba shi
yasa baki ganta ta ɓata ƙafar ta zuwa suna ko barka ba. Amma kuma Tahir ya Haihu ya manta da tashi
uwar a barzahu ya saka sunan wata tsohuwar najadu"
Mamaki ne matuƙa ya kama Hajiya Hauwa ta riƙe baki tare da zaro idanu "Hasbunallahu wa niimal
wakeel. Shine kuma kuka bari ya aure ta?"
"Yaya muka iya an gama wanke shi? Barazanar zare hannun shi cikin lamarin kasuwancin mu ya fara yi, ya
shiga fushi da kowa daga lokacin muka gane ba laifin shi bane."
Hajiya hauwa ta jinjina kai "Aini na sha mamaki yanda naga rana ɗaya Abban su Jamal ya amince da
zancen ashe da walakin goro a miya" tana nufin mijin ta Alhaji Salisu.
"toh a lokacin ma kenan balle yanzu da an bashi ya ci, ya sha, ya shaƙa, ya taka ya yi wanka dashi. Kinga
ba abun mamaki bane idan rana ɗaya ma yace ɗaukar iyalan shi zaiyi ya bar ƙasar, muda sake ganin Tahir
hala saidai a darussalam."
Hajiya lubabatu tayi saurin amshewa da "Wallahi indai kuka ga Tahir ya bar Nigeria kai ko Bauchi bai isa
ya bari ba saidai idan ƙasa ce ta rufe idanu na. Auren ma saboda lafiyar shi da hankalin shi yasa muka
barshi ya yi ba wai don Fauziyya tafi ƙarfin mu ba, inba haka ba me aka yi aka yi dangin ta baki ɗaya da a
rana ɗaya naga dama zan iya sakawa a shafe tarihin su baki ɗaya?"
"Uhmm kun dai matsa ma Masarauta iyayen Sarauniya"
saida Hajiya lubabatu ta kai wa Hajiya Farida duka kafin taji daɗi bakin ta kuwa bai mutu ba tana ta ƙara
ƙular da su har suka isa Gidan Alhaji Salisu suka baje capacityn su a can, sun samu sunyi sallar maghriba
haɗe da isha suka ci abinci, domin kare aji ya hana su cin na suna kafin suka ɗaura da caccakar Hajiya
Fauziyya daga inda suka tsaya.
.....
Kwana biyu kenan da zuwan Goggo Halime daga jama'are tare da kishiyar ta da suke kira da Amarya,
daman haka suke tun zamanin yarinta tunda anyi zaman lafiya zaman amana sai kowa a cikin su ta mayar
da lamarin ƴar uwar ta ya dawo nata suna hidimar su tare har tsufa ya kama su gashi ana kan zuba jikoki.
Tuwon dawa miyar kuka suke ci daga gindin bishiyar neem dake tsakar gidan, hasken cikakken farin wata
shi yake haska musu cikin farantin suna ganin wurin da suke yanka, tunda rashin wuta har ya saka raka ni
kashin goggon ma ta mutu ba caji.
Daga uwar ɗaka Saudat take fifita a hankali yanda goggon ba zata ji ba don ta hana ta amma zafin da ake
kamar zai hallaka mutum har jaririn ma ƙurajen zafi sun dabaibaye masa jiki.
Ga sirkin da aka ciko ƙaton kofin silver dashi yana tururi, tabbas tasha wannan kam zaifi narka ta zaiyi har
hanji.
Wutar da aka kawo ya haska ɗan madaidaicin tsakar gidan da yalon haske. Suhail da yaron huwaila suka
saka shewar "nepaa" kana suka fara wawan abinci don su gama da sauri suje ɗakin Saudat kallo.
Ba'a daɗe da kawo wutan ba Kamal ya shigo sannan ya tsuguna a gaban mahaifiyar shi yana miƙa mata
canjin Naira 300 "gashi sun karɓi dubu uku da ɗari bakwai da ƙyar don an ɗauki lokaci ba'a biya kuɗin ba
shi yasa ma suka yanke.
Hannunta ta tsame daga cikin tuwon ta suɗe shi tass sannan ta zuba idon ta cikin na Kamal, Allah ya gani
bata kunyar ɗan fari da kamal domin idan bata bashi kulawa ba waye zai bashi, tunda gashi ƴan uwan da
ya kamata su ɗauki nauyin shi a ko wani ɓangare na rayuwa sun banzantar dashi.
Shekarun shi huɗu kenan da dawowa cikin garin Bauchi da iyalan shi a kan cewa Alhaji Kalabu zai sama
mishi aiki amma bata san irin rayuwar da yake yi ba kenan, har ita ma idan damuwar ta ya tashi take turo
mishi ƙorafin kuɗi kuma yayi ƙoƙarin mata ba tare da ƙorafi ba saidai a samu jinkiri, ashe ita ma ta fishi
samu tunda ba aikin arziƙi aka sama mishi ba.
Gadin makaranta ce ta firamare ana bashi dubu ashirin a wata, a wannan zamani na tsadar rayuwa ga
mata da ƴaƴa guda biyu yanzu sun zamo uku, ga mahaifiya da ƴan uwa masu bani-bani a ƙauye.
Hannun ta miƙa da nufin karɓan kuɗin tace "kace ma da kaje wurin Alhaji Tahir nawa ya baka?"
"Dubu ashirin" ya bata amsa.
"Babu komai zanje in same shi"
Ta sake mishi kuɗin sannan ta miƙe da nufin wanke hannun ta.
Duban shi ya mayar ga Amarya da bata rabuwa da murmushi a ɗan yamutsattsen fuskar ta, halin su ɗaya
da goggo shi yasa tasu tazo ɗaya, don haka ganin ɓacin rai a fuskar ta yau ya ɗaga hankalin shi matuƙa.
"Amarya ki bata hakuri kada taje ta tayar musu da hankali don Allah"
Murmusawa tayi kaman damuwar shin ba komai bane tace "kada ka damu zuwa gobe zata huce, yanzu
ka ƙaro wa mai jego sikari da canjin hannun ka".
Da toh ya amsa sannan ya miƙe, ya shiga ɗakin kwanan su duba Saudat kafin goggo ta dawo daga ban
ɗaki.
Tana fifita ya riske ta ga gumi nata karyo mata don haka ya jefa mata tambayar, "yaya baku kunna fanka
ba"
Ƙasa da murya tayi yanda na waje ba zai jisu ba tace "goggo tace sanyi zai kama yaro"
Jin sunan goggo yasa bai tanka zancen ba saima sauya akalar zancen da yayi. "Saudatu wani suna kika ga
ya dace mu saka mishi?"
"Duk sunan da kake so ka saka bani da haufi a kan zaɓin ka"
Ɗan shiru yayi yana sosa ƙeya kafin yace "dama ni naso wai ko mu saka mishi Tahir ne tunda naga kaman
shi bayi da takwara"
Nan da nan annurin fuskar Saudat yayi saurin ɗaukewa ta kuwa tamke shi tamau. "Wani irin Tahir kuma?
Mu ke da alhakin mishi takwara saboda Allah?"
"Ai shiyasa na tambayi ra'ayin ki."
Ta san ba lallai zaɓin ta ya faranta ran kowa ba domin tafi son sunayen zamani ita, kaman na Suhail da
aka bata zaɓi, toh yanzu ma in ta sake zaɓa surakanan ta zasu ga taso kanta don haka tace "toh a tambayi
Goggo"
"Idan itama tace a saka Tahir ɗin kuma fa? Koma kalabu? Kinga ba zamu iya ja da ita ba gwanda ki zaɓa
sai ince mata ra'ayi na ne."
Shiru tayi tana nazari kafin tace "toh a saka mishi Sabir."
"Shikkenan an gama amma zan shawarce ta a kan sunan kafin mu saka" gyaɗa kai tayi, ya saka hannu
yana share ma yaron gumin da ya jiƙa farin powdern goshin shi. Yace "ɗan albarka baka da rikici"
Saudat ta karɓe da "gaskiya kam, saidai idan yaji yunwa ko barci amma ko zafin bayi damun shi sosai.
akwai haƙuri kam yaci sunan shi haka muka yi da Yaseer ma, baba na ne mai rikici dai har yanzu."
"Allah ya raya mana shi da imani, ya kuma basu ingantaccen rayuwa baki ɗayan su" da ameen Saudat ta
amsa sai ya ƙara da "baki buƙatar wani abu?"
"goggo ta sayi komai ni har kunya ma ta kama ni wallahi"
"Babu komai, haka iyaye suke koda mun hana su idan suna da halin yi sai sunyi mana, Allah dai ya bamu
ikon kyautata mata muma" ta ƙara amsawa da ameen sannan ya miƙe.
Suhail na ganin zai fita ya maƙale dole ya fita dasu biyun zuwa shagon dake can bakin titi.
.....
Har yanzu goggo bata bar Mamakin yanda Yaseer ya iya komai a cikin gidan ba, yanda bayi barin su su
ɗauki ko tsintsiya Idan dai yana nan.
Shi zaiyi shara, wanke-wanke, wanke ban ɗaki, ɗebo ruwa, wanki, yabi ya wanke yara harda na makwafta
idan sun shigo bayi barin su su fita da dauɗa kuma ya shirya ya tafi makaranta da ya dawo yaci abinci ya
wuce hadda ranar da babu ya tafi shagon ɗinki.
"Saudatu so kuke yi ku kar yaron nan ko?" Goggo ta shiga rikici bayan Yaseer yayi musu sallama ya fice,
daman ita bata yiwa iyaye faɗa a gaban yaro don hakan ba a ko wani lokaci yake daidai ba.
Shiru Saudat tayi don bata da ta cewa, goggo ta ci gaba da zuba zance"kunyi mishi horo mai tsanani yaro
bai san ya huta ba ko kaɗan? Ko mace kuke son maida shi ne iye?!"
Saudat dai tana shiru sai huwaila dake aza ice a ƙasan tunkyar wankan mai jego ne tace "wallahi Goggo
ko kince ya bari bayi bari, haka nan yake da zafin nama jikin shi bayi son zaman banza, ga fannin karatu
ma ba baya ba ance har monita ake bashi a boko a hadda kuwa idan baizo na ɗaya ba bayi wuce na biyu."
Goggo da Saudat suka saki murmushi a tare duk da ba kallon juna suke ba. Amarya dake daga uwar ɗaka
tana wanke jaririn tace.
"Huwaila bar Halime kishi kawai take kada mijin yace yana son sabuwar amarya kwanan nan tunda girma
da hankali sun zo"
Da haka suka ci gaba da hira cikin nishaɗi Saudat na saka musu baki jifa-jifa idan buƙatar hakan ta taso,
yara kuwa duk an wuce boko Kamal ya tafi wurin aiki.
.....
"Baba kiyi haƙuri Alhajin bayi gida nace miki" mai gadin nan ne na gidan Alhaji Tahir.
Yanzu haka daga gidan Alhaji Salisu suke shima an hana su shiga wai Hajiya da Alhaji duk sun tafi aiki
shine suka gangaro nan don fushi take da Alhaji Kalabu.
"Toh matar gidan fah? Ko itama bata gida?"
"Eh bata nan" ya amsa kai tsaye yana daɗa haɗe giran sama da na ƙasa.
"Mai jegon ne bata gida?" Sai yanzu kamal ya sako musu baki cikin zancen su. "Ko yau ma zaka ce baka
gane ni bane?" Ya ƙara matsowa kusa dashi da confidence yau gashi da shaidar shi a tare da shi.
"Wannan da kake ganin ta ƙanwar Uban mai gidan ne, don haka kafin yazo ka rasa aikin ka bata hanya ta
wuce"
Ƙaramin tsaki yaja sannan ya bada izini aka buɗe musu ƙofar suka shige Kamal har wani boƙarewa yake
kan shi yana mishi faɗi suka shige direct har parlourn Hajiya Fauziyya wanda Wannan shine shigan shi
cikin gidan a karo na farko, duk cikin sauran ƴan iwan ma idan yaje gidajen su toh saidai ya jira a waje.
*Saliha Ahmad Na'ibi (Mrs Imran ✨)*
*REINA í ½í²�*
08.....juye-juye kamal yake yi a tsakiyar parlourn kaman wuyan shi zai tsinke. Ba don shi da ƙafar shi ya
shigo ba zai iya rantsuwa cewa ba a Najeriya yake ba amma wai ƴan uwan shi Hausawa ne ke rayuwa a
irin wannan aljannar duniya.
Sallamar Hajiya Fauziyya ne ya maida hankalin su duka biyu gare ta, tana tafe da jaririyar ta rungume a
ƙirjin ta, kamar kullum fuskar ta ɗauke da murmushi.
"Mama Bismillah ku zauna, sannun ku da zuwa" tace yayin da itama take niman wurin zama a kujeran
dake kallon nasu.
Parlourn tsit babu hanayiya ko kaɗan sai ƙarar na'urar sanyaya wuri dake aikin sa babu gajiyawa. Har
goggo saida tayi mamakin saurin fitowar hajiya Fauziyya don ta ɗauka sai sun gama shanya ta kafin ta fito
kaman yanda sauran matan ƴan uwan Tahir ɗin ke yi.
Gyara zaman Reina tayi a cinyar ta cikin kiyayewa saboda kada ta tashe ta daga baccin da aka samu tayi
da ƙyar bayan ta gama ihun ta ta gaji, sannan ta ɗan zame kaɗan daga kujerar ta gaida Goggo Halime.
"Mama Ina wuni, kun iso lafiya?" Kasancewar yau ne rana ta farko da ta fara ganin ta yasa tayi tunanin ba
a nan cikin gari suke ba, domin bata san kamal ba bata taɓa haɗuwa da shi ba don haka bata san shi
waye ba, masu aikin ta dai sun shaida mata ƴan uwan mai gidan ne, sai dai fuskar shi yana mata kaman
ta san shi a wani wurin amma ta rasa ina?.
A take Goggo Halime ta saki fuska ta ɗauko murmushi ta yafa ganin kirkin matar Tahir. "Sannu dai ƴar
nan, mun same ku Lafiya? Yaya kishiyar tawa?"
Miƙewa tayi da nufin ta miƙa mata Reina ta ganta, tana amsawa da "lafiya ƙalau, an gode Allah" karɓan
ta goggo tayi "Masha Allah, kishiyar tawa jajawur abin ta"
Komawa Hajiya Fauziyya tayi ta zauna tana dariya "Ai da shirin ta tazo na ƙwace mai gida"
"Ta makara ai, tunda har rai yayi halin sa, saidai mu jira wanda zata dirje ta zaɓo mu aure shi tare"
"Allah sarki, Allah yayi mishi rahama" tace cikin alhini.
Goggo ta amsa da "ameen ƴata"
Daidai lokacin masu aikin gidan guda biyu suka shigo kowa ɗauke da tray a hannun ta suka dire a gaban
su.
Na farkon na ɗauke da ruwan gora mai sanyi ɗaya da mara sanyi kuma, sai juice ɗin kwali da kuma glass
cup. Sai ɗayan mai ɗauke da soyayyar naman kaza anyi pepper ɗin shi da kuma kayan ƙwalam na fulawa
irin su donut.
"A'a har da wahala haka?" Tace tana washe baki, murmushi kawai hajiya Fauziyya tayi "Kamalu kaga zuba
min ruwan nasha" ya durƙusa ya bude lemon kwali ya tuttuɗa mata a kofi domin da hankalin shi ba zai
bata baƙin ruwa ba bayan ga mai kala nan a kusa.
Shima ya cika nasa kofin kafin ya koma ya zauna sannan suka shiga gaisawa da Hajiya Fauziyya yana yi
yana kurɓan lemo, kana ya shiga mata bayanin daga inda suke don akwai buƙatar hakan.
"Ban san ko kin gane ni ba, mijin Saudatu ne da tazo miji barka Ranar Alhamis"
kaikaitar da kai tayi tana son tuna wata Saudatu ce, domin yawan wa'inda suka dinga zuwa mata barka a
kullum ba zata iya kiyaye su ba.
Daga ranar suna ne ma Alhaji Tahir ya samu saran dawowa da wuri suna cike a gidan sai yayi musu kora
da hali ko kuma ya ɗauke Hajiya Fauziyya su yi ciki ba zasu sake ganin ta ba, toh fa shine suka shafa musu
lafiya yau babu wanda yazo.
Ganin bata gane ba yasa ya canza akalar bayanin nasa "Ai ni ɗan uwan su Alhaji ne. Goggo nan da kika
gani ƙanin mahaifin su ne uba ɗaya"
Da sauri ta gyaɗa kai "Kai ne baban Yaseer kenan?"
Ya ƙara washe baki ganin yanzu ta gane "eh wallahi Hajiya"
"Yaya jikin umman Yaseer ɗin? Don tace bata ji daɗi ba ranan"
"Ai ta sauƙa ai, an samu ɗa namiji" goggo ta amshe zancen,
Hajiya Fauziyya ta ƙara washe baki."Ah Masha Allah, Allah ya raya, yau kenan ko jiya?"
"A'a yau kwana uku kenan, suna barin nan gidan abun yazo"
Tunawa tayi da alƙawarin da tayi musu na za'a maida su gida, ashe baiwar Allah kanma na cikin halin
naƙuda, Allah dai yasa da suka fita sun samu abun hawa ba wai a sanadin ta haihuwar ta taso mata ba.
"Allah sarki, ai kuwa bamu ji ba, zamu je muga baby in Allah ya yarda"
"Shiyasa ma muka zo ƙafa da ƙafa domin mu sanar da ku don ma kada kuce baku jin ba" Goggo Halime ta
amshe. ina amfanin zumuncin ɓangare ɗaya kawai? Idan ɗaya bangaren suma suka sada nasu zumucin ai
abun zaifi armashi- Take tunani a ranta.
"gashi kuwa baban ta bai dawo gidan ba tukunna, zaku jira shi ina babu matsala?"
Goggo da ta shanye lemon ta tass ta miƙa wa Kamal kofi ya ƙara mata sannan ta tambayi "zai kai dare
ne?"
"Eh gaskiya amma zan kira shi in sanar da shi, in sha Allah zai dawo da wuri"
Ta tashi da niyyar taje ta ɗauki wayar ta ta kira shin a ciki dai-dai lokacin da Reina ta tsalla wani ihu
kaman wanda aka mitstsine ta.
Sauƙe numfashin ƙosawa Fauziyya tayi tare da juyowa tana kallon jaririyar dake ƙara sautin kukan ta har
wani sassandarewa take