Showing 51001 words to 54000 words out of 79955 words
Chapter 18 - Rai da kaddara Book Complete by Lubna Sufyan .pdf
fal cikinta ta dauka da ledar
litattafan ta kai daki ta ajiye su kan gadon ta sannan ta dawo tana nufar kitchen, abinci ta zubo
ta dawo ta zauna suka fara hira da Daada, duka yau hirar akan wayar tane da abinda zatayi da
wayar.
*
Ta dauka bambancin ranar zai kare ne da kyautar da ta samu daga wajen Salim, da kuma
wayar da sukayi, duk da sukanyi a land-line din Daada, amman sai take jin wannan din ta sha
bamban, sanda duk ta so magana da shi zata iya, flashing kawai zatayi mishi ta san zai kirata.
Har ta fara bacci, wajen karfe goma da rabi ta farka, sai ta sauko daga kan gado ta nufi dakin
Daada, ba bakonta bane ba, ba kuma ranar bace ta farko da ta saba barin dakinta taje bayan
Daada ta kwanta, wasu lokuttan ma cikin bacci takeyin hakan, sai da asuba take sanin ta koma
dakin.
Karfe daya da kusan rabi taji Daada tana zare jikinta daga rikon da tayi mata, saukarta daga
kan gadon yayi dai-dai da bude idon da Madina tayi tana juyawa, wani yunkurin amai da Daada
tayi yasa Madina dirowa daga gadon tana jin ta wartsake gabaki daya, bandakin ta shiga, da
yake da wuta kwan a kunne yake, amai Daada takeyi kamar zata zazzage hanjin cikinta, banda
sannu babu abinda Madina takeyi mata. Ita ta taimaka mata ta wanke fuskarta ta kuskure
bakinta suka fito, zazzabi ne a jikin Daada kamar wuta, cikin kasa da minti talatin harta fara fita
daga hayyacinta saboda zafin zazzabi.
Madina bata san hawayen ta zai iya yin nisa ba sai yau, banda bari babu abinda jikinta yakeyi,
musamman da ta jijjiga Daada tana kiran sunanta taga ko jinta batayi, dakyar ta samu ta
sauketa daga jikinta, dakinta ta nufa tana dauko wayarta ta kunna, sai take ganin ta dade bata
gama lodin ba, tana karasawa lambar Salim ta lalubo tana kiran shi, tana jin bugun wayar na
daidaituwa da na zuciyarta, sai dai harta yanke bai dauka ba, sai da tayi mishi kira hudu, ana
biyar ya daga yana fadin
"Mug...lafiya?"
Numfashinta na wani irin sama, muryarta na sarkewa saboda nauyin da harshenta yayi tace
"Da... Daada bata da lafiya... Hamma, Daada..."
Ta karasa a wahalce
"Ki nutsu, ki tuna abinda na fada miki na taimakon gaggawa, kina jina? You can do this, kije
wajen ta, yanzun zan taho"
Kai Madina take dagawa tana fita daga dakin, wayar ta ajiye a gefe tana karasawa wajen
Daada da sauri ganin tana yunkurin amai, juyata tayi kan hannunta kamar yanda ya sha fada
mata, saboda a rigingine Daada take, zata iya shakewa idan tayi amai a haka, sai zazzabin
jikinta yayi yawa, bandaki ta nufa tana zubo ruwa a bokiti ta dauko towel ta zo tana tsomawa,
idan ta matse sai ta goge ma Daada duk inda ta samu a jikinta. Bata san iya tsayin lokacin da
suka dauka, ko inda ta samo nutsuwar da ta samu ba.
Da Salim ya kira wayarta ma, da kanta ta dauki mukulli taje ta bude mishi gidan suka koma ciki
tare, batayi mamakin yanda ya kama Daada yana dagata ya saba a kafadar shi ba, ko nishi
bata ji yayi ba, hijabin Daada ta daukar mata, tana komawa dakinta ta saka karamin hijabi
itama. A kofar gida ta samu Salim, shiya karbi mukullin yana rufe gidan, baya ta shiga kusa da
Daada tana kama hannunta ta rike, Salim ya zagaya mazaunin direba yaja motar. Asibitin
Aminu Kano inda can yake aiki suka nufa, babu wani bata lokaci aka samarwa Daada daki ita
kadai aka kuma fara bata taimakon da take bukata, saboda Salim din, shi baibi sauran likitocin
ba sai da ya tsaya aka binciko file din Daada tunda nan asibitin take zuwa duk idan bata da
lafiya.
Da kanshi ya bude yana bincika record dinta kafin ya bisu dakin, har an saka mata ruwa an
mata allurar jini, wata Nurse tace mishi an dauki jininta don a gudanar da gwaji, tambayoyi ya
shiga yi ma likitan daya duba Daada din suna magana cikin harshen da in ba fannin aikin su ka
karanta ba sai sun fassara maka zaka gane me suke cewa. Tare suka fito da likitan, shi yana
wucewa, Salim kuma yana kallon inda Madina take tsaye ta jingina bayanta da bangon wajen,
ko takalma bata da shi, safa ce a kafarta, dan dai tana da kauri, sai kayan baccin da ko shi ya
saka tsayin wandon ne kawai zai mishi kadan. Dan murmushi yayi yana karasawa ya taba
kafadarta.
Da sauri ta kalle shi
"Hamma? Me yake damun ta?"
Kai Salim ya girgiza mata
"Komai zaiyi dai-dai"
Ganin yanda take kallon shi ya sa shi dorawa da
"In shaa Allah"
Kai ta jinjina badan ta yarda ba
"Ki shiga ki zauna da ita, zan kira Nanna in fada mata"
Kan dai ta sake jinjina mishi, murmushin karin kwarin gwiwa yayi mata, baya son yanda tayi
sanyi, sai da ta tura kofar dakin da Daadan take ta shiga tukunna ya sauke numfashi. Ya kanji
Julde yace Daada bata da lafiya, ko kuma ya biya ya kai mata magungunan ta, wasu lokuttan
ma tare suke zuwa su duba ta, amman yaune ranar farko da yasan tana dauke da ciwon zuciya,
saboda bai taba tambayar Julde me yake damun Daada ba, yanzun ma a file din ta ya gani,
jininta ma yakan hau ya sauka, amman baya irin hawan da za'ace yana barazana da rayuwar
ta, ciwon zuciyar ne dai.
Da alama Madina ma bata sani ba, kuma ba zai zama na farko da zai fada mata ba. Lambar
Julde ya fara kira sai yaji ta a kashe, hannu ya kai yana murza goshin shi, yana da round din da
zaiyi, ba yanda za'ayi ya zauna da Madina, kuma ba zai yiwu abarta ita kadai ba. Baya son
wayar ta tashi Saratu, Khalid ya kira, bugu biyu ya daga
"Hamma, lafiya dai ko?"
Yanayin muryar Khalid din ya sa Salim fadin
"Uban me kakeyi ba kai bacci ba har uku na dare?"
Yanajin yanda Khalid ya sauke mishi numfashi a kunnen shi, abinda ya tsana, shisa in zai waya
yawanci yake sakata a speaker ya ajiye a kasa, ya rasa dalilin da zaisa anna waya ana
numfarfashi da wasu kananun nishi da yake bakanta mishi rai
"Kira na kayi kaji ido na biyu ko akwai abinda zaka fada mun?"
Cewar Khalid din
"Daada bata da lafiya, gata a asibitin mu, ka fadawa Nanna, bana so in tasheta da waya"
Yana jin motsi alamar Khalid din ya tashi
"Subhanallah, tun yaushe?"
Kashe wayar Salim yayi, saboda zai iya watsama Khalid din zagi, yana da tambaye-tambaye
marassa amfani, a aljihu ma ya saka wayar, yana barin bangaren gabaki daya zuwa inda ofishin
shi yake.
*
"Daga jikin wa ka baro ka taho?"
Cewar Saratu bayan Julde ya shigo dakin tana binshi da wani mugun kallo, bacci takeyi taji ana
kwankwasa dakinta, dakyar ta rabu da gado tana zuwa ta bude
"Nanna..."
Khalid ya kira yana dorawa da
"Daada ce bata da lafiya, tana asibiti, yanzun Hamma ya kira yake fadamun"
Dan dakuna fuska tayi, kafin ta jinjina ma Khalid kai tana juyawa batare da tace komai ba
"Bari in sakko dogon wando in dauko id card dina sai in zo mu tafi"
Har ranta batayi niyyar zuwa ba, rashin lafiyar Daada ba matsalarta bace ba saboda dalilai
masu yawa, amman akwai halayenta da bata cika son yaran nata suna gani ba, musamman
Khalid, shisa ma ta daga mishi kai kawai, kayanta ta sake itama, suna hanya tana hamma
saboda baccin da ko awa batayi da samun shi ba. Fadan da sukayi da Julde kafin ya fita ya sa
taita juyi a gado ranta na mata zafi
"Bunsuru kika taba kirana Saratu, ko kin manta? Ban canza ba har yanzun, bunsurun ne, ki
daina yin kamar baki san abinda zan fita yi ba"
Duk tashin hankalin da tayi bayan nan ko inda take bai kalla ba, tasani, ta fi kowa sanin me
yake fita yi duk daren da zai shirya tsaf ya fice, tana kauda kaine yanda ta saba, tana kuma
amaye abinda take ji idan yazo mata wuya. Kamar yanda tayi jiya, sai dai ko yaushe ita ce take
faduwa kasa warwas, dan fada da Julde babu riba a cikin shi, ko tace bata samun riba a fada
da shi. Sai ya tabbatar ya nuna mata bata da muhimmanci a rayuwar shi, zaman da takeyi da
shi zabinta ne, in ta barshi babu abinda zai canza. Hakan yafi mata ciwo fiye da neman matan
shi, ba zatayi karya ba, zata so ko kadan ne ta samu wani muhimmanci a rayuwar shi.
Don shi yana da shi a tata rayuwar, akan ce wasu mazan na duba darajar 'ya'ya, to a idanuwan
Julde bata taba cin darajar yaran su ba, zaka rantse da Allah shi yayi dakon cikin su, nakuda da
rainon su
"Saratu"
Julde ya kira cike da kashedi yana kallon Daada da take kwance, da alama bacci takeyi, sanin
cewa bai daina halin shi ba shine karshen abinda zai so taji
"Meye? Baka so ta sani? Baka so taji babu abinda ya canza daga mugun halin ka?"
Runtsa idanuwan shi Julde yayi yana sake bude su akan Daada, ko motsi baiga tayi ba.
Likitanta daya gani kafin ya shigo ya fada mishi ciwon zuciyarta ne, amman babu wata matsala
in dai ta samu hutu kwana biyu, a kuma tabbatar babu wani abu daya faru da zai daga mata
hankali, in dai an kiyaye wannan zata samu sauki. Wannan maganar da Saratu take son ya biye
mata suyi na cikin abinda zai daga hankalin Daada. Shisa yaja kujera ya zauna yana yin shiru
ya kyale ta. Yana jin yanda take watsa mishi wani irin kallo, kafin ta ja tsaki tana mikewa ta fice
daga dakin.
Daman ko bai zo ba, ita gida zata tafi, bata da dalilin zama asibiti, ta dai cewa Madina zata
zauna ne dan taje gida ta watsa ruwa ta sake kaya ta kuma dauko musu abinda suke bukata.
Salim ne ya tafi ya kaita tunda gari ya waye. Da kanta ta kira Adee ta fada mata, saboda tasan
zata kawo abincin kari
"Saboda Yelwa kawai"
Ta fadi cikin ranta bayan ta rufo musu kofar. Ko Daada ba darajar Julde take ci ba a wajenta,
saboda Yelwa ne, in har mutunci zai shiga tsakanin su bayan tarin kiyayyar da ta nuna mata to
saboda Yelwa ne. Julde kuwa numfashi ya sake saukewa yana kallon Daada, wayar shi a kashe
take, cikin mota ma yabar ta, sanda ya fito bayan asuba ya zo ya kunna ya ga sakon Khalid, kai
tsaye asibitin yayo, sai dai da nisa daga inda yake, tunda yafi zuwa hotels din wajen gari, inda
kafin ya hadu da wanda ya sani za'a dauki lokaci, ko gidan gonar da yayi shi don wannan dalilin
kawai ba don komai ba.
Kafin yayi wani tunani an turo dakin da sallama
"Daddy..."
Salim ya fadi cikin gaisuwa, Adee da ta shigo bayan shi da murmushi a fuskarta ta gaishe da
shi itama, kallon ta Salim yayi, suna hanyar gidan Daada wayar Salim ta shiga vibrating,
dagawa yayi ganin Nawfal ne ya sa shi kai wayar kunnen shi
"Na kira Hamma Khalid bai daga ba, me ya sami Daada? Yace mun bata da lafiya tana asibiti,
me suka ce yana damun ta? Ya jikin ta?"
Yanda yayi duka tambayoyin a numfashi daya yasa Salim fadin
"Da sauki"
Cikin taushin murya yana dorawa da
"Zazzabi ne kawai, da sauki kuma sun riketa ne dan ta huta sosai"
Duk da baiga Nawfal ba yasan ya ciza gefen leben shi na kasa yanda yakan yi duk idan yana
cikin damuwa
"Dan Allah Hamma ka fadamun gaskiya, ya take? Boye mun ba zaiyi amfani ba, is not like zan
iya tahowa yanzun-yanzun, kawai ina bukatar in san halin da take ciki"
Bai fada mishi dukkan gaskiya ba, amman da sauki, zazzabin ya sauka, da kan shi ya duba
kafin su taho, kuma jininta lafiya kalau, bai hau ba
"Ga Madina..."
Salim ya fadi yana mika mata wayar, saboda baisan me zai fada Nawfal ya yarda da shi ba
"Madina"
Muryar Nawfal ta daki kunnen ta tana sakata jin wani abu ya tsirga mata
"Hamma"
Cikin wani irin yanayi Nawfal yace
"Ya take Madina? Ki fada mun? Ke nasan ba zaki mun karya ba"
Numfashi ta sauke
"Da sauki, bata kara yin amai ba, tana ta bacci ne, gani ma Hamma zai kaini gida in watsa ruwa
in dauko mana su kafet haka..."
Tana jin ajiyar zuciyar da Nawfal ya sauke yana ma Allah godiya cikin harshen fulatancin
"Ban san ya zanyi ba in wani abu ya same ta, ban sani ba...na kusa dawowa gabaki daya in
shaa Allah, saura yan watanni, ba zan kara nisa ba idan na dawo..."
Madina bata jin ko ya dawo zata daina jin yanda yayi mata nisa
"Idan ta tashi ki kirani, tana tashi Madina"
Kai ta jinjina
"Zan kira ka Hamma..."
Kamar ba zata sake cewa komai ba tace
"Ka yarda dani, da sauki, da sauki sosai"
Yanda ta karasa maganar ne ya kasa barin kunnen Salim, kulawar da take cikin muryarta yaji ta
sa kirjin shi ya matse, sai kuma yanda ta mika mishi wayar tana fadin
"Hamma ya cika saka damuwa a ran shi"
Tana saka shi dana sanin bata wayar da yayi, har ya jirata bai daina jin wani zafi-zafi a kirjin shi
ba, yanzun ma da yake kallon ta yana jin yanayin na karuwa ne, akan me zata sauke murya da
yawa haka, shi bai taba ma jin ta sauke mishi murya cikin kulawa yanda ta sauke ma Nawfal ba,
wayar shi da yaji tana zuu cikin aljihun shi ya zaro ya duba
"Hamma ne?"
Madina ta tambaya, shi dinne, baisan me yasa ya girgiza mata kai yana juyawa ya fice daga
dakin kafin ya daga wayar ba
"Hamma ta tashi?"
Nawfal ya tambaya daga dayan bangaren
"Yanzun muka dawo Bajjo, bacci takeyi, tana tashi ni da kaina zan kira ka"
Yana jin Nawfal din ya sauke numfashi cike da damuwa
"Bacci takeyi, bacci take Bajjo, na taba maka karya?"
Cewar Salim yana jin yanda baya son damuwar Nawfal din da yake karanta ta cikin wayar
"Zan kara kira"
Kawai Nawfal yace yana kashe wayar. Dakin Salim ya koma, camera din wayar shi ya shiga
yana kashe hasken sannan ya dauki Daada hotuna guda biyu, batare da tunanin komai ba ya
bude whatsapp din shi yana tura ma Nawfal
"Kagani, da sauki, kuma kaci abinci"
Ya rubuta a kasan hotunan yana sauka daga whatsapp din bayan yaga shigar sakon na shi ya
mayar da wayar a aljihu, bashi da matsala da kula da Nawfal, kawai baya son Madina tayi ne,
ko kadan baya so, bai taba sanin baya so ba sai yau.
©
✏
FIKRA WRITER'S ASSOCIATION
Facebook: Lubna Sufyan
IG: SufyanLubna
Email: Calmlubna@gmail.com
Whatsapp: 08074545149
*RAI DA KADDARA 1*
15
Sake runtsa idanuwan ta tayi a karo na babu adadi, saboda duk lokacin da zata bude idanuwan
sai ta dinga jinta a wata duniya tsakanin rayuwa da wani abu da ba zata iya kira da mutuwa ba
tunda bata san yanda take ba. Ko wacce gaba ta jikinta ciwo takeyi, ga kirjin ta da yayi nauyi
tamkar an dora wani irin dutse a saman shi
"Daga jikin wa ka baro ka taho?"
Kunnuwan ta sun jiye mata wannan kalaman, idan ba karya suka isarwa kwakwalwar ta ba
tabbas muryar ta Saratu ce, a tsayin shekarun nan duk wasu kalamanta na rashin kirki ta koyi
takaita su ne akan Julde kawai, shisa zuciyar Daada take hasasa mata cewa wannan karin ma
da Julden take, wani irin hijabi taji ya gifta tsakanin ta da zantukan su Saratun shisa ta hakura
tana barin duhun da ya janyeta yin nasara.
"Daada ga Hamma can ana dukan shi a gonar mai saje, kiyi sauri kizo, kiyi sauri kar su illata
shi"
Yelwa ta sauke kowacce kalma a tsakanin numfashin da take kokawa da shi cikin alamun gudu
tayi, a cikin harshen fulatanci, murfin tukunyar tuwon da Daada ta gama tuqawa ta dauka tana
rufewa, kafin ta daga idanuwanta tana sauke su kan Yelwa cike da nutsuwar da zakayi
mamakin ta a tattare da mahaifiyar da aka zo ma da sakon ana dukan danta. Sai dai bashi bane
karo na farko, ba kuma na biyu bane ba, idan Daada zata runtsa idanuwan ta, lokutta irin
wannan zasu bace a tunanin ta, ba zata iya lissafa adadin su ba saboda yawaitar faruwar su
"Daada ki ta so"
Yelwa ta sake fadi a kagauce, murmushi Daada tayi, murmushin da taji ya fito daga tsakankanin
zuciyar ta inda yake yawaita yi mata ciwo da labarai irin wa'annan
"Me zan musu Yelwa? Zan iya hana su dukan shi ne?"
Kai Yelwa ta girgiza cikin alamar rashin yarda, daga inda Daada take zaune tana ganin kyallin
hawayen da yake cike da idanuwan Yelwar, kafin ta kai hannu tana daukar muciyar da take a
jingine da bango, ko gama bushewa daga wankin da Daada tayi mata ba tayi ba
"Ba zasu kashe shi ba, ba zan bari su kashe shi ba Daada"
Yelwa ta karashe maganar tana kai dayan hannunta ta dauke hawayen da take jin alamun
zubowar shi tana juyawa
"Allah ya tsine miki albarka idan kika saka kafa kika fita