Showing 1 words to 3000 words out of 33181 words
Chapter 1 - MAJANUNI BOOK 4 BY BINTA UMAR ABBALE.txt
61&62
Wani irin kallo take masa. bakinta na rawa magana ta take so tayi amma tsabar tashin hankali! da mamakin al'amarin ya sa bakinta yin nauyi, ta gagara furta komai sai kallonshi take tana ayyana abubuwa da yawa a kansa, gaskiyar magana yau ne ta tabbatar da cewa yana da matsalar kwakwalwa, kamar yanda jama'a suke zarginsa, idan ba mara hankali da tunani ba waye zai d'auki matar auransa ta sunnah ya mi'ka ga wani 'kato, tabbas basu da hankali! gabadaya har maigidan nasa dukkaninsu suna bukatar ganin likitan k'wak'walwa! ita kam ba zata yarda da wannan yahudancin ba, tana ganin duk abinda zai faru sai da ya faru, ba zata amince da wannan manufar ba.
To bayan tafiyarsa sai ta kasance cikin damuwa da tunanin hanyar da zata bi gurin ganin ta warware matsalarta, gaskiyar lamari barin gidan shine samun nutsuwarta, ashe dama wannan matsalar Baba Asabe ke hango mata, gashi kuwa tun ba a je ko'ina ba al'amura sun jagwalgwale.
Ita kanta Hajiya Saude kwana biyu ta kasa gane me yake damunta, domin ko ta je gurinta ba ta iya sakin jikinta, suna gaisawa take tafiya domin ba ta yarda ta zauna maigidan ya same ta, gabad'aya ta sanja taku a gidan, da wurwuri take kukkule ko'ina na sashenta, sai ta shige can uwar daki ta kulle kanta, duk a kokarinta na tsaretar da rayuwarta.
Sai dai duk yunkurin da za tayi masu tsaron gidan idonsu a kanta, domin zuwa yanzu sun santa a gidan, amma ba su san matsayinta ba.
Sai ta sanja shawara da kuma shirya yanda za tayi ta gudu daga gidan.
Ranar Juma'a ita ce ranar da gidan ke cika da jama'a maza da mata domin a ranar ne maigidan ke raba kud'i ga mabukata.
To tana ganin za tayi basaja ne kawai ta shiga cikin jama'ar a matsayin mai neman taimako.
Gidan ya cika sosai da jama'a gabad'aya masu tsaron gidan suna can suna shirya mutane domin su daidaita layi kafin ya fito, wannan ya bata damar shiga jerin matan da suke ja dogon layin da ba zai 'kirgu ba.
Sule ya fito ya sanar musu da cewa; saboda yamma tayi kuma dab ake da a kira sallar magariba su yi hakuri sai anyi sallah tukkuna maigidan zai fito.
Babu wanda ya nuna damuwarsa da hakan, kowa dai burinsa ya samu abinda zai sa a aljihunsa.
Fitowarsa ta hango sai tayi saurin sunkuyar da kanta. tana addua Allah yasa kada ya gane ta.
Jama'a su ka dinga zubewa suna kwasar gaisuwa, ya amsa daidai gwargwado kafin ya wuce zuwa massalacinsa dake jikin gidan, wasu suka bi bayansa wasu kuma suka gabatar da sallarsu a cikin gidan mussaman mata tunda akwai manya manyan rumfuna dake shimfide da kafet da tabarmi.
Kan wata kujera ya zaune a nutse ya fara gudanar da abinda ya tarasu a gurin.
Duk wanda aka bawa zai yi godiya ya kama hanya ya fita cikin farin ciki da annashuwa.
Layi yana ta tafiya har aka zo kanta, kallo daya yayi mata ya gane ko wacece a gabansa, mamaki sosai ya kamashi, sai ya tsira mata idonsa kamar koda yaushe, ita kuma sai jikinta ta daburce! da sauri ta dauke kanta tana sake gyara zaman hijab din da ya rufe mata fuska sai 'kwayar idonta kawai ake gani.
Sannu take mik'a masa tana risinawa wai ya bata kudin. bai yi 'kasa a gwiwa ba ya bata domin ganin abinda take shirin aikatawa domin ya tabbatar da zarginsa. aikuwa tana kar'ba hanyar fita ta nufa da saurin gaske.
Da azama ya juya in da escort d'inshi biyu ke tsaye a kansa.
Duka suka sunkuyo domin jin umarninsa.
Da sauri wanda yake hannun damarsa ya nufi bakin gate wanda a lokacin har tasa kafarta a waje za ta fita, aka dakatar da ita.
Gabanta ya buga da karfin gaske! shikkenan ta faru ta kare.
Jami'in tsaron ya nuna mata bindiga kafin ya bata umarnin komawa ciki da hannunsa.
Da sauri ta bi umarninsa ta koma ciki domin ba ta so hankalin jama'a ya dawo kansu, dama yanayin kallon yayi mata tasha jinin jikinta cewa ya sheda ta.
Ganin masu tsaro gidan da masu gadin hankalin su ya karkata wani guri da sauri ta kama hanyar sashenta tana ta addua a cikinta.
Rurrufe ko'ina tayi ta zube kan kujera! sai kawai kuka ya 'kwace mata, wannan masifa dame ta yi kama? shikkenan haka za tayi ta zama cikin fargaba da damuwa, wai shin ya za tayi ne da rayuwarta.
Abokiyar shawararta wato zuciyarta ita ce ta tunasar da ita cewa dukkan tsanani yana tare da sauki, kuma Allah yana nan saboda haka ta nemi sauki a gurinsa.
Don haka sai ta ji k'warin gwiwa! lallai wannan shawarar ita ce abin yi.
Alwala tayi ta gabatar da nafila raka'a biyu sannan ta daga hannunta tana zubar da hawaye take rokon Allah ya kawo mata sassauci a rayuwarta, Allah ya zaba mata abinda ya fi alheri.
Da safe ta tashi sakayau! lallai ta yarda al'kur'ani yana maganin kowace irin masifa, kuma dukkan wanda ya shiga damuwa ya mika lamuransa ga Allah zai isar masa.
Kwana d'aya biyu babu wani lamari na tashin hankali da ya biyo baya duk da cewa sun had'u amma bai yi mata komai ba ballantana ya tuhume ta akan matakin guduwa da ta d'auka!
Ranar litinin da sassafe Hajiya ta je asibiti domin a duba lafiyarta, tare da Shukura su ka tafi domin daga Asibitin za su wuce wata unguwa.
Da k'warin gwiwarta ta shiga da sallama a bakinta.
Sai dai ganinsa a hakimce! a kan kujera ya tsoratar da ita, da sauri ta juya da nufin fita.
Ya dakatar da ita babu yabo babu fallasa ya ce." Ya zaki juya kuma ko ba gaida Hajiya ki ka zo ba?"
Kanta kawai ta iya daga masa alamun "Eh hakane"
Ya bata umarnin zama da fadin." Zo ki zauna yanzu za ta fito.''
kallonsa tayi amma bata yarda da maganarsa ba domin a irin wannan lokacin take samun hajiyan a zaune a falo a duk sanda ta zo gaishe ta.
Ya ce." Matsalata dake gardama zo ki zauna na ce." Yafada yana nuna mata saman kujera.
A jiyar zuciya ta sauke a tsarge ta je ta zauna kasan k'afafunsa domin babu yanda za a yi ta zauna kan kujera bayan yana kai.
K'amshinsa ne duk ya cika mata hanci! jikinta yayi la'asar, a duk sanda za ta ji 'kamshin jikinsa sai ta rasa gane abinda yake damunta, ita dai 'kamshin yana mata dad'i
Tsaye ya mi'ke tayi saurin kallonsa sai ta ga ya nufi hanyar fita, ta sauke sanyayyar azuciyar zuciya domin duk a zaton ta fita zai yi ga mamakinta kawai sai ta ga yana kulle kofar da key (mukulli) "Innalillahi wa'ina ilahi raji'un! wannan kalmar ta kira kafin ta tashi tsaye suka hada ido a lokacin da ya juyo. ta tsorata da ganin yanayin fuskarsa don babu fara'a ko kad'an.
Daf da ita ya tsaya saura kadan jikinsu ya had'u.
Ta ja da baya, ya sake matsowa ta sake ja da baya! Still ya sake kusantarta! sai ta daga hannu da niyyar tayi masa gargad'i! ya bar abinda yake, ya r'ike hannun ya had'a da nasa yatsun suka had'u guri d'aya! wani irin taushi tafin hannunsa.
Jin saukar hannunsa kan mazaunata yana kokarin rungumeta, ta fizge jikinta ta matse gefe kwalla duk ta cika kwarmin idonta.
Wannan mutumin shu'umi ne!
Gabad'aya ta sanya hannu ta 'kan'kame kirjinta. domin ganin yanda ya tsira musu ido.
Murmushi yayi gabad'aya kwayar idonsa ta sauya.
Bud'e muryarsa yayi sosai kafin ya ce." Kwanaki ina ki ka shirya zuwa ne? ki ka yi basaja cikin mutane, ko kin dauka ba zan gane ki ba.
Kai tsaye ta ce." Zan gujewa sharrin ka ne."
"Da gaske?" yafad'a yana lumshe mata tsummamun idanuwansa da suka 'kankace!
Kai ta daga da fadin." Kwarai kuwa domin zama a wannan gidan had'ari ne ga rayuwata.
Le'bansa ya d'an lasa kafin yayi wani munafikin murmushi ya ce." Ai kin shigo gidan nan kenan har abadah."
Wani kallo tayi masa mai kama da harara! sosai kallon ya tafi dashi, jikinsa ya 'kara rikicewa.
Ya nemi kujera ya zauna yana sauke ajiyar zuciya.
"Sonki nake yi." ta ji sautin maganarsa yana fad'in wannan kalma.
Ta dinga kallonsa a lokacin da yake ta nanata maganar...."Sonki ne keyi ina sha'awar ki mallaka min kanki"
Wani tashin hankali ta shiga a lokacin ta kalle shi wanda har yanzu ita yake kallo irin kallon da ta tsana!
ta ce." Har abada na haramta a gare ka domin komai kulafucin ka na fi karfinka."
Murmushi yayi ya d'an sake lasar le'bansa a karo na biyu! gabad'aya sha'awa ta gama kashe masa, Ya ce" Ki daina cika min baki domin idan kin shiga hannuna ba zan sassauta miki kawai ina so mu yi komai cikin nutsuwa da walwala shiyasa nake rarrashinki."
Ta ce" Ba zaka ta'ba samun biyan bukatarka."
Sai ya tashi ya nufi gurin da take. tayi sakare domin ta d'auka wani abin zai mata. kawai sai ta ga ya zube a gabanta gwiwarsa a 'kasa ya 'kask'antar da kansa tare da rauntar da murya cikin sigar lallashi da yaudara ya ce....
[1/12, 11:25 PM] Binta Umar Abbale: 63&64
"So nake ki amince da b'ukata ta, ina nufin ki mallaka min kan ki koda na rana d'aya ne, wallahi ni kuma nayi miki alkawarin faranta miki rai, tun daga kan miliyan d'aya zuwa miliyan d'ari zan mallaka miki mutukar zaki bani kanki, sannan zan saya miki mota mai tsada, na kuma gidanawa mahaifinki gida, ke nayi miki alk'awarin duk danganinki za su fita daga cikin kangi na talauci muddun kin amince min na dand'ana zumar ki, wallahi zan iya sadaukar miki da duk abinda na mallaka."
Yana maganar ne a lokacin da yake ka'sk'antar da kansa amma ya bud'e muryarsa sosai yanda za ta ji sa'kon nasa!
Ta dinga girgiza kanta tana auziyya a cikin ranta, wasu hawaye masu d'umi! ne suka shiga sauka a kumatunta, dama duk wani kwane-kwane da yake ta riga ta fahimci abinda yake bukata kenan da ita, ko ga yanayin kallon da yake mata a duk lokacin da suka had'u! ai talauci ba hauka bane, tana ganin ko me zai mallaka mata ba zata amince da bukatarsa ba.
Ganin tayi shuru kawai tana kallonsa da hawaye a fuskarta, sai ya tashi jikinsa na rawa! ya 'kan'kameta yana shashshafa bayanta sai kisses yake mata har ya samu nasarar cire mata dankwalin kanta yana hargitsa mata gashi wanda ta wanke ta d'aure shi da ribbon.
Wani 'karfi ne ya zo mata a lokacin, ta ture shi tare da kurma uban ihu! ta sa hannuwanta duk biyun aka tana kiran sunan Allah! kuka take tukuru! dan ganin yanda yanayin sa ya sauya gabad'aya! ya rikirkice! yana nema ya kwantar da ita a saman kujera tana duddukansa ta ko'ina! kuma ba ta fasa kurma ihu ba tana kiran Allah ya kawo mata dauki.
K'arfi ya sa mata sosai ya ri'ke ta da kyau! don ganin ihun da take yana nema ya tarwatsa 'kwanyarsa! ya matse ta a jikin bango! sannan ya had'e bakinsa da nata! gam! ya ri'ke ya hana ta ihu! a lokacin da bakinsu ya had'u ji tayi kamar an bubbuga mata 'tabarya a k'afafunta sai kyarma take tana ta so ta k'wace bakinta abin ya fassakara, ya ri'ke harshenta da kyau! so yake kawai ta samu nutsuwa!
Sanyi jikinta yayi sai uban hawayen da yake gararanba a saman fuskarta, wanda shima tasa fuskar duk ta ji'ke da ruwan hawaye, ba kuka yake ba amma tsabar tashin hankalin da ya ke ciki a lokacin ya sanya kwayoyin idanuwansa mugun ja! ita da shi suka dinga rawar jiki ita dai na tsananin tashin hankali da fargaba ne, shi kuwa na tsantsar sha'awa ne da bukatuwa zuwa wani abu da yayi shekara da shekaru bai samu ba.
Sai da ya tabbatar ta nutsu jikinta ya mutu sannan ya cire bakinsa daga nata, ya dan ja baya tare da zuba hannuwansa cikin aljihu yana yi mata wani irin kallo na tausayi da mugun so!
Ta zube 'kasan 'kafafunsa tare da ri'ke daya ta ce" Don darajar Allah da Annabi ka da ka aikata fasadi dani, kada ka janyo mana fushin ubangiji! zina babu kyau! mussaman ga masu aure hukunci mai tsanani Ubangiji ya tanadar ga masu aikata wannan lamari, wallahi tunda nake ban ta'ba zina ba, kuma bana fata na fara da kai, bana bukatar komai daga gare ka, ni na yarda na cigaba da zama matalauciya mai rangwamin gata, shin wai ma me za kayi da ni? duk ga mata nan a gari kyawawa masu aji da kyawun jiki, mai za kayi da iri na nakassashiya mara gata, kana da kudi ka je ka nemi irinka amma ni don girman Allah ka fita daga cikin rayuwata.
Cikin tsantsar tashin hankali da kuka matsananci take wannan maganganu.
Amma ko a fuska bai nuna sadudarsa ba ya cire k'afarsa tare da komawa kan kujera ya zauna yana kallonta babu alamun sassauci a tare da shi ya ce.'' Wannan shine karo na farko dana bukaci wani abu a gurin wata 'ya mace ta yi min gardama! kamar ni, na nemi da ki bani kan ki, amma ki cika min kunne da ihu! har kina kai min duka da cizo da yakushi! wai shin meye a ciki ne? na farko dai wannan lamari idan ya faru tsakanina dake ne, babu wanda ya ji ko ya gani, amma duk kin tashi hankalinki a banza a wofi wanda ni kuma duk abinda za kiyi ba zan janye kudiri na ba, dole sai na kwanta dake domin zuciya da gangar jikina suna bukatar hakan, saboda haka zan baki kwana uku ki je kiyi tunani, amma ki zo min da abinda zan gamsu, tunda na fada miki ni dai ba zan iya hakuri dake ba. cikin jaddada aniyarsa ya kai karshen maganar.
Hannu tasa ta goge ruwan hawayen da yake zuba ta ce." Wai kai baka tsoron Allah? ba ka tsoron ranar da zaka tsaya a gabansa, ranar tonan asiri, ranar da kudi da mulki ba za suyi tasiri ba, a ranar ne Allah zai nuna wa jama'a waye kai cikinsu kuwa harda mutanan da suke ganin girma da mutuncinka, a gidan duniya, kowa yana ganin girmanka, dalilin taimako da sadaukarwar da kake da dukiyarka, a zahiri kai mutumin kirki ne, amma kuma wani 'bangaran ka samu nakasu! saboda miyagun halayen da kake aikatawa irin wanda Allah ya haramta.
A cikin al'kur'ani mai girma Ubangiji subahanahu-wata'ala ya umarce ku da ku aura daga d'aya zuwa biyu da abinda yayi sama, mutukar kuna da iko kuma za kuyi adalci." Ta d'an sauke ajiyar zuciya kafin ta cigaba da cewa; Allah yayi maka komai na daga jin dadin duniya ya wadataka da arziki da rai da lafiya da ji da gani bai tauye ka ba, to mai zai sanya ka butulce masa? kana da dukiyar da zaka auri mata hud'u ka ajiye a gidanka domin raya sunnar ma'aiki salallahu alaiyi wassalam, amma kana zubar da 'kima da mutuncinka, ka sani cewa duk abinda ka yi a kan dan wani sai anyi da naka, saboda haka ka ji tsoron Allah ka daina bibiyar rayuwata."
A maimakon jikinsa ya mutu da nasihar ta, sai kawai ta ga yana murmushi tare da wasa da gemunsa kamar wacce tayi abin dariya sai kallonta yake yana murmushi, tsayin mintina uku kafin ya ce" Na gode da nasiha malama, amma ina sheda miki cewe; ina nan akan bakana, ba zan janye kudiri na ba, dole zaki bani kanki ko kina so ko ba kya so, ki je kiyi shawara na baki kwana uku kamar yanda na fad'a miki da farko." Ya na gama maganarsa ya tashi ya haye sama ya bar ta zaune a gurin cikin tsantsar damuwa da tashin hankali.
A tsakanin kwanakin sosai ta mayar da hankalinta gurin karatun al'kurani mai girma tare da shedawa Allah damuwarta, a yanzu dai ba ta ga tsuntsu ba ta ga tarko, dalili babu wanda za ta je ta fada masa damuwarta saboda wayar da take hannunta ma tun ranar da su kayi magana da Saliha ya 'kwace! har ya tafi bai bata ba.
Tana dai zaune a gidan tare da mi'ka lamuranta ga Allah.
Yau ne cikar kwanakin da ya gindaya mata.
Tayi ta k'o'karin danne damuwarta amma hakan bai samu ba, sai da Hajiya Saude ta fahimci damuwa a tattare da ita a lokacin da ta shiga domin gaishe ta.
Ta kalle ta, kafin ta ce." Shahida cikin kwana biyun nan ina ganin damuwa a tare dake ko da akwai wani abu da mu ke miki?"
Ta ji kamar ta fad'a mata abubuwan da suke faruwa, sai kuma wata zuciyar ta tsawatar mata saboda gudun abinda ka iya zuwa ya dawo, watakila idan ta tona maganar ita ce zata kwana a ciki, domin babu wanda zai yarda da ita.
Ta girgiza kai da fadin." Hajiya babu komai kawai dai bana jin dadin jiki na ne."
Tayi murmurshi kafin ta ce" Wai cikin naki wata nawa ne?"
Da sauri ta ce." Hajiya bani da ciki fa."
"Ke haba dai 'yar nan, to wannan laulaye-laulayen da ki ke na menene?"
Shuru tayi ba tace komai ba.
Shukura ta fito daga d'akinta ta shirya tsaf sai kamshin turare take, ta nemi kujera ta zauna hankalinta a kan wayarta ciki bada Umarni ta ce." Ke Shahida ki shiga dakina ki gyara min sannan kuma ki wanke toilet."
Hajiya Ta ce." Ai yau sai dai kiyi da kan ki ba ta da lafiya"
Wani irin kallo tayi wa Shahidan tana ta'be baki da fad'in." Hajiya gaskiya ba zan iya wani abu ba yanzu na riga nayi wanka ai d'akin nawa babu wani datti sosai! kawai ta tashi ta je tayi dama