Showing 36001 words to 39000 words out of 79955 words

Chapter 13 - Rai da kaddara Book Complete by Lubna Sufyan .pdf

budurwa sai ba zamu huta ba?"

Kallon shi Nawfal yayi

"Aure zanyi Hamma..."

Ya sake maimaitawa yana sa Khalid kallon shi

"Ina nufin kafin in koma za'a daura, aure zanyi kafin in koma"

Sosai Khalid yake kallon shi wannan karin

"Nasan ya kamata in fada maka tunda na dawo, amman nabari ne in fadama Daddy tukunna,
shi ya kamata ya fara sani kafin kowa"

Kai Khalid ya jinjina

"Allah ya sa alkhairi"

Ya furta yana rasa abinda yayi niyyar yi kafin Nawfal din ya sauke mishi wannan zancen saman
kai

"Hamma..."

Nawfal ya kira, amman hankalin Khalid din yaki komawa kan shi

"Hamma mana..."

Waje Khalid ya samu gefen gadon ya zauna yana daukar wasu dakika kafin ya daga kai ya kalli
Nawfal

"Me yasa? Ka fahimtar dani yanda zangane"

Saboda har a ranshi yana son gane dalilin da zaisa Nawfal yanke wannan babban hukuncin da
yake ganin baiyi hankalin da zaiyi shi ba, duk da tsiran da yake tsakanin su bawani mai yawa
bane ba. Yayi girman da yasan duk inda za'ayi magana ta aure ba karamin abu bane ba.

"Ni kadai ne Hamma, tun banda hankalin mutanen daya kamata su tsaya tare dani suka fara
watsar dani, ina da ku na sani, ina jin kamar bai kamata ba da nace maka ni kadai ne..."

Kallon shin dai Khalid yakeyi

"Ina kaunar ku, ina kaunar ku fiye da yanda zan fada, nasan kuna kaunata, da yawa, ba zan
kira ku nawa ni kadai ba, ba zan kiraka nawa ni kadai ba, ina rabaka da mutane da yawa a
yanzun, lokaci zaizo da zan sake rabaka da wata... Ina son abinda zan kira nawa"

Wani sauti ne ya kwace ma Khalid din da yake tsakanin dariya da wani yanayi da bashi da suna

"Ita din ba zaka rabata da wani ba?"

Ya tambaya yana jin wani abu ya tokare mishi makoshi

"Ba kaman ku ba..."

Kokarin hadiye abin da yake a makoshin shi Khalid yakeyi, maganganun Nawfal sun mishi zafin
da ya kasa fahimtar su

"Tana da iyaye da yan uwan da ta taso da kaunar su kafin taka, ka fadamun bambancin da yake
tsakanin ta da mu... Kana so ka fadamun mu ba zamu taba zama naka kai kadai ba, amman ita
zata iya zama? Mu muna da wani lokaci na barin rayuwar ka... Ko dan kaine kasa lokacin barin
mu saboda ka samu wadda zaka kira taka?"
Tunda ya fara magana Nawfal yake girgiza mishi kai

"Idan baka fahimce ni ba babu wanda zai fahimce ni Hamma, dan Allah karka fassara kalamai
na idan baka fahimta ba, karkayi mun haka"

Nawfal ya karasa muryar shi na karyewa

"Ka fahimtar dani Bajjo..."

Numfashi Nawfal ya sauke zuciyar shi na rawa

"Idan baka so zan hakura, zan bar maganar nan... "

Dan tunda ya yanke hukunci bai dauka akwai wani dalili da wani zai bashi ya sauya mishi ra'ayi
ba. Yasan Khalid na da muhimmanci a wajen shi, bai taba tsayawa ya auna girman
muhimmancin ba sai yanzun, da a karo na farko tun haduwar shi da Murjanatu yaji zai iya
barinta idan har zata zama silar samun matsala tsakanin shi da Khalid din

"Babu wani abu a yar duniyar nan tawa da yake da muhimmancin alakar da take tsakanin mu"

Cewar Nawfal yana saka Khalid jin kafafuwan shi sunyi sanyin da in ba'a zaune yake ba zasu
kasa daukar shi, yaja iska ta bakin shi yana fitarwa yafi a kirga kafin ya samu natsuwar fadin

"Ka kalleni Bajjo, lokaci daya nake da shi na barin rayuwar ka, lokacin da ba rayuwar ka bace
kawai abinda zan bari, duniyar ce gabaki daya...ba kai kadai bane ba, duk tunanin da yake fada
maka haka ka karya tashi, idan kana jin baka da kowa kana da ni, kana jina ko?"

Kai kawai Nawfal ya iya daga mishi

"Idan aure ne zabin da kayi ni banda matsala da hakan, kawai ina so kasan ba abu bane da
zaka zaba yanzun ka canza anjima, rayuwar yarinyar mutane ce akan layi Nawfal"

Khalid ya karasa da kiran asalin sunan shi dan ya san maganar da yake na da muhimmanci

"Bana jin zan iya ba mai shekarun ka 'ya ta Bajjo, ba kuma zan daina ganin wautar mutumin
nan ba...kadaici kowa yakan ji shi lokaci zuwa lokaci, karya zama dalilin da kawai zaka aure ta,
ka hanga shekaru masu zuwa, a cikin shekarun ka duba hali na rashin tabbas, hali na rashin
lafiya, ka duba yiwuwar jin dadi da rashin shi, kana ganin kanka a tare da ita a duka
yanayoyin?"

Numfashi Nawfal ya sauke, kalaman Khalid din na ratsa zuciyar shi

"Idan ka shiga cikin auren ba zaka iya fita da saurin da ka shige shi ba... Ba zaka iya ba...Bajjo
wasan nan ba da rayuwarka kawai zakayi shi ba harda ta Murjanatu da duka ahalinta... Karka
fara abinda ba zaka iya karasawa ba..."

Cikin idanuwa Nawfal ya kalli Khalid din

"Ina son ta"

Ya amsa

"Soyayya kawai tayi kadan"

Idan Nawfal bai sani ba, shiya sani, wasu zasu karyata ana ganin soyayya kwance a idanuwan
mutane, idan baiga soyayyar Julde a idanuwan Saratu ba shima zai iya karyatawa, amman bata
hana su samun matsalar da suke tunanin baya kula ba, suna fada ko da baisan me yake hada
su ba, sosai suke yawan yin fada yana kula da hakan. Da soyayya ta isa da wadda Nannar shi
take ma Daddy ta hana musu samun matsala

"Bansan sauran abubuwan ba Hamma, amman zamu neme su a tare, shine kawai alkawarin da
zan iya a yanzun..."

Kai Khalid ya jinjina

"Aure zakayi Bajjo, aure zakayi"

Khalid yake fadi wata dariyar mamaki da tsoron wannan babban matakin da rayuwa ta kawo
dan uwan shi na kwace mishi, shima dariya Nawfal yayi, tsoron da yake gani a fuskar Khalid din
na taba shi, a karo na farko shima matakin na bashi tsoro, sai dai tare da tsoron babu shakku
ko kadan
Rai da kaddara
Murjanatu na daya daga cikin kaddarorin shi
Tana daya daga cikin hasken da zai yaye wani bangare na duhun da yake bibiyar rayuwar shi
yana jiran cikar lokaci.

©

FIKRA WRITER'S ASSOCIATION

Facebook: Lubna Sufyan
IG: SufyanLubna
Email: Calmlubna@gmail.com

*RAI DA KADDARA 1*

11

Shiru bai taba mishi yawa ba, lokutta da yawa ma yana jin yayi mishi kadan, ko shi kadai ne
zaune a bangaren su cikin gida, sai ya dinga jin hayaniya a cikin shirun dakin, karar agogo,
fanka ko AC din cikin dakin, ko wani kwaro da ba zaice ga inda yake ba, hakan kawai na hana
shi sukuni, shisa ya siyi abin toshe kunne, yana da su wajen kala hudu, su kansu basa taimaka
mishi, idan yasa duk kananun hayaniyar sai ta daina isa cikin kunnuwan shi, sai kuma ya dinga
jin surutun da yake wanzuwa tsakanin kwakwalwar shi da zuciyar shi.

Yana rasa a cikin mutane shi din wanne iri ne? Ya kanyi tunanin ko irin shi guda nawa ne, ko ya
suke ji da hayaniyar da take cikin yau da kullum? Musamman idan ya hasaso kasancewar su
cikin halin rashi, babu wadatar da zasu samu wajen kebewa su kadai. Amman yau shirun da
yake cikin motar yayi mishi yawa, ba dan gilasan suna kulle ba, idan shi kadaine zai dinga jin
karar sauran motoci harda ma kukan tashi motar. Sai dai duk lokacin da zai zamana shi da
Madina ne a zaune cikin mota, ko kuma tana gefen shi baya jin kowacce irin hayaniya.

Asalima banda muryarta da dariyarta babu wani abu da yake isowa kunnen shi, ko bata
magana kamar ganinta na saka komai yin shiru ne. Sai dai yau shirun nata yayi mishi yawa,
tunda ta fito ta gaishe da shi ta koma cikin mota ta kwanta kamar marar lafiya, har suka fita
daga layin suka hau titi ko motsi baiga tayi ba, lokaci zuwa lokaci yana kallonta. Matsalar bai iya
hira ba, bai taba fara hira da wani ba, ko a cikin yan gidan su kuwa, banda gaisuwa sai dai in
kaine ka tambaye shi wani abin, ya rasa me ya kamata yace mata.

"Lokacin damuna ne ake noma tumatiri ko?"

Tambayar ta kubce mishi tana saka Madina juyo da kanta tana kallon shi na wasu dakika cike
da mamaki, shima dan raba idon shi yayi daga titi yana kallon ta

"Shine abinda ya fara zuwa kai na..."

Ya fadi yana maida hankalin shi kan titi, wata irin dariya Madina ta kwashe da ita

"Da gaske Hamma?"

Ta tambaya, kafadu yadan daga yana rausayar mata da kai

"Kinki mun hira... Bansan me zance ba"

Yayi maganar da dukkan gaskiyar shi, hannu takai ta gyara gilashin fuskarta tana sauke
numfashi, har lokacin da murmushi a fuskarta. Kawai ba zatace ga asalin abinda yake damunta
ba duk satin. Ta san zazzabi, da shine zata gane, babu inda take ji yana mata ciwo, kawai tana
jin kamar dai akwai wani abu da babu a cikin rayuwarta a satin.
"Bajjo zaiyi aure"

Daada ta fada mata, ta zabi ta fada mata lokacin da ta cika bakinta da ruwa tana shirin hadiye
wa, ta kuwa sarke tana tarin da ta kusan shafe mintina biyar bai tsagaita mata ba, idanuwanta
duk sun tara hawayen wahala

"Cikin satin nan idan Allah ya bamu aron rai"

Daadar ta sake fadi, ko da taso yin wata tambaya bata san ta inda zata fara ba, tambayoyin
nata da yawa, wata na danne wata haka suka dinga tasowa cikin kanta. A lokaci daya kuma
tana nemar ma maganar wajen zama a tare da ita cike da son gane me hakan yake nufi da tata
rayuwar ko wata dangantaka da take tsakanin auren na shi da ita. Shisa sai komai yayi mata
yawa, abu dayane take jin zata iya cewa, kamar Nawfal din bai kyauta mata ba, kamar daga
bakin shi ya kamata ta fara ji. Kamar ya kamata ace tasan maganar.

"Kunyi shakuwar da zai gaya miki zaiyi aure ne?"

Wata murya ta tambayeta, ta so tayi gardama, taso ta zayyano ma muryar shekarunta na
kuruciya, lokuttan da Nawfal yake daukota akan bayan shi daga makarantar islamiyyar su zuwa
gida kamar bata da wani nauyi, lokuttan da take jiran zuwan shi dan ta zayyana mishi duk wasu
kananun bukatunta ya kuma cire kudin shi ya biya mata su. Sai ta tuna da shekaru biyun da
suka ja layi a tsakanin su, abubuwa da yawa zasu iya fara a cikin awanni biyu, balle a tsallaka
awannin da suke cikin ranakun da suka shude tare da shekara biyu.

"Ma shaa Allah. Allah ya tabbatar da alkhairi"

Tace maimakon furta ko da daya daga cikin tambayoyin da take da su ne. Hidimar da ta fito da
ita ta cigaba dayi, ba dai tasan dalilin Daada na binta da wani irin kallo mai cike da ma'anoni ba.
Ba zatace tausayawa kawai ta gani a cikin kallon ba, kamar Daada na son sanar da ita auren
Nawfal din yana da alaka da rayuwarta ne, ta kasa fahimtar kalaman da Daada ta zabi tabar su
cikin idanuwanta maimakon ta furta mata su. A ranar da ta shiga dakin ta, bayan ta zauna ta
dauki agogon Nawfal kamar yanda sabonta yake sai ta tsinci kanta da saukowa daga kan gado
tana neman waje ta jefa agogon a ciki.

Har yau da take zaune a cikin motar Salim da yazo daukarta zuwa restaurant din da suka yanke
hukunci zuwa yasu-yasu dan gudanar da yar walima ta taya Nawfal din murnar auren shi da
aka daura a safiyar Asabar din ba zatace ga dalilinta na adana agogon ba. Hannun Salim da taji
a gefen kuncinta na sata saurin janye jikinta kamar wadda wuta ta taba, sake mika hannun shi
yayi kamar bai ga yanda ta hade da murfin motar ba, ji yayi babu zazzabi a jikinta. Sannan ya
janye hannun shi yana gyara zaman shi yana fadin

"Shirun ki yayi mun yawa"

Numfashi ta sake saukewa a karo na biyu

"Banda labari ne fa... Yau zan missing karatu a islamiyya, bana fashi in ba rashin lafiya ba sai
bikin Adee, zasu ga banje ba yau ma kuma ban fada ba"

Kai ya jinjina

"Zasu dake ki ne?"

Saboda tunanin wani zai taba lafiyarta na sa jikin shi daukar dumi da wani yanayi na bacin rai

"A'a, ba su cika dukan fashi ba inba kana yawan yi ba"

Duk da haka hankalin shi yaki kwanciya

"Kin tabbata?"

Yayi tambayar cikin harshen turanci

"Na tabbata"

Ta bashi amsa cikin harshen itama, yana shan wata kwana ya dan rage gudu alamar yana son
samun damar da zai tsallaka titi ne, tana kuma iya ganin sunan restaurant din Tasty Corner. Sai
da ya tsallaka ya samu waje yayi ajiye motar yana kashewa tukunna take kara ganin kyawun
restaurant din tun kafin ma su shiga. Da yake banda makaranta babu inda take zuwa, sai nan
cikin unguwar su, sai kuma gidan Julde da shima tana dadewa bataje ba, a garin Kano tsaf
zaka siyar da ita. Babu inda ta sani, yanzun ne ma da Salim ke yawon dauko ta daga
makaranta yakan biya wani wajen yayi mata siyayya, har wani wajen saida litattafai sukaje da
bata san a ina bane ba, amman yayi mata kyau matuka.

Da kan shi ya zagaya ya bude mata murfin motar ta fito. Sai lokacin ya kalli kayan jikinta, jeans
ne baki, kamar yanda ta saba ta nannade shi har kwaurinta ya dan fito, sai fararen kambas,
rigace ta sanyi mai dogon hannun da taja baya, itama farace kamar hijabin kanta. Ta dora wata
farar hular sanyi a saman kanta. Murmushi yayi yana tsayawa a gabanta yana kara mamakin
gajartar Madina, da kadan kanta ya wuce cikin shi, kama hular yayi yana cire ta daga kanta ya
duba kamar mai son gano wani abu a jiki.

Murmushin dai ya kasa barin fuskar shi har lokacin, gyara hular yayi a cikin hannun shi yana
dorawa saman kanta kafin ya gyara mata ita saman kanta, ganin yanda take kallon shi yasa shi
amfani da dan yatsa ya tura mata gilashin da yasan gab take da dago nata hannun ta gyara
mishi zama.
"You look like a Mug"

Salim yace muryar shi dauke da wani irin yanayi da yake jin fitowar shi daga zuciyar shi, kai
Madina take girgiza mishi tana kokarin danne dariyar da take son yi saboda hada tsayinta da
kofi da yayi

"Ba zaka fara kirana da Mug ba Hamma"

Girar shi daya ya daga mata

"Gargadi ne?"

Kai ta girgiza da sauri tana saka shi lumshe idanuwan shi yana bude su a kanta

"Mug it's then... Muje"

Juyawa tayi kuwa, wani murmushin na kara kwace ma Salim, da gaske tayi kama da yan

kofinan nan masu kyau da ake zuba coffee a ciki, masu murfin da marassa murfi, amman masu
kyan cikin haka yake ganin tsayinta a gaban shi

"Mug"

Ya furta dai-dai kunnuwan shi da murmushi a labban shi, har takai kofar wajen ta juyo tana
kallon shi da tunanin abinda ya tsayar da shi, taku biyar yayi ya karasa inda take suna shiga
tare, can wani teburi da yake karshen wajen ya hango su Khalid, sai kuma hannuwan Adee
duka biyun da take daga musu kamar yace bai gansu ba. Baima san me yasa mijinta yabar ta
fitowa ba duka sati daya da aure, dariya take tana sake daga musu hannuwa, dakuwa Salim
yayi mata daga inda yake yana kallo ta sake kwashewa da dariya kamar wadda ya bawa
kyauta.

Suna karasawa tana tashi daga wajen da take zaune ta kama hannun Salim din da yake
kokarin kwacewa yana daure fuska

"Wallahi nayi kewar ku sosai"

Ji tayi kamar tayi waya bakwai bata gansu ba

"Sakeni dalla"

Tabe baki Adee tayi, matsalar Salim ba'a mishi gwaninta, tana zame hannuwanta daga nashi ya
daga ya dillar mata bakin da ta tabe mishi

"Dan kinyi aure zaki mun rashin kunya"

Dafe labbanta tayi babu shiri

"Ouchh... Hamma"

Kallon da yayi mata yasa ta koma ta zauna, kujera yaja shima ya zauna yana dan kara janta
gaba, kafin ya kalli agogon hannun shi

"Minti talatin..."

Ya fadi yana kallon su, yana da hidimar da zaiyi, ko bashi da ita baida hirar da zaiyi da su,
hayaniyar zata dame shi. Gara yaci abinci ya barsu suyi hirar su cikin nutsuwa. Kallon juna
Khalid da Nawfal sukayi, dan sunyi gulmar shi, babu ma wanda ya kawo zaiyi minti talatin din
duk a cikin su
"Ni nace maka Hamma ba zai minti biyar a wajen nan ba"

Cewar Khalid

"In za'a iya mishi takeaway din duk abinda yake so a kasa da minti biyar ba zai kai ba"

Nawfal ya kara, basu taba tunanin zai zauna a waje irin haka yaci abinci ba

"Nasan kunyi gulmata"

Ya fadi kasan makoshi yana duba menu din da waiter din wajen ya kawo mishi bayan ya dan
daga hannu cikin alamar kira, dankali da kaza ya zaba sai bakin lemo yana kallon Madina da
tunda ta zauna idanuwanta na kan Nawfal, bata ganshi ba tun da akayi mata zancen bikin, bai
kwana a gidan Daada ba, sanda yazo tana makaranta sai dai inta dawo Daada tace mata
Nawfal ya zo. Yanzun da ta ganshi kawai sai take jin kamar abin wasanta da ta dade tare da
shine aka fisge daga hannun ta.

Kai tsaye ba zatace ranta ya baci ba, amman kuma bata farin cikin da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login