Showing 9001 words to 12000 words out of 18502 words

Chapter 4 - SO DA ALAQA Book Complete By Ummu Aisha.doc

01 Nov 2025

846

gaba Waya acikin Waki tayi shi duk da dama hakan Wabi'arta ce yanzu amma na yau kam kamar na dabanne, shigowar baba saude mai aikinta wadda yanzu ita kaWai ta rage acikin ma'aikatan gidan dan duk sauran ta sallamesu tun jimawa,shigowarta ne yasa ta tashi zaune da koWaWWun idanuwanta take kallon baba sauden,

"Ruhaima... Lafiya kuwa yau duk baki fito ko falo ba? Ko wani wurin ke yi miki ciwo?"

"Wallahi lafiya lau baba saude.... Kawai dai akwai abinda ke damuna"

"Hakane.... Kowa ka gani dama akwai abinda ya dameshi sai dai hakuri, duk abinda yake damun bawa idan yayi hakuri zai wuce, na san kina cikin damuwa amma ki kara ha?uri akan wanda kikayi abaya Insha Allah ubangiji Allah zai baki mafita sannan yana tare dake a koda yaushe... Allah ya fiki sanin damuwarki Ruhaima kuma zai kawo miki Wauki Insha Allah "

Duk da bata bayyanawa baba saude damuwarta ba amma kalaman na baba saude sun samar mata da nutsuwa kuma sun sanyaya mata zuciyarta haka kuma sun rage mata wani kaso mai yawa daga cikin damuwarta, ?warin gwiwa taji ta sake samu akan ?udurinta da kuma nufinta,

Bata san lokacin da ta Wauki wayarta ta kira hajiya ba, da sallama hajiya ta Wauki wayar tata lokacin suna tare da Sameer acikin bedroom Winta yana kwance kan gadonta Ajmal yana kan ruwan cikinshi yana doki dashi,

Saida ta gaida hajiya sannan cikin sanyin muryarta wanda ya gaurayu da damuwa tace "Hajiya dan Allah ina son magana da Umaima da Sameer da kuma ke harma da Alhaji sabo idan zai yuyu... Ma'ana dai ina so mu haWu gaba Wayanmu anan gidan ki kuma gabanki dan akwai wata sar?a?iya da nake son warwarewa....."

"To shikenan Ruhaima amma ni da sai nake ganin idan har akan waccar maganar ce ta abinda ya faru da kin barshi..."

"a'a hajiya a dai taimaka min a saurareni...."

"to shikenan sai mu barshi asabar ko saboda kinga suna zuwa aiki...."

"hakan yayi hajiya nagode Allah ya ?ara girma..."

Sallama suka yi, Wan tashi zaune Sameer yayi yana kallon hajiya,

"me kuma ya faru?"

"Ruhaima ke son Magana damu gaba Waya.... Ina jin zata koma gida ne amma dai bata faWi hakanba kawai hasashe na ne..."

"zata koma gida kuma? To amma hajiya ai bai kamata mu barta ta tafi ba..." ya fada cikin damuwa yana ?arasa tashi zaune,

"to ya za ayi Sameer? Bari dai lokacin yayi sai muji me take tafe dashi"

Bai ?ara cewa komai ba ya tashi ya fita cikin damuwar dashi kansa bai san ko ta mecece ba, farfajiyar gidan ya fita ya samu ya jingina hannayensa cikin aljihun bakin trouser Win dake jikinsa..........
'


*_Ummi Shatu_*=?L? [16/08, 7:32 am] Baby Aysher: ?? *HASKE WRITERS ASSOCIATION*




*SO DA ALA?A...!*



_*NA*_

_*UMMI A'ISHA*_



*Wattpad:@Ummishatu*



Free page


6


****Rasa abinda zai yi yayi sai faman zancen zuci yake ta yi shi kaWai,

"to ko maganar da na fada mata ne ta Sata mata rai? Na faWa mata wani abu mai zafi ne?" ya tambayi kansa yana kallon harabar gidan,

"amma ni a iya sanina ai gaskiya na faWa mata, bai kamata ta rin?a Wauko mana magana ba dan kawai tana missing mijinta...." ya sake bawa kansa amsa, "oho dai..." daga haka ya fita daga ma gidan baki Waya a ?afa batare da ya Wauki motar shi ba, sai dai duk da ya zurfafa tunaninsa ya kasa gano dalilin da yasa Ruhaima tace tana son ganinsu gaba Waya, tafiya yayi sosai acikin unguwar yana zagayawa daga ?arshe ya yada zango a masallacin wani ?ofar gida dake da ma?otaka da unguwar tasu ganin lokacin sallar magariba yayi.

Sai da yayi salla sannan ya koma gida, sashensa ya wuce kai tsaye yayi wanka sannan ya fito ri?e da magensa pretty, lokacin da ya koma part Win hajiya samu yayi Ajmal yana tv game a falon hajiya nan ya biyeshi suka yita yi tare kamar wani sa'ansa har saida Ajmal Win yayi bacci. Washe gari itace ta kama ranar da Ruhaima zata zo domin ganawa dasu kamar yadda ta ro?a, duk da tana cikin tsananin fargaba da da tsoro amma ta dake ta daure tana ta addu'a da haka ta shirya, navy blue color na leshi ta saka mai duwatsu Winkin riga da skirt, turare kaWan ta Wan fesa sama sama sannan ta kawo blue Win mayafi ta yafa, sam bata Satawa kanta lokaci ba wurin yin kwalliya domin ko mai bata shafa ba saboda a ha?i?anin gaskiya bata cikin nutsuwa da farin ciki tun daga ranar da Alhaji sabo yayi mata wannan sharrin,

Misalin ?arfe 12 na rana ta isa gidan hajiya duk da dai gabanta sai faman faWuwa yake, a falo ta tarar da hajiya da umaima wadda ko kallo bata isheta ba, duk sai ta sake jin babu daWi ga kuma yaransu nan suna wasa tare wato su Abid tare da Wanta Ajmal, daurewa tayi bayan ta gaisar da hajiya ta saki fuska tace,

"umaima ina wuni?"

Kamar ba zata amsa ba dan aciki ciki ta amsa gaisuwa, duk da hakan yayiwa Ruhaima ciwo amma sai ta basar ta danni zuciyarta, itama hajiya ganin haka yasata kiran Sameer awaya aganinta gara yazo su yi su yi abinda ya tarasu kowa ya koma gidansa bata son irin wannan zaman na doya da manja,

Ita dai Ruhaima a ranta tunani take to ya taga umaima ita kaWai? Ina mijin nata ko dai ba zai zo bane? Tana son ta sani amma babu damar tambaya, jin horn acikin gidan ya tabbatar musu da zuwan wani ba?on,

"yawwa ga abbansu Abid Win nan ma ya ?araso hajiya" inji umaima, Wani sanyi Ruhaima taji acikin ranta,

Zuwan Alhaji sabo yayi daidai da fitowar Sameer daga part Winsa, sanye yake cikin ?ananan kaya farar t shirt ta polo sai blue Win wando jeans, gaisawa suka yi da Alhaji sabo sannan ya jagoranceshi zuwa ciki,

Bayan gaishe gaishe Sameer ya dubi hajiya wadda ke zaune Wan gaba dashi kaWan,

"Hajiya Nifa inada uzuri.... Dan Allah ayi abinda za ayi"

Kallonsa Ruhaima tayi ta ?asan ido ita dai a rayuwa ta rasa me tayiwa bawan Allahn nan da bata burgeshi tsakaninta dashi ko yaushe sai harara sai Waure fuska sannan babu wata magana mai daWi da take shiga tsakaninsu dan ko gaishe shi tayi tun lokacin da yayansa yana nan a ciki ciki yake amsawa kai kamar ma a dole yake amsawar dama kuma bama zuwa gidan nata yake yiba sai da ?wa??waran dalili,

"to ai Ruhaima ce ta taramu dan haka ita muke saurara...." maganar hajiya ta ratsa kunnuwanta nan ta dawo cikin hankalinta daga tunanin da take yi, gaba Waya kowa ita yake kallo kuma yake saurare banda Sameer wanda ko kallo bata isheshi ba dan wayar shi ma yake dannawa, shi kuwa alhaji sabo ido ya ?ura mata acikin ransa yana bakin ciki da takaicin rashin cikar burinsa yaso ya WanWana kayannan yaji dan ya san zai samu cikakkiyar nutsuwar da yake so, amma yanzun ma bai ha?ura ba kuma bai sare ba zai sake jarraba wata hanyar har sai ya dace,

"Kamar yadda kowa ya sani, ni marainiya ce na taso cikin maraici, cikin babu......"

"To sai me? Kowa ya san wannan, idan dan shi kika taramu muna da abin yi..." Sameer ya faWa ta hanyar Waga mata hannu alamar dakatarwa, bata kula shi ba taci gaba da faWin abinda take da niyyar faWa,

"Duk da na taso cikin babu, babu cin yau babu na gobe, babu suttura babu kayan ?yale ?yale ko more rayuwa hakan bai taSa sani tunanin inyi sata ko in Wauki abin wani ba, ban taSa ji araina zan saci kayan wani ko in bada mutuncina dan in mallaki wani abu ba.... A koda yaushe kakata tana faWa min cewa wadatar zuciya itace babban arzi?i koda mutum baida cin yau baida na gobe, nasha wahalar rayuwa iri iri a lokacin da nake tasowa saboda babu, amma haka na jure nayi hakuri har zuwa girmana, wallahi tallahi kayan wani ko dukiyar wani bata taSa burgeni ba bare har inji araina zan iya Wauka da sunan sata..... Abban Ajmal ya taSa sanar dani sunyi haWin gwiwa da Alhaji sabo wurin gina wani kasuwanci, nikuma a halin yanzu inada bu?atar kuWi dan in gina rayuwar Wana, lokacin da naje gida nemansa umaima tace yayi tafiya, ganin maganar ko a waya zan iya yi masa shiyasa na bu?aci da ta bani no wayarsa, shi da kansa yace bazan iya ganinsa ba a gida saboda yana da meeting amma zan iya samun ganinsa a guest house Winsa dan kusan gaba Waya harkokinsa yanzu acan yake gudanar dasu, wallahi zuciyata Waya na shirya naje ban taSa tunanin wai da wata manufa ya gayyaceni can ba, lokacin da naje ya fito min da ?udurinsa ban amince ba dan aganina wannan cin amana ne amma sai ya nemi da yayi min ta ?arfi..... " wani kuka ne yaci ?arfinta dama kuma tun lokacin da ta fara maganar hawaye ke bin kuncinta, duk jikin kowa yayi sanyi da kalamanta duk da wai basu gaskata cewa alhaji sabo yayi yunkurin yi mata fyaWe ba,

" Ta yaya zamu yarda da abinda kike faWa? Kina da wata shaida?" umaima ta faWa a kufule saboda jin abin da ake faWa akan mijinta, yayin da shi kuma alhaji sabo kallon Ruhaima kawai yake yana tunanin ta inda yakamata ya soma wanke kansa ya sake Waureta sannan ya Satata a idon kowa,

Handbag Winta ta buWe ta ciro wayarta tana goge hawaye,

"wannan itace maganar da muka yi awaya...." ta faWa tana kunna recording Win da tayi, bayan duk an gama saurara ta sake kunna wani tana cewa "wannan shine abinda ya faru a guest house Winsa"

Kowa nutsuwa yayi yana sauraren maganganun alhaji sabo wanda suke fita tar kamar yanzu yake yi, duk abinda ya faru tun daga zuwanta har lokacin da suka yi magana da mai gadi ya kirashi awaya har shigarta da yadda ya rin?a hilatarta tana ?i da kokawar da suka gwabza da komai kai har zuwan ?ansanda duk sai da kowa yaji, kunya ce ta lulluSe alhaji sabo yaji kamar ?asa ta buWe ya shige dan tsabar kunya, bai taSa jin kunya irin ta yau ba, da ya san wannan ranar zata zo tabbas da bai aikata abinda ya aikata ba, ita kuwa umaima kuka ta fashe dashi, babu wanda ya iya magana daga hajiya har Sameer, itama Ruhaima kukan take yi duk da bata so ta tona masa asiri ba amma bata da wani zaSi illa hakan ko dan ta wanke kanta daga kallon da kowa ke yi mata, mi?ewa tayi ta ciro kuWin da ya bata dubu Wari, ta ajiye a gabansa tace,

"waWannan sune kuWin da ka bani.... Bani da bu?atarsu a yanzu, gashi na dawo maka dashi...."

Shi dai alhaji sabo kansa na sunkuye a ?asa gumi sai yanko masa yake tako ina saboda tashin hankali,ganin ta juya tana ?o?arin barin falon tana kuka umaima tace,

" Ruhaima dan Allah ki yafe min.... Nabi daWin bakin namiji na biyewa kishi idanuwana sun rufe na kasa fahimtarki... Wallahi koda wasa ban san mijina yana da irin wannan halin ba" tsayawa tayi cak tana sauraren maganganun umaima, kai kawai ta Waga mata alamun gamsuwa amma daga haka bata iya cewa komai ba ta fita daga falon tana share hawaye......
'


*_Ummi Shatu_*=?L? [17/08, 9:41 am] Baby Aysher: ?? *HASKE WRITERS ASSOCIATION*



*SO DA ALA?A....!*



_*NA*_

_*UMMI A'ISHA*_



Free page


7



***Ita kanta bata san a halin da take ciki ba ahalin yanzu dan ko shakka babu da za a tambayeta ba zata iya kwatanta yanayin da take ciki ba, ba?in ciki da farin ciki duk a lokaci guda duk da cewa dai ba?in cikin yafi yawa amma duk da haka taji daWin yanda Allah ya kawo mata mafita har ta samu zarafin wanke kanta, dama ita gaskiya haka take duk daren daWewa sai ta bayyana kanta sannan bata bu?atar taron dangi wurin bayyanarta saSanin ?arya, tana tafe tana share hawayenta har ta samu ta fita daga cikin gidan. Yanda Ruhaima ta fita ta barsu haka duk suke zaune kowa ya gaza koda ?wa??waran motsi bama kamar ya alhaji sabo da gaba Waya yake jinsa kamar an dasa shi a wurin da yake zaune, shi yanzu koda magana zai yi baima san me zai ce ba, sannan ba zai yuyu ya tashi ya fita haka kawai ba tare da yace wani abu ba, bugu da kari baida koda kalma Waya da yake ganin zai iya amfani da ita wurin kare kansa, gaba Waya Ruhaima ta gama kunce masa zani acikin kasuwa, ta gama tona masa asirin da ya jima yana binnewa wannan fa shi ake kira da rana dubu ta Sarawo rana Waya tak ta mai kaya, gaba Waya ilahirin falon yayi tsit baka jin komai sai shasshe?ar kukan umaima wanda ya fara karaWe falon,

"wallahi ka cuceni.... Amma ka sani kaima ka cuci kanka kuma na gama zama da kai dan bazan iya cigaba da zama da mazinaci ba....." daga haka ta yi ciki tana rusar kuka bata ko sake bi ta kansa ba,

Sameer kam kallonsa kawai yake a ?ule zuciya ta zo masa wuya amma dai bai yi magana ba dan ya san kome zai faWa to ba mai daWi bane a wannan lokacin shiyasa ya zaSi yayi shiru, mi?ewa ma kawai yayi ya fita, fitarsa babu jimawa itama hajiya ta shiga ciki ba tace da Alhaji sabo ko kanzil ba, nan ya sha zamansa ya gaji daga ?arshe ya tashi yabar gidan.

Yanda ta fito daga gidan hajiya haka taci gaba da tafiyarta tana kuka duk da masu napep na tsaya mata wai ko zata shiga amma sam bata tanka su dan bata jin zata hau abin hawa, tana dab da fita daga cikin unguwar su hajiya taji alamar mota a bayanta ko juyawa bata yi ba duk da uban horn Win da ya addabi kunnuwanta da ?ara, har ya ?araso kusa da ita bata kalli motar ba sai da ta jiyo sautin muryarsa,

"Shigo in kaiki gida....."

Cak! ta tsaya kamar mai nazari, wai shi wannan wanne irin murWaWWen mutum ne? Salon ta shiga yau ma ya yaSa mata duk maganar da tazo ransa? Daurewa tayi ta zagaya ta buWe gaban motar ta shiga,

Tun bayan shigowarta taji ?amshin turarensa wanda ita dai zata iya cewa tun ranar da ta fara ganinsa taji wannan ?amshin kuma har yau bata ?ara jinsa a???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?wurin wani ba,

Shiru motar tayi kamar babu kowa aciki wanda har hakan saida ya takurata, shi Winma kamar kusan hakan ?ila ma wannan dalilinne ya sanya shi kunna radion dake ma?ale cikin motar, daga ita ita har shi ba wani sauraren radion suke yiba, Wan satar kallonsa tayi ta gefen ido, fuskar shi yau babu yabo babu fallasa saSanin irin yadda ta saba gani ko yaushe, a fisge dai yana yi mata kama da Imran sosai sai dai akwai ta inda suka bambanta da yawa, shi Imran fari ne dan za a iya saka shi cikin layin farare amma Sameer ba?i ne bawai chocolate color ba a'a ba?ine sosai amma duk da hakan tana mamakin yadda mutane tun ba yanzu ba suke faWin kyawun Sameer fiye da na Imran koda yake ita bata taSa tsayawa tayi masa kallon ?urulla ba sai dai ta kalleshi a sace shi Winma sau Waya take bata ?arawa, amma dai ta san yanayin tsayinsu da jikinsu kusan duk iri Waya ne dan yanda Imran yake a tsaye shima haka Sameer Win yake sannan wani abu dake sake ruWata shine muryarsu kusan iri Waya dan duk lokacin da taji yayi magana sai taji kamar Imran ne yayi,

Har suka isa gidanta babu wanda yace uffan, bayan yayi parking tana ?o?arin fita yayi ta maza wurin dakatar da ita bayan ya gama tattaro juriyarsa wuri guda dan shima kunyar ta yake ji na maganganun da ya fada mata ba tare da taunawa ba,

"amm.... Dama nace.... Kiyi ha?uri da abinda ya faru ranar nan..... Raina ne a Sace shiyasa...... Kiyi hakuri"

"babu komai.... Ya wuce" daga haka ta fita ta rufe masa ?ofar motar, bai tafi ba saima fita da yayi domin yin sallar azahar yabar motar tashi nan cikin gidanta. Ita dai ciki ta shiga bata sanma yabar motarshi a gidan ba, ko ba komai yau dai ta samu nutsuwa cikin ranta sannan ta samu sau?in halin da take ciki, alwala tayi tai salla bayan ta idar ta yiwa Allah godiya da ya kubutar da ita sannan kuma ya wanketa daga zargi, tana zaune kan abin sallar taga kiran mukhtar ya shigo cikin wayarta, mukhtar wani matashin magidanci ne dake rike da matsayin manager na wani babban store wanda yayi suna sannan yake kan shura har yanzu cikin wannan jaha mai albarka, tunda ya ?yalla ido ya ganta lokacin da suka je shopping ita da Ajmal yabi ya li?e mata, a zahiri dai ta san ba shida makusa duk da bai kai tsohon mijinta ba amma shi dinma zata iya sakashi sahun mazan ?warai sai dai da yake zahiri daban sannan baWini daban haka kuma mutane yanzu sanin ha?i?anin waye su sai ubangiji domin shi kaWai ne masanin sirrin Soye da fili, ji tayi har cikin ranta ta gamsu da mukhtar yanzu sannan tana ganin lokaci yayi da zata bashi dama su sasanta su fahimci juna har su kai ga aure tunda dai yana mutu?ar ?aunarta, gara dai kawaima tayi auren nan ta huta ko ba komai igiyar auren zata tare mata abubuwa da yawa, ayanda dai ya faWa mata matarshi Waya wacce ta kasance cousin Winshi ce domin auren zumunci suka yi sai yaran su guda biyu mace Waya namiji Waya suna zaune a unguwar court road,

Da sallama a bakinta ta Wauki wayar, ita sam bata saba da irin wannan hirarrakin ba da samari tun farko balle yanzu da take zawarci duk dai take jinta wata iri kamar sabuwar Ruhaima bawai waccan Ruhaiman ta asali ba, wani lokacin ma kunya ce ke hanata sukuni bare har ta tsaya ta saurari bazawari sai ta jita duk a takure dan bata saba ba, kai zata ma iya cewa tun tasowarta har tayi aure bata taSa tsayawa da saurayi ba har shi kansa Imran Win basu taSa tsayawa dashi ba, jin amsar da ta bashi wacce ya jima yana jira daga gareta ai bai san lokacin da yace mata gashi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login