Showing 3001 words to 6000 words out of 79955 words
Chapter 2 - Rai da kaddara Book Complete by Lubna Sufyan .pdf
hanani rikon yaron nan zanji kamar
saboda kina dubana da abinda nake sa Allah ya shafe mun shi a littafina... Halayena ba zasu
taba kulawar shi ba Daada, na rantse miki tarbiyar shi ba zata samu tangarda ba, kina kallon
kaunar da take tsakanin mu, ko ita ki duba"
Wannan kaunar kuwa ta ganta tun a ranar farko da Nawfal ya fara dora idanuwan shi akan
Julde yana da shekaru uku a duniya, sati biyu bayan tafiyar Bukar, sati biyun da daga ita har
Nawfal din sukayi su a matukar jigace saboda kukan Daddyn shi da yake yi mata. Amman yana
ganin Julde ya ruga ya makale shi yana kiran
"Daddy..."
Ta ga Julde da yaran shi, ta ga kalar kaunar da yake yi musu, amman yaro daya taga ya kalla
da kallon da yake yiwa Nawfal, yaron da yayi sanadin komai. Har yanzun idan Nawfal da Julde
na waje daya zaka ga yana kallon Nawfal din kamar shine tilon abu a duniya da yake cike mishi
gurbin duk wani abu daya taba rasawa, kamar Nawfal ne hasken da ya yaye duk wani duhu
daya taba samun rayuwar shi. Kome zata gani, ko me zatayi tunani bata da zuciyar da zata
yiwa Julde maganar Nawfal ya dawo wajen ta, ko da ya yarda bata da tabbas akan Nawfal din
zai amince, yanda Julde yake kallon shi, haka take ganin Nawfal din na kallon shi shima, kamar
duka duniyar shi ta tsaya ne duk inda Julden yake.
Dawowar da su Nawfal sukayi falon da surutun Madina na katse mata tunanin da takeyi, bata
san ya akayi daga rike hannun Nawfal Madina ta koma kan wuyan shi ba. Dariya takeyi cike da
wani irin farin ciki da zuwan Nawfal kadai yakan bayyana shi a fuskarta.
"Da shiriritar nan da kukeyi da zuwa kayi kayo mun cefane ka siyo mun kifi"
Kafin ya amsa Madina ta riga shi da
"Zan bika Hamma, dan Allah zan bika"
Saukota yayi a hankali
"Je ki dauko hijabin ki da takalmi..."
Da gudunta ta tafi, Daada ya kalla
"Ina kudin?"
Itama mikewa tayi tana bin bayan Madina zuwa dakin baccin su. Ita ta dauko mata takalmi da
yake mai madauri ne sai da ta saka mata, ta bata hijabin a hannun ta, bata jirata ba ta fita da
gudu, haka Julde yake kwaso mata su, duk yawancin takalmanta irin sune. Kudi ta dauko ta fito
ta same su a tsaye suna jiranta, bashi tayi ta kuma fada mishi na yanda take so. Yana rike da
hannun Madina suka fita, Daada na tsaye tana kallon su. Zuciyarta da adanannen tunanin da
takeyi akan su, jikokinta biyu da suka fi har 'yayanta matsayi a zuciyar ta.
Amanar ta
Kaddarar ta
Sai dai taya zata san abinda kaddara ta tanadar musu yasha bamban da tunanin ta?
A lokacin da ta hade Madina da Nawfal a waje daya
A lokacin da ta hango su karkashin inuwa daya suna tayata rike amanar junan su
Kaddara ta rubuta musu yin hannun riga da juna
Inuwar guda daya ce kamar yanda Daada ta hango
Amman hannun rigar da zasuyi da juna dole mutum daya inuwar zata bi
Dole dayan su zaiyi gararamba a ranar da babu tabbacin samun inuwar fakewa.
©
✏
FIKRA WRITER'S ASSOCIATION
Facebook: Lubna Sufyan
IG: SufyanLubna
Email: Calmlubna@gmail.com
*RAI DA KADDARA 1*
02
Kamshin turaren shi ya fara cika mata hanci ta zo juya kwanciya, dan tana daya daga cikin
mutanen da in har zasuyi juyi komin baccin da suke sai sun farka. Wani lokacin ma sai ta tashi
zaune, kamar yanzun dinma haka ta faru da Saratu. Idanuwanta ta sauke akan Julde cikin
shaddar shi ruwan toka da tayi matukar amsar farar fatar shi, agogon da yake manne jikin
bango ta kalla tana ganin karfe sha daya harda wani abu na dare
"Ina zaka cikin daren nan?"
Ta bukata tana jin wani abu da ya tokare mata makoshi. Sai da tayi tunanin ba zai amsa ba, dan
har hula sai da ya saka sama kan shi batare da ya juyo ba yace
"Yaushe inda zanje ko karfe nawa ya fara damun ki?"
Gyara zamanta tayi, dan batayi magana akai ba baya nufin abin baya damunta. Halayen shi kaf
ta san su, zata rubuta littafi akan halayen nashi da ko shi ya karanta sai ya sha mamaki. Yau
dinma bata san me yasa take son mishi magana kan fitar da zaiyi ba, tafi alakanta hakan da
gajiyar da take jin tayi da halayen shi a satukan
"Karfe sha daya na dare, idan ba maza masu aikin kwana ba, kowanne namiji mai mutunci yana
tare da matar shi..."
Numfashi ya sauke yana dan tabe bakin shi, surutun ta ko a jikin shi, ita dinma bawai ta dame
shi bane ba balle kuma abinda ya fito daga bakinta
"Me kake tunanin Daada zatayi idan taji babu wani abu daya canza daga halayen ka? Sai ma
abinda yayi gaba?"
Wannan karin juyawa yayi ya kalleta da murmushi dauke akan labban shi
"Babu abinda zatayi tunani saboda ba zaki fada mata ba, saboda zaman ki a cikin gidana yafi
miki komai muhimmanci, kuma fadama Daada abune da zaiyi barazana da zaman"
Abinda yake tsaye a makoshinta take kokarin hadiyewa amman yaki wucewa, tana kallon shi ya
dauki mukullin motar ya fice daga dakin hadi da ja mata kofar. Runtsa idanuwan ta takeyi tana
bude su da sauri-sauri cikin son mayar da hawayen da suka cika su taf. Ta gama kuka akan
Julde, ta gama zubar da hawayenta akan kishin shi, ba zai zamo karshenta ba. Bata san ko tun
farko bata nuna mishi wadatacciyar soyayya bane shisa yanzun yake ganin duk wani abu da
zatayi domin kudin shine, dan arzikin da yake da shi.
Ko kanta ba zata yaudara ba, tana son rayuwar hutu, tana jin dadin kudin da yake da shi,
sauyin da rayuwarta ta samu a tare da shine babban cigaban da zata mutu tana alfahari da shi.
Shisa bata son taga kwandala ta fita daga aljihun shi da sunan yiwa wani alkhairi bayan ita da
yaran su. Har wani duhu take ji ya lullube mata idanuwa saboda bakin ciki. Amman hakan baya
nufin bata son shi, tana son shi, tana jin soyayyar shi a ranaku mabanbanta, yau na daya daga
cikin wadannan ranakun. Ko da ba zasu kasance da juna cikin raya daren ba taso duk juyin da
zatayi taji shi a kusa da ita.
Kamshin shine gauraye da dakin, kamshin da zai cika dakin wata ko dakin otel a tare da wata
da ba ita ba. Dumin shi da take son ji fiye da komai a daren shine wata zata kwana tana mora.
Ta ya zata ce abin baya mata ciwo? Ance lokaci na sa ka saba da abubuwa da yawa, amman
kullum Julde saiya karyata mata hakan, saiya nuna mata ba zata taba sabawa da halin bin
matan shi ba. Duk yanda take kishin shi, duk yanda bata son wani ya rabar mata shi bai hanata
tsugunnawa kan gwiwoyin ta ta roke shi daya kara aure ba
"Idan uku zaka kara dan Allah ka karo, da wannan biye-biyen da kakeyi ka karo uku ka ajiye mu
zama mu hudu, zamu isheka, mun isheka Julde, dan Allah..."
Murmushin da baka raba fuskar shi da shi yayi mata, ko ranshi a bace yake kuwa zaiyi
murmushi
"Ajiye mata hudu ba zai hanani hangen wasu ba Saratu, ke dinma ya na kare dake? Aure,
yarana kawai da nake kallo suke hanani dana sanin zaman aure dake, ko dan irin wannan
surutan da kike yawan yi mun. Zan sake maimaita miki in ba zaki iya zama dani ba furtawa
kawai zakiyi...kiyi harkarki inyi tawa, zaki iya nemar mun shiriya idan kina da wannan lokacin, in
baki dashi kibar ni da halina..."
Ba dan tana da wani ilimin addini ba, sallah da tsarki ma yanda zatayi su a tsarin addini a gidan
Radio ta koya. Anan taji kalar kuskuren da take tafkawa a rayuwarta, amman zata iya cewa
jahilci na daya daga cikin babbar cutar da take damun Julde. Watakila da yayi makaranta, ta
boko ko ta addini zai rage wasu abubuwan. Yanzun ma lokaci bai kure mishi ba idan har yayi
niyya, tunda ita ma takan saurari kasa-kasai da ta siyo na wa'azi kala-kala kuma tana karuwa.
Shisa halayen shi suka hadu suna mata ciwo biyu yanzun, kishin shi da kuma matsayin abinda
yakeyi ga makomar goben yaran su.
Komawa tayi ta kwanta, bata koyi kokarin share kwallar da take zubo mata ba. Sosai kirjinta
yake zafi, musamman da zuciyarta ta shiga hasaso mata hotunan inda Julde yake da abinda
yakeyi. Idanuwanta taji sun bushe rayau, ko alamun bacci babu. Tana jin hawayenta tun suna
zuba har suka daina, banda ajiyar zuciya babu abinda takeyi, ko juya kwanciya batayi ba, ta dai
ja jikinta sosai ta dunkule waje daya ko zata samu saukin zafin da kirjinta yakeyi. Ba duba
agogo takeyi ba balle ta san ko karfe nawa, kawai dai taga daren yayi mata wani irin tsayi ne.
Kiran sallar asuba kawai take saurare taji an turo kofar.
Tana jin kai kawon shi, tasan kayan jikin shi yake ragewa. Bata dai motsa ba, kwan dakin daya
kunna kafin ya fita yaje ya kashe ya dawo yana hawa gadon. Jin da tayi ya rikota yana juyawa
da ita ta fuskance shi ya sa ta fara kiciniyar kwacewa, sai dai karfin su sam ba iri daya bace ba,
ko sirantaka irin ta yawancin fulani Julde ba shida ita, ba zaka kira shi namiji mai jiki ba, amman
dogone na misali, ko ina a jikin shi bai nuna rama ba.
"Kina son gwada karfi dani Saratu, in kin ganni a irin yanayin nan ki daina mun gardama kar inji
miki ciwo wata rana"
Wasu hawayen ne masu zafi taji sun cika mata ido, da daudar zinar daya kwaso yake neman
hada jiki da ita, ko wankan tsarki baiyi ba, lokacin da taji yanda zata tsarkake jikinta tayi kokarin
ganin shima ya sani, kwanaki ta jera kullum sai ta karanta mishi yanda zai tsarkake najasar da
yake yawo da ita, bai nuna mata alamar ya dauka ba, amman yaji ta, kuma tana fatan ya dauka
din.
"Dan Allah ka kyaleni..."
Ta furta a raunane, ta san halin shi, abinda yayi niyya ba zai fasa ba, kuka takeyi sosai, kukan
ta bai karu ba sai da bayan ya gama abinda yayi niyya ya juya mata baya cikin wani irin yanayi
da ya fito da tsantsar kunar rai ya furta
"Babu kamar Mero, har yanzun banji irin Mero ba"
Kamar ita tayi sanadi ko ta zama dalilin da ya rasa Mero kuma ya kasa samun madadinta ba
har yanzun. Kukanta kara mishi kunar rai yakeyi. Mata uku ita cikon ta hudu a dare daya
amman ko kusa da natsuwar da yake samu da Mero basu kusanta ba balle su cike mishi ramin
da ta bari. Akan yaran shi yasan menene soyayya, akan Nawfal yasan asalin kauna da dukkan
zuciyar shi. Mace, ita din a wajen shi kamar riga ce da zai saka wadda yake so don biyan
bukatar shi ya cire ya sauya a lokacin da yayi niyya. Me yasa Mero ta kasa barin ran shi?
Zuciyar shi babu wajen kaunar wata mace banda Daada, amman yana jin wani rami a cikin
kirjin shi inda baisan Mero ta zauna ba sai da tabar shi.
"Baka taba sona ba Julde, da akwai soyayyata a ranka ko yaya ne ba zaka zubar mun da
mutunci har haka ba, ba zaka mayar dani abin nunawa a dangi ba..."
Maganar Mero ta dawo mishi tana saka shi runtsa idanuwan shi yana hango fuskarta,
idanuwanta, jan bakin da baka raba labbanta da shi. Ita da kanta ta fada mishi baya son ta, me
yasa zata manne mishi har haka? Mata nawa ya sani kafin ita? Mata nawa ya sani bayan ita,
me yasa ta fita daban? Me take da shi da ya kasa samu tare da sauran? Kullum, tun bayan ita
kullum saiya nemi gamsuwar da yake samu da ita a tare da mata daban-daban amman ya kasa
samu. Baya bibiyar mata da yawa haka kafin Mero, ta sake bude mishi sabon shafin da babu
kalaman da zasu iya fasaltawa.
Bai bude idanuwan shi ba har bacci ya dauke shi cike da mafarkin Mero, ya kuma bude su da
wayewar gari cike da tunaninta. Da yake Juma'a ce shi yake kai yaran makaranta in ba wani
babban uzuri ba, a gaggauce yayi wanka ya shirya sannan yayi sallar asubar da ba kullum ya
damu daya sameta a cikin jam'i ba. Duk tare suka karya yana hira da yaran kamar bashi da
wata matsala in har yana ganin su a kusa da shi. Salim ne dan shi na farko, Fadila da itace ta
biyu kuma tana makarantar kwana ta Science and Technical da take nan garin Kano, Khalid sai
Lukman.
Suna gamawa ya saka su a gaba suna fita tare, daya sauke sune ma Khalid yace mishi
"Daddy idan na dawo zanje gidan Daada acan zamuyi Weekend tare da Bajjo..."
Khalid din ya karasa yana kallon Julde da yake girgiza kai
"Har kwana biyu zaku je kuyi, ka dai je idan na dawo daga kasuwa da dare in biyo in dauke ku...
Shima Nawfal din zan hadu da shi daya tafi bai fada mun ba"
Gardama ba halin Khalid bace ba, duk a cikin yaran shi kadaine ba zai ja magana sau biyu da
babba ba. Hakan yasa shi jinjina kai kawai yayi ma Julden sallama yana bin bayan yan uwan
shi ya shige cikin makaranta. Julde kuma yaja motar shi yana nufar kasuwa, zuciyar shi tayi
mishi nauyi fiye da kowanne lokaci.
*
Yanda yake cin abincin Daada take kallo, ya tattara hankalin shi kamar bai taba yin wani abu
mai muhimmanci kamar wannan ba. Tausayin shine cike da zuciyar ta, daren jiya da ta zubo
mishi taliya da miyar kifin da tayi ta zallar tumatiri da albasa taga ya kalleta
"Tumatir ne kawai da albasa Bajjo"
Ta fadi tana kiran shi da sunan da ta makala mishi kasancewar shi da daya tilo a wajen mahaifin
shi. Tana dadewa bata kira shi da Nawfal ba. Tana gani ya saka cokali ya fara dibar miyar da
kifin yana kaiwa bakin shi, saida ya sauke numfashi tukunna ya fara cin abincin. Yau ma haka,
kwano ta samu daban tana zuba mishi miyar da tayi saboda shi kawai.
"Daada abincin nan yayi mun dadi"
Cewar Nawfal yana jin kamar ya samu waje ya adana dandanon abincin ya dinga daukowa
yana tunawa a ranakun da zaici mai da yaji ko ya sha shayi saboda Nanna ba zatayi abincin da
zai iya ci ba. Ya dade idan ya kalleta yana so ya tambayeta laifin shi, yana so yaji me ya taba yi
mata mai zafi da ta dauki karan tsana ta dora mishi ba.
"Yarana da gidan uban sune ma abinda na dafa shi suke ci, ba zaka sakani girki biyu saboda
baka cin yaji ba wallahi, ba zan iya wannan jidalin ba"
Ta kan yawaita fada mishi, ko a makaranta Nawfal Bukar yake amfani da shi ba Isiyaku ba. Ya
san bashi bane baban shi ko bata tuna mishi ba, amman shi din yake ma kaunar da ya kamata
yayi wa baban shi da bai san komai game dashi ba bayan suna. Sai dai abu na farko daya fara
koya bayan magana shine yin shiru, akan abubuwa da yawa, musamman abubuwan da suka fi
karfin fahimtar shi, da kuma wanda suke damun shi. Shiru yafi komai saukin yi, furta wasu
abubuwan baya kawo gyaran su, ya taba furtawa Julde cewa Nanna tace gidan ba gidan uban
shi bane ba.
Fadan da sukayi a gaban idanuwan shi harya mutu ba zai manta ba, yana da tabon dukan da
Saratu tayi mishi a bayan shi har gobe. Shiru yafi komai sauki a wajen shi, yanzun ya kara
fahimtar duk abinda ake so yaji za'a iya fada mishi ba saiya tambaya ba, abinda yake son ji
kuwa koya tambaya idan ba'a son fada mishi ba zaiji ba.
"Kar dai ka fado daga kujerar nan wajen santi"
Daada ta fadi tana mishi dariya
"Ba dai zai hanani yabon girkin nan ba dan yayi mun dadi... Idan zan tafi kika dibar mun miyar
nan zata dade bata lalace ba?"
Kallon shi Daada tayi
"Zata iya kwana biyu dai tunda ba sake dafawa zakayi ba, ko akwai fridge a dakin ku?"
Kai ya daga mata saboda ya cika bakin shi da shinkafa
"To bari sai ka karo kayan miya da kifin in maka da yawa, idan kaje saika saka cikin fridge ka
dinga diba"
Murmushi yayi, matsayin Daada daban yake a wajen shi, ko ganinta yayi sai yaji wani sauki a
cikin ran shi. Da duk wani abu da zatayi kuma da yanda take faranta mishi. Mikewa tayi tana
shiga daki ta fito da hijabi a hannunta
"Gara inje barkar nan sai ma in biya in taho da Madina..."
Cewar Daada tana saka hijabin ta
"Kibari zanje in dauko ta"
Kai ta girgiza mishi
"Ba nisa da inda zanje... Sai na dawo"
Kai Nawfal ya daga
"Allah ya tsare. A dawo lafiya"
Daada ta amsa tana ficewa daga dakin. Abincin shi ya gama ci ya dauke kwanonin ya kai
kitchen, ya dawo ya zauna yaji sallamar Khalid daya amsa, uniform din da yake jikin Khalid din
na tabbatar mishi daga makaranta kai tsaye nan din ya nufo
"Da baka jirani mun taho tare ba gashi na zo ai"
Dariya Nawfal yayi
"Ka kyauta. Daman bance