Showing 1 words to 3000 words out of 18502 words

Chapter 1 - SO DA ALAQA Book Complete By Ummu Aisha.doc

01 Nov 2025

845

??ࡱ?>?? ????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????

 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?Root Entry???????? ?F?WordDocument????1?0Table????????? Data
???????????????????? P?)KSKS?1??????????rrGGGG+??k?G?? ? ? ? ? ? ? ? ? $??*rGG? ? GGGG? ??+?? +? ?+? ? G+ [10/08, 6:38 pm] Baby Aysher: ?? *HASKE WRITERS ASSOCIATION*
_(Home of expert & perfect writers)_


*SO DA ALA?A....!*


_*NA*_

_*UMMI A'ISHA*_



*Wattpad:@ummishatu*


Free page

*1*



*DA SUNAN ALLAH MAI RAHMA MAI JIN ?AI*


~~~Gudu take yi a hankali kaWan kaWan tana motsa jikinta cikin salon jan hankali da burgewa, shi Winma da yake biye da ita a hankalin yake yin nasa gudun inda yake ?arewa halittar da ubangiji Allah yayi mata kallo, duk da cewa gudun tsere suke yi amma ya kasa zuwa ya wuceta saboda nishaWin da yake samun zuciyarsa a ciki duk sa'ilin da yake kallonta,

Sake ?urawa bayanta ido yayi sanye take cikin ?ananan kaya riga da wando blue black, rigar iyakacinta cibiyarta shi kuma wando a cinyarta ya tsaya sai dai kayan sun kamata matu?a, shi kuma sanye yake da riga armless da wando boxer dukkaninsu kalar ruwan madara,

Sake rage gudun tayi tana Wan numfarfashi cikin kissa da jan hankali, dariya yayi ya ?arawa gudunsa mai yazo ya wuceta hakan da ta gani ya sata rakwarkwaSe fuska tabi bayansa, kwance ta sameshi saman korayen ciyayin dake shimfide awurin kamar carpet ya wani baje yana sha?ar iska, kansa ta faWa tana turo baki alamun yin fushi, hannu biyu yasa ya rungumeta yana faWin,

"what's wrong with my baby?"

"Me yasa yau ka wuce ni?" ta faWa cikin muryarta mai sanyi da rashin hayaniya,

"I told you kinyi ?iba da yawa tun bayan da kika haifi Ajmal kika buWe gaki nan da?yar kike Waya ?afa...."

Duka ta kai masa a ?irji tana shusshura ?afa kamar zata yi kuka, hannun ya ri?e bai barta ta dakeshi ba, a madadin hakanma sai ya soma sunbatar hannayen nata da lips Winshi masu tsananin taushi,

" Kin san ina son ki.... Babu ruwana da ?ibarki zan cigaba da sonki koda zaki ninka haka ?iba sau goma..."

Murmushi tayi ta kwantar da kanta saman ?irjinsa ta sake rungumeshi ?am,

"thank you darling..... Thank you for making my heart smile and my eyes shine...."

"I love you..." ya faWa yana sunbatar goshinta, mayar masa da martani tayi ta hanyar sunbatar wuyansa,

"Lokacin salla ya kusa, kuma na bar baby na shi kaWai a bedroom yana bacci may be yanzu ma ya tashi...."

"Za kiyi min wayo dai kawai.... Oya let's go" ya faWa yana ?o?arin mi?ewa ri?e da ita,

Ma?ale kafaWa tayi alamar ba zata tafi ba, ya san abinda take nufi shiyasa cikin salon so ya du?a ta haye bayansa ya nufi ciki da ita bayan ya rufe garden Win. Kwantar da kanta tayi tana mai lumshe idanuwanta dan idan da akwai abinda ke sanyata nishadi a duniya bai wuce tajita kwance cikin jikinsa ko gadon bayansa ba. A hankali yake tafiya da ita har cikin bedroom Winsu, kan gado ya sauketa idanuwansa na kan Wan ?aramin gadon Wansu Ajmal Wan kimanin wata biyu wanda ke kwance yana bacci, wurin da yake kwance ya ?arasa ya sunkuya ya manna masa kiss a kumatunsa sannan ya Wago fuskarsa Wauke da murmushi yana kallonta,

"Ada kince dake Ajmal yake kama... Yanzu fa?"

"yanzun ma da ni Win dai yake kamar" ta faWa tana tashi zaune,

"To zo ki gani.... Wallahi yanzu da yake baccin nan dani yake kama, these days ma gaba Waya kamanninshi sun koma nawa.... Ko jiya abinda hajiya ta faWa kenan"

Tashi tayi taje ta bayanshi ta rungumeshi ta karkatar da kanta ta le?a dan ya fita tsayi nesa ba kusa ba,

"Yanzu a hakane zaka ce kuna kama? Dan dai kawai kace hajiya ma ta faWa ne shiyasa ba zan musa ba"

"Kalli idon shi ki kalli nawa...." ya faWa yana juyo da ita gabanshi,

"Na san idon shi irin naka ne..."

"Hancin shi fa?"

"shima irin naka ne"

"Bakinshi fa?"

"irin nawa ne..."

Dariya yayi ya Wagata sama yana faWin,

"kin dai faWi son ranki kawai malama.... Muyi wanka ko tunda gashi can naji ana kiran salla"

Dariyar itama take tana harharba ?afafu sakamakon cakulkulin da yake yi mata ta hanyar cusa kansa a cikinta. Cike da so da ?auna suka yi wankan suka fito daidai lokacin Ajmal ya tashi, Waukarsa tayi tana daure da towel ta zauna gefen gado dan shayar dashi tana kallon gogan nata wanda yake tsaye gaban mirror yana goge jikinsa da Wan ?aramin farin towel body spray kaWai ya feshe jikinsa dashi kusan kala biyar kasancewarshi ma'abocin ?amshi daga bisani yawuce closet ya buWe, juyowa yayi yana kallonta bayan ya ri?e ?ugunsa,ta gane nufinsa so yake ta shirya shi domin da haka ta sabar masa, langaSar da kai tayi tana kallonsa,

"Ayya daddy kayi ha?uri ka shirya da kanka mana..... Ajmal yunwa yake ji"

Juyawa yayi yana kallon jerin tarin kayansa dake shirye cikin closet Win, yafi mintuna biyu amma ya kasa ciro wanda zai saka,

"Ciro wannan blue Win trouser Win da maroon Win t shirt pls" ta faWa daga nan inda take zaune, hakan yayi kamar yadda tace sannan yazo gabanta ya shirya,

"zan je salla... Ki shirya kafin na dawo zamu fita dinner....."

"a dawo lafiya"

Kissing Win goshinta yayi ya juya ya fita yana balle botiran gaban rigar shi. Da murmushi ta rakashi har sai da ya Sacewa ganinta sannan ta mayar da hankalinta kan Ajmal, bayan ya ?oshi ta kwantar dashi ta mi?e, salla tayi bayan ta idar ta wuce gaban mirror ta soma shiryawa simple make up tayi dan iya powder kadai ta shafa sai gazal sannan ta shafa lips glow akan leSenta, turarenta mai sanyin ?amshi da daWi na arabian oad ta shafa, doguwar riga ta saka ba?a ta sake komawa kan abun salla domin gabatar da sallar ishah dama shi kam ta san ba zai dawo yanzu ba har sai yayi sallar ishah kamar yadda ?a'idarsa take,

Tana zaune kan prayer mat taji motsin shigowarsa, addu'ar da take yi ta shafa tare da mi?ewa tsaye hakan yayi daidai da shigowarsa,

"Sannu da zuwa...."

Ta bayanta yayi hugging Winta sannan ya sumbaci kumatunta kafin ya amsa da "Yawwa Darling"

Ajmal ya Wauka ya fita tana biye dashi har gaban motarshi, sai da ya buWe mata ta shiga ta zauna ya mi?a mata Ajmal sannan ya zagaya mazaunin driver ya zauna, a hankali yake tu?in yana ri?e da hannunta guda Waya har suka isa wurin cin abincin, yanzunma shine ya buWe mata ?ofar motar ta fito ya karSi Ajmal sannan suka shiga cikin restaurant Win, da kanshi yayi musu order Win abinda zasu ci bayan sun kammala ya biya suka nufi gida.

Tare suka yi shirin bacci yana ma?ale da ita a gefenshi laptop akan cinyarshi yana duba wasu ayyuka da zai yi, juyawa yayi ya kalleta idanuwanta a lumshe kanta bisa kafaWarshi,

"Darling..... Kinyi bacci ne?"

Kai ta girgiza masa bayan ta buWe manyan fararen idanuwanta,

"kwanakin baya na taSa faWa miki akwai wani aikin hanya da zan yi a Niger ko?"

Kai ta sake Waga masa tana kallonsa,

"yawwa to yanzu maganar aikin ta taso.... Insha Allah zuwa Friday zan je inga ta yadda aikin zai kasance"

Sake ?an?ameshi tayi ta shige cikin jikinsa,

"Zamu bika"

Dariya taga yayi kafin ya shafi fuskarta,

"Zan so hakan nima"

"Allah yasa kayi aikin ka gama cikin nasara"

"Amin Darling..... Me kike so in siya miki idan na gama wannan aikin"

"Mota" ta faWa tana kissing hannunshi,

"Angama.... Nayi miki al?awarin sabuwar mota insha Allah idan na dawo..."

"Yehhhh" ta faWa tare da faWawa kanshi gaba Waya, janye laptop Win yayi ya tureta can gefe yayi mata masauki a jikinsa sosai yana dariya.

Washe gari kamar yadda ya saba bayan ya gama shiryawa zai tafi office sai da ya fara biyawa ta gidan mahaifiyarshi domin ya gaisheta,

?ar kyakkyawar dattijuwar tana zaune saman sallaya da alama sallar walaha ta idar hannunta ri?e da carbi tana ja, har gabanta ya ?arasa ya zauna yana murmushi,

"Hajiya barka da hutawa"

Murmushin itama take yi tana binsa da kallo,

"Imran..... An fito?"

"Allah ya nufa Hajiya.... Ina kwana?"

"Lafiya lau, ya iyalin, ina Angon nawa da alama rowarsa ake yimin ko?"

Dariya yayi har sai da ha?oransa suka bayyana kumatunsa suka lotsa ciki,

"Haba hajiya ai da kai da kaya duk mallakar wuya ne, idanma cewa kika yi ya dawo nan da zama gaba Waya to hakan za ayi"

"A'a, har yanzu ku Winma baku gama Wokinsa ba ai"

Murmushi ya sake yi ya sunkuyar da kanshi ?asa kafin ya Wago cike da farin ciki yace "Hajiya albishirinki...."

"Goro fari tas Imrana....."

"Hajiya wannan babbar kwangilar da zanyi ta samu.... Insha Allah zuwa nan da juma'a zan je Niger..... Bayan na kammala aikin zaki sake komawa umarah"

FaWaWa fara'arta tayi cikin murna da tsantsar farin ciki tace "Alhamdulillah..... Kai kai kai, Lallai kam dole a koma umarah ayiwa Allah godiya.... Allah yasa ayi lafiya agama da tarin nasarori Imran.... Allah ya sake Wagaka, ya ?arawa rayuwarka albarka"

"Amin hajiya... Allah ya ?ara lafiya da nisan kwana"

Sallama yayi mata ya fita, tun yana hanya yake kiran gimbiyar tasa kamar yadda ya saba, wayar na dab da tsinkewa yaji ta Waga a kasalance,

"Baccin ne?" Ya tambaya a hankali,

"uhmmmm"

"Ayya sorry na tasheki..."

"Dama ina son jin muryarka ai"

"An fara missing Winane?"

"Over ma"

"To ko in dawo...?"

"uhmmmm uhmmmm kawai ina missing dinka ne fa"

Murmushi yayi kafin ya bata amsa da "I miss you more.... Ina Ajmal?"

"Yana bayan Dija ta goyashi.... Yana ta bacci"

"Ok, sai na dawo, I love you"

"I love you much more"

Ta faWa tare da katse wayar, da farin ciki dan?are a zuciyarsa ya ?arasa office, shi dai haka rayuwarshi take baya taSa haWa komai da iyalinsa, wani irin so yake yi musu mai tsanani wanda sam baki ba zai iya faWarshi ba.

Cikin ?an kwanakin ya gama shirye shiryensa na tafiya amma sai ya fara zuwa birnin tarayya Abuja wanda daga can ne zai bi flight,

Yana ma?ale da ita ajikinshi ya haWasu ita da Ajmal Win gaba Waya ya rungume lokacin da ta iyo masa rakiya domin tafiya,

"Zaka biya ta gidan hajiya ne?"

"No, munyi sallama da ita tun daren jiya lokacin da naje, amma yanzu idan na fita zan kirata awaya"

"To Allah ya kiyaye hanya ya kaika lafiya ya kuma dawo da kai lafiya"

"Amin darling.... Am already missing you my Angel"

Sai da ta Wora kanta a ?irjinsa sannan tace "same here sweetheart"

Kissing Winsu yayi babu adadi sannan ya tafi, tana tsaye tana kallonsa har motarshi ta fita daga cikin gidan mai gadi ya mayar da gate Win ya rufe sannan ta koma ciki, bayan kamar mintuna 15 da tafiyarsa ya kirata yake sanar da ita ya kama hanya, wannan itace wayarsu ta ?arshe da ita daga nan bata ?ara jinsa ba, idan ta kira wayar sai taji a kashe da haka har dare yayi anan ne kuma hankalinta ya soma tashi daga ?arshe ta kasa jurewa har sai da ta kira hajiya ta sanar da ita,

Yanda hajiya bata runtsa ba haka itama ta kasa runtsawa sai uban tashin hankali da tunani iri iri dake faman kai komo acikin zuciyarta. Washe gari tunda sassafe hajiya tazo gidan nan suka zauna tare sunata tsammanin warabbuka, amma shiru idan an kira wayarsa ma zancen Waya ne wai a kashe, sai zuwa yamma suka samu labarin wai ?an ta'adda sunyi garkuwa da mutane sama da 10 a hanyar Abuja wannan labarin shi ya sake gigitasu ya Wimautasu, dukkansu su biyun suna cikin mawuyacin hali,

"Ruhaima sai ha?uri da addu'a... Addu'a za mu yi masa a halin yanzu dan ita yafi bu?ata, Allah ya kuSutar dasu....." Hajiya ta faWa tana share hawayenta, ita dai bata iya cewa komai daga ?arshe ma tsintar kanta tayi a gadon asibiti dan bata san me yake faruwa ba. Kwana da kwanaki ta kwashe a gadon asibiti kafin suka dawo gida amma ko bayan da suka dawo Winma babu wanda ya kira su yayi musu maganar Imran ko maganar kuWin fansa kamar yadda aka tsammata shiru shiru tun ana kwanaki har aka share watanni da haka har aka shekara shiru babu wani sabon labari tun ana saka rai har aka fara cirewa, wasa wasa ?aramar magana sai ta zama babba domin kamar an shuka dusa ko kuma an aiki bawa garinsu shiru babu labarin ko wanda ya ga Imran bare shi kansa.......
'



*_Ummi Shatu_*=?L? [12/08, 10:06 am] Baby Aysher: ?? *H.W.A*

Paid Book


*SO DA ALA?A!*


*_NA_*

*_UMMI A'ISHA_*



*Wattpad:@ummishatu*



2


~~~Tun bayan Satan Imran rayuwarta ta shiga cikin mawuyacin hali da ?unci gaba Waya an kasa gane kanta, kusan kowa ita yafi tausayawa ko hajiya da take mahaifiyarsa kamar ta fita dauriya akan lamarin.

Yau ma kamar kullum tana kwance saman gado da Ajmal kwance a jikinta, wayarta ce a hannunta ta tsura mata ido ko kiftawa bata yi, hoton Imran take kallo wanda suka Wauka tare ranar sunan Ajmal, hawayene ya soma bin kumatunta babu ?a??autawa, har aka buWe ?ofa hajiya ta shigo bata sani ba kuka kawai take yi sautin sansanyar muryarta yana fita a hankali, zama hajiya tayi a gefen gadon ta dafa kafaWarta itama tana jin kanta kamar zata fashe da kukan,

"Ruhaima..... Kiyi ha?uri kiyi ha?uri..... Lokaci yayi da zaki daina zubar da hawayenki haka, addu'ar nan dai da muke yi ita zamu cigaba da yi ba zamu fasa ba, insha Allah duk inda Imran yake yana cikin tsarewar ubangiji..... Kiyi ha?uri ki share hawayenki ga Umaima can tazo tare da ba?i tace dama kin san da zuwansu..... "

Da ?yar ta iya tsayar da hawayen ta Wauki tissue ta goge fuskarta ta tashi, karSar Ajmal hajiya tayi ita kuma ta gyara zaman dogon hijabinta wanda yake har ?asa ta fita tana goge hawaye hajiya na biye da ita, Umaima ta hango zaune a cikin babban falonta, tun daga nesa ta fahimci cewa itama Umaima kukan take yi dan gashi nan idanuwanta sunyi ja baya da luhu luhu da suka yi, kusa da ita taje ta zauna kasancewar kujerar da take kai mai mazaunin mutum uku ce,

Rungume juna suka yi suna sake yin wani sabon kukan a haka hajiya tazo ta iskesu,

"Assha..... Nan Winma wani kukan kuke yi Ruhaima? Haba Umaima, wai shin wannan kukan da kuke yi zai ba mu mafita ne? Kuka fa baya magani...... Addu'a zaku yi masa"

Daga haka hajiya ta wuce bedroom wanda yake mazaunin nata a halin yanzu tun bayan da aka samu labarin Satan Imran tana tafe tana share nata hawayen itama. Sai da su Ruhaima suka ci kukan su suka more sannan suka ha?ura,

"ga ba?in can na zo dasu..." Umaima ta faWa tana kallon Ruhaiman,

"kunyi magana dasu?" ta bu?ata tana kallonta da jajayen idanuwanta,

"Ehh sunce insha Allahu tsawon watanni biyu zasu kwashe suna gudanar da saukar alqur'ani da addu'o'i..... Kuma anan gidan zasu zauna, idan sun kammala za a basu abin sadaka dubu Wari biyu"

?aga kai tayi alamun gamsuwa da bayanin da umaiman ta gama yi mata,

"Wannan ba matsala bace sai akaisu can B/Q a saukesu, ni dai dama abinda bana so shirka da kauce hanya.... Amma tunda su karatun alqur'ani ne da addu'a hakan yayi min"

"Nima wannan dalilin ne yasa na kawo su, ubangiji Allah ya wuce mana gaba yasa mu dace"

"Amin Inlaw" ta faWa tana murmushin ya?e saboda halin da zuciyarta ke ciki, Umaima ?anwar Imran ce kuma Allah ya haWa jininsu da Ruhaima, tashi suka yi gaba Waya suke je wurin ba?in Ruhaima ta gaisa dasu sannan suka Wan tattauna tasa aka rakasu B/Q, jin hayaniyar almajirai a ?ofar gida ya sanyata komawa cikin bedroom Winta ta buWe drawer Win jikin mudubinta ta Wauko kuWi ?an dari bibbiyu rafa biyu ta fito, da kanta ta fita ta rarrabawa almajiran sadaka kamar yadda ta saba kullum ta Allah, sai da ta tabbatar almajiran sun ?are babu wani sauran wanda ya rage bai zo ya karSa ba sannan ta koma ciki tana tafe tana tasbihi da carbin dake makale a yatsanta,

Hajiya ta iske a falo tare da Umaima wadda ke ?o?arin haWawa Ajmal abincinshi,zama tayi gefen umaima tana kallon yanda suke kokawa da Ajmal yanata zillo yana mi?a hannu zai kamo Wan ?aramin vowel Win da take dama masa kunun madara,

"wait mana my dear... Yunwa kake ji ne haka?" umaima ta faWa tana dariya,

"Ba dole yaji yunwa ba..... Uwa bata ci ta ?oshi ba bare shima ya samu.... Ni yau sam sam ma banga ta ci wani abu ba a cikin nan nata ko ruwa banga ta sha ba...."

Juyawa umaima tayi ga Ruhaima ta kalle ta idanuwanta a lumshe tana istigfari sai dai tana sauraren duk abubuwan da suke faWa,

" inlaw bakya cin abinci why? Dan Allah ki rin?a daurewa komai ?an?antarshi ko dan Ajmal.... Yanzu me zaki ci? Sai in dafa miki"

"Azumi nake yi" ta faWa cikin taushin murya idanuwanta a lumshe,

"Hajiya kinji wai azumi take yi"

"Ni na kasa gane kan wannan azumi na wannan yarinya, kullum azumi babu hutawa? Wannan wanne irin azumi ne?"

Jin abinda hajiya tace ya sata buWe idonta tana murmushi,

"Hajiya jiya fa banyi ba,irin azumin Annabi Dawud nake yi, yau kayi azumi gobe ka huta, jibi kayi gata ka huta.... Jiya banyi ba dan har kika sa Mama Saude ta dafa min zogale naci ko kin manta?"

"Eh anyi haka.... Ban manta ba"

"Inlaw adai yi ta ha?uri dan Allah, a cigaba da ha?uri da rayuwa... Haka Allah ya ?addaro mana"

Bata sake cewa komai ba ta mi?e ta fita ta ?ofar kitchen ta nufi babban kitchen wanda su mama Saude ke kwarafniyar girke girke,

Aiki ta samesu suna yi na abincin sadaka da ake kaiwa gidan marayu da gidan yari kullum ta Allah, Wan dafe kanta tayi wanda ke yi mata ciwo koda yaushe sanadiyyar kukan da take yi a kai akai shiyasa kowanne lokaci bata rabo dashi,

"mama Saude idan kun kammala dan Allah akwai ba?i a B/Q mutum huWu sai akai musu abinci da dukkan abinda ya kamata, zan Wan shiga in kwanta daren jiya ban samu bacci ba watakila shiyasa kaina ke ciwo"

"To shikenan hajiya... Babu komai, Allah ya sauwa?e, a fito lafiya"

Juyawa tayi ta nufi hanyar komawa ciki mama Saude ta bita da kallo tare da girgiza kai alamun tausayawa, ita dai tana tausayin wannan baiwar Allah domin tana cikin babbar jarrabawa,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login