Showing 27001 words to 30000 words out of 33181 words

Chapter 10 - MAJANUNI BOOK 4 BY BINTA UMAR ABBALE.txt

ce" Shikkenan zanyi 'kokarin ganin nayi hakan muddin zan fita daga zargi don bana so wani abu ya same ka mutane su ce ni ce sanadi.

Murmushi yayi, yana min wani irin kallo kafin ya ce'' Babu wanda zai zarge ki don kin taka sawun 'barawo, kin 'karasa gawar da ba taki ba, dama can bani da cikakkiyar lafiya, ko da Hajiya tayi wannan maganar, ba da wata manufa ba, tayi ne domin ki gyara kuskuranki, ma'ana ki zama mai kula da mijinki domin ki samu rabauta ranar gobe 'kiyama."

Sunkuyar da kaina nayi tare da wasa da yatsun hannuna, ya tashi a hankali ya nufi band'aki cikin 'kwarin jiki, sai kawai na tsinci kaina da bin sa da kallo da tausayinsa 'kadan a cikin raina.
[1/12, 11:25 PM] Binta Umar Abbale: 88&89
Gadon na shiga bi da kallo kamar me neman wani abu. wayoyinsa ne akai sai farin gilashinsa da kuma littafin husunul muslim a ajiye a gefe, sai kuma 'kamshin turaransa da ya mamaye d'akin, komai nasa a tsanake babu harigido a ciki, dattijo ne mai kamala da hallin dattako.

Ajiyar zuciya na sauke tare da tsirawa k'ofar 'bandakin ido! fitowarsa daga band'akin yasa nayi gaggawar d'auke kaina, kai tsaye 'katuwar wardrobe din da ta cinye bango guda ya nufa yana neman kayan sawa.

A nutse na je na tsaya a kusa dashi tare da fad'in" Ka je ka zauna na duba maka kayan.

Kallo na yayi da mamakin magana ta.

Sai na d'an saki fuskata tare dasa hannuna kan kayan nasa ina dubawa.

Ban an kara ba kawai na ji shi a jikina, ya zagaye k'ugu na da hannuwansa tare da d'ora ha'barsa a kafad'ata.

Cikin fad'uwar gaba na juyo rigar dake hannuna ta fad'i a gurin.

'Kokarin k'wace jikina nake yana sake matse ni a jikinsa dake wani irin karkarwa!

'Kafafuna suka shiga kyarma! jin yanda yake yawo da hannuwansa a sassan jikina.

Kuka nasa tare da ture shi da 'karfi na matsa gefe ina gyara zif d'in rigata da ya zuge min.


Da azama! na kama hanyar fita, sai yayi saurin tarar gabana, ya sanya mukulli a jikin 'kofar d'akin, ba tare da ya ce komai ba ya ja jikinsa da babu 'kwari ya hau gado ya kwanta har da jan bargo.


A sanyaye na ce" Ka bud'e min 'kofar na fita.

Shiru yayi be ce min komai ba.

Ganin haka yasa na zauna kan kujera tare da zabga tagumi! abinda yayi min yanzu ya tsorata ni, mutumin da bashi da lafiya.

Motsin ta'ba 'kofa na ji sai nayi sauri na kalle shi har yanzu yana cikin bargo a lullu'be.

Na ce" Za'a shigo fa."

Shiru babu amsa.

Gurinsa na nufa domin neman mukkulin, ya bud'e fuskarsa da alamun bacci ya bani mukullin da fad'in."Amma don Allah kada ki ce zaki koma wannan gurin ina bukatar ki zauna tare dani, ina neman wannan alfarmar."

Jikina ne yayi sanyi jin yana had'a ni da Allah kamar ya san kud'iri na kenan. Ni kaina ina jin wani iri a duk lokacin da yake 'kas'kantar min da kai.

A sanyaye na je na bud'e 'kofar. Shukura ce ta shigo hannunta ri'ke da kwandon abincin. wani irin wula'kantaccan kallo tayi min kafin ta wuce cikin d'akin.

Sosai raina ya 'baci da iskancin da yarinyar take min, idan tayi min wulakanci a can baya nayi ha'kuri, to yanzu zahirin gaskiya ba zan iya jura ba, domin kuwa a matsayin uwa nake a gurinta ko tana so ko ba ta so dole ta girmama ni kamar yanda zata girmama mahaifinta. idan ma ba zata gaishe ni ba to ba zan jure kallon banza da zagi ba.

K'ofar na rufe na je na zauna ina kallonta tana fad'in" Daddy ka tashi ka ci abinci ka sha magani."

Na kalle ta babu walwala a fuskata na ce" Ki rabu da shi mana ko ba kya ganin bacci yake?"

Ta juyo a fusace! tare da cewa" Kin ga malama kada kiyi min shishshigi"

Kafin nayi magana har ya 'bud'e fuskarsa. rai a 'bace! ya kalle ta da fad'in" Tun da kin kawo min abincin, tashi ki je kawai."

A sanyaye ta tashi ta fita kamar ta fashe da kuka.

Na kalle shi yana 'ko'karin sake rufe fuskarsa na ce" Yana da kyau! ka tashi ka ci abincin sai ka sha magani ko."

Minti biyu da magana ta ya ta shi tare da cire bargon dake jikinsa ya sauko da 'kafafunsa 'kasa! sai kuma na ga ya dafe kansa da duk hannuwansa.

Ganin haka sai jikina yayi sanyi na tashi na je kusa dashi na zauna. Cikin zuciyata nake jin d'an tausayinsa, da alama yana jin jiki daurewa kawai yake. kafad'arsa na dafa a hankali na ce"Sannu kan ka ne yake ciwo ne?"

Girgiza kansa yayi ba tare da ya kalle ni ba.

Na sauke ajiyar zuciya da fad'in" Na ga ka dafa kai ne, shine nake tunanin ko ciwon kai ne ya matsanta maka.

Ya cire hannuwan nasa tare da zuba min ido.

Kasa kallonsa nayi sakamakon ganin yanda 'kwayoyin idanuwansa suka sauya jajawur! yanayin kallon da yake min ne yasa jikina mutuwa! gabana kuma na cigaba da fad'uwa!


Hannu na ya ri'ke tare da fad'in" Ina da damuwa mai tsanani."

Nayi shiru ina kallonsa. Ya cigaba da cewa; Kasancewar ki a kusa da ni ya janyo min sha'awa mai tsanani, gashi idan ina cikin wannan halin bana iya sarrafa kaina."

Na kalle shi a lokacin da yake bin ilahirin jikina da kallon kurulla, gabad'aya yanayinsa ya sauya yayi sanyi sosai, hannunsa dake ri'ke da nawa sai karkarwa yake.


"Yanzu me ka ke bu'kata?" Na tambaye shi duk da na harbo jirgin nasa.

"Ki mallaka min kan ki a wannan lokacin." Ya fad'a tare da kusantar jiki na.

Kai na girgiza. alamar ba zan iya ba.

Ya ce."Saboda me?" Shiru nayi ban bashi amsa ba saboda na san da cewa bani da wata hujja.

Rungume ni yayi tsam! a jikinsa! yana makyarkyata! kuka nasa ina ture shi tare da fad'in" Ka rabu da ni don Allah.

Cikin kunnuwana na ji yana fad'in" Ki taimaka min na rage damuwa ta shekara da shekaru matata ba zan cutar dake ba."

"Ni dai A'a ban shirya faruwar hakan ba.'' Cikin shagwab'a da sangarta nayi maganar ina kokarin raba jikina da na sa.

Yanda na fahimta hakan da nake kamar 'kara masa 'karfin gwiwa nayi domin rikicewa yayi yasa 'karfi sosai ya kwantar dani kan gadon yayi min rufa!

Sosai nayi mamakin abubuwan da yake min tamkar ba mara lafiya ba, hannayensa sai yawo suke a sassan jikinta.

Gabad'aya gwiwa ta tayi sanyi sakamakon abubuwan da yake min, 'kamshin jikinsa ma ya taka muhimiyyar rawa gurin hana ni 'kwatar kaina.

Kamar a mafarki mu ka ji an bud'e 'kofar d'akin an shigo
da saurin gaske ya sauka daga kaina tare da juyawa domin ganin waye ya shigo. gefen rigarta kawai mu ka yi katarin gani domin da saurin ta bar gurin ba tare da ta rufe 'kofar d'akin ba.


Takaice yasa na fashe da kuka da fad'in" Ka gani ko?"

Ba tare da ya ce komai ba ya juyo da nufin sake kwantar da ni, sai na matsa gefe da sauri ina gyara wuyan rigata, sauka nayi daga gadon, k'afafuna sai rawa suke, na ce" Yanzu kayi wannan abun ya za a yi su yarda baka da lafiya.

Murmushi kawai yayi ya tashi ya shiga band'aki ba tare da ya ce min komai ba.

Na zauna kan kujera gabana sai bugawa yake, komai yana bu'katar sirri ya zama dole ya takawa yarinyar nan burki ta daina bankad'o mana d'aki tana shigowa ba tare da neman izini ba.

Ko da ya fito daga toilet din ban iya kallonsa ba, saboda tawol ne d'aure a jikinsa, cikin zuciyata na ce" Dole ciwo yayi ta damunsa ko da yaushe cikin watsawa jiki ruwa.

Band'akin na shiga na tsafta ce jikina, domin ni kaina ban yarda da kaina ba, abinda ya faru a tsakaninmu yasa wandon dake jikina ya 'baci! wanke wa nayi na shanya a band'akin na fito na same shi a zaune kasan kafet yana duba wayarsa.

Har nayi nufin zama kan kujera, na ji maganarsa. "Kada ki zauna zuba min abinci nan." Ya fad'a ba tare da ya kalle ni ba.


Na zuba masa daidai gwargwado na ajiye a gabansa, niyyar barin gurin nayi, ya ce" Zauna ina so muyi magana.

Zama nayi kaina a 'kasa


Ya ajiye wayar hannunsa a gefe, kafin ya kalle ni, ya ce." Za mu ci abincin tare ko?"

Girgiza kai nayi. Ya ce." me ki ka ci to?" shiru nayi masa tare da d'auke kaina. Ya ce." Na fara gajiya fa da wannan abubuwan da ki ke min zan kai 'karar ki gurin mahaifinki"

Kallonsa nayi da mamakin maganarsa, ya ce." 'Kwarai kuwa! ki kalle ni da kyau! kin san a shekaru na haife ki ko? amma na ajiye girmana ina rarrashinki duk don mu zauna lafiya kina min wasu abubuwa saboda kin fahimci cewa Allah ya jarrabe ni da sonki shin ko ba haka bane?"

Ban ce masa komai ba.

Ya cigaba da cewa" Ki kula da ni a matsayin mijinki, kiyi kokarin sauke hakkina dake kanki kada ki zalince ni, sannan ina so ki d'auki wannan al'amari a matsayin 'kaddararki, kada ki butulcewa Ubangiji mana, da can kin yi soyayya da mahaukaci mara galihu! sai kuma Allah ya sauya tunaninki ki ka tsinci kanki a matsayin matar babban mutum wanda ya shallake tunaninki, shin me ya kamata ki yi?''

Jin nayi shiru ban ce komai ba ya cigaba da cewa" Allah subahanahu wata'alah za ki godewa a bi sa ni'imar da yayi miki, duk wad'an nan abubuwan da ki ke min kamar 'kara min 'karfin gwiwa ki ke domin ni ba zan iya rabuwa dake ba har abada don kin zama jinin jikina. Ya 'kare maganar tare da tsira min ido.

Na ce" Ni yanda zanyi rayuwar aure da kai ne ban sani ba."

Sihirtaccen murmushi yayi kafin ya ce." Saboda nayi miki tsufa ko?"

Shiru nayi masa.

Sai ya cigaba da cewa" Wace rayuwa ki ka shirya yi da masoyinki Baban-baba?"

Kallonsa nayi sai na gana yana murmushi wanda ya 'kara masa kyau!

Da sauri na ce"Rayuwa mai sau'ki da sau'ka'awa."

Dariya yasa sosai yana mamakin yarinyar. 'kuruciya ce kawai take damunta, a ganinsa ai rayuwar da za ta yi dashi a yanzu sai ta fi armashi da wacce za tayi dashi yana fa'kiri (talaka) gabad'aya ya gaza fahimtar inda ta nufa, wata irin bahaguwa ce, ko da yake yana yawan ji daga bakin mutane suna fad'in (Kurame) ba su da saurin yarda domin duk abinka sai sun zarge ka a wasu lukatan( A yi min afuwa masu wannan laluran ban yi dan na ci fuska ba)

Ya kalle ta da fad'in "Me yasa lokaci guda ki ka aminta da ni a lokacin da nake mahaukaci na 'kar'kashin mota"

"Tausayinka na ke ji har cikin raina ina jin takaicin irin rayuwar da ka ke, kuma ina shiga 'bacin rai a duk lokacin da na ji ana kiran ka da mahaukaci! har kuka nake wani sa'in."


Ya sake jin wani irin k'aunarta a cikin ransa.

"Ni ma a lokacin ji nake duk duniya bani da mai 'kauna ta kamar ke, domin baki 'kyama ce ni ba, kin bani abinci kin bani ruwa, kin share min makwancina, wannan dalilin yasa na tsaya kai da fata naga na mallake ki domin samun mace irinki a yanzu babban aiki ne."


'Dakin yayi shiru na minti biyu, kafin ya cigaba da cewa; ki sa a ranki cewa abinda mahaukacin nan zai yi miki na kulawa da soyayya, to ni zan yi miki wanda ya fi shi, buri na kawai ki amince da ni cewar ba zan cuce ki ba, kuma nayi miki al'kawarin ba zan gaza miki ta kowane fanni ba.


Kalamansa su suka sanyyayar min da jiki cikin zuciyata na ji ina sha'awar zaman aure da shi, sa'banin tunanin da na keyi , ganin kamar ya fi 'karfina, tabbas duk maganganunsa akan hanya suke, yanda yake rantsuwa da Allah a kan 'kaunar da yake min, hakan ya 'kara min 'karfin gwiwa, sai dai kuma tils na cigaba da addu'a akan Allah ya kore mana fitina a cikin al'amarin.


Tare muka ci abincin, yana ta jana da hira, ni dai umm kawai nake cewa, sosai ya warware kamar ba mara lafiya ba, ya saki jikinsa yana ta zuba min kalaman soyayya wanda suka ragargaza min ga'bo'bin jikina, domin da abincin ma wai a baki zai ba ni, na no'ke don gabad'aya kunyarsa nake ji ganin kamar yana so ya wuce gona da iri.

Har dare ina d'akinsa kunya nake ji na sauka 'kasa, shi kuma tun bayan da ya fita sallar magariba bai dawo ba, duk na takura! a dak'in, gashi ina da bu'katar zuwa tsohon guri na, domin d'auko rigar bacci amma ya hana ni, daga ni sai doguwar rigar atamfar dake jikina sai kuma mayafin dana yafo ina zaune nayi tsuru tare da tunanin abunda zai faru tsakanina dashi a wannan rana.
[1/12, 11:28 PM] GARKUWAR MATA: 90&91
Hajiya da kanta ta shigo ta kawo mana abinci. Fuskarta kawai na kalla na fahimci cewa tana cikin farin ciki da abinda nayi, don babban burinta shine na zauna tare da su, ganin haka yasa na k'arawa kaina 'karfin gwiwar ha'kurin zama a d'akin mijina, ko don saboda 'yar tsohuwar ta kasance cikin walwala da farin ciki.

A can 'kasa kuwa Hajiya na zama Shukura ta fara 'kananun maganganu na rashin mutunci, domin kishi 'karara take nunawa akan matar mahaifin nata, ita dai bu'katar ta mahaifiyarta ta dawo gidan.

Hajiya ta katse ta da fad'in" Idan zaki kwantar da hankalinki akan wannan al'amari to, domin da mahaifinki zai dawo da Fatima gidansa da tuntuni ya dawo da ita, sannan kina fadin na tilasta shi, akan me zanyi masa dole? shine mai auran kuma yace ba zai zauna da ita ba saboda wasu dalilai, to akan me zan matsanta masa, don Allah Shukura ki samu nutsuwa, kada ki tayar mana da hankali a gida da fitina mara dalili.

Hawaye ta share ta ce" Hajiya ni kawai yarinyar ce ba tayi min ba, ai ba tsaran auransa ba ce, don wulakanci shine zai auri 'yar 'karamar yarinya bayan duk ga mata nan a gari."

Cike da mamaki! ta ce" Mahaifin naki shine wulakantacce?"

Hanci ta sha'ka ta zumbura baki ta ce" Ai dama ba kya 'kaunar Mommyna kamar ba ke ki ka haifi Ubanta, 'kiri-'kiri ki ke nuna fifiko saboda kawai Daddyna yana da kud'i."

Hajiya ta ri'ke baki da d'umbun mamaki! a tare da ita ta ce" Rashin kunya za kiyi min Shukura yanzu ni ki ke fad'awa wannan magana?"


Ta bud'e baki za tayi magana ya shigo falon, duk sai su ka yi shiru, amma fuskokinsu da alamun 'bacin rai! don ita Shukuran ma kuka take.

Cike da kulawa ya kalle ta da fad'in."Menene?" yana son yarinyar sosai! saboda ita kad'ai gare shi, halayenta ne baya so shiyasa ba kasafai yake yarda ta je gurin gurin uwarta ba.

Sake rurucewa! tayi da kuka tana takure jikinta a cikin kujera!

Ya zauna yana kallon Hajiya domin tayi masa 'karin bayani.

Tsaki! ta ja ta ce" Wannan yarinyar sam bata da hali wallahi. kuma yanzu na fahimci abinda ka ke gudu tsakaninta da mahaifiyarta, domin dai wasu halaye take masu kama da na uwarta.

Ya ce." Menene ya faru?"

Nan ta kwashe komai ta fad'a masa.

Ya sha kunu sosai! yana kallonta da kakkausar murya ya ce." Wallahi ki kiyaye ni Shukura ki bar ganin ina biye miki ko ina nuna miki 'kauna, akan Shahida za mu 'bata sosai ranki zai 'baci mutuk'ar baki daidaita hankalinki ba, ina ruwanki da ita? muddin kin d'auke ni uba to itama uwarki ce, saboda haka kada na ji ko na gani kinyi mata rashin kunya, duk ranar da hakan ta faru sai na 'bata miki rai."

Cikin kuka ta ce" Daddy kayi hakuri don Allah, amma ina neman alfarma a gurinka.

Ya kalle ta babu fara'a a fuskarsa, ta ce" Don Allah ka dawo da Momnyna wallahi tayi nadama, kuma 'yar uwarka ce."


Shiru na minti biyu kafin ya ce." Zanyi shawara akai." Daga haka bai sake magana ba ya tashi ya hau sama.

Itama Hajiya tashi tayi ta shige dakinta cike da takaicin abinda yarinyar tayi mata.

Ganin saura ita kadai a falon yasa ta dauki wayarta

"Mommy kin san wani abu?"

Daga d'aya 'bangaran Hajiya Fatima ta ce" Sai kin fad'a min."

"Na roki alfarma a gurin Daddy zai mayar dake d'akin ki." Cike da murna ta fadi maganar.

Hajiya Fatima kamar ta zuba ruwa a 'kasa ta sha don farin ciki, ta ce"Shukura da gaske ki ke ?" Tafad'a cike da zumud'i.

"Wallahi kuwa Mommy amma ya ce"Zai duba ya ga ni, nan da kwana biyu zan sake yi masa maganar."


Ta ce" To shikkenan zan zo a shirye in sha Allahu. amma ki cigaba da matsanta masa akan maganar, kuma kada ki bar matarsa tasha iska a gidan, 'yar iska nakasashshiya."

"Mommy cewa yayi fa akanta zai 'bata min rai! wai dole sai na girmama ta! kamar yanda zan girmama shi."


Tsaki! ta ja ta ce" A gaban idonsa ki bata girma amma a bayan idonsa ki ci ubanta, idan na shigo gidan, da k'afafunta zata gudu.

"To shikkenan Mommy yaushe zaki dawo?"

"Cikin satin da za mu shiga in sha Allahu."

"Mommy kada ki manta don Allah ina son abaya masu kyau da takalma."

Ta ce" Su nayi order baki da matsala daughter sai na dawo in sha Allah."

Sallama su kayi da juna, kafin ta shiga d'akinta cikin farin ciki da an Nashua's mamanta zata dawo kusa da ita.


Zaune a gefen gado ya same ni ina ta nazari da tunanin abinda zai biyo baya.

Koda ya shigo d'akin, can wata kusurawa ya nufa ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login