Showing 21001 words to 24000 words out of 24918 words
Chapter 8 - WAYAYYAR MACE COMPLETE BOOK BY FATIMA USMAR (YAR NIGER).txt
tsantsar takaici bayan ta ja wani dogon numfashi ta ci gaba da cewa, "ina zama ya tashi daga inda yake zaune ya dawo ya zauna kusa da ni tare da zubo min mayun idanunsa, zabura nayi na tashi tsaye tare da ce mata sir me ye haka kuma.Lumshe idanu yayi ya bud'e kana yace min wai tun da ya gan ni ya kwad'aitu da ni, in amince masa komai nake so zai mallaka min, yana so na sosai a ransa, in dai har zan rink'a ba shi had'in kai, shi kuma yayi min alk'awarin duk abin da nake so kowacce irin buk'ata ce, shi dai fatansa na yarda da shi.Mutuwar tsaye kawai nayi zuciyata cike da tsantsar mamaki na k'asa ce masa komai, mik'ewa yayi ban ankara ba ya rungumo ni jikinsa, wata k'ara na saki gami da fizgewa a fusace na juyo nace masa daman haka halinsa yake, to ni Humaira na fi k'arfin abin da yake nufi da ni, sam bana cikin irin d'alibai da kake zato, dan haka kar k'ara gigin tab'a jikina", ina fad'in haka na juya na fice daga Office d'in raina ya kai k'ololuwar tashi, ina ji yana ta kirana amma nayi biris da shi nayi ficewata".
Flddo ido Zainab tayi cike da tsantsar mamaki tace, "lallai d'an adam mai wuyan gane hali, sam a haka bazaka d'auka haka halinsa yake ba, ashe a fili yake Musa a zuciya kuwa Fir'auna, Allah dai ya shirya masu hali irin nasa ya ganar da su gaskiya, ya kuma kare ki daga mugun nufinsa".
"Ameen summa Ameen".
"Kin ga direban ma ya iso", Zainab ta fad'i haka daidai lokacin da direban yayi parking gabansu.
"Maganar da kike zaki fad'a min sai gobe kenan".
"Eh sai gobe na fad'a miki duk da na so na fad'a miki yanzu".
"Ok Allah ya kai mu goben", tana fad'in haka suka tashi suka shiga motar, direba ya ja suka fice daga harabar makarantar.
Zainab na komawa gida ta zayyanawa Mamy komai.Kwarai Mamy tayi murna da farin ciki dan ta san Humaira da k'yawawan halayenta.
"Ba sai kin je ba an jima zan je na samu yaya mu tattauna akan maganar", Mamy ta fad'i haka cike da tsantsar farin ciki.
"To Mamy ni kuma zan iya zuwa gidansu yanzu ?", ta tambaye ta tana mai neman izinin ta.
"Eh zaki iya zuwa ki gaida min da mutanen gidan nasu".
"To Mamy zasu ji insha Allah", tana fad'in haka ta tashi ta shige d'akinta dan shiryawa...
*Pls kuyi manage da wannan, kwana biyu ina da uzurori ne, luv u all my fans 😘😍*
https://www.facebook.com/Zauren-Brilliant-Writers-Pans-111419110389493/
*🅱️RILLIANT WRITERS ASSO🖊️*
{Pen of freedom, home of magnificent and exceptional writers}
*🧕WAYAYYAR MACE🧕*
*NA*
*FATIMA USMAN*
*Inayiwa d'aukacin al'ummar Musulmai barka da Sallah, Allah ya maimaita mana ya nuna mana na bad'in bad'ad'a, aci nama sannu sannu fans dan tsaro ba tsoro ba 😂🤣🤣*
*BISMILLAHIRRAHMANIR RAHIM*
Page 65 - 66
Bata jima ba ta fito daman mayafi kawai ta shiga ta d'auka da handbag.Sallama tayiwa Mamy ta fita.Tana fita harabar gidan direba da ke zaune kusa da maigadi yayi saurin tashi da nufin ya kai ta, ta tare shi da cewa ya bari zata yi driving da kanta, ta isa inda motar ke fake ta shiga ta ja ta bar harabar gidan, shi kuma ya koma ya zauna kusa da maigadi suka ci gaba da hirar da suke.
Daidai k'ofar gidan tayi parking ta fito ta k'wank'wasa k'ofar da ke rufe, ta d'an d'auki lokaci tana k'wank'wasa k'ofar ba tare da an zo an bud'e ba, jimawa can taji muryar Humaira na cewa waye ?, amsa tayi da cewa ni ce besty, tana jin haka tayi saurin bud'ewa.
"Dan Allah besty kiyi hak'uri wanka nake yi, fitowata kenan kuma ba kowa a gidan kaya kawai na zura na zo na bud'e miki", Humaira tayi saurin fad'in haka lokacin da idanunta suka d'oru kan na Zainab.
Murmushi Zainab tayi tace, "kar ki damu besty ba komai wallahi", ita ma murmushi tayi ta kama hannunta suka shiga cikin gidan, suka shiga d'akinsu ita da Latifa.
Sai bayan sun zauna ta kalle ta sosai tace, "besty na dawo na fad'a miki maganar da nace zan fad'a miki ne, wato ba komai ba ne Yayana ne ya mato akanki, shine ya tuntub'e ni nace ya bari zanyi miki magana, yanzu ina san in ji ta bakinki, ke ma kin mato ne, ko da yake da alama ke ma kin mato dan na san yayana ba daga baya ba", ta fad'i haka cikin zolaya.
Fiddo idanunta tayi tace, "tab!, waya fad'i miki haka ?".
Girgiza kanta tayi tace, "a'a ba wanda ya fad'a min, amma ai labarin zuciya a tambayi fuska, ina lura da yanayinki lokacin da na ce ya mato akanki har da lumlumshe idanu saboda dad'in da ya mamaye zuciyarki"
"Hmmm!, to gaskiya fuskar tawa bata ba ki ainihin labarin da ke cikin zuciyata ba".
Maka mata hararaa tayi cikin wasa tace, "yarinya kar ki ce zaki ja mana aji fa, dan na san aji kawai kika ja mana amma tuni kika mato akanmu".
Girgiza kanta ta shiga yi tana cewa, "ba aji nake ja muku ba".
"To besty dan Allah yanzu mu aje wasa a gefe ki fad'a min gaskiyar abin da ke zuciyarki game da shi".
Ajiyar zuciya ta ja tace, "ki ban d'an lokaci zanyi tunani akai
Kallon ta tayi fuskarta na nuna rashin jin dad'i tace, "to amma dan Allah kar ki ja lokaci, dan a watan nan ake ce ayi komai", tana fad'in haka ta mik'e ta rataya jakarta tana cewa, "ni zan tafi insha Allah zai fad'a masa dan ni 'yar aike ce", juyawa tayi da nufin fita, da sauri Humaira ta kamo hannu rausayar da kanta tayi tace, "dan Allah kiyi hak'uri besty na san baki ji dad'in maganata ba, ba wai ina k'in Yayanmu bane, ina san dai nayi shawara ne tukun".
Juyowa tayi ta harare ta cikin wasa tace, "kya ce haka mana saboda nace bros ya mato akanki ne zaki wani ja mana aji, har da cewa wai sai kinyi tunani akai, a zatona ko albarkacina kya amince masa".
Murmushi mai sauti tayi tace, "besty badai mita ba, to kiyi hak'uri ki bar mitar haka insha Allah zuwa gobe zan sanar da ke, kin ji besty d'ina".
Wata hararar ta k'ara maka mata tace, "au ni ce mai mita, yo ai gaskiya na fad'a dan na tabbatar ke ma kin riga da kin mato kan bros, amma ina koma zan sanar da shi da ba ki amince ba tun wuri ya nemi wata".
A zabure ta kalle ta tace, "ni fa ban ce haka ba cewa nayi sai nayi tunani tukun".
Zainab bata lokacin da fashe da dariya ba har da rik'e ciki, sai da tayi mai isar ta kana ta kalle ta tace, "hmmm!, su besty ana so ana kaiwa kasuwa", tana fad'in haka dukkansu suka sa dariya.
"Ni zan tafi kuma insha Allah zai sanar da shi abin da kika ce", ta fad'i haka bayan sun tsagaita dariyar.Tare suka flta dan yi mata rakiya.
"Kin ga har zan tafi mum bata dawo ba idan ta dawo ki gaida ta ki ce Mamy ma na gaida ta", Zainab ta fad'i haka da fitowarsu tsakar gidan.
"Zata ji insha Allah", tana fad'in suka fice daga gidan.
Ranta fari kal ta dawo daga rakiyar ta, wani irin farin ciki ya mamaye zuciyarta, wani irin dad'i da sanyi ke ratsa zuciyarta.Da shigarta d'aki ta fad'a kan gado tana lumshe ido.Tun ranar da suka had'u soyayyarsa ta sa ta a gaba take wahalar da zuciyarta, rok'on Allah ta shiga yi da ya sa shi ma ya kamu da san ta, dan yarda soyayyarsa ta mamaye zuciyarta farar d'aya, tabbas zata shiga damuwa idan ya kasance so maso wani take.Ba shakka kamar yarda Zainab ta fad'a aji kawai take san jan, dan so tana san sa.Wani irin dad'i ne ke ratsa ta godiya kawai take ga Allah, zuciyata cike da nishad'i cikin wani yanayi na jin dad'i...
*https://www.facebook.com/Zauren-Brilliant-Writers-Pans-111419110389493/ WRITERS ASSO🖊️*
{Pen of freedom, home of magnificent and exceptional writers}
*🧕WAYAYYAR MACE🧕*
*NA*
*FATIMA USMAN*
*BISMILLAHIRRAHMANIR RAHIM*
Page 67 - 68
Zainab na isa gida bayan tayi parking ta fito daga mota, wayarta da ke cikin handbag d'inta ta hau ringing.Ba ta tare da ta tsaya d'agawa ba ta nufi k'ofar falon gidan.Zama tayi kan two seater d'in da ke falon ta ciro wayar da ke faman ringing daga cikin handbag d'inta, ta dubi sunan wanda ya bayyana akan screen d'in wayar, murmushi tayi ganin wanda ke kiran ta kana ta d'aga wayar.
"Ina kika shiga ne ina ta kiran ki baki d'aga ba ?", tana d'agawa aka tambaye ta daga can d'ayan b'angaren.
"Afuwan bros ina parking kiranka ya shigo, shi ne na bari sai da na shiga falo"
"Ok to yaya kin isar da sak'ona kuwa ?", ya k'ara tambayar ta.
"Eh dawowata kenan daga gidansu dan ban samu damar sanar da ita a Makaranta ba ".
"Yauwa shi yasa nake ji da ke da fatan dai na dace", ya fad'i haka zuciyarsa cike da fargabar abin da zai fito daga bakinta.
"Ka bari idan ka zo zan sanar da kai yarda muka yi da ita",
"Ga ni nan tafe yanzun nan", yana fad'in haka ya katse wayar bai jira abin da zata ce ba.Ita kuwa yana katse ta k'yalk'yale da dariya dan ya matuk'ar ba ta dariya jin yarda ya rud'e.
"Ikon Allah me ya faru kike dariya ke kad'ai ?", Mamy da fitowarta kenan daga kitchen.
"Bros ne ya ban dariya Mamy ", ta fad'i haka cikin dariya.
"Ke kuwa dariyar me ya ba ki ?".Tsagaita dariyar tayi ta fad'a mata yarda suka yi da shi a waya ta k'are da cewa, "rud'ewar da yayi ne ya ban dariya ",tana fad'in haka ta k'ara sa dariya.
Murmushi mai sauti Mamy ta saki tace, "yanzu rud'ewar da yayi ne kike yiwa dariya, to kamar a kunnensa sai na fad'a mas...".
"Ba sai kin fad'a min ba Mamy na ji komai", Abdul da ke tsaye bakin k'ofar falon ya katse ta tun kafin ta kai ga kammala abin da tayi niyyar fad'a.Su duka juyowa suka yi suna kallon sa.
Zainab ce tayi saurin cewa, "la!, bros ka ce har ka iso, lallai su bros an k...", bata kai ga k'arasawa ba tayi gum da bakinta dan wani irin harara da taga yake zabga mata.
K'arasawa yayi cikin falon inda take zaune ya kama kunnenta yace, "na ga alama yanzu ki zamar da ni kamar sa'anki, to daga yau idan kika k'ara yi min dariya bulala zanyi miki", ya fad'a tare d'an murd'e kunnen nata.
"Wayyo Mamy kin ga shi ko", ta fad'i haka tana cuno bakinta cike da shagwab'a.
"A'a ni ba ruwa tsakaninku ne kin ga tashina ma zan je na dubo girkin da nake", Mamy ta fad'a tana dariya, tana dariya ta tashi ta shiga kitchen.
Kallon sa tayi tana cuno bakinta tace, "to na fasa ma fad'a maka yarda muka yi da ita".
Da sauri ya rik'o hannayenta yace, "dan Allah kiyi hak'uri duk cikin wasa ne fa, kin ji 'yar siririyar k'anwata", yana fad'in haka suka sa dariya.
"Na k'i wayon", ta fad'a tana nok'e kafad'arta bayan sun tsagaita dariyar .
"Please lil sis kiyi hak'uri ki fad'a min kin ji 'yar siririyar k'anwata", ya fad'i haka yana langwab'e kansa.Dariya ta sa ganin yarda ya langwab'e kai.
Kwashe komai tayi ta fad'a masa bayan sun dakatar da dariyar ta k'are da cewa, "ka kwantar da hankalinka bros insha Allah ita ma tana san ka zata amince da Kai, dan na ga alama haka tarada ita".
Saki d'an murmushin jin dad'i yayi yace, "Allah ya amshi addu'arki".
"Ameen summa Ameen", Mamy wacce fitowarta daga kitchen kenan d'auke da tray d'in abinci ta furta haka.Da sauri Zainab ta tashi ta je ta karb'e tray d'in daga hannunta ta nufi dining.
Kallon sa Mamy tayi bayan ta zauna tace masa kar ya damu zata je wajen su dad d'insa su tattauna akan maganar, za'a je a nemo masa izinin zuwa wajenta su gana su fahimci juna tukun, ya so daga baya sai ayi maganar aure.Tashi tayi tace zataje tayi wanka, tana gamawa zata je wajen nasu suyi maganar.Shi ma tashi yayi ya fice daga falon zuciyarsa cike da fatan samun dacewa, Zainab kuwa tana ajiye tray d'in kan dining ta shige d'akinta...
https://www.facebook.com/Zauren-Brilliant-Writers-Pans-111419110389493/
{Pen of freedom, home of magnificent and exceptional writers}
*🧕WAYAYYAR MACE 🧕*
*NA*
*FATIMA USMAN*
*BISMILLAHIRRAHMANIR RAHIM*
Page 69 - 70
Dad d'insa na dawowa bayan yayi wanka ya huta ta zayyana masa komai ta k'are da cewa, "yanzu abin da ya saura shine gidansu za'a je a gabatar da musu da cewa, d'anmu ya ga 'yarsu yana so muna nema masa auranta, dan kar ya kasance akwai maganar wani akanta".
Gyad'a kai yayi cike da gamsuwa yace, "tabbas haka ya kamata ayi, nayi farin ciki sosai dan kwarai nake son ganin Abdul ya aje iyal...", Sallamar da Mamy tayi ne ya sa ya katse maganar, a tare suka amsa mata.
Bayan sun gaisa ta bayyana musu maganar da ta kawo ta.Wayarsa ya d'auka yayi kiran wansa wanda suke uba d'aya ya sanar da shi komai, cewa yayi ga shi zuwa gida yanzu.Bai wani jima ba ya iso, nan suka taru suka tattauna kan maganar, suka yanke shawarar gobe insha Allah zasu je gidan.Washe garin ranar kawu Sani wato wan dad da maigidan Mamy kuma aminin dad suka je gidan bisa jagorancin direban gidan Mamy.
Daidai k'ofar gidan yayi parking suka fito.Yaro suka aika da yayi musu sallama da maigidan.Bai dad'e ba ya fito yace ga shi nan fitowa.
Jim kad'an da fitowar yaron ya fito, basu hannu yayi suka yi musabaha.Bud'e musu d'akin da yake sauke bak'i yayi suka shiga.Fita yayi bayan sun zauna tare da cewa yana zuwa.Humaira ce ta shigo d'akin bayan tayi sallama sun amsa mata, d'auke da tray ta yafa babban mayafi kan atamfar da ke jikinta.K'anta na kasa cikin girmamawa ta gaida su, ajiye tray d'in tayi a gabansu ta tsiyaya musu ruwa cikin cups ta mik'awa kowannensu cike da nutsuwa.Tana mik'a musu ta tashi ta fice daga d'akin.
"Da alama munyi sa'ar suruka", kawu Sani ya fad'i haka da fitarta cikin jin dad'i.Yana rufe baki Abba yayi sallama ya shigo d'aki.
"Dan Allah kuyi hak'uri na bar ku kuna jira", Abba ya fad'i haka bayan ya zauna.
"Ba komai kar ka damu", kawu Sani ya fad'i haka murmushi d'auke a fuskarsa.
Gyara zama kawu Sani yayi ya sanar da shi abin da ke tafe da su tare da yi masa gamsashen bayanin kan zuri'arsu ya k'ara da cewa, "ba ma san a ja wani dogon lokaci, idan ba maganar wani akanta".
Gyad'a kai yayi bayan ta gama sauraran bayaninsa cike da gamsuwa yace, "tabbas ba maganar kowa akanta, yana damar zuwa su ga juna, idan ta amince tana san sa shi kenan Allah dai ya tabbatar da alkairi", dukkansu suka amsa da Ameen Ameen.
Kawu Sani ne ya fiddo kud'i daga aljihun rigarsa ya ajiye gaban Abba.K'arewa kud'in kallo yace, "a'a na gode sosai, kuyi hak'uri bazan karb'i kud'in nan ba".
Alhaji Ahmad ne wato maigidan Mamy yayi saurin cewa, "haba dai idan kayi haka sai mu ga kamar ba mu samu karb'uwa ba ne ", badan ya so ba ya amince ya d'auki kud'in.Sallama suka yi cike da ganin dattakon juna suka tashi suka fice tare dan yi musu rakiya...
https://www.facebook.com/Zauren-Brilliant-Writers-Pans-111419110389493/
{Pen of freedom, home of magnificent and exceptional writers}
*🧕WAYAYYAR MACE 🧕*
*NA*
*FATIMA USMAN*
*Afuwan da ji na shiru kwana biyu, luv u all my fans 😘😍*
*BISMILLAHIRRAHMANIR RAHIM*
Page 71 - 72
Yana dawowa daga rakiyar su yayi kiran ta ya zaunar da ita ya bayyana mata komai ya k'are da cewa, "ni dai na ba shi izinin zuwa wajenki ku gana da juna, dan kwarai na yaba da dattakon magabatansa", shiru yayi yana sauraran abin da zata ce.
Kanta a sunkuye tace, "Abba ai ni ban da abin da zai ce, tun da ka amince ni ma na amince da ya zo d'in", tana rufe baki ummanta ta shigo falon ba tare da tayi sallama ba, wuce su tayi ko kallan inda suke bata yi ta shiga bedroom d'inta.
Girgiza kansa Abba yayi cike da takaicin halin matar tasa, ace mace bata komai sai gantali, idan ta fita tun safe sai fad'uwar rana zata dawo, hakan na matuk'ar yi masa ciwo a zuciya, amma babu yarda zai yi, yana k'arfin halin yi mata magana zata hayyak'o masa, bai sa me yasa ba ya ke shakkar ta, baya iya maida mata magana ba.
Murya a sanyaye cikin yanayin damuwa Humaira tace, "Abba dan Allah ka daina sanya damuwa a zuciyarka, wani ciwon zai iya kama ka, tabbas kowana bawa akwai ta inda Allah ke jarabta shi, ka fawwalawa Allah komai shi ne zai yi maka maganin komai".
Naunauyan ajiyar zuciya ya sauke yace, "tabbas haka ne na yarda da cewa nawa jarabtar kenan, kar ki damu tuni na daina sa damuwa cikin zuciyata, a kullum addu'a nake Allah ya shirya ta ya ganar da ita gaskiya".Muryarta a raunane tace "Ameen Abba".
Kud'in ya ciro daga aljihunsa ya nuna mata tare da cewa, "kin ga wannan kud'in su suka bada shi, na so maida musu amma suka k'i yarda, dan ba ni da tabbacin zaki amince da soyayyarsa, dan idan kika ce ba ki so bazan yi miki auran dole ba, yanzu shawarar da na yanke shi ne zan ajiye kud'in baza mu tab'a ko kwandala ba a ciki ba tukun,, yanzu ki tashi ki je ki ci gaba da girkin da kike yi kafin nayi kiran ki, Allah yayi miki albarka yayi ya kuma tabbatar da alkairi",Tashi tayi ta koma kitchen, shi kuma tashi yayi ya shiga bedroom d'in ummanta.
Tarar da ita yayi b'ararraje kan gado, kiran sunanta yayi ba tare da ta amsa ba ta kalle shi fuskarta a tsuke tace, "kunne ne ke ji ai ina sauraran ka".Tabbas ransa ya kai