Showing 75001 words to 78000 words out of 79955 words

Chapter 26 - Rai da kaddara Book Complete by Lubna Sufyan .pdf

bafa wata
matsala bace da ba za'a iya shawo kanta ba, idan ma surgery dinne bashi da wata matsala..."

Salim yake fadi cikin tausasawa

"Ko kasar za'a bari da ita, Alhamdulillah akwai halin yin hakan... Dan Allah ka kwantar da
hankalin ka"

Kai kawai Julde yake daga ma Salim din ba dan yasan ta inda zai fara kwantar da hankalin shi
ba. Har ruwa ya bashi mai sanyi, da kan shi ya bude mishi robar, kurba daya yayi yana jin
ruwan ya wuce dakyar, kan shi ya dora a jikin teburin office din Salim din yana maida numfashi,
yaji dadin shirun da Salim yayi yana bashi dama ya nemi nutsuwa da kan shi. Bugun da zuciyar
shi takeyi shi dinma in aka auna za'a iya bukatar yi mishi aiki a cikinta.

"Ina jin kamar ba zan sake saka su a idanuwa na ba Julde"

Muryar Daada a waccen jinyar da tayi ya dawo mishi, shirun da ya biyo bayan maganar tata na
biyo shi tun daga wancen lokacin zuwa yanzun da yake zaune a ofishin Salim. Shiru ya zaba,
Daada bata matsa mishi ba, bata ambaci sunaye ba, amman yasan me take nufi, bata bukatar
ta ambaci sunan kowa. Ya zabi shiru ne ya kuma zabi danna tambayoyin ta can kasa tare da
duk wani abu daya danganci Yelwa da Bukar din. Bata sake daga mishi zancen ba, shima bai
sake bari ya dawo mishi ba sai yanzun. Saboda ya zabi ya so kan shi, ya dora bukatar shi akan
tata. Son kan da sai yanzun yake ganin shi

Su duka Yelwa ta tsalla ke
Ba shi ka dai ta bari ba
Har da Daada.

©

FIKRA WRITER'S ASSOCIATION

Facebook: Lubna Sufyan
IG: SufyanLubna
Email: Calmlubna@gmail.com
Whatsapp: 08074545149

*RAI DA KADDARA 1*

20

A karo na farko a rayuwar shi da ya rike jaka a hannun shi batare da yasan abinda zai zuba a
ciki ba

"Kana da passport Bajjo, Daada ma nata baiyi expire ba, da kai ya kamata ku tafi, zan biyo ku
daga baya dan kar a bata lokaci"

Abinda Julde yace mishi kenan, yana kallon gamsuwar da su Khalid sukayi da maganar Julden
a cikin idanuwan su tun kafin ma su furta. Shisa yayi shiru, yanda duk ya so ya girgiza wani ya
fada mishi cewa ba yajin zai iya tafiya shi kadai, bayajin yana da karfin halin da zai kula da
Daada batare da zuciyar shi ta rarrabu kashi-kashi a cikin kirjin shi ba, sai ya kasa. Kai kawai ya
daga musu cikin yarda shima. Hadiye tsoron da fargaba yayi har sai da ya koma gida a ranar,
ya saka mukulli yana kulle dakin bayan ya shiga sannan ya budema Murjanatu zuciyar shi yana
jin rashin ta fiye da kowanne lokaci

"Bana jin zan iya Jaan, Daada ce, yau dana ganta a kwance babu abinda naji ina so inyi sai in
zauna a gefen ta inyi kuka har sai ta bude idanuwanta tace mun komai zaiyi dai-dai... Ban taba
kula da ita ba, ita ta saba kulawa da ni, taya zan fara yanzun?"

Ya karasa yana jan wani irin numfashi hadi da fitar da shi cike da nauyin da yake ji a kirjin shi,
saboda yanda yayi maganar batare daya ba kanshi damar numfasawa ba

"Waya yace kai kadai zaka kula da ita? Ba India kace ba? Zaka sameni a filin jirgi ina jiran ku
Gidado...idan na kula da kai zaka iya kula da ita? Zan so ince maka zan kula da ku duka biyun,
amman Daada ce, zaka so kayi komai daya dangance ta da kan ka... Na san hakan, kaima in
ka nutsu ka duba zuciyar ka zaka ga hakane..."
Numfashin dai ya sake ja yana fitarwa

"Babu abinda ba zaka iya ba in dai akan Daada ne, in baka yarda da kan ka ba, ka yarda dani,
kasan ba zan maka karya ba, duk da ina son ka"

Baisan murmushi ya kwace mishi da kalamanta na karshe ba sai da yaji alamar shi har a
zuciyar shi da nauyinta bai ragu ba, amman numfashin da yaja ya kai mishi har ciki

"Kinsan bangane komai da kikace sosai ba...komai ya kare ne da yanda kika ce kina so na"

Dariyar da tayi sai da ta kara fadada murmushin shi

"Ina son ka... Ina son ka Gidado"

Kai ya jinjina, ya sani, saboda yanda bata gajiya da nuna mishi duk rana haka bata gajiya da
fada mishi tana son shi. Wasu ranakun in ta fada sai yaita kallon ta, musamman labbanta da
yanda kalaman suke fitowa kamar basu da wani nauyi a wajen ta. Da shi bahaushe ne, daya
boye a bayan yaren yace shisa fada mata yana son ta a duk rana yake mishi wahala. To shi
bafullatani ne, babu kunya a tsakanin su, sun wuce wannan matakin tuntuni, bashi da abinda
zaiyi amfani da shi a matsayin kariya.

Amman kalmomin suna masa nauyin furtawa, zai iya kirga lokuttan daya fada mata su, yana dai

kokarin ganin a rana ya zama dalilin da zatayi dariya ko sau dayane, yana kuma kokarin
kyautata mata dai-dai iyawar shi, fada mata yana son ta na mishi wahala, amman nuna mata
abune mai sauki saboda ta cancanci fiye da hakan a wajen shi, ta bashi abubuwan da zai dauki
lokaci idan an bashi dama yana bayanin su.
"Wai har yanzun kana nan tsaye Bajjo?"

Khalid da ya turo kofar yana katse ma Nawfal tunanin shi ya furta

"Na rasa abinda zan dauka, Murjanatu ta shiryamun jakata da zan taho"

Gira daya Khalid ya daga

"Nasan kana da aure Bajjo, ban manta kana da mata ba"

Dariya Nawfal yayi

"Yi hakuri ba haka nake nufi ba"

Labban shi Khalid ya matse waje daya yana jinjina kai, cikin yanayin dake fassara "Ka dai
cigaba Allah yana kallon ka". Dariya ya sake na Nawfal

"Da gaske na rasa abinda zan dauka"

Numfashi Khalid ya sauke

"Me yasa kake fadamun? Ka kira Murjanatu mana sai ta fada maka abinda ta shiryo maka
sanda zaka taho ka sake daukar su"

Kai Nawfal ya jinjina cikin yarda da shawarar Khalid din yana nufar inda wayar shi take ya
dauko

"Me zakai?"

Cewar Khalid yana bude baki cike da mamaki

"Kiran Murjanatu mana?"

Dafe kirji Khalid yayi yana samun waje kan gadon ya zauna

"Me ka dafe? In zuciyar ka ce ba'a bangaren dama take ba, saika dan matsar da hannun ka
tsakiya..."

Wani irin kallo Khalid yake ma Nawfal din daya cigaba da fadin

"Daga bangaren haggu kadan"

Ta baki Khalid ya furzar da numfashi yana sauke hannun shi

"Baka ga kallon da nake maka ba ko? Ba zakayi shiru ba"

Dariya Nawfal yake yi

"Da gaske, wannan ai son kunyata Hamma Salim ne, ace baka san inda zuciyar ka ta ke..."

Robar ruwan da Khalid din ya dauka na sa sauran kalaman Nawfal din makale mishi tare da
dariyar da yayi niyyar yi

"I dare you Nawfal Bukar..."

Khalid ya fadi muryar shi babu alamar wasa

"In kira Murjanatun ko..."

Kallon "Magana kake har yanzun" da Khalid ya watsa mishi yasa shi daga hannun shi cikin
saranda yana mayar da wayar ya ajiye. A duniya dai yasan in ta bangaren samun yan uwa ne
Allah ya gama masa komai, ko da ace dama aka bashi zai wahala ya zabo irin su Khalid. Shisa
yake kara godema Allah da kyautar su da Ya yi masa a cikin rayuwar shi. A cikin mintina kadan
Khalid kan saka shi yaji yanda zai iya jure duk wani abu da zai faru da shi a cikin kowacce rana.
Numfashi da bai san yana rike da shi ba ya sauke. Kananan abubuwa ya fara tattarawa kamar
su brush da cajar waya da duk wani abu da yake tunanin zai bukata.

"Ba zance maka Daada zata zauna tare da mu har karshen rayuwar mu ba Bajjo, amman komai
zai faru Allah ba zai dora mana abinda ba zamu iya dauka ba, daga karshe komai zaiyi dai-dai...
In shaa Allah"

Khalid ya fadi muryar shi na fitowa da wani sanyi da yasa nauyin da Nawfal yake ji a kirjin shi
karuwa. Baice komai ba, kayan shi ya cigaba da hadawa, ko ya so ya fadi wani abu bai san me
zaice ba

"Hamma yaje ya dauko su"

Khalid ya fada dan ya rage musu nauyin shirun da ya lullube su gabaki daya, kai kawai Nawfal
ya jinjina batare da yace komai ba, mikewa Khalid yayi tare da fadin

"Matar ka kake son kira, na bar maka dakin Bajjo"

Murmushi Nawfal yayi, ba dan zai kira Murjanatu bane ya fita, abinda ya zo ya fada mishi ne ya
gama fada shisa ya bashi waje yayi tunanin duk da yake bukata

"Nagode Hamma..."

Ya furta a hankali duk da Khalid din ya rigada ya fita daga dakin. Kayan shi ya cigaba da
hadawa zuciyar shi da kan shi cunkushe da abubuwa mabanbanta.

*

Da yawa kance lokaci sakarai ne, idan ya wuce baya dawowa. Ta kuma ga hakan a al'amura
daban-daban. Ta ga sauri da rashin saurin lokaci musamman idan tana jiran wani abu. Kwanaki
bakwai dai basu taba zuwa sun wuce mata haka batare da ta rike wani abu guda daya mai
muhimmanci da tayi a cikin su ba. Tayi kuka har sai da ta fara tunanin anya ba duk rana ake
halitta ma bawa sababbin hawaye ba? In ba haka bane ba tasan ta inda take samun hawayen
fitarwa bayan tarin wanda ta zubda ba.

Ta sha jin labarin kadaici, har ma take tunanin idan ta runtsa idanuwan ta a wasu ranakun takan
ji shi, takan ji kewar iyayen da ko fuskar su bata sani ba. Ashe wannan ba kadaici bane ba,
yaudara ce da zuciyar ta take yi mata, asalin kadaici na cikin ranar da Khalid ya maida ta gida
dan ta dauko kayanta. Yanda ta shiga cikin gidan tana tunanin ta inda zata fara inda ace ta rasa
Daada, lokacin ne ta duba tsakar gidan da yayi mata fadi kamar duka duniyar ta ce ta tattaru a
waje daya, ta kuma ganta ita kadai a tsaye. Ranar ne ta fara sanin menene kadaici, yanayi ne
da yayi matukar firgitata, ranar kuma ta hango maraicin da bata fatan ya kusanto inda take.

Tun jiya aka sallame su, tunda daman sun kara barin Daada ne dan a tabbatar ta samu saukin
da zata iya zaman jirgin tunda an riga an gama kammala duk shirye-shiryen da za'ayi da ya
danganci tafiyar ta su. Ita dai ce take ta hada kayanta tunda ance gidan Julde zata zauna har su
Daadar suje su dawo, ta so ta tambaya me yasa ba za'a tafi da ita ba, me yasa za'a barta, waye
zai kula da Daada bayan bata tunanin akwai wanda yasan abinda Daadar take so da wanda
bata so fiye da ita.

Amman tunda take bata taba ganin damuwa karara a fuskar Julde ba irin wannan karin. Yau ma
da yazo gidan idanuwan shi duk sun kumbura kamar wanda yayi kuka. Maganar shima a shake
take fitowa, shisa ta rasa kwarin gwiwar da zata tsare shi da wasu tambayoyi. In da zata iya
daukar dakinta kacokan din shi da haka zatayi, saboda komai da yake ciki bukatar shi takeyi.
Bata taba kwana wani waje ba bayan asibiti tare da Daada tunda take.

"Kwana nawa zakuyi Hamma?"

Tayi ma Nawfal tambayar da ta kasa yiwa Julde, amman kafadu ya daga mata cike da rashin
sani kafin ya amsa da

"Ba zance ga exact kwanakin ba Madina...zan fada miki da na san kwana nawa zamuyi"

Kai kawai ta iya jinjina mishi, tana ture tunanin can kasan zuciyarta saboda bata son hasaso
kwanakin da zatayi batare da Daada ba. Ba zata taba daukar duk abinda take da bukata ba, ta
sani. Shisa ta rufe jakar kawai tana daukarta ta fito da ita falo ta ajiye. Dakin Daada ta nufa ta
sameta a zaune in da tayi sallar la'asar, karasawa tayi ta zauna a gefenta tana matsawa sosai
yanda zata iya jingina da jikin Daadar, bata da lafiya, amman tana bukatar hakan ko na yan
mintina ne ko zuciyar ta zatayi mata sanyi.

"Allah ya baki lafiya Daada Am... Allah ya kaiku lafiya ya dawo da ku lafiya... Zanyi kewar ki"

Madina ta karasa maganar muryarta na fitowa a karye, hannu takai ta dan daga gilashinta tana
sa yatsa ta goge hawayen da take jin ya taru a gefen idanuwan ta. Numfashi Daada ta sauke,
akwai ciwo na daban da zuciyarta take fama da shi da yafi karfin ganin duk wani likita a fadin
duniya.
"Kina da tambayoyi Madina, na san kina da tambayoyi masu yawa... Nagode da yanda baki
taba tsare ni da in fada miki ba"

Sake shigewa jikin ta Madina tayi tana jin zuciya ta na kara karyewa

"Dan Allah kibar maganar nan Daada... Ke dai Allah ya baki lafiya, in akwai abinda ya kamata in
sani ai ba saina tambaya ba na san zaki fadamun"

Cewar Madina, tana jin gaskiyar kalaman har ruhin ta. Koma menene bashi da muhimmancin
lafiyar Daada a wajen ta. A yanzun ma gabaki daya babu wani abu da take so sama da ganin
Daada ta dawo lafiya, an duba ance babu sauran abinda yake damun ta. Murmushi Daada tayi,
murmushin da ya fito daga wani tsagi na zuciyar ta da har ya daina bugawa tare da yan uwan
shi ba zai daina godema Allah da kyautar su Madina ba, akan su ta kara yarda da yanda Allah
yake fitar da mai kyau a cikin mummuna.

Sallamar da suka ji na sa Madina mikewa, a daki ta baro wayar ta, tasan da zai wahala Salim
ya shigo gidan. Zai kira ta ne yace mata yana kofar gida, tana fitowa falon kuwa ta ganshi a
tsaye, kallon shi tayi tana ganin yanda yafi kofar tsayi. Salim dogo ne, irin dogayen da ko a cikin
masu tsayi zaka duba da yawa baka sami kalar shi ba
"Hamma..."

Ta furta yana sauke mata numfashin da yake rike da shi a matsayin amsa kiran sunan shi da
tayi, kallon ta yakeyi da gajiya kwance akan fuskar shi, kasan idanuwan shi ya danyi duhun da
in baka san shi ba zaka dauka haka suke. Madina ta san rashin wadataccen bacci ne

"Ina ta kiran ki..."

Salim yayi maganar yana daga mata karamar wayar shi da yake rike da ita

"Nabar wayar a daki, amman ga jakunkunan mu nan, na hada komai, bari ince ma Daada ta fito
sai mu tafi"

Kai Salim ya dan daga mata yana shiga cikin dakin sosai ya dauki jakunkunan nasu kamar basu
da wani nauyi ya fice daga dakin. Ita kuma ta koma tana fada ma Daada ta fito su tafi. Sai da ta
shiga dakin ta ta dauko wayarta sannan ta fito, tana kallon yanda Daada take daga kafarta tana
saukewa dakyar, amman ba zata yarda ka kamata ba, in dai zata samu ta mike to zatayi tafiya
ko yaya ne. Ita ta kulle ko ina tana sauke numfashi bayan ta fita kofar gida taga ta kulle nan ma.
Tana juyawa ta ga Salim ya fito daga motar yana zagayowa ya bude ma Daada gidan baya ta
shiga.

Ya mayar ya rufe sannan ya zagaya yana komawa mota, sanda ta taka ta shiga, tana rufe kofar
taji yace ma Daada

"Ya jikin naki Daada? Kan baya ciwo yau?"

Cikin yaren fulatanci

"Alhamdulillah, gashi ka ganni garas"

Dan murmushi yayi

"Allah ya kara lafiya"

Ya furta da hausa wannan karin, yana jan motar tunda daman yayi kwana kafin ya ajiye ta. Shi
Madina take kallo tana son gane abinda yake damun shi a kwanakin nan, rashin maganar shi
ya karu, sai suyi zaman awa daya baice mata komai ba, duk hirar da zatayi sai dai in
idanuwanta nakan fuskar shine zata kula da yanda yake amsa ta da gira, kai ko nashi idanuwan
da zai lumshe ya sake bude mata a kasalance. Salim najin idanuwan Madina da suke
yawatawa a jikin shi kamar tana son budo duk wasu sirrikan shi.

Yana jin yanda kallon nata ke sa wani abu amsawa a cikin kirjin shi. Sharewa yayi kamar bai
san tanayi ba har suka karasa gida. Kamar wanda yake kan kaya haka ya fice daga motar da
sauri. Shi ya bude ma Daada da tace mishi

"Da ba sai na fito ba tunda zamu juya ne... Ko ba yanzun za'a tafi ba?"

A kasalance Salim ya kalle ta

"Ki fito Daada, ko ruwa ki sha, ki dan mike kafafuwan ki kafin kowa ya shirya, ba zakiyi ta zama
a mota ba"

Har zuciyar ta zaman motar zata zaba in da wani abu a muryar Salim ya bata damar hakan.
Amman tsaye yayi yana jiranta, dole ta sauko da kafafuwanta daga motar. Rabonta da gidan
tun bikin Adee, shima ba dadewa tayi ba. Tunda har gida mijin Adeen yaje ya gaishe da ita, ko
yanzun yakan biyo lokaci zuwa lokaci, bai taba zuwa mata hannu biyu ba. Zatace yana da kirki,
amman ta san kirkin na shine ya hadu da yanda Adee ta nuna mishi darajarta. Sai da yaga ta
fito ya rufe murfin motar. Madina ma fitowa tayi ta zagayo suna jerawa da Daada.

"Jakar ki Mug...wacce ce jakar ki?"

Salim ya tambaya ganin ta bi Daada

"Babbar..."

Ta amsa mishi a takaice batare da ta juyo ba tunda ta san zai biyo su. Tare suka shiga har falon
gidan suna dan hira da Daadar. Madina ce tay sallamar da Saratu ta fito tana amsawa, fara'ar
da take fuskarta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login