Showing 12001 words to 15000 words out of 24918 words

Chapter 5 - WAYAYYAR MACE COMPLETE BOOK BY FATIMA USMAR (YAR NIGER).txt

kiran k'anin nasa.

Zaune suke a had'ad'an falonsu suna yiwa twins d'insu dariya kan musun da suke tun da suka ji haihuwar yayarsu, cikin nishad'i da annushuwa cike da tsantsar farin ciki.

Abbansu ne ya tsagaita dariyar da yake tare da gyaran murya, dukkansu shiru suka yi suka maida hankalinsu gare shi", haba my cute twins naga duk kamanninku d'aya, menene na musu akan da wanda baby yake kama daga cikinku"

"Haba Abba ni fa na san da ni yake kama, dan na fi ta kama da Yaya", Hussaini ya fad'i haka cike da hak'ik'ancewa.

"To shine aka ce maka da shi babyn yake kama, to ni na ga ma dukkaninku kamanninku d'aya, to menene kuma na musun", Ummansu ta fad'i haka cikin dariya.

"Haka ne kuwa Umma, ni fa Umma Allah Allah nake gari ya waye mu tafi Kano lafiya (da ke su a Kaduna suke da zama), nayi tozali da my cute baby", Hassana ta fad'i haka cike tsantsar farin ciki.Wayar Abbansu da tayi ringing ce ta katse hirar tasu, da sauri ya d'auka ganin sunan wanda ke yawo kan screen d'in wayar.

Shiru ne ya biyo baya bayan sun gama gaisawa."Yaya ya naji ka yi shiru", ya fad'i haka jin ya d'au mintina bai ce komai ba".

Wani gwauron numfashi ya ja yace, "dama ina san nayi maka wata tambaye wacce nake so ka ba ni amsa".

"Ina sauraran ka Yaya insha Allahu idan na sani zan fad'a maka".

"Kai ne wani ya ba ka aron kaya to sai ya zo karb'an kayansa, zaka ba shi ko zaka hana shi ?"

"Haba dai Yaya zan ba shi man tun na san ba nawa ba ne"

"To haka nake so ku yi tawakkali ku rungumi k'addara, Allah da ya ba ku Zainab ya karb'i abarsa, Allah dai ya bamu hak'uri da juriyar rashin ta", yana fad'i haka ya katse wayar cike da jimami, zuciyarsa cike da tsantsar tausayin d'an uwa, dan ya san irin matsanancin kaunar da suke yiwa 'yar tasu.

Shi kuwa rintse idanunsa yayi ba sai nanata "innalillahi wa'innailahir raji'un yake.Cike da tsoro matsananci da fargaba dukkansu suka yi riga rigen tambayar sa, "Me ya faru ?"

Cike da daurewa yana k'ok'arin matse hawayen da ke san zubo masa ya sanar da su, bayan ya nusar da su tare da yi musu nasiha mai ratsa zuciya, akan su yi tawakkali.Ai yana gama fad'a twins suka zube kasa suna kuka, su kuwa iyayen nasu wasu zafafan hawayen suka shiga zubarwa.Cike da juriya dan shi ma k'arfin hali kawai yake, ya rik'o su zuwa jikinsa ya shiga rarrashin su.Da k'yar ya shawo kansu suka yi shiru.

Kallon su yayi idanunsa jajir cikin taushin murya yace, "ku yi shiru kukan ya isa haka kar wanda ya k'ara, addu'a take buk'ata gare mu", cikin dauriya ya fad'i haka dan shi ma ji yake kamar ya rushe da kukan.A daren kam ba wanda ya rintsa daga cikinsu, raba dare suka yi suna nema mata gafara wajen Ubangiji (S.W.T).Washe gari k'arfe shida daidai suka yi sammakon zuwa Kano.

Tafiyar awa biyu ne ya kawo su Kano, tarar da gidan suka yi cike da jama'a 'yan uwa da abokan arziki, dan kafin safiya labarin rasuwar ya gama kewaye gari, har an had'a ta.Haka dai aka mik'a ta makwancinta na gaskiya bayan sun yi mata addu'ar sallama kark'ashin rakiyar d'imbin al'ummar musulmai...



Fatinku ce 😘😍
*BRILLIANT WRITERS ASSOCIATION*
( _pens of freedom, home of exceptional and magnificent writers_)


https://www.facebook.com/Zauren-Brilliant-Writers-Pans-111419110389493/


*🧕WAYAYYAR MACE🧕*

*NA*

*FATIMA USMAN*


*BISMILLAHIRRAHMANIR RAHIM*


Page 43 - 44


Zaune take a falo tare da d'imbin 'yan uwa da abokan arziki cikin alhini da jimamin wannan rashin da suka yi.Mahaifiyar marigayiyar ita ma na zaune tana k'ok'arin b'oye tashin hankalin da damuwar da take ciki, ta girgiza kwarai da gaske, ba k'aramin k'ok'ari tayi ba wajen danne firgici da razanin da ta shiga.Ita ma Khadija haka yake wajenta, lokacin da ta ga an fito da ita za'a kai ta makwancinta na gaskiya.Hussaina kuwa kasa b'oye nata tayi, sai da ta rushe da kuka tana cewa, "wayyo shi kenan Aunty ta tafi ta bar ni bazan k'ara ganin ta ba, way...", Ummanta ce tayi saurin rufe bakinta da hannunta tana girgiza mata kai tace, "ambatan Allah ne ya kamata ya fito daga bakinki ba wannan furucin ba, addu'a ya kamata kiyi mata ba kuka ba, dan ita mamaci ke buk'ata", ci gaba da rarrashin ta tayi tana tunatar da ita ayoyi da hadisai na tawakkali da hak'uri.

Kallon su Khadija take cike da tausayi mai tsanani, ko shakka babu dole Hussaina ce tayi kukan, sun shak'u matuk'a suna kaunar junansu sosai, su kad'ai Allah ya bawa iyayensu, Marigayiyar ita ce ta fari sai su twins d'in.Tun tasowarsu take musu wani irin kulawa da tattali har kawo girmansu, tana matuk'ar ji da su tamkar tsoka d'aya a miya, sam bata san abin da zai tab'a su, tabbas wannan ya isa dalili mai k'arfi da zai sa tayi kuka mai yawan gaske na rashin 'yar uwa Yayarsu mai tsananin kaunar su.

A cikin kwanakin bakwan da aka yi ana amsar ta'aziyya, kullum gidan cike yake da jama'a.A kwana bakwan mahaifan marigayiyar suka koma amma ban da Hussaina, Khadija ce ta nemi alfarmar da su bar ta har ayi arba'i, nan take suka amince jin ta suke tamkar d'iyarsu Zainab.Ita kuwa Hussaina taji dad'in haka sosai, dan sam bata san tayi nesa da AbdulHakeem (sunan da aka sakawa babyn).

A ranar arba'in da suka zo suka so komawa tare da ita, amma ganin ta shiga tsantsar damuwa suka ce ta zauna ta taya Auntynta rainon babynsu.Nan take wani irin farin ciki ya kama ta, nan take damuwar tata ta gushe, jin bazata yi nesa da babynta ba, wanda ta d'auki san duniya ta d'ora masa, sam bata san tayi nesa da shi.

Haka dai zamanta ya ci gaba da kasancewa a gidan, suna nuna masa wani irin kulawa da tattali, tana dawowa daga school rainonsa ke dawo hannunta, sam bata san abin da zai tab'a shi.Haka suka ci gaba da rayuwa tare, tana matuk'a girmama Khadija ta d'auke ta tamkar marigayiyaYayarta, kamar yarda ita ma ta d'auke ta tamkar k'anwata.Kullum cikin yiwa Marigayiyar addu'a suke, tare da sauke mata Alqur'ani mai girma duk shekara.Shi kuwa gina masallaci yayi da niyyar ya zama Sadakatul Jariya gare ta, Khadija ce ta ba shi shawarar haka (Allah na rok'e ka had'a mu da kishiya mai k'yakkyawar zuciya irin ta Khadija, Ameen summa Ameen).



Fatinku ce 😘😍
*BRILLIANT WRITERS ASSOCIATION*
( _pens of freedom, home of exceptional and magnificent writers_)


https://www.facebook.com/Zauren-Brilliant-Writers-Pans-111419110389493/


*🧕WAYAYYAR MACE🧕*

*NA*

*FATIMA USMAN*


*This page is for u my Suruka Mugirat Musa marubuciyar LAHANI, Allah ya k'ara basira da d'aukaka, ina yin ki my Suruka irin sosai d'in nan 🥰😍👍*


*BISMILLAHIRRAHMANIR RAHIM*


Page 45 - 46


Haka rayuwarsu ta ci gaba da kasancewa suna tattali da ririta shi, hakan bai lalata shi ba, domin yaro ne mai hankali gami da nutsuwa.Haka ya girma a cikin wannan ingantacciyar rayuwa, yana samun cikakkiyar kulawa daga kowannensu, duk abin da yake muddin abin ya dace sai sun nema a ba shi, duk da ririta shi da suke bai sa sun sangarta shi ba, suna k'ok'arin kwab'ar sa a duk lokacin da yayi abin da bai dace ba.

Yana da shekara goma a duniya, Allah buwayi gagara misali, mai yin komai a duk lokacin da ya so, ya bawa Hajiya Khadija juna biyu.Sadak'a da salloli suka rink'a yi na godiya, haka ma Hussaina (wacce tuni tayi aure, aminin Daddyn Abdul take aure har da d'anta d'aya) da duk dangi tare da masoyansu su taya su farin ciki.Cikin na da wata tara ta haifo sankaceceyar 'yarta k'yakkyawar gaske, sak marigayiya Zainab, shi kuwa Abdul cike yake da murnar an haifo masa baby ya samu k'anwa.Ranar suna babyn ta ci sunan marigayiya wato Zainab, wanda hakan zab'in Khadija ne.Hakan ya matuk'ar farantawa Hussaina da iyayenta rai, suka k'ara ganin k'ima da mutuncinta.Wani irin so da tattali babyn take samu daga wajen Abdul da Hussaina da kuma sauran dangi musamman iyayen marigayiya, dake ba wani nisa tsananinsu hasalima a unguwa d'aya suke, wajen kullum sai Hussain ta zo ganin babyn, tana matuk'ar tattalin ta tare da nuna mata zallar kauna, sam bata san ta ji kukanta.

Watanni sun gushe, shekaru sun tafi, Abdul ya kai shekaru goma sha takwas, ita kuma Zainab wacce suke kira da little shekara rta takwas, tuni little ta saba da Hussaina wacce suke kira da Mamy sun shak'u da ita sosai, tun tana zuwa gidanta tayi kwana biyu har ta kai ta koma can da zama,haka Hajiya Khadija ta had'o mata dukkanin kayayyakinta ta rik'e su tare da d'anta, lokacin shekararsa goma sha hud'u.

Lokacin ya gama Secondary ya nacewa Abbansa shi ya fi san ya fita waje yayi karatunsa na Jami'a.Hak'uri ya ba shi akan ya fi san yayi karatunsa anan dan baya san yayi nesa da shi.Bayan sun tashi daga falon da daddare, Mummy wato Hajiya Khadija bayan sun koma d'aki, sun yi komai kamar kullum kafin sun kwanta, ta kalle shi tace, "ni kam Abban Abdul ina san muyi magana kan karatun Abdul ", tana fad'in haka tayi shiru tana sauraran abin da yace.

"Ina sauraran ki ya kuma kika yi shiru", ya fad'i haka jin tayi shiru.

Ajiyar zuciya ta sauke kana ta ci gaba da cewa, "ni a ganina ka bar ya tafi kasar wajen, na san abin da kake gudu kana tsoran kar ya je can tarbiyyarsa ta gurb'ata, kayi hak'uri ka bar shi ya tafi mu dage da addu'a insha Allah ba abin da zai faru sai alheri.

Wani dogon numfashi yaja yace, "to shi kenan na amince Allah ya sa hakan shi ya fi alkairi".

Da sauri ta rungumo shi zuwa gare ta cike da farin ciki ta kank'ame shi tace, "Ameen summa Ameen, na gode sosai da ka fahimce ni".

Shi ma k'ara kank'ame ta tayi a k'irjinsa yace, "kar ki damu uwargidanta matar kwarai, kin fi k'arfin haka a wajena", yana fad'in haka ya d'ora lips d'insa kan nata, daga nan fa labarin ya sha bambam suka lula duniyar ma'aurata.

Washe gari farin ciki sosai Abdul yayi da suka sanar da shi.Nasiha sosai suka yi masa akan yayi abin da ya kai sa wato karatu.Haka dai aka shirya masa ta tafi tare da abokan nasa classmates d'insa, daman su suka kwad'aita masa fita wajen karatu.

A can ne fa suka lalace idonsu ya bud'e da neman mata.Da farko shi Abdul sam bai bi ra'ayinsu ba, dan yana kan nasihar da iyayensa suka yi masa, amma da yake yana tare da tantirai gogaggun 'yan bariki, sai da suka yi galaba akansa, ta hanyar sa shayar da shi maganin tada sha'awa masu k'arfi kullum ba tare da saninsa ba.Dalilin haka shi ma ya zamo manemin mata har ya zamo masa jiki.Cikin wannan halin suka had'a masters suka dawo gida Nigeria.

A b'oye yake neman mata sam bai bari iyayensa sun sani ba, can gidansa da Abbansa ya mallaka masa yake kai matan.Kwatsam Abbansa ya bijiro masa da maganar aure, wanda shi a lokacin bai ga macen da yake so ya aura ba.Haka ya d'au lokaci ba tare da ya samu mafita ba, shi kuma Abban nasa bai k'ara bijiro masa da maganar ba, ganin haka ya shiriritar da magana.Ganin har watanni sun shud'e bai kawo musu matar aure, ya sa ba shi lokaci ko kuma ya ba shi zab'insa...



Fatinku ce 😘😍
*BRILLIANT WRITERS ASSOCIATION*
( _pens of freedom, home of exceptional and magnificent writers_)


https://www.facebook.com/Zauren-Brilliant-Writers-Pans-111419110389493/


*🧕WAYAYYAR MACE🧕*

*NA*

*FATIMA USMAN*


*BISMILLAHIRRAHMANIR RAHIM*


Page 47 - 48


*Ci gaban labarin*


B'angarensa ya nufa ya bud'e k'ofar falon ya shige jagwab ya zube kan two seater yana maida numfashi.Tagumi ya zube fuskarsa d'auke da tsantsar damuwa, yayi iyakar tunaninsa bai gano mafita ba, bai san wacce yarinya ya dace ya aura ba, yana da 'yan mata da basu da adadi, amma bazai iya tantance guda d'aya wacce zai ce yana yi mata hak'ik'anin so ba son sha'awa ba, so na gaskiya na aure, ko Latifa da suka had'u shekaran jiya a wajen birthday d'in abokinsa ita ma sha'awar ta kawai yake ji bai jin wani san ta cikin zuciyarsa.

Wayarsa ce ta kama k'ara, d'auka yayi dan ya kashe, ganin wacce ke kiran sa ya fasa, yayi picking.

"To ga ni nan zuwa yanzun nan", ya fad'i haka muryarsa a matuk'ar sanyaye bayan ya gama sauraran wanda yayi kiran nasa.

B'angaren mahaifan nasa ya koma, zaune ya tarar da su a falon.Fuskar mahaifinsa ba alamar wasa ya kalle shi bayan ya zauna a gabansu kansa a sunkuye yace ya yarda ya ba shi nan da wata biyu
ya nemo matar aure.Rok'on sa ya shiga yi da ya k'ara masa wata d'aya dan yayi nazarin matar da ya dace ya aura.

Harara ya zabga masa yace, "kai!, shiga hankalinka, ni bazan k'ara dad'a maka wani lokacin ba, na ba ka nan da wata biyu ka nemo yarinya 'yar mutunci ka aura, idan ka d'auki maganata da mihimmanci ke nan, idan ba ka d'auka ba zaka gane kuskurenka", yana fad'in haka ya mik'e ya haura sama, ya bar shi zaune cikin damuwa.

A damuwance ta kalle shi cike da tsantsar kulawa ta shiga nusar da shi tana cewa ya bi umarnin mahaifinsa yayi yarda yace kafin lokacin da ya ba shi, ya kuma fauwalawa Allah komai, shine zaiyi masa zab'in mafi alkairi."Yanzu ka tashi ka je kayi alwala kar ka rasa jam'i", ta fad'i haka jin an fara kiraye kirayen Sallar Magrib.Jikinsa a matuk'ar sanyaye ya tashi ya fice daga falon.

Pls kuyi manage da wannan, uzururruka ne sukayi min yawa shi yasa kuka ji ni shiru kwana biyu, luv u all my fans.



Fatinku ce 😘😍
*BRILLIANT WRITERS ASSOCIATION*
( _pens of freedom, home of exceptional and magnificent writers_)


https://www.facebook.com/Zauren-Brilliant-Writers-Pans-111419110389493/


*🧕WAYAYYAR MACE🧕*

*NA*

*FATIMA USMAN*


*Wannan page naku ne Ummu Auwal da Hassanan Maska (Asmeenat Zeeyan fans grp), I really appreciate ur love and cares 😍*


*BISMILLAHIRRAHMANIR RAHIM*


Page 49 - 50


A damuwance ce ya koma b'angarensa jikinsa a sanyaye ya d'ora alwala ya tafi masallaci, ana tayar da Sallah ya isa.Sai da aka yi Sallar Isha'i suka bar masallaci kamar yarda kullum suka saba shi da mahaifinsa.Yana fita daga masallacin bai zarce ko'ina ba sai gidan Mamy wato gwaggonsa Hussaina.Da isarsa yayi knocking gate d'in gidan, bud'e masa maigadi yayi ya shiga bayan ya tambaye shi waye ya fad'a masa.

Bai tarar da kowa ba a falon zama yayi kan two seater da ke falon ya kama hab'arsa da dukkan hannayensa biyu.Cikin wannan hali Mamy ta zo ta tarar da shi, dafa kafad'arsa tayi tare da d'an girgiza shi ganin ta dad'e tsaye akansa amma bai ankara da wanzuwarta ba
tace, "tunanin me kake yi haka kai kuwa ?"

Firgigit ya d'ago ya kalle ta tare da sauke wata nannauyar ajiyar zuciya ba tare da yace mata komai ba.Kan kujerar da ke facing d'insa taje ta zauna kana ta dube shi tace, "ina sauraran ka, ina san ka fad'i min abin da kike tunani haka".Sai da ya gyara zama sosai sannan ya kwashe komai ya fad'a mata, ya k'ara da cewa, "ni damuwata lokacin da ya bani yayi kad'an, da ya dad'a min wasu watanni shine zanyi nazarin matar da ya dace na aura sosai".

Numfashi ta ja bayan ta gama sauraran sa tace, "a gaskiya ni ma ina bayansa kan wannan maganar, dan ka kai munzalin aure, kayi k'ok'arin nemo matar aure kafin lokacin da ya ba ka ya cika".

Wani gwauran numfashi ya ja kana yace, "na ji kuma insha Allah zan yi yarda kuka ce kafin lokacin".

"Yauwa ko kai fa d'an albarka, Allah ya had'a ka da mace 'yar mutunci nutsatstsiya mai kamun kai", daidai nan Zainab ta fito daga d'akinta, gefe kusa da shi ta zauna tana cewa, "bros shi ne ko ka tambaye ni da ka zo, kuma yau nayi kiran ka yau amma ka k'i d'auka", a shagwab'e ta fad'i haka.

"Afuwan kiyi hak'uri na amshi laifina, kiyi min uzuri bazan k'ala ba kin ji little 'yar lukuta", yana fad'in haka shi da Mamy suka fashe da dariya.

K'ara shagwab'e fuska tayi tana cuno baki tace, "na k'i na hak'ura tun da ka ce min 'yar lukuta", k'ara sa mata dariya suka yi, kukan shagwab'a ta sa musu.

Tsagaita dariyar Abdul yayi ya rik'o hannunta ya shiga aikin rarrashin ta yana cewa, "yi shiru kin ji na daina fad'a miki haka, gobe ki shirya zan zo na Kai ki shopping, ki zab'i duk abin da kike so".

Tashi tayi ta daka wani tsalle yayin da wani dad'i ya ziyarci zuciyarta, cike da farin ciki tace, "kai amma na ji dad'i sosai bros, kamar ko ka san kayan cosmetics d'ina sun k'are ga shi Abba yayi tafiya".

"Kun ga ku bar surutun haka ku tashi mu je mu yi dinner", Mamy na fad'i haka ta tashi ta nufi dining table, daidai nan Faruq (d'an Mamy na fari bayansa ta k'ara haihuwar d'a namiji yana Kaduna gidan kawunsu Hassan, shekararsa d'aya kenan da samun admission a A.B.U Zaria) ya shigo falon bakinsa d'auke da sallama.

"Daman kana cikin gidan nan tun da nazo ban ji d'uriyar ka ba", Abdul ya fad'i haka bayan su amsa masa sallama.

Cikin zolaya Zainab tace, "ai bros ko yanzu dan yunwa ce ta koro shi da baza ka gan shi ba har ka tafi, ka san acici ne sam baya wasa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login