Showing 66001 words to 69000 words out of 79955 words
Chapter 23 - Rai da kaddara Book Complete by Lubna Sufyan .pdf
kafafuwan shi suka fara daukar shi
"Mero... Mero Na"
Ya furta a kasan numfashi
"Daddy... Ina zaka je kuma?"
Salim ya tambaya, amman ko jinshi Julde baiyi ba, mutane yake turewa yana ratsa tsakanin
motocin da suke wajen, kafin ma ya tsallaka har anja motar anyi gaba, wani mashin ya dafa
yana mayar da numfashi, shekaru goma sha sai yau ya dora idanuwan shi akanta, kafin ya
maida numfashin da yake fatan zai dan nutsar da bugun zuciyar shi yaji an dafa shi
"Daddy... Lafiya kuwa?"
Salim ya tambaya yana ganin fuskar Julden ta kara mishi haske kamar babu jini a jikinta
"Lafiya?"
Ya sake tambaya, kai Julde kawai ya daga mishi
"Mu tafi gida kawai, gobe na dawo in duba motar Khalid da safe..."
Kan dai Julde ya sake daga mishi, bai yarda da muryar shi ba shisa bai amsa ba, haka suka
karasa, Salim ya bude mishi gaban motar ya shiga. Zuciyar shi kamar kara bugawa take a cikin
kirjin shi.
Ashe zai sake ganin Mero?
Ko dai alama ce kaddara take nuna mishi?
"Inajin kamar don kai kawai aka halitta mun zuciya a kirjina, ko dan kai ta fara numfasawa?
Wanne irin so nake maka dana watsar da maganar kowa Julde?"
Kalaman ta kenan
Kalaman da suka zauna mishi
Kowanne RAI da tashi KADDARAR.
©
✏
FIKRA WRITER'S ASSOCIATION
Facebook: Lubna Sufyan
IG: SufyanLubna
Email: Calmlubna@gmail.com
Whatsapp: 08074545149
*RAI DA KADDARA 1*
18
Da idanuwa Saratu take bin shi ba tun safiyar ranar ba, tun sati biyu da suka wuce saboda
tambaya babu irin wadda batayi mishi ba akan me yake damun shi yana amfani da damar
wajen nuna mata cewa da gaske bata da wani muhimmanci a wajen shi. A tsayin shekarun
auren su zata kirga adadin lokuttan da yayi rashin lafiya har ya kwanta, a cikin adadin zatace
sau daya ya taba wadda ta kai shi da kwanaki a kwance, wannan kuma rashin lafiya ce da take
son shafewa a kundin tarihi idan har tana da halin haka.
Sai kuma satikan nan da suka wuce da alamu duka suka nuna cewa ba ciwo yake ba, ya dai
koma kamar wani gunki-gunki ne, abinci haka zai ta wasa da cokali a ciki, a yinin rana baifi ya
saka ruwan shayi da yar wainar kwai a cikin shi ba, satin farko ya jera kwanaki hudu yana fita
tunda sassafe sai yammaci liqis zai dawo, kafin daga baya ya koma rabuwa da kan gadon dakin
shi ma sai yaji su Khalid a falon ne zata ga yayi ta. Suna kuma fita zai koma ya sake bin gadon
ya kwanta. Har daki take bin shi da abincin safe, rana da na dare. Yau na safen da na ranar
duka haka ta zo ta dauke ta sake fita da su, babu alamar da ta nuna ya ko bude balle ya ci.
Rashin muhimmanci da take da shi a wajen Julde ba sabon abu bane, abune da lokaci bai sa ta
daina jin ciwon shi ba, wannan karin dai tunanin halin da yake ciki shiya danne mata ciwon da
take ji. Ta na son shi, ta na son Julde fiye da yanda kalamai zasuyi mata adalci wajen
misaltawa, saboda ko wulakancin shi na yau da kullum bai dakushe tasirin soyayyar shi a
zuciyar ta ba. Na dole sun dawo wuni cikin dakin kamar marassa gaskiya, bai kore ta ba, yanda
yake nunawa ma kamar bai san tana cikin dakin ba tunda ko inda take baya kallo.
Ta kai zuciyar ta nesa dai wajen ganin bata yi komai daya wuce taya shi zama a cikin dakin ba.
Tana kallon shi bayan la'asar ya shiga bayi, tana nan zaune ya fito, idanuwan ta suka fara
sauka kan fuskar shi da ta manta rabon da ta ganta babu gashi, a kwanakin nan ma ta cika
sosai saboda bai damu da yunwar cikin shi ba balle wata sumar fuska, yanzun ya kwashe
komai, ko fuskar Lukman akwai gashin baki daya fara fitowa luf da shi, har tana tsokanar shi a
kai ma. Fuskar Julde da bayan kwai basu da bambanci. Haka kawai sai yanayin ya hasko mata
wani hoto da yasa zuciyar ta bugawa kamar tana neman hanyar fita daga cikin kirjin ta.
Tabbas shekaru ba karya bane ba, don sun nuna kan su a tare da Julden, bata san ko
idanuwanta bane suka rage wannan shekarun akan fuskar shi suna dai-daita mata fuskar da
hoton da take da shi a cikin kanta. Bambancin ba a zanen fuskar yake ba, a sarkar da babu ita
yanzun a wuyan shi ce, kayan fulanin da yake sakawa a wancen lokacin, sai kuma askin kan
shi da yake kasa sosai, sabanin wancen lokacin da ya tara gashin, bayan kadai ake ragewa an
tado gaban yayi tozo irin na samarin fulani da suke ji da kan su a wancen lokacin. Julden ta,
Julden da zuciyarta ta zaba tun kafin ma tayi wayon sanin haka.
Mata da yawa na son maza masu kasumba, maza da yawa sukan ce cikar kamala ta da namiji
kenan, musamman magidanci kamar Julde, in ba dalili na aikin kaki da kan hana ma wasu
mazan yin hakan ba, banda Saratu, a yau, a yanzun kuma ban da ita
"Kayi kyau"
Kalmomin biyu da tayi nufin furtawa a zuciyarta suka kubce mata suna kuma saka Julde sauke
idanuwan shi da yanayin da yake ciki bai sa farin su canzawa ba, kyallin na shigar mata wani
waje da bata san da shi a zuciyar ta ba, har yana sata gasgata maganar cewa so baya tsufa da
masu azancin magana suke yawan fada
"Da ka aske sumar sai kayi kyau"
Ta furta muryarta na sauke kasa tunda kalaman farko suka subuce sai suka bata kwarin gwiwar
furta sauran. Har lokacin dai kallon ta yake yi, tun kafin ya san menene soyayya, tun kafin Mero
yake ganin soyayyar shi a idanuwan Saratu, a irin wannan lokacin a baya da take fito mishi da
asalin kaunar da take mishi ya sha tambayar kan shi dalilin da yasa ya kasa mayar mata ko da
kadan ne daga cikin tarin soyayyar da ya gani, kuma ya san tana mishi. Watakila da ta rage
mishi radadin rashin Mero da yake fama da shi.
Da bai gan ta ba, da bai sake ganin ta ba da bata fama mishi tsohon ciwon da yake riritawa ba,
kamar mahaukaci haka ya dinga zagaye unguwar da ya ganta yana tambayar duk wani wanda
zai tsaya ya saurare shi ko ya ganta ta hanyar zayyana mishi kamannin ta, a idanuwan mutane
mabanbanta yaga mamakin da suke da ya kasance cikin shiga ta kamala, ko kadan alamu basu
nuna cewa yana dauke da cutar rangwamen hankali ba, amman daga ya bude bakin shi sai
kalaman shi su sha bamban da kamammin shi. Ziyara ta zo, ya san iya wannan in ba kuma
dalili ya raba auren da tayi a Kaduna ba kamar yanda yake fata.
Har yanzun, yana kuma jin har abada Mero zata kasance rike da kaso mafi girma na zuciyar shi
da duka walwalar shi. Baiyi karya ba da ya taba ce mata
"Ina jin kamar ban san farin ciki ba sai da kika shigo rayuwa ta Mero"
Akan ta ya fara sanin menene asalin farin ciki kafin ya samu su Salim da suka karasa cika mishi
abinda ya rage na daga cikin farin cikin. A yanzun kuma duk wata yar walwala da yake yi a
duniya su ne sanadi, su kadai yake kallo ya samu nutsuwa. Ko sauran matan da yake bibiya
baya samun nutsuwar da yake nema a tare da su, kamar akwai wani duhu da yake mamaye da
shi ya hana mishi sukuni.
"Ko kana sha'awar cin wani abu?"
Maganar Saratu ta kutsa ta cikin tunanin shi
"Idan anyi sallah ki kira su Khalid sai muci gabaki daya"
Yana kallon murmushin da tayi tana daga kai hadi da mikewa ta fice daga dakin, da zai iya da
ya so ta, ko kadan da ya so matar nan. Amman ba zai iya ba, lokaci dai ya koya mishi sabo da
ita, amman babu soyayyar ta ko daya a cikin zuciyar shi, akwai dai jin ko na rana daya ya
kamata yayi mata godiya, da ta bashi su Salim, da ta ke tare da shi tana kula da gidan shi duk
fitowar rana da faduwar ta. Ta cancanci ko da iya wannan jinjinawar ne.
Komai da sanyi-sanyi yake tayin shi, sanda ya gama shiryawa cikin wani farin yadi da ya karbi
jikin shi har ana kiran magriba, fita masallaci yayi, bai hadu da kowa ba wajen dawowa sai
Khalid da suka taho tare, Nawfal daman ya saba ya zauna masallaci bayan Magriba wasu
ranakun ma har sai anyi isha'i yake dawowa. In kuma bai tsaya ba to sai ya gama duka azkar
din shi, Khalid ya sha zama tare da shi sai yaga ya samu waje ya jingina bayan shi da bangon
masallacin, kamar akwai wata nutsuwa ta daban da sai a cikin masallacin ya ke samun ta.
"Ku zo muci abinci, ka fada ma su Bajjo"
Julde ya cewa Khalid daya daga mishi kai
"Yanzun kuwa... Me Nanna ta dafa?"
Kai Julde ya girgiza mishi
"Ni ma ban sani ba fa..."
Yana ba Khalid din dariya kafin su rabu kowa ya wuce bangaren shi. Sanda Julde ya shiga har
Saratu ta shirya teburin cin abincin mai mazaunin mutum takwas. Kujera yaja ya zauna. Ya
kusan mintina goma kafin Khalid da Nawfal su shigo da sallamar da ko amsa musu Julde baiyi
ba suka cigaba da maganar da sukeyi
"Ni fa bana son wannan tattare-tattaren da kake mun... Jiya ba akan gado na ajiye takardar ba?
Saboda idan na zo in dauka, yanzun duk ka hade su waje daya..."
Kallon shi Nawfal yakeyi
"Kan gado wajen ajiye takarda ne Hamma? Kan gado fa? Meye amfanin teburin dakin?"
Kafin Khalid daya daga ido a zafafe ya amsa, Salim ya rike wuyan kowannen su da hannun shi,
yana saka su fadin
"Hamma mana..."
A tare
"Tun kafin in shigo nake jin hayaniyar ku...sai kace kaji"
Nawfal ya fara zamewa sannan Khalid, babu shiri kowa ya samu kujera ya zauna, Khalid na sa
kafa cikin kokarin ture kujerar Nawfal daya zauna kusa da shi
"Daddy kai ma Hamma magana"
Kallon su Julde yakeyi fuskar shi dauke da murmushi, yanajin wani abu daya kulle mishi kirji
yana sassautawa
"Kai da baka ma jin yunwa? Me ka zo yi?"
Khalid din ya amsa
"Idan banzo ba waye zai takura maka?"
Wannan karin Khalid din ne ya kalli Julde
"Kana jin shi ko Daddy? Kana jin me yake cewa"
Khalid ya karasa yana kaima Nawfal dukan daya kauce yana dariya
"Har yanzun kun kasa wuce shekara sha biyu"
Lukman daya karaso wajen ya fadi cikin harshen fulatanci yana tsayawa kan kujerar da Nawfal
yake hadi da fadin
"Ka koma can Hamma"
Akwai wani yanayi tattare da Lukman da yake saka kowa yi mishi abinda yake so, ko sanyin
halin shine ko kuma kwarjini ne daya ke yalwace saman fuskar shi duk da karancin shekarun
shi. Tashin Nawfal yayi, Lukman ya ja kujerar yana zama a tsakiyar Khalid din da Nawfal kafin
ya gaishe da Salim da Daddy
"Lukman ba'a ganin ka sam"
Nawfal ya fadi, har mantawa yake Lukman yana gidan, sai ya ga giccin shi
"Ina nan Hamma"
Ya amsa a takaice yana mikewa dan yaga alamar kamar ba yunwa suke ji ba, shi ko abincin
rana baici ba, cake ne kwara daya yaci a makaranta. Bubbude warmers din yayi, shinkafa ce da
miyar kaji, sai kamshi yake tashi, in dai girki ne Allah ya hore ma Saratu, gashi tana son yin shi,
ko wani gidan taje aka bata abinda bata sani ba bata girman kai take tambayar sunan shi da
kuma yanda akeyi, hakan ne ya sa ta kara gogewa da abincin gayu kala-kala. Lukman ya zuba
ma kowa yana kallon Nawfal daya girgiza mishi kai a hankali. Zai so yaci abinci a cikin su, sai
dai ko kifi aka saka ba nama ba a abincin haramiyar shine tunda ya san akwai yaji.
Numfashin da ya shaka yaji yaki kaiwa in da ya kamata da zuwan Saratu wajen, yana kuma jin
illar hakan a muryar shi lokacin daya furta
"Nanna..."
Cikin sigar gaisuwa. Bata kalle shi ba, amman ta amsa da
"Bajjo"
Salim da yake kusa da Julde ya mike ta zauna a kujerar shikuma ya zauna a ta kusa da ita
"Na bar wayata a daki, za'a iya kirana"
Yace yana mikewa batare daya kalli kowa ba balle yaga yanda suka san karya yake, suka san
uzuri ne dan kawai ya bar wajen tunda Saratu ta zo, babu kuma wanda yayi yunkurin hana shi,
akwai abubuwa da yawa da lokaci yake koya maka ciki kuwa harda kiyaye halayen makusancin
ka. Yanda duk Saratu da Nawfal zasuyi kokarin boye rashin kaunar da yake tsakanin su idan
wani yana nan, duk su Khalid din na fahimta, kamar yanda suka san daga Saratun har Nawfal
sun san biye musu kawai sukeyi. Fitar Nawfal tayi dai-dai da dagowar kan Salim yana sauke
idanuwan shi cikin na Khalid da suke shimfide da tuhuma, shakku da alamar tarin tambayoyi.
Baya so, tun shekaranjiya Khalid yake bin shi da idanuwa haka, har yau ya so kauce ma
dawowa gidan ya kwana. Ocean Palace guest Inn ne karshen in da yai tsammanin wani wanda
ya san shi zai gan shi balle kuma Khalid
"Nagan ka Hamma... Na ganka yau"
Khalid din ya fadi, ba shi bane karo na farko da wani a cikin shi ko Nawfal suka ce sun ganshi,
sai dai a shekaranjiyan kawai sai yaji zuciyar shi tayo tsalle zuwa makoshin shi da ya bushe
lokaci daya yana kuma neman yawun da zai samu ya jiqa shi ya rasa
"Nagan ka"
Khalid din ya sake maimaitawa muryar shi dauke da wani abu da Salim bai taba tunanin zai
gifta a tsakanin su ba
"Kila ya kamata in nuna kamar ban gan ka ba, kamar banga yarinyar da ka hada da jikin ka ba
Hamma, amman ba zan iya ba, ban san ya zanki maka magana ba. Kace mun iya abinda
nagani ne kawai...dan Allah kace mun iya abinda nagani ne kawai bai kai inda tunani ya nufa
ba..."
Duk kalma daya da Khalid din zai furta wani irin abune yake lullube Salim, ko dai haka kunyar
da yaji mutane na fada take shisa ya kasa daga idanuwa ya kalli Khalid, a karo na farko a
rayuwar shi da yake son kasa ta bude ya shige ciki akan ya fuskanci Khalid a yanzun. Rabon da
yaji kamar abinda yake bashi da kyau har ya manta sai a lokacin. Yana jin numfashin da Khalid
ya ja ya fitar
"Hamma..."
Ya kira zuciyar shi a shimfide cikin yanayin yanda ya kira sunan Salim din, bai daga kai ba, kasa
yake kallo, haka Khalid din bai sake furta komai ba ya juya kawai. Amman tun shekaranjiya din
yake bin shi da irin wannan kallon tuhumar duk haduwar da zasuyi, banda gaisuwa wata kalma
bata gifta a tsakanin su ba sai yau din nan, shima ya san saboda su Nawfal suna wajen ne. Ya
sa shi yanajin babu dadi tun shekaranjiya, abinci ma ya daina gane dandanon shi saboda
taraddadin da ya kasa fassara kona menene takamaimai.
Yanda Salim baiyi tsammanin ganin Khalid din ba haka shima. Dan dakyar ma ya gane wajen
da kwatance da komai. Wani abokin aikin shine kirista dan kabilar Igala yake aure a cikin satin,
to abokan shi da suka zo daga garin su sai suka sauka a wannan Guest Inn din. Akwai takardun
daya manta bai bari ba a wajen aiki kafin ya dauki gajeran hutun, sune ya roki Khalid da zaije
dasu hotel din da yaje ya karba. Saboda nisan wajen ma yana tafiya yana jan karamin tsaki
harya karasa, kawai dan dai Michael din yana da kirki, bashi da matsala sam, amman Khalid na
daya daga cikin mutanen da kunya bata cika saka su yin abinda zasu takura ba.
Ya kira Micheal din kuma yace mishi baima karaso wajen ba, shine abinda ya saka shi zama
cikin mota in da yayi parking yana jira, kalle-kalle yake yanda ake shige da fice, mata da maza a
hade. Waje irin haka ya kamata ace ya zama wajen da uzuri zai iya kawo kowa, amman ya
kasa kauda zargin da yake ma matan da yake ta gani suna shige da fice daga cikin hotel din,
watakila tare da mazajen su suke, watakila sako suka zo karba kamar yanda yayi, ko wani
uzurin mai tsafta, amman bata gari sun riga sun fesa ma waje irin wannan ruwan da har abada
jirwayen shi ba zai taba wankewa ba.
Idanuwan shi da yake ta yawata wa yana kalle-kalle ya sauke kan wata jar mota da baiga
lambar ba, amman sak irin ta Salim, sai dai baya tunanin akwai abinda zai kawo Salim wajen
nan, watakila ma yana asibiti ko gida a wannan lokacin. Kafin Salim din ya fito yana karyata
tunanin Khalid da ya kama murfin mota zai bude da nufin fita ya karasa wajen Salim din,
yarinyar da yaga ta sakala hannunta a kugun Salim na saka duk wani abu da yake kirjin shi
amsawa cikin yanayi marar dadin misaltawa. Dakyar ya iya runtsa idanuwan shi yana sake
bude su dai-dai lokacin da Salim ya juyo da yarinyar da duka alamu suka nuna bambancin
addini da yare a tsakanin su,Khalid na sake runtsa idanuwan shi babu shiri
"Inalillahi wa ina ilaihi