Showing 6001 words to 9000 words out of 24918 words
Chapter 3 - WAYAYYAR MACE COMPLETE BOOK BY FATIMA USMAR (YAR NIGER).txt
su cikin k'ok'on.
"Eh boka dan shi muka zo ", Hajiya Rabi ta fad'i haka tana k'ara jinjina lamarin bokan, tana k'ara amanna da aikinsa wanda yake tamkar yankan wuk'a.
"Kar ku damu tun da kun riga da kun zo wajena ta gama mallakar sa sai yarda tayi da shi, idanunsa zasu rufe daga kallon kowacce mace sai ita, ko uwarsa da ta haife shi bazata nuna mata iko akansa ba", ya fad'in haka cike da hak'ik'ancewa.
"Ku karb'i wannan ku bata tayi tsarki da shi, wannan garin maganin kuma ta barbad'a inda ta san zai tsallake, ya kuma kwanta da ita to magana ta k'are sai ya manta da kowa in ba ita ba, ya daina jin maganar kowa sai nata ko da kuwa iyayensa ne", cike da farin ciki suka karb'i maganin daga hannunsa, zube masa dubu d'ari Hajiya Rabi tayi tace, "Boka daman ni zuwa nayi inyi godiya dan buk'atata ta biya fiye da yarda nake zato".
Fashewa da wata iriyar dariya mara dad'in ji yayi yace, "ai ni ban tab'a gazawa a aikina ba, duk wanda ya zo wajena sai ya samu biye buk'atarsu, zaku iya tafiya yanzu, ku dai tabbatar kuyi yarda nace to ba tantama zaku ga aiki da cikawa", yana fad'in haka suka tashi suka fice da baya da baya kamar yarda suka shigo.
Suna cikin tafiya Hajiya Rabi ta kalli mum d'in Latifa tace, "ki sa a ranki kamar Latifa ta gama mallakar sa sam kar kiyi shakkan hakan, dan tabbas aikinsa yankan wuk'a ne dan yayi min kuma na sami biyan buk'atata, ke dai ki tabbatar tayi yarda yace ba tare da kuskure ba".
Jinjina kai tayi tace ", ai ni dama sam ba shakkar aikinsa a raina, balle yanzu da na gama sallama masa, wai akan me yayi miki aiki dan a iya sanina baki da matsala, kina juya kambunki yarda kike so ?".
"Tabbas maganarki haka ne, yanzu ki bari mu fita daga daji nan muje gida zan fad'a miki".Ci gaba da tafiya sukayi har suka isa bakin titi inda direba ke jiran su, yana ganin su ya bud'e musu seat d'in baya, kana ya shiga ya tada motar suka bar wajen.
A b'angaren su Latifa kuwa bacci ne ya kama su bayan sun gama masha'arsu, baccinsu suke cike da kwanciyar hankali.Basu farka ba sai yamma sosa, fitowa sukayi falo bayan sunyi wanka sun sa kaya.Suna fitowa wayarsa dake kan had'add'en center table d'in dake falon ya hau k'ara, d'aukan wayar yayi yana ganin sunan wanda ya bayyana kan screen d'in wayar ya saki wani k'ayatattan murmushi, kana yayi picking d'in wayar yace, yana d'aukan wayar wacce tayi kiran sa ta fara magana da cewa, "ka zo yanzun nan ina neman ka".
"To first love ga ni nan zuwa", yana fad'in haka suka katse wayar.Juyowa yayi ya kalli Latifa wacce ta ji wani irin haushi da kishi sun dirar mata a ranta yace, "first love na kirana ki zauna ki ci wani abu, idan kin gama ki fito direba ya maida ke gida zan fad'a masa idan na fita", yana fad'in haka ba tare da ya jira abin da zata ce ba ya sa kai ya fice daga falon da sauri...
Fatinku ce 😘😍
https://www.facebook.com/Zauren-Brilliant-Writers-Pans-111419110389493/
*🅱️RILLIANT WRITERS ASSO🖊️*
{Pen of freedom, home of magnificent and exceptional writers}
*🧕WAYAYYAR MACE🧕*
*NA*
*FATIMA USMAN*
*BISMILLAHIRRAHMANIR RAHIM*
Page 23 - 24
Jagwab ta zauna kan kujera tana jin wani irin abu ya tokare mata a mak'oshi.Tabbas zuciyarta san sa take, tun da take harka da maza bata tab'a shiga irin wannan yanayin ba dan sunyi magana ko sun kula wata mace ba.A yau bambance tsakanin aya da tsakuwa, tabbas shi bilhakk'i san sa take ba kamar na sauran samarinta ba wanda na rud'i ne da kuma sha'awa ne.Lallai ya zama dole taje ta samu mum d'inta sunyi gaggawar zuwa inda za'a rik'e mata shi, ya daina huld'a da duk wata mace, tana so ya kasance da ita kad'ai.Tana fad'in haka tayi saurin tashi ta fice daga falon, ko ta kan abincin da yace ta ci bata bi ba.Tana fita harabar gidan direban da ke zaune kusa da maigadi yayi saurin tashi ya k'araso ya bud'e mata wata had'add'iyar mota ta shiga ta hakimce, ya shiga ya ja suka fice daga gidan.
A b'angaren su mum d'inta suna isa gidan Hajiya Rabi, ta k'walawa mai aikinta kira ta iso da sauri ta tsuguna tace, "ga ni Hajiya".
A wulak'ance ta kalle tace, "je ki kawo mana abinci da drinks", tana fad'in haka da sauri ta tashi ta shiga kitchen ta jera abinci da drinks tare da cups kan tray.
"Ke waya ce miki ki kai kan dining ?", ta fad'i haka a hasale ganin ta nufi dining da tray d'in.Da sauri ta juyo ta ajiye kan centre table d'in dake falon.
Kallon ta tayi a wulak'ance tace, "da fatan kin gyara min d'aki ki kuma wanke band'aki da k'yau dan na lura kwana biyu kina saken da kika ga dama a aikinki, ki sani akwai mutane da yawa masu neman damar da kika samu basu samu ba, dan haka ki kiyaye idan ba so kike in sauya ki da wani ba".
"Eh Hajiya nayi su da k'yau, kiyi hak'uri zan kiyaye insha Allah".
"Kar ma ki kiyaye idan baki kiyaye ba ai dai kinji abin da na fad'a miki, tashi ki bawa mutane waje", tana fad'in haka ta mik'e ta fita tana takaicin irin wulak'ancin da ake yi mata dan kawai basu da shi, tana aikin da zata taimaki kanta su samu abin da zasu ci ita da marayun 'ya'yanta.
Bayan sun gama cin abincin ta Hajiya ta dubi mum d'in Latifa tace, "kin san me wai kama ta *Wayayyar mace*,wacce ba abin da wata mace zata nuna min, ace wai za'ayi min kishiya", ta fad'i haka cike da takaici zuciyarta nayi mata wani irin ciwo".
Zabura tayi tare da zaro ido tace, "kishiya kuma, garin yaya kika bari hakan ya faru".
Wani gwauran numfashi ta sauke tace, "tsinannun 'yan uwansa ne suka sa shi a gaba wai sai ya auri wata 'yar uwarsa wacce ta tsofe a gida ba mashinshinni, shine suke san lik'e masa ita dole, ganin haka yasa nayi gaggawar zuwa wajen wannan bokan yayi min maganinsu, in fad'a miki yanzu shiru kake ji, duk sunyi fatali da wani zancen auren, ahalin yanzu fantamawata nake yarda nake so, ba mai sa min ido da kuma takura min ni da gidan mijina dan na sa an rufe min bakunan 'yan banza", tana fad'in haka ta mik'a mata hannu suka tafa tare da k'yalk'yalewa da dariya.
"Hakan da kikayi shine daidai da kikayi maganinsu tun da wuri", mum d'in Latifa ta fad'i haka bayan sun tsagaita dariyar da suke.
"Ke dai bari ai da ni suke maganar, sun d'auka ni k'anwar lasa ce, sun d'auka ni irin bagidajun matan nan ne masu d'aukar wargi daga dangin miji, wallahi ba wanda ya isa ya nuna min iko akan mijina da kuma gidana daga cikinsu", tana fad'i haka suka sa shewa tare da k'ara tafawa...
Fatinku ce 😘😍
https://www.facebook.com/Zauren-Brilliant-Writers-Pans-111419110389493/
*🅱️RILLIANT WRITERS ASSO🖊️*
*🧕WAYAYYAR MACE🧕*
*NA*
*FATIMA USMAN*
*This page is for u dear Asmeenat Zeeyan, marubuciyar shahararren littafin nan mai cike da ilmantarwa, fad'akarwa da kuma nishad'antarwa wato MAZA (Allurar guba), Allah ya k'ara basira da d'aukaka luv u so much dear 🥰🥰🥰👍*
*BISMILLAHIRRAHMANIR RAHIM*
Page 25 - 26
Dukkansu k'yalk'yalewa da dariya sukayi, Hajiya Rabi tace, "ai da ni suke maganar shegu wahalallu kawai, sun d'auka zan zauna in sa musu ido suyi yarda suka dama akan mijina da kuma gidana, dan tsabar shishshiginsu da munafincinsu zasu wani zai ce ya k'ara aure, basu san cewa wannan gidan mallakina ne ni kad'ai ba wacce ta isa ta shigo, kai ni fa ko uwar kishiyata ba'a haifa ba balle ita kishiyar tawa", k'ara mik'a mata hannu tayi suka tafa suna dariya, Mum Latifa tace, "ai ni ina ganin tsantsar wauta da gidadancin wasu matan da ke tsaya sanya ayi musu kishiya, yarda kai ya waye yanzu ai wallahi yanzu duk wacce kika ga sa kishiya sam ba *WAYAYYAR MACE* ba, duk.macen da ta waye bazata tab'a yarda da wata aba kishiya, ai wannan sai kidahuman mata wad'anda rashin wayewa ke damun su", haka suka shantake suna shan hirarsu sai shewa suke.
Direban na parking ya fito ya bud'e mata k'ofa ta fito, zuciyarta a cunkushe ta shiga gidan nasu.Mum d'inta wacce ita ma bata jima sosai da dawowa ba na kishingid'e kan three seater ta shigo falon.
"Lafiya kuwa na gan ki haka", Mum d'inta ta fad'i haka ganin fuskarta sam ba walwala.
Wani gwauron numfashi ta sauke tace, "Mum ai dole ki gan ni cikin wannan yanayin, dan zuciyata cike take da takaici...", nan ta fad'a mata duk abin da ya faru ta fad'a mata ta k'are da cewa, "dan haka Mum ina san kiyi gaggawar zuwa inda kika ce zaki je, a cire masa so da sha'awar kowacce mace sai nawa, ya zamanto idanunsa sun rufe daga kallon wacce mace sai ni, na zama ni kad'ai ce tauraruwar zuciyarsa.
"Idan wannan ne damuwarki to ki d'auka baki da wata damuwa, ki sa a ranki kamar ki mallake shi kin gama, sai ki juya shi yarda kike so", tana fad'in haka ta sa hannu cikin handbag d'inta ta ciro k'unshin leda guda biyu ta shiga yi mata bayanin yarda zatayi amfani da su kamar yarda boka ya fad'a mata.
Cikin tsantsar farin ciki ta rungume ta ta tace, "amma Mum kin gama yi min komai dan ina bala'in san sa".
"Kar ki damu ai duk abin da na san zai sa ki farin ciki sai na nemo miki shi, ke dai ki tabbatar kiyi yarda na fad'a miki, yanzu ki tashi kije kiyi wanka ki huta".
"To Mum amma idan nayi wanka abinci zan zo na ci, dan yunwa nake ji".
"Ok je kiyi wankan ki dawo ga abincin daren da Humaira ta girka kan dining", tana fad'in haka ta tashi ta fice daga falon.
Zaune ta tarar da Humaira tana duba wani littafi dan gobe insha Allah za'ayi musu test akansa gobe insha Allah.D'ago kanta tayi ta kalle ta cike da takaici, harara Latifa ta zabga mata tare da jan tsaki.Murmushin yak'e kawai tayi gami da girgiza kanta, kana ta ci gaba da karatun da take.Cire kayan jikinta tayi ta d'ora towel ta shiga band'aki.
Zuciyar Humaira cike take da tsantsar bak'in cikin irin muguwar rayuwar da mahaifiyarta da kuma yayarta ke gudanarwa, dan sarai taji abin da suka fad'a d'azu, ta zo zata shiga falon ta cak ta tsaya bakin k'ofa, dan jin irin maganganun da ke fitowa daga bakin mahaifiyarsu.Da sauri ta bar wajen lokacin da taji tace ta tashi taje tayi wanka, zuciyarta cike da bak'in cikin irin mummunar rayuwar da mahaifiyarsu ta jefa yayarta.Wai shin duniya guda nawa take da har mutum zaiyi sak'aci da lokacinsa ?, shi fa lokaci wani abu ne mai matuk'ar mihimmanci ga mutum, wanda muddin ya yarda yayi asararsa to shi kenan ya tafi bazai dawo ba har abada, duk abin da ya riga ya wuce bazai tab'a dawowa ba har abada, mutuwa kuwa bata da lokaci da zarar ance lokacinka yayi, to baza'a k'ara maka ko da second d'aya ba, shi yasa ake san a kodayaushe mutum ya kasance cikin aikata alkairi, yarda ko mutuwa ta riske ka to baka da da na sani.
Wani gwauron numfashi ta ja tace, "Allah kai ne mai shiryar da bawa a duk lokacin da ka so, ka ganar da wannan bayi naka gaskiya, dan duk yarda na so su shiryu muddin bakai ka so ba, hakan bazai yiwu ba", tana fad'in haka ta ci gaba da karatun da take...
Fatinku ce 😘😍
https://www.facebook.com/Zauren-Brilliant-Writers-Pans-111419110389493/
*🅱️RILLIANT WRITERS ASSO🖊️*
{Pen of freedom, home of magnificent and exceptional writers}
*🧕WAYAYYAR MACE🧕*
*NA*
*FATIMA USMAN*
~Kuyi hak'uri da ji na shiru kwana biyu, luv u all my fans~
*This page is dedicated to u bro Hayat, Allah ya k'aro shekaru masu albarka*
*BISMILLAHIRRAHMANIR RAHIM*
Page 27 - 28
Zuciyarta fal da farin ciki dan ta san muddin Mominta ta sa abu a gaba bata karaya har sai taga bayansa, ta kammala wanka ta fito.Ta shirya cikin riga da skirt d'in English wears sun matse ta sosai, da sauri ta fice daga d'akin dan ji tayi cikinta na wani irin k'ugi saboda yunwa.
"Allah ya k'yauta ya kuma ganar da ke gaskiya", Humaira ta fad'i haka, kana ta tashi ta shiga band'aki dan d'ora alwala jin an fara kiran Sallar Magrib.
Cikin k'ank'anin lokaci ya isa gidansu, dan ba wani nisa tsakaninsu.Horn yayi gaban k'aton gate d'in gidan, maigadi ya taso ya wangale masa gate d'in ya shiga ciki.parking yayi a parking space d'in da ke had'add'iya kuma tsararrariyar harabar gidan wacce aka matuk'ar k'awatawa, duka mable ne a harabar gidan.Fitowa yayi ya nufi b'angaren Mahaifansa.
Wani irin k'ayataccen k'aton falon ya shiga bayan yayi sallama an ba shi izinin shiga.Wata mata ce zaune kan d'aya daga cikin luntsuma-luntsuman kujerun da ke falon wacce akalla zata kai shekara arba'in da takwas, amma idan ka gan ta bazaka ba ta wad'anda shekarun ba saboda hutu da ya ratsa ta, iyakar had'uwa matar ta had'u kana ganin ta ka sa naira ta zauna a jikinta, ga wani irin shiga da tayi na alfarma cikin wani tsadadden dakakken shadda wanda k'yawunsa ya bayyana tsadarsa, maroon in colour anyi masa wani irin had'adden d'inki doguwar riga, sai walwali take.Kawar da kanta gefe tayi bayan ya shigo falon alamar tayi fushi.
Da sauri ya k'araso ya zauna kusa da ita tare da rik'o hannunta yace, "dan Allah first love kiyi hak'uri, kar kiyi fushi bazan k'ara ba", ya fad'i haka yana marairaice fuska kamar zaiyi kuka.
Juyowa tayi ta kalle shi cike da kulawa tace, "ba komai son daman zolayar ka kawai nake banyi fushi ba".
"Yauwa first love ai daman na san bazaki iya fushi da ni ba".
"Au haka ma zaka ce, to nayi fushin", ta fad'i haka cike da zolaya, dukkansu dariya suka sa.
Gyara zama tayi bayan suka tsagaita da dariya tayi kiran sunansa "Abdul"
"Na'am", ya amsa mata tare da maida hankalinsa wajenta yana sauraran ta.
"Ni kam har yanzu baka samo yarinyar da kake so ba, ya kamata ka nemo matar aure ka yi aure, me kake jira wanda ya wuce kayi aure ?", Allah ya hore maka komai.
Da k'yar ya had'iyi yawu cikin tsananin damuwa yace, "ni fa har yanzu ban samu wacce ta dace na aura ba, dan Allah ku k'ara min lokaci insha Allah nan ba dad'ewa ba zan kawo muku wacce zan aura".
"A gaskiya ni ma son ina ma ina bayanta akan wannan maganar, dole ne ka nemo matar aure ka yi aure", dad d'insa saukowarsa kenan daga upstairs ya fad'i haka.
Sunkuyar da kansa yayi yana share zufa, zuciyarsa a cunkushe dan shi bai tashi yin aure yanzu ba.
K'arasowa yayi ya zauna ya kalle shi fuskarsa a d'aure yace, "na ba ka nan da wata d'aya ka kawo min wacce ka aura, idan kana san ci gaba da zama lafiya da ni da ganin walwalata, fakat na gama magana", yana fad'i haka ya tashi ya haura sama ba tare da ya saurari abin da zai ce ba.
"Ka ga ni dad d'inka ma baya bayanka, dan haka kayi k'ok'arin bin umarninsa".
"To amma dan Allah ki rok'e shi ya k'ara min lokaci kan lokacin da ya fad'a", ya fad'i haka a marairaice.
"Kar ka damu yanzu nan zanje na rarrashe shi insha Allah zai k'ara maka", tana fad'in haka ta tashi ta haura sama.Zuciyarsa a cunkushe ya tashi ya fice daga falon.
*Waye Abdul*
Muje zuwa next page d'in.
Fatinku ce 😘😍
https://www.facebook.com/Zauren-Brilliant-Writers-Pans-111419110389493/
*🅱️RILLIANT WRITERS ASSO🖊️*
{Pen of freedom, home of exceptional and magnificent writers}
*🧕WAYAYYAR MACE🧕*
*NA*
*FATIMA USMAN*
*BISMILLAHIRRAHMANIR RAHIM*
Page 29 - 30
AbdulHakeem Ibrahim Ahmad shine cikakken sunansa, mahaifinsa minister ne, amma ya sauka yanzu haka kasuwanci yake yi, hamshak'in d'an kasuwa ne, wanda ake damawa da shi a harkar kasuwanci a dukkan k'asar nan gaba d'aya.Matansa biyu, Hajiya Khadija uwargida sai kuma Hajiya Zainab, wacce ta rasu bayan ta haifi Abdul.
Marigayiya Zainab ita ce ta haifi Abdul, washe garin haihuwarsa ta rasu bayan ta dank'awa Hajiya Khadija shi k tace ta bar mata shi halak malak ko bayan ranta kar ta sake ya san ba ita ta haife shi ba, dan ta san zata rik'e shi amana tare da ba shi ingantacciyar tarbiyya.A daren ranan ta amsa kiran mahaliccinta (Allahu Akbar, kullun nafsin za'ikatul maut, Allah ya kyautata namu zuwan, ya kuma sa mu cika da imani, Ameen summa Ameen).Mutuwarta ta matuk'ar tab'a Hajiya Khadija, dan ta tabbatar ta rasa abokiyar zama tagari, tsawon zamansu ba'a tab'a jin kansu ba suna zamansu lafiya tare da fahimtar juna gwanin sha'awa, dan dukkanninsu *wayayyun mata* ne, masu halin kwarai wad'anda suka san rayuwa.Sam ba k'yashi ko bak'in ciki, ba kishin hauka irin na wad'ansu ballagazazzun mata masu rasa imaninsu saboda kishin banzansu (kalubale gare mu 'yan uwa mata, mu yi koyi da ummuhatil Muminina wato matan Annabin rahama (S.A.W), wajen yin halatacciyar kishi, mu daina haramtacciyar kishi mai sa ku saki hanya, daga baya kuma ya kai ku gidan nadama, Allah ya sa mu dace ya kuma ganar da mu gaskiya, Ameen).
Haka ta raina shi ta kuma dama ita Allah bai ba ta haihuwaba, hasalima saboda rashin haihuwarta danginsa suka masa akan ya k'ara aure ko ya samu haihuwa.Badan ya so ba suka aura masa Zainab wacce take cousin d'insa, mahaifinsa da nata uwa d'aya uba d'aya, dan ba dama yayi musu da su.Hajiya Khadija ce kasancewata *wayayyar mace* mai aji wacce ta san ta kan rayuwa, sam bata nuna damuwarta ba, ta saki ranta sam bata nuna alamun kishi ko haushi ba, hakan ba k'aramin k'ima da daraja ya jawo mata wajen danginsa har da shi kansa maigidan.Bayan auren amarya ta tare a gidan, sukayi zamansu lafiya kasancewa ita ma Zainab akwai hankali ga