Showing 6001 words to 9000 words out of 18502 words

Chapter 3 - SO DA ALAQA Book Complete By Ummu Aisha.doc

01 Nov 2025

848

da?yar na ?wace jakata.... Kai garin in ?wace Winne ma ta Wauko makami tayi amfani dashi ta jimin wannan ciwon da kake gani wanda sai da ta kaini ga zuwa asibiti...... "

Kallonta DPO yayi na Wan wasu sakanni yayin da ita kuma idanuwanta ke kallon ?asa tana zubar da hawayen ba?in ciki da Sacin rai, wannan wacce irin ?addara ce? Alhaji sabo ya yaudareta ya so yaci amanarta ya keta mata rigar mutuncinta Allah ya tsallakar da ita amma yanzu kuma yazo yana yi mata sharri da ?age,muryar DPO ce ta dawo da ita daga duniyar tunanin da ta tafi,

"Hajiya kin aikata laifi kan laifi.... Laifinki da yawa, ta yaya zaki nemi yiwa mutum sata, sannan dan ya kare dukiyarsa kiyi yun?urin Waukar rayuwarsa? This is a very serious case.... We can take it as criminal offense....."

"Ni banyi niyyar yi masa sata ba, asali ma shine ya gayyace ni zuwa guest house Winsa duk da na kawo maganar mu haWu a gidansa amma ya?i yace baida lokaci..... Wannan ciwon da naji masa yun?urin keta min haddi yayi shiyasa nayi amfani da kwalbar giyar dake cikin sitting room Win na buga masa..... "

" sharri zaka yimin Ruhaima? Abin naki harda sharri ya koma? Saboda kin bu?aci mu ?ulla mummumar ala?a na?i amincewa na nuna miki wannan ba halayyar mutanen ?warai bace shiyasa yanzu zaki zo nan kiyi min sharri? Alhaji sabo ya faWa cikin hayaniya kamar gaske,

"Ya isa haka YallaSai... Amm Ruhaima kika ce yayi yun?urin keta miki haddi ko?" DPO ya bu?ata yana Kallonta,

"Ehh yallabai haka nace"

"To a lokacin me ya hana ki kiyi ihun neman taimako? Wanne yun?uri kika yi dan ankarar da mutanen dake ma?otaka da wurin dan akawo miki Wauki?"

"Banyi ihu ba kawai dai nayi ?o?arin ganin na kare kaina...." ta bashi amsa hawaye na bin kumatunta,

"wannan ba hujja bace.... Sannan wannan maganar taki ba wacce hankali zai Wauka bace Ruhaima... Idan har dagaske kike abinda kika faWa cewar yayi yun?urin keta miki haddi to kamata yayi kiyi ihu a matsayinki na mai hankali, sannan ni sai nake ganin babu abinda zai sa ki ziyarci guest house Winsa mutukar abinda kike faWa gaskiya ne, me ya hana kije gidansa? Duk wanda aka ce mace taje guest house abinda zai fara zuwa ransa shine kinje taya shi hutawa ne..... Yanzu dai duk ba wannan ba, Alhaji sabo babu bu?atar mu fitar da maganar nan waje ko mu tura court, kamata yayi kuje gida kuyi sulhu, zamu bada belinta sannan dole zamuyi rubutu saboda gaba, domin case irin wannan bama Waukarsa da wasa..... "

Har suka yi suka gama bata sake furta koda kalma guda Waya ba saboda tama rasa me zata ce, binsu kawai take da ido har zuwa lokacin da DPO yace ta bada no wanda za a kira yazo yayi belinta, bata da zaSi wanda ya wuce ta bada no din hajiya. Hajiya aka kira lokacin tana zaune kan sallaya bayan ta idar da sallar magrib tana azkhar, tana jiyo hayaniyar su Ajmal wanda ke ta ?iriniya dasu Abid wanda suka zo weekend,

A gigice hajiya ta fita da wayar a hannunta bayan ta saurari bayanin da aka yi mata a wayar wai daga police station ne aje ayi belin Ruhaima, part din da ke kusa da nata ta nufa a kiWime dan ?afarta ko takalmi babu tana tafe tana cin tuntuSe,

Fitowarshi daga wanka kenan yana goge jikinsa da towel yaji shigowar hajiya tana ?wala masa kira cikin tashin hankali,

"Sameer..... Sameer..... Kana ina ne? Wai ko baka ciki?"

Jin kiran da take yi masa kamar bana lafiya bane yasashi saurin fitowa a yanda yake daga shi sai gajeren wando da towel a hannunsa,

"Hajiya lafiya......?"

"Babu maganar lafiya Sameer.... Yi maza ka shirya ka tafi police station Ruhaima aka kama.... Sauri kaje ka jiyo me ya faru...."

Saida yaji gabansa ya tsinke ya faWi amma sai ya dake bai bari hajiya ta fahimta ba,

"Hajiya..... Kuma ni zan je?"

"To wa kake so yaje? Ni zanje ko wa?"

Shiru yayi bai amsa ba, sannan cikin halin ko in kula ya kawar da kai,

"kayi maza ka shirya nace maka kaje, ko baka ji?" hajiya ta fada cikin faWa,

"Naji"

Daga haka ya juya ciki, tsaki ya ja ya wuce gaban mirror ya fesa body spray sannan ya wuce gaban closet dinsa, farar jallabiya kar ya ciro yasaka yana jan tsaki, gefen gadonsa yaje ya Wauki wayar shi da key Win mota ya fita yana ta faman ciccin magani,

Part Win hajiya ya shiga, bai bi ta kan yaran dake ta faman guje guje ba a cikin babban falon gidan sannan da alama suma Win babu wanda ya ankara da shigowar tashi,

Samun hajiya yayi ta kasa zaune ta kasa tsaye sai faman safa da marwa take ta faman yi tana ta kaiwa da kawowa a falonta,

"Hajiya wanne division ne?" ya fada fuska ba fara'a, faWa masa tayi ya juya ya fita yana ta SaSSata rai, tafiyar mintuna 30 ce ta kai shi division Win,

Lokacin da yaje iya DPO kaWai da Alhaji sabo ya samu bai ga Ruhaima ba, kamar yadda Alhaji sabo ya tsare dpo ?arya da gaskiya haka ya tsare Sameer wanda kusan gaba Waya ma zancensa ?arya ne,

Sai da suka yi rubutu kowa yasa hannu daga ?arshe aka shigo da Ruhaima dan itama ta saka hannu, kawar da kai Sameer yayi lokacin da take shigowa, fuskar ta jajur da idanuwanta saboda taci kuka har ta gaji, Wankwalinta a hannu sai ko gyalenta dake kanta wanda ta yafa, hannu tasa Sameer yayi sallama dasu ya fita tabi bayansa, handbag Winta aka bata da takalminta, a hannu ta ri?e su dan tsabar ba?in ciki ko takalmin bata saka ba, tana biye dashi har gaban motarsa, ko Kallonta baiyi ba ya buWe ya shiga itama ta shiga ranta a cunkushe kuma a dagule me yafi wannan tozarci da kunya? Ayi mata ?azafin sata da bin maza? Yanzu ta san bata da wata hanya wacce zata wanke kanta sai abinda hali yayi, amma dai abinda ta yarda dashi shine Allah baya zalunci sannan baya bacci, ta san komai daren daWewa Allah zai tona asirin alhaji sabo,

Tunda suka fito daga police station Win bata yi gigin kallon ko inda yake ba sai yanzu da suka hau titi sannan ta saci kallonsa ta gefen ido, sai da tayi danasanin kallonsa saboda yadda taga ya haWe girar sama da ?asa ya cika fam kaWan yake jira ya fashe,

Tu?i kawai yake yi gaba Waya ya tattara nutsuwarsa akai kamar babu wata halitta acikin motar sai shi Waya, ransa a Sace yake tu?in cikin tsananin ba?in ciki, kai tsaye gidanta ya wuce da ita, har cikin gidan ya tura hancin motarsa lokacin da mai gadi ya buWe musu ?ofa, birki yaci da ?arfi wanda sanadiyyar hakan har sai da ta buge kanta amma bai ko kalleta ba, buWe ?ofa tayi ta fita dan jikinta ya bata hakan kawai yake bu?ata ahalin yanzu, tafiya kawai take bata ko sake marmarin juyowa ba taji alamun fitowarsa daga cikin motar shima, tana dab da hawa barandar falonta tajiyo amon muryarsa cikin kaushi yake yi mata magana,

"Be kamata ba sannan kuma ba daidai bane ki rin?a bin mazajen mutane awaje ciki harda mijin ?awarki, mijin ?anwar mijinki dan kawai mijinki ya rasu, sannan saboda tsabar rashin tunani da toshewar basira harda sata..... Tirr.... Akwai mata da yawa da suka rasa mazajensu kuma suka daure suka yi hakuri suka kame kansu suka killace mutuncinsu, idan ba zaki iya ha?uri ba ki rungumi azumi a matsayin magani..... " daga haka ya juya ya nufi motarsa cikin tsananin fushi da Sacin rai, tana tsaye tana kallonsa takalminta da jakarta da Wankwalinta duk sun zame sun faWi awurin saboda jinta take kamar ba ita ba, waWannan ba?a?en maganganun da Sameer ya faWa mata su suka fi yi mata ciwo fiye da abinda Alhaji sabo yayi mata, yanzu ta san ba iya Sameer kaWai ba kusan kowa kallon da zai rin?a yi mata kenan, jarababbiya marar ha?uri ta kasa jure rashin mijinta tana neman wasu mazan, mai halin Sera wadda Allah Allah take taga wasarere ta sata, tana nan tsaye kamar an dasata tana zubar da hawaye har motar Sameer ta fita, tafi mintuna 20 tsaye bayan tafiyarsa dan ba?in ciki dan har ?afafuwanta saida suka yi tsami suka ?age, da?yar ta jasu ta shiga ciki sauran kayanta da ta zubar kuwa nan ta barsu ko bi ta kai bata yiba sai maigadi ne ya shigo mata dasu, zaman dirshan tayi a tsakiyar bedroom Winta tana kuka wiwi saboda ba?in ciki, da?yar ta rarrashi zuciyarta bayan taci kuka ta ?oshi, tana ?o?arin yin shirin bacci lokacin misalin ?arfe 9:30 na dare taji wayar ta dake cikin jaka tana faman neman agaji sakamakon ?arajinta da ya karade ko ina na cikin dakin.......
'


*HASKE! HASKE!! HASKE!!!*=ء?

IT'S *HASKE WRITERS*=ء?AGAIN THE HOME OF EXPERTS AND PERFECT WRITERS
'
HA?I?A JIMIRIN ZAMAN JIRA YA ?ARE MASOYA DOMIN ?UNGIYARKU MAI FARIN JINI TA AMANA WATO *HASKE WRITERS ASSOCIATION*=ء? ITACE TA MOTSO KUMA TA DAWO DAN NISHA?ANTAR DAKU KAMAR YADDA TA SABA, *TAURARI HU?U* SHINE TAKEN TAFIYAR TAMU A INDA ZAMU GABATAR MUKU DA FASIHAI, HAZI?AN MARUBUTA GUDA HU?U DA AL?ALIMANSU CIKIN TAFIYAR DA BABU NADAMA ACIKINTA,

*1.AYUSHER:-*
Writing by FERTYMERH XARAH

*2.?AZAFI NE:-*
Writing by RAHAMA NALELE

*3.DA UBA AKE ADO (Bada riga ba):-*
Writing by ZAINAB BAWA

*4 SO DA ALA?A:-*
Writing by UMMI A'ISHA

WAI WAI WAI... =?%?BAHAUSHE YAYI GASKIYA LALLAI TAFIYA DA GWANI MAI DA?I, NIMA DAI GA NAWA GWANAYEN 4 STARS DUKKA WA?ANNAN LITTATTAFAN GUDA HU?U ZAKU SAMESU CIKIN FARASHI DAIDAI DA ALJIHUNKU....MY SISTER WHAT ARE YOU WAITING FOR?? MAZA HANZARTA KI GARZAYA KI NEMI NAKI DAN ZASU FARA NAN BADA JIMAWA BA, KAR KI BARI A BAKI LABARI..... COMING TO YOUR WAY SOON, DON'T MISS IT =??=??

Guda 4:- 1500
Guda 3:-1200
Guda 2:- 800
Guda 1:- 400

7033027658
Palmpay Bank
Aisha Muhammad Salis
+447894142004

Katin wayar MTN ta...
07044644433 da shaidar biya


*HASKE WRITER'S ASSOCIATION*=ء?


*_Ummi Shatu_*=?L? [15/08, 8:58 am] Baby Aysher: ?? *HASKE WRITERS ASSOCIATION*



*SO DA ALA?A....!*



_*NA*_


_*UMMI A'ISHA*_


*Wattpad:@Ummishatu*


Free page


5


***Driving yake amma tunaninsa na wani waje, shi gaba Waya lamarin mata yanzu tsoro yake bashi ba mamaki ba, banda lalacewar zamani ta yaya mace zata rin?a ?as?antar da kanta tana ajiye darajar da Allah yayi mata tana cire kunyar da aka santa da ita tun tale tale tana kaiwa namiji kanta? Tsaki yaja a karo na ba adadi tun bayan da yabaro gidan Ruhaima, shi dai idan da abinda ya tsana a duniya to zina ce, ya?i jinin zina sannan ya tsani duk wani mai aikatata amma yanzu yaga kamar tama zama ado dan idan mutum ba yayi wai gani ake bai waye ba, sannan masu yi basa kunyar bayyana kansu ya fahimci hakanne dalilin yawan kawo masa hari da mata keyi shi dai ya rasa wannan masifa ya rasa me suke gani atare dashi da suke yawan kawo masa farmaki, da zancen zucin da yake yi ya shiga unguwar su ransa a cunkushe kuma a Sace, sallar ishah ya tsaya yayi sannan ya shiga gida, tun a hanya yaketa ganin kiran hajiya amma bai Waga ba.


Kamar yadda ya tafi yabarta hankali tashe yanzun ma haka ya sake dawowa ya sameta, duk bata da cikakkiyar nutsuwa, yana shiga ta mi?e daga zaunen da take bayan ta ajiye Ajmal a gefe wanda ada yake kwance a jikinta yana bacci,

"Ina Ruhaiman take? Me ya faru? Me ya hadata da ?an sanda har ta kaisu ga zuwa police station? Yanzu ya aka ?are?"

Duk da a cikin fushi yake sai da yayi murmushi jin irin tarin jerin tambayoyin da hajiya ta jero masa lokaci guda kuma ya san kowacce tambaya tana bu?atar amsarta,

" Sameer..... Kabani amsa mana "

" Hajiya ba wata matsala bace babba... Harma ai an kashe case Win, tana can gidanta na sauketa..."

Daga haka ya wuce kitchen, zama hajiya tayi a ranta tana juya wannan al'amari, kwata kwata Sameer ya?i wayar mata da kai ya sakata a duhu ya?i ya bata gamsasshiyar amsar da take bu?ata, kiran da ya shigo wayarta ne ya katse mata tunanin da take yi,

" Umaima....."

"Hajiya kinji bada?alar da Ruhaima tayi ko? Wallahi sai na yi mata rashin mutunci sai na nuna mata true color Wina.... Ta rasa wa zata bi sai mijina?"

Jin abin da Umaima ke faWi yasa hajiya zaro ido cikin duburburcewa dan sam ma sai ta kasa fahimtar inda zancen ya dosa,

" wai Umaima me kike faWa hakane.... Meyake faruwa? "

" Hajiya Sameer bai sanar dake abinda yake faruwa ba?? "

" Bai sanar dani komai ba, kin ganshi shigowarshi kenan ya bani amsa a dun?ule ya?i ya fayyace min komai...."

Daidai lokacin Sameer Win ya shigo cikin falon ri?e da filet wanda ya zubo abinci aciki, jin abin da hajiya ke faWa a waya ya tabbatar masa da Umaima suke waya, ji yayi ransa ya kuma Saci, bai zauna ba ya wuce ya fita shi koma maganar fa ya tsana baya son yaji ana sake maimaitata dan hakan sake ?ona ransa yake yi, wannan wacce irin fitina ce ke damun Ruhaima? Koda yake kusan haka yanzu gaba Waya zamanin ya koma, wasu matan ma suna da auren amma hakan bai hanasu bibiyar wasu mazan ba a waje, shi kansa ba dan kariyar ubangiji ba matan aure nawa ne suka kawo masa hari? Kasa cin abincin yayi saboda damuwa.

In banda salati babu abinda hajiya ke yi jin labarin abinda ya faru da Umaima ta kwashe ta sanar da ita yanzu kamar yadda itama Alhaji sabo mijinta ya sanar da ita babu abinda ta ragewa hajiya ta sanar da ita komai, jiki a sanyaye kuma a mace hajiya ta kashe wayar bayan ta gama jin abinda ya faru, tabbas ta san Ruhaima tana da nutsuwa da kunya da halin ?warai to amma yanzu ba a shaidar mutum shine matsalar, mutum yana iya canjawa akoda yaushe sannan kowanne mutum tara yake bai cika goma ba, haka kuma wani abin ?addara ce wadda babu yadda mutum zai yi da ita, ita ta Wauki Ruhaima tamkar ?ar da ta haifa ta cikinta ba wai sirika ba, duk abinda zata yiwa Wan cikinta shi zata yiwa Ruhaima,wayarta ta sake Wauka ta fara kiran layin Ruhaima,

Jiki a sanyaye ta ?arasa gaban handbag Winta ta ciro wayar ganin hajiya ce me kiran yasata jin kunyar duniya ta lulluSeta ta san Sameer yaje ya sanar da ita halin da ake ciki,

"Haba Ruhaima.... Ya ina yabon ki salla amma zaki kasa alwala.... Dan kina cikin wani hali Ruhaima sai ki kifara ?o?arin Sata rawarki da tsalle?? Ai ko wani ne awaje Ruhaima bai dace ki kai masa kanki ba harda yun?urin sata bare mijin Umaima....."

"Hajiya dan Allah ki fahimceni ke kadai na san zaki fahimceni akan wannan lamari wallahi yanda ake tunani ba haka abin yake ba...." ta faWa cikin kuka,

"Wannan ai ya wuce Ruhaima sai dai a kiyaye gaba, dukkan Wan adam ajizi ne amma ki kiyaye, dan Allah.... Ni tunda Sameer ya dawo naji ya?i magana dama naji hankalina bai kwanta ba sai da Umaima ta kirani yanzu, Allah ya rufa asiri amma ki kiyaye dan Allah" daga haka taji hajiya ta katse wayar, take kuma wani kiran ya sake shigowa kamar dama jira ake, ganin Umaima ce sai da gabanta yai muguwar faWuwa,

"Hello inlaw....."

"Karki fara... Karki kuskura ki sake kirana da haka Ruhaima... Ai baki Waukeni a hakan ba tunda har kike bibiyar mijina, dama wannan shine dalilin da yasa kika zo har gida neman sa?"

"Dan Allah ki fahimceni Umaima, kema kin san wallahi ko a mafarki bazan taSa aikata hakan ba...."

"Daga yau sai yau wallahi babu ke babu mijina, idan kika sake yun?urin kusantar mijina zaki gane shayi ruwa ne......"

"Umaima karki bari shaidan ya shiga tsakaninmu dan All....." ?itt taji Umaima ta datse kiran, wasu hawayen ba?in ciki ne suka sake Sarke mata, daman ta san yanzu babu wanda zai yarda da ita kowa kallon mai laifi yake yi mata duk da irin kokarin da hajiya ke yi a kanta ace ta aikata haka ai da ta tabbata butulu, kukan nan dai shi take ta yi har tsawon wani lokaci da ita kanta bata sani ba.

Samun kansa yayi cikin wani ?arin Sacin ran a duk sa'ilin da ya tuna wayar da yaji hajiya suna yi da umaima, wato Alhaji sabo sai da ya kwashe duk abinda ya faru ya fadawa umaima kenan saboda tsabar rashin kara, Meyasa bazai rufa mata asiri ba sai ya sake zubar mata da mutunci acikin family? Haushi ne ya kamashi ya ja tsaki,

"Kawai salon ta jawowa mutane magana..... Sai da ta dauko mana magana dai hankalin ta ya kwanta" ya faWa cikin Sacin rai yana tashi daga kwancen da yake kan madaidaicin gadonsa,

Kukan magensa ne ya sake tunzura shi, dan shi yama manta da ita, ba dan ya so ba ya mi?e ya buWe ?ofa, yana buWewa ta shigo tana shinshina ?afarsa sunkuyawa yayi ya Wauketa yana shafata, ganin tana lasar baki yasa shi dafe kai,

"am sorry pretty.... Yau ban baki abinci ba sai sau Waya... Wallahi kaina ne a caje daren yau Winnan...." Saman gadonshi yaje ya Worata sannan ya fita, part Win hajiya ya sake komawa bai jima ba ya fito ri?e da glass cup cike da madarar kwali sai abinci a wani Wan ?aramin filet, part Winsa ya koma ya Wauki magen ya Wora akan cinyarsa ya soma bata abincin da madara tana ci,har ta cinye tas ya kwantar da ita kusa dashi, haka dama yake rayuwa da wannan magen wadda ya sakawa suna pretty tun tana yar ?arama da ya tsinceta a lambun gidan ya Waukota, tare suke kwana.


Da ?yar ta samu bacci daren ranar dan sai bacci Sarawo, bayan asubah ta samu ta farka, amma tana farkawa abinda yafara zuwa ranta shine abinda ya faru jiya, take ta ji wani sabon bakin ciki ya sake turnu?eta sai da ta share hawaye sannan ta shiga bathroom ta Wauro alwala tazo tayi salla, bayan ta idar ta Wauki alqur'aninta dake ajiye gefe ta karanta abinda ya sawwa?a sannan ta rufe ta soma azkhar. Wunin ranar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login