Showing 33001 words to 33181 words out of 33181 words

Chapter 12 - MAJANUNI BOOK 4 BY BINTA UMAR ABBALE.txt

na mallaka a duniya na baki saboda farin cikin da ki ka sanya ni a ciki, saboda haka ki dauki al'amarin da muhimanci, ki kuma sa a ranki cewa; kin bani abu mai daraja wanda bani da abinda zan biya ki dashi.

Gabad'aya jikina yayi sanyi da kalamsa. kawai na ri'ke takardun tare da zuba masa ido, ni dai ban ga abinda zanyi da gidan mai ba, ina lefin rumfar kasuwar.

Kira ne ya shigo wayarsa ya d'auka! nan na ji yana fad'in" In sha Allahu gobe zan shigo kano d'in sai a san yanda za a yi.

Na ce" Don Allah mu tafi tare."

Girgiza kansa yayi da fad'in" Za ki je amma ba yanzu ba sai kinyi nauyi.

Sai na rasa inda maganarsa ta nufa, sai nayi nauyi kamar yaya?

Ya katse tunani na ta hanyar fad'in." Kina bu'katar zama a wannan sashen ko za ki koma naki domin na riga na gama shirya miki komai."

Girgiza kai nayi da cewa" A'a gwara nan d'in."

Ajiyar zuciya ya sauke da tare da cewa "Shikkenan abinda ki ka za'ba shine za'bi na."

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login