Showing 15001 words to 18000 words out of 18502 words

Chapter 6 - SO DA ALAQA Book Complete By Ummu Aisha.doc

01 Nov 2025

849

yi ko zai samu sai da ita, tunani tayi a ranta tunda har taga marar lafiyar ya tashi ai gara itama ta tattara sawunta a likkafa ta koma inda ta fito dan dama anan Win a takure take a duk lokacin da akace yana nan, shiyasa da mukhtar ya kirata tace yazo su tafi kamar yadda ya bu?ata amma yace sai yayi sallar magrib, bata sake saka Sameer a idonta ba har lokacin da suka fito zasu tafi,

Shi kuwa Sameer duk abinda yake faruwa akan idonshi sune basu ganshi ba amma shi yana hangosu daga inda yake zaune cikin motarsa wacce ke ajiye cikin farfajiyar gidan, a ransa kawai sake jaddada taurin kan Ruhaima yake, yayi mata hannunka mai sanda akan mutumin nan, yayi mata wanka mai kama da jurwaye akan mutumin nan amma duk a banza dan tsabar jaraba ta toshe kunnenta, ko idan sunyi auren me wannan mutumin zai bata oho, tsaki yaja ya cigaba da daddanna wayarsa, shi bashi ma ko lambar wayarta kuma ya dace ace yana da ita fa, "me zanyi da no dinta ma" ya fada cikin zuciyarsa kamar da wani ne yace sai ya mallaka, akan idonsa suka bar gidan wanda bai wuce dasu gida direct ba sai da yafara biyawa da ita wurin wani gashin kaza yayi musu take away sannan ya mayar da ita gida, ita dai ta gama amincewa zuciyarta cewa kawai zata yarda ta auri mukhtar ba wai dan tana sonsa ko tana ?aunarsa ba, ba kuma wai dan yayi mata ba a'a kawai dai halayensa sunyi mata dan mutum ne mai ha?uri da rashin fushi sannan ga barkwanci da fara'a,

Lokacin da tayi shirin bacci sai taji ta gagara domin babu abinda take tunawa a wannan lokacin sai halin da Sameer ya kasance Wazu, ko yanzu yana cikin wanne hali oho? Ko ya samu yayi bacci ko kuma har yanzu yana cikin damuwar ciwon Allahu a'alamu, Ajmal ta rungume wanda ke gefenta yana bacci, a can ?asan zuciyarta kuma tana yi masa addu'ar rabuwa da wannan ciwon rabuwa ta har abada. Shima Sameer a nasa Sangaren lokacin da ya hau kan gadonsa domin yin bacci ji yayi Ruhaima ta faWo masa gaskiya ya zama dole ya sanar da hajiya yakamata a tattaro Ruhaima ta dawo gidan nan ko dan kare mutuncinta da darajar ta, yanzu tana can tana rayuwa ita kaWai sannan ta baiwa wani fuskar da zai je mata hira gida tofa komai zai iya faruwa yanda mutane yanzu basu da tabbas, shi tausayi Waya take bashi idan ya tuno irin yanda tayi sabo da mijinta yanzu kuma tazo ta rasa shi, lumshe idanuwanshi yayi amma ya san bacci kam ba yanzu ba, wani Sangaren na zuciyarshi kuma alla alla yake gobe tayi domin yaje ya sauke nauyin da yake kan shi.

Kasancewar bata yi bacci da wuri ba shiyasa ta kasa tashi dan sai bayan da tayi sallar asuba sannan ta samu bacci, shima Ajmal Win da ya saba tashi da wuri har ya dameta yau bai tashin ba bare ya hanata rawar gaban hantsi,baccinsu suke kamar za a sake yi musu wani daren. Agogon hannunshi ya kalla misalin ?arfe 10 har da rabi na safe agogon ya nuna masa, sake gyara tsayuwarsa yayi yana tunani a ransa to ko dai sun fita ne? To amma tayaya zasu fita ba tare da maigadi ya sani ba? Maigadi ya tabbatar masa da suna ciki, ?ofar falon ya sake zuwa a karo na huWu ya Wan bubbuga, cikin bacci taji muryar Ajmal yana cemata,

"mommy inje in buWe? ?ofa ake bugawa"

"uhmmm jeka" ta faWa tare da sake jan bargo dan jin maganganun Ajmal Win take yi kamar a mafarki, da gudu ya sauka daga kan gadon ya fita, saida ya jima yana murWe murWe sannan ya buWe, ganin Sameer tsaye hannayensa cikin aljihun wandonsa yayi saurin rungumeshi, Waukarsa Sameer yayi yana kallonsa dan ya fahimci daga bacci ya tashi, falon yake bi da kallo ganin komai a karkashe alamar itama Ruhaiman bata fito ba, wuri ya samu ya zauna yana gyara zaman face mask Win dake fuskarshi dan tun jiya numfashinsa babu ?arfi,

Kimanin mintuna 15 ya shafe zaune a falon amma babu ko motsinta kai babu ma ko alamar cewa zata fito hakan yasa shi duban Ajmal dake lilo akan ?afafunsa,

"mommy bata da lafiya ne?"

"uhmm.... Uhmmm...."

Kasa gane amsar da Ajmal ya bashi yayi, ehh yake nufi ko a'a? Cikin azama ya mi?e shi kansa bai san lokacin da ya tashin ba yana tambayar Ajmal tana ina? Tiryan tiryan yake biye dashi har cikin bedroom Winta inda take kwance tana bacci......



*HASKE! HASKE!! HASKE!!!*=ء?

IT'S *HASKE WRITERS*=ء?AGAIN THE HOME OF EXPERTS AND PERFECT WRITERS
'
HA?I?A JIMIRIN ZAMAN JIRA YA ?ARE MASOYA DOMIN ?UNGIYARKU MAI FARIN JINI TA AMANA WATO *HASKE WRITERS ASSOCIATION*=ء? ITACE TA MOTSO KUMA TA DAWO DAN NISHA?ANTAR DAKU KAMAR YADDA TA SABA, *TAURARI HU?U* SHINE TAKEN TAFIYAR TAMU A INDA ZAMU GABATAR MUKU DA FASIHAI, HAZI?AN MARUBUTA GUDA HU?U DA AL?ALIMANSU CIKIN TAFIYAR DA BABU NADAMA ACIKINTA,

*1.AYUSHER:-*
Writing by FERTYMERH XARAH

*2.?AZAFI NE:-*
Writing by RAHAMA NALELE

*3.DA UBA AKE ADO (Bada riga ba):-*
Writing by ZAINAB BAWA

*4 SO DA ALA?A:-*
Writing by UMMI A'ISHA

WAI WAI WAI... =?%?BAHAUSHE YAYI GASKIYA LALLAI TAFIYA DA GWANI MAI DA?I, NIMA DAI GA NAWA GWANAYEN 4 STARS DUKKA WA?ANNAN LITTATTAFAN GUDA HU?U ZAKU SAMESU CIKIN FARASHI DAIDAI DA ALJIHUNKU....MY SISTER WHAT ARE YOU WAITING FOR?? MAZA HANZARTA KI GARZAYA KI NEMI NAKI DAN ZASU FARA NAN BADA JIMAWA BA, KAR KI BARI A BAKI LABARI..... COMING TO YOUR WAY SOON, DON'T MISS IT =??=??

Guda 4:- 1500
Guda 3:-1200
Guda 2:- 800
Guda 1:- 400

7033027658
Palmpay Bank
Aisha Muhammad Salis

Katin wayar MTN ta...
07044644433 da shaidar biya


*HASKE WRITER'S ASSOCIATION*=ء?

*_Ummi Shatu_*=?L? [20/08, 11:53 am] Baby Aysher: ?? *HASKE WRITERS ASSOCIATION*

4 stars......


*SO DA ALA?A.....!*




_*NA*_

_*UMMI A'ISHA*_


Wattpad :@Ummishatu


Last free page


10


***Sake juyi tayi lokacin da taji Ajmal yana kiranta bayan ya hayo kan gadon "mommy.... Mommy"

Bata amsa ba sai ma sake jan bargo da tayi amma kamar acikin mafarki sai kuma ta fara jiyo amon muryar Sameer,

"bari tashinta Ajmal.... Daina...." ya fada yana bin cikin bedroom Win ta da kallo duk da babu wani wadataccen haske sosai domin ko ina WiWim yake da duhu haka duk da hancinsa a toshe yake bai hana shi jin irin sanyin ?amshin da cikin Wakin keyi ba, ai bata san lokacin da ta zabura ba ta tashi zaune kamar wacce aka tsikara sai kuma ta tuna da kayan bacci ne a jikinta cikin azama ta sake ?udundune kanta,

Yanda ta tsorata shi Winma tsoratar yayi sai dai ya dake, cikin tausasa murya kamar yadda ya saba magana taji yana faWin,

"sorry.... Mun tadaki... Am... Am.... Dama nazo Waukar Ajmal ne sai naji shiru kuma na kasa gane amsar da ya bani lokacin da na tambayeshi ko baki da lafiya...."

"lafiya ta ?alau" ta fada cikin kiWimewa wadda shi kansa ya fahimci hakan, bai ?ara cewa komaiba ya juya ya fita Ajmal ya rufa masa baya, tafi mintina biyu ahaka kafin ta samu ta tashi ta zira hijabinta ta fita, suna zaune falo Ajmal na kan cinyar sa,ita dai tana mamakin yadda yake sakarwa Ajmal bayan ayadda ta lura baya son raini,

"ina kwana...?" ta fada kanta a ?asa bayan ta zauna can nesa dasu,

"lafiya lau.... Ina so zan kai Ajmal makaranta ne, ki shirya shi"

Bata ce masa komai ba ta mi?e ta shiga ciki Ajmal yabita, wanka tayi masa gashi matsalar ko breakfast basu yi ba ga baba saude bata nan ita fa yau abin yayi mata yawa, shirya shi tayi cikin jeans da t shirt duka ba?ake ta fesa masa turare kaWan sannan ta saka masa ba?in combos,

Kamar yadda suka tafi suka barshi haka suka fito suka sameshi sai dai yanzu hankalinsa akan waya yake yana lallatsawa,

"zaku jira in haWa breakfast ne?" ta tambayeshi tana gyarawa Ajmal belt Win wandonshi,

"no.... Zan kaishi yaci abinci"

"to shikenan..."

Kiss Ajmal yayi mata a kumatu yana haddane dasu amma shi abin mamaki ya bashi ya aka yi yaron yasan kiss? Koda yake ta yuyu itace take yi masa amma duk da haka ya kasa mantawa shiyasa a hanya lokacin da suka tafi sai da ya tambayi yaron wai a ina ya gani,

"mommy ce take yi min" murmushi yayi dama yasan hakan mai yuyuwa ne. Kasancewar shima bai karya ba sai da ya fara biyawa dasu ta restaurant suka ci abinci sannan suka wuce makarantar sa zai saka Ajmal, makaranta ce mai tsada dan ta ?a?an masu kuWi ce kuma ?an gata dan babu students ma da yawa sosai, registration yayi masa sannan ya biya dukkan abubuwan da suka dace kuma bugu da kari makarantar haWe take da islamiyya dan haka sai 5:30 ake tashi idan yaro ya tafi tun safe,

Koda suka gama gidan hajiya ya wuce da su kai tsaye dan sai gobe zai fara zuwa lokacin komai nasa ya zama ready kama daga kan uniform, school bag, lunch box, sandal da sauransu dan komai a makarantar ake badawa yana cikin kuWin registration,lokacin da suka isa gidan sun samu umaima tana shirin komawa gidan mijinta bayan hajiya ta jajja masa kunne domin yazo shi dai Sameer har yau ya kasa daina ganin ba?in mutumin nan tun bayan da yaji irin aika aikar da yai niyyar yi Allah ya kare. Bai ce komai ba kawai ya wuce part Win shi yaje ya kwanta dan wani mashahurin bacci ke shamayarshi tunda safe amma ya daure bai yi ba wannan dalilin ne ma ya haddasa masa ciwon kai kadan kadan, baccin ya Wan samu ya rage zuwa yamma lokacin da ya shiga wurin hajiya sai ita kaWai ya samu da Ajmal domin su umaima sun tafi, abinci ya zubo ya zauna yana sauraren hirar da hajiya keyi masa wacce ta shafi matsalar umaima zuwa can ta Wan sauya akalar hirar daga wacce take yi masa zuwa wata ta daban,

"wai Sameer har yanzu shiru baka samo budurwar ba?"

Sai da ya lumshe idanuwansa sannan ya buWe kan filet Win abincin da yake kan cinyarsa yana ci, ita dai hajiya ayita magana Waya koda yaushe ba canji?

"Sameer baka jina ne?"

"hajiya ina jinki mana...... Ai maganar ce nakan rasa amsar da zan baki wani lokacin"

"ban gane kana rasa amsar da zaka bani ba?"

"to hajiya maganar budurwa ya?i ?arewa.... Ni har yanzu Allah bai nuna min wadda tayi min ba"

"kullum haka kake faWa, koda yaushe maganar kenan baka ga wadda tayi maka ba....... Ni ina ganin tunda kai dubawar awurinka ta gagara ni inada idon da zan dubo maka, Wazu hajja Maimuna ta kirani wai Arfat ta samu admission anan BUK, wai zata zauna a hostel nikuma nace a'a ga gida yaushe zata zauna a hostel, kawai tazo nan ta zauna, to ni yanzu wani tunani ne ma yazo min, Sameer tunda ka rasa budurwa ni ina ganin kawai ka nemi Arfat..... "

Tunani yafara yi acikin ransa wacece ma Arfat? Idan bai manta ba tun yarinyar bata san kanta ba rabon da ya sake Wora idanuwansa akanta, ?ar ?anwar hajiya ce uwa Waya uba Waya domin hajja Maimuna itace autar su hajiya, yanzu haka tana can Gombe da yaranta, ji yayi ya tsani Arfat Win tun kafin ya ganta, shi kansa bai san me yake damunsa ba a duk lokacin da hajiya tayi yun?urin haWashi da wata sai yaji ya tsani yarinyar, ko wani ne ya kawo masa maganar wata haushi abin yake bashi, shi fa baya maraba da irin wannan haWe haWen,

"kaji abinda na faWa maka ko?" muryar hajiya ta katse masa tunanin da yake yi,

"eh naji hajiya amma gaskiya wannan maganar a barta"

"koda yaushe abinda kake faWa kenan... Sameer nima fa ina son inga iyalinka, ina son inga ?a?anka"

"zaki gani hajiya Insha Allah amma sai lokacin yayi, har yanzu ni banga wacce tayi min ba kinga babu amfanin inyi auren favor daga baya inga irin type Wina hankalina ya karkata can ta farkon ta rin?a ganin kamar banyi mata adalci ba..."

"duk mace macece Sameer duk abinda zaka samu a wurin wadda kake kira da type Winka itama wannan Win zaka samu awurinta, Arfat yarinya ce mai nutsuwa mai hankali mai addini.... Insha Allah zaka ji daWin zama da ita, sannan idan har nice na haife ka kuma na isa da kai to ita na zaSa maka a matsayin mata "

" hmmm ji hajiya tana maganar wai duk mata Waya suke, wallahi mata suna suka tara especially ma matan yanzu " ya fada a cikin zuciyatarsa, shi dai yau yaga ta kansa wallahi da ya san irin abinda zai biyo baya kenan da baima shigo part Win hajiya yanzu ba, yana jinta taci gaba da yi masa ?ar nasiha akan ya sakawa zuciyarsa so da ?aunar wannan zaSin da tayi masa Insha Allah ba zai yi nadama ko dana sani ba, ji yayi abincin da yake ci ya fita daga ransa dan haka ya tashi ya fita ya kai abincin kitchen ya koma sashensa dan bashi da wurin zuwa, pretty ya Wauka dama itace abokiyar wasan shi. Sai da yayi sallar magrib sannan ya tafi mayar da Ajmal gida, abin ya bashi mamaki mutu?a sannan ya saka shi cikin tunani mai zurfi lokacin da yaga Ruhaima cikin kwalliya sosai a wannan daren,falonta sai ?amshin turaren wuta yake yi ko ina da komai a gyare, banda gaisuwa babu abinda ya sake shiga tsakaninsu sai dai irin yanda yake kallon falon ta san akwai magana acikin zuciyarsa, mi?ewa yayi dan tafiya amma sai ya zuba duka hannuwanshi cikin aljihu ba tare da ya kal?????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????leta ba yace,

"kiyi hankali da irin mutanen da kike kawowa gidan nan wai da sunan zawarci..... Sannan ki guji bin mutum da sunan kai ki unguwa"

Da kallo ta bishi ba tace masa komai ba kamar yadda shima bai so tace Winba dan yana gama faWar abinda ke ransa ya juya ya fita, maida hankali tayi kan Ajmal wanda ke bata labarin irin abubuwan da suka faru a makaranta tun daga farko har ?arshe, taji daWi sosai dan dama wannan shine burinta taga ya samu ingantaccen ilmi wanda kowa zai yi alfahari dashi kuma zai amfana, kai ai Sameer halinsa sai shi haka kawai ya dage yayi ta kafa mata dokoki da sharuWWa kamar wani wanda yake aurenta, harda wani ta kiyayi bin mutane su kaita unguwa, lallai ma, duk waWannan maganganun tana yin su ne cikin ranta.

Kamar yadda Ajmal ya sanar da ita wai yau zai fara zuwa makaranta tunda tayi sallar asuba bata koma ba, abincin da zai ci da wanda zai tafi makaranta duk ta haWa tayi masa, 7 saura ta tashe shi tayi masa wanka ta shirya shi cikin kaya personal saboda uniform Win sai yau, suna falo yana yin breakfast duk sai murna yake Woki ya cika shi suka ji alamun shigowar Sameer, kayan bacci ne ajikinsa blue color daga waje ya tsaya bai shiga ba, tare suka fito da Ajmal Win tana ri?e da flask Win abincinsa, abun ya bata mamaki duk da ba sabon abu bane ganin tana gaida shi amma bai ko kalleta ba koda yake dama haka ya saba wannan halinshi ne sai dai ta bawa wani labari shan ?amshi da ciki ciki ajininsa yake,

Sai da taga fitarsu daga gidan sannan ta koma ciki, bacci ta koma, haka ta wuni tana bacci daga ?arshe ta rasa ma me zata yi gashi sunyi wayar har ta gaji da mukhtar, kallon ma ta kunna duk bai wani yi mata ba, kiran umaima ne ma ya Wan Webe mata kewa dan ta kirata tana sanar da ita ta koma gidanta, sai da suka Wan taSa hira sannan take sanar da umaima Ajmal ya fara zuwa school yau, duk gidan babu daWi yayi mata shuru ta rasa me zata yi dariya umaima tayi tace,

"haka abinfa yake, idan suna nan su dameka bakinka bazai huta ba idan basa nan kuma kaWaici ya takura maka.... Kawai ki faWa social media, zaki fi Webe kewa yanzun nan lokacin zai Wan rin?a tafiya, kije can kiyi ta kallon films da karance karancen novels"

Wannan shawarar tabi ta umaima kuma hakan ya taimaka mata dan tabbas tana cikin nishaWi, ita social media bata taSa burgeta ba dan akwai abubuwan da bata ma taSa amfani dasu ba kuma suna kan wayarta dan ada gani take kamar Sata lokacine ko kuma rashin aikin yi ne. Sai 6 na yamma Sameer ya dawo da Ajmal yanzun ma bai shigo ba, iya Ajmal Winne kaWai ya shigo da kayansa a hannu kashi kashi dan an bashi komai yau sai murna yake tsabar Woki tun a daren ranar ya gwada kayan (uniform) bai bari gari ya waye ba, washe gari kam sai da tayi masa pics kafin Sameer yazo bayan ta shirya shi ya sha uniform Win shi wanda ya amshe shi yayi masa masifar kyau, milk color Win riga da necktie blue black sai blue black color Win wando, kamar jiya yau ma bai shigo ba itama bata fita ba sai iya Ajmal Win ta tura masa suka tafi.

Rabon da ya shigo ciki harta manta dan ba zata iya tunawa ba amma kullum zai zo ya Waukeshi babu fashi sannan zai dawo da shi sai ko a weekend shine zai huta, yau dai kam ta kwana da ciwon nata na gado kuma ta tashi da shi dan ko bacci bata samu ba sai juye juye ta kwana tana yi shiyasa ma ba zata iya shirya Ajmal ba, tana jin lokacin da Sameer ya shigo gidan domin Waukarsa, cikin ?arfin hali ta tashi Ajmal tace yaje ya faWa masa yau ba zai je school ba bata da lafiya, yana zaune cikin mota sai ga Ajmal Win ya fito babu shirin makaranta, tun kafin ya tambayeshi ya sanar dashi abinda mommy ta aiko shi,

"bata da lafiya meke damunta? Ina wannan baban dake yi muku aiki?"

Ba dan Ajmal yarone mai wayo ba da bazai iya amsa masa waWannan tambayoyin ba domin sunyi masa yawa, kama hannunsa yayi suka shiga ciki ya tsaya a falo yace yaje ya kirata,

Da ?yar da dafa bango ta samu ta fito a dur?ushe ma take tafiya kuma da?yar, koda tazo falon a ?asa ta zauna ta kifa kanta a kujera,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login