Showing 6001 words to 9000 words out of 33181 words

Chapter 3 - MAJANUNI BOOK 4 BY BINTA UMAR ABBALE.txt

yawunsu ba, muddun nace dole sai na auri Na'ima sai dai na sanja iyaye, gabad'aya suka had'e bakinsu, Kawu Audu dashi Baba Auta din, babu wanda ya fahimce ni.

Mamana ta umarce ni cewa na janye maganar auran Na'ima na amince da auran Fatima domin samun kwanciyar hankali, amma zata tsananta da yi min addua insha Allahu ba zan lalace ba.

Jin haka yasa na amince ba don raina yaso ba, sai don samun zaman lafiyarmu bakid'aya. amma sam Fatima bata daga cikin tsarin matan da nake so na aura.


'Bangaran wacce ake dambawar don ita, ko da ta samu labarin abinda yake faruwa, sam bata nuna damuwa ba, domin ta jima da sona a cikin zuciyarta, duk da bata furta min ba, amma duk alamomi sun bayyana, idan zamu had'u a ko'ina ne sai tayi min magana irin ta rashin kamun kai, "Wallahi kana burgeni, ina son namiji dogo giant (ingarma) wanda na san ya cika cif, zai gamsar da ni a shimfida, ire-iren wannan maganganun banzan take min a duk sanda za mu had'u, sai nayi mata jan ido sannan! na nuna mata cewa; ni nafi k'arfinta, amma hakan baya hana ta sake zuwar min da maganganun banza makamanta wannan. a duk sanda zamu had'u a wani guri

Tunda ake maganar auran ban taka k'afa na je gurin yarinyar ba, komai suke ina kallonsu ne kawai, nayi iyakar abunda zan iya na lefe da sauran abubuwan bukata na aure.


Sai ga ta tazo ta same ni a gurin aiki na tare da 'kawarta, kallo daya nayi musu na kawar da kaina domin raina ya 'baci da ganin sutturar dake jikinsu, komai a bayyane.

''Magana na zo nayi da kai" tafada a lokacin da take tsaye a kaina.

Na kalleta tare da fadin."Me yake tafe dake?" kai tsaye ta ce."Kudin 'kunshi da kitso nake bukata.

Dubu uku na bata amma na gargade ta kan cewa; kada ta kuskura ta zo min gida da gashin doki, domin gwanar 'karin gashi ce da tara farce, ga uban bilicin da take, duk ta lalata fatarta!

Ta'be bakinta tayi ta ja hannun 'kawarta suka tafi, tana maganganu kasa-kasa wanda na san dani take.


'Daki da rumfa kawai na samu na kammala, na dan kwaskware! dai-dai gwargwado. amma kicin da band'aki da sauran aiki, dan babu fulasta ballanatana rufi, haka nan na hakura, saboda yanda wahala tayi yawa, ga bikin ya matso komai ya kacame! babu mataimaki sai Allah.


To tunda aka d'aura auran, ban wani saki jikina da ita ba, na dai sanya mata ido ne kawai ina nazari a kanta.

Duk wani hakkinta da ya rataya a wuya na, ina kokarin ganin na sauke shi, amma kuma ban ta'ba had'a shimfida da ita ba, a falo nake kwanciyata ita kuma a cikin uwar daki, haka nan, za tayi shigar fitar da tsaraici a gabana tayi ta juyawa, amma cikin ikon Allah ba ta iya jan ra'ayi na zuwa gare ta.

Sai kawai ta je ta fad'awa Hajiya cewa; bani da lafiya domin tunda akayi auranmu wata hud'u ban ta'ba kwanciya da ita ba.

Hajiya ta samu abin yi ta je har d'akin mamana ta rufe ta da fad'a, ta inda take shiga ba ta nan take fita ba, cin mutumci iri-iri abin mamaki! Fatima har tana sanya baki, anan ne Sadiya ta gaza hakuri ta fara mayar da martani, Hajiya ta gaura mata mari tana fadin" Wato za ta goyi da bayan uwarta kenan! to shikkenan zata sanya kafar wando daya dasu gabad'aya!

Sai da nazo gidan Sadiya ke sheda min abinda ya faru, sosai raina ya 'baci! idan Hajiya ta ci zarafin mamana na rabu da ita to babu shakka Fatima ba zata wanye lafiya ba, domin bani da hakuri a kan mahaifiyata da nake jinta a cikin ko'kon raina!


Sosai ta ga 'bacin raina akan abinda tayi, na ce kuma lallai in tana bukatar zama dani to ta je ta bata hakuri, idan ta'ki wallahi sai na sake ta. wannan shine hukuncin dana yanke mata.

'Kwana d'aya biyu shuru ba tabi umarnina ba, a cikin kwana na ukun, na rubuta mata saki daya a takarda na ce lallai kafin na dawo ta fice min daga gida.

Yanda na fahimta al'amarin ya bata tsoro sosai, domin ba tayi tunanin zan iya sakinta ba, haka na fita na barta cikin damuwa mai tsanani, wanda ni hakan bai dameni ba, mutukar zata ta'ba martabar mahaifiyata to wallahi na gama zama da ita.
[1/12, 11:25 PM] Binta Umar Abbale: 67&68


ASALIN LABARI.

"Ni mutumin jahar katsina ne, a cikin karamar hukumar jibia a ka haife ni, tare da 'yan uwa na biyu wanda suka kasance mata, sai dai Allah yayi wa babbar cikinmu rasuwa a lokacin da ta zo haihuwar fari, tayi mutuwar shahada, ina rokon Allah ya jikan Amina yasa aljanna makomarta, mahaifinmu Malam Sani kafinta ne ma'ana mai sarrafawa katako ta kowace siga, daidai gwargwado yana samun rufin asiri da wannan sana'ar duk ya d'auki d'awainiyarmu, ci da sha suttura da harkokin karatunmu.

Ya kasance mutum mai sha'awar karatun boko tun yana yaro, amma Allah bai sa yayi ba, dalili mahaifinsa bashi da wannan ra'ayi a cewarsa duk wani karatu ya bi bayan na addinin musulunci, wannan dalili yasa ya daukeshi ya kai shi can jamhuriyar nijar karatun allo, anan ya sauke al'kur'ani mai girma ya kuma haddace shi, sannan ya dawo gida domin taimakawa mahaifinsa akan sana'arsa ta gado, wacce shima ya gada a gurinsa, yake kuma cin abincinta da ita tare da biyan buk'atar yau da gobe.

Sosai ya tsaya min da 'karfinsa dana aljihunsa har sai da ya ga na samu gurbin karatu, a jami'ar bayaro university dake jahar kano, hankalinsa ya kwanta, burinsa kawai nayi karatu sosai wanda zan samu aiki na d'auki nauyin kaina, na kuma yi aure domin rike iyali.

A lokacin mahaifiyarsa tayi ta k'orafi da k'ananun maganganu, kan cewa; da Mahaifinsa yana raye wannan d'anyan aikin ba za'ayi ba, domin itama akwai 'karancin rashin fahimta a tare da ita, a ganinta duk wani karatu da za ayi a yanzu mutukar bana al'kurani bane to bashi da amfani, kuma a lokaci fa nayi saukar al'kur'ani, nasan hadisai da sauran littaffan addinin musulunci, kawai dai ita bata son karatun bokon ne, ganin haka yasa mahaifiyata yin shuru da bakinta, domin tana iya magana laifin ya dawo da kanta, sai tayi shuru kawai, amma cikin zuciyarta addua. take min.

Tun ina yaro 'karami nake jangwale-jangwale, duk lalacewar abu idan nasa masa hannu sai ya tashi, musamman irinsu tv keken d'inki babur, mota da sauransu, wannan dalilin yasa mahaifina ya bani shawarar karantar Engineering, cikin ikon Allah kuwa cos din beyi min wahala ba, ni nake zuwa na d'aya duk jarrabawar da za muyi bana fad'uwa, sosai nake taimakawa wasu daga cikin abokan karatuna.

Na kammala karatuna cikin narasa takarduna sun yi kyau sosai! irin yanda ake bukata, sai dai fafur! aiki ya'ki samuwa, tunda na dawo gida nake yawon neman aikin abin ya fassakara a cikin jahata babu local goment din da ban je neman aiki ba, amma Allah bai sa na samu ba,

A lokacin Hajiya ta samu bakin magana, fad'i take dama ai na fad'a! wannan karatun bashi da wani amfani, gashin tsayin shekara hud'u kana fagauniya duk ka lalace! ka yi rama, shi kuma da yake daure maka gindi yayi asarar kudinsa a banza, sai a zo a rungumi sana'ar gado tunda abinda ake nema bai samu ba.

Mahaifina dai shuru kawai yayi mata ba wai don bashi da abin fada ba, amma ya fi kowa jin ciwon abin a cikin ransa.

Haka na ajiye takarduna, na sanya hannu domin tamaikawa mahaifina alokacin dama k'arfinsa yayi rauni.


Rayuwa tayi mana tsanani domin mahaifina bashi da wani cikakken jarin da zamu juya mu kasa mu sayar, sai dai kullum idan mun fita shago mu zauna jiran masu kawo kwaskwarima, idan hakan ta samu kenan, domin watarana yanda muka fita haka zamu dawo babu ko kwabo cikin aljihunmu, gashi rayuwa tayi tsada kullum 'kara tsanani take.

Ganin abinda zamu ci yana nema ya fi k'arfin bakinmu, yasa na fara shiga cikin kasuwani domin daukar dako, to anan ne na samu na tara kud'in da na sayi kayan gyaran babur da faci, sannan na nemi albarkar iyaye na, na fita bakin titi, domin gwada sa'a ta akan sana'ar ko Allah zai sa a dace.

Cikin ikon Allah kuwa sai Ubangiji ya bani sa'a, kullum idan nayi sana'oi na, na kan tashi da kud'i masu kauri wanda zanyi awo da cefene a gidanmu sannan da safe na basu kudin karin kummalo.

Iyaye na sunyi farin ciki sosai da wannan sana'a da nake, kullum cikin yi min fatan alheri suke, ita kuma Hajiya lokacin ta matsanta min lallai sai na fito da matar aure, duk yanda naso na fahimtar da ita abinda ke da akwai amma fafur! taki saurarata, ita dai tunda na samu sana'a to nayi aure.

Ni kuma tunani a yanzu shine, shi aure sai mutum yana da kwakwarar sana'a! saboda yau da gobe gashi bani da muhalli uwa uba nauyin iyayena da 'kawanta Sadiya dake kaina

Haka dai rayuwa ta cigaba da gurgurawa, yau da dadi gobe babu, cikin wannan yanayi ciwon ajali ya kwantar da mahaifinta! gabadaya ya daina fita yana gida a kwance sakamakon wani irin tari da ha-ki! da ya ci k'arfinsa, na d'auk'e shi na kai shi asibiti, a lokacin akayi masa gwaje-gwaje! amma cikin ikon Allah ba'a gane abinda ke damunsa ba, sai dai likita ya rubuta masa maganin da yake ganin zai taimaka masa.

To koda naje gurin siyan maganin hankalina ya tashi sosai sakamakon yanda mai siyar da maganin ya fada min adadin kudin da zan biya domin a bani magungunan da likita ya rubuta a katin.

Kudin dake aljihuna duka-duka dubu biyu ne, wanda ko guda daya ba zai siya ba, gashi likitan yace lallai a sayi magungunan duka domin suna da mutukar amfani.

Jiki a sanyaye na koma gida da tunanin hanyar da zan bi gurin samun dubu ashirin da hudu wanda zan sayawa mahaifina magani, 'Yan uwansa ba su dashi, amma ya zama dole na je gurinsu, domin na sheda musu halin da ake ciki, saboda haka kai tsaye gurin sana'ar Malam Audu na nufa inda yake sana'ar faskare na icce. duk na sheda masa halin da ake ciki, na kuma nuna masa katin asibitin domin ya tabbatar.

Sosai ya jajanta al'amarin, ya kuma tausayawa d'an uwansa halin da yake ciki, da karshe ya dauko dari uku ya bani tare da bani hakuri kan cewa shima bashi da kudi ga wahalhalu na iyali sunyi masa yawa.

Kwata-kwata ban ji haushinsa ba, domin na san da gaske bashi dashi, d'an abinda ya ke samu bai taka kara ya karya ba, kuma dashi yake daukar nauyin iyalinsa.

Gurin d'an autansu na nufa wanda muke kiransa da Baba Auta babu laifi shi yana d'an samu a kasuwa tunda harkar hatsi yake gidansa babu yunwa kuma sannan a cikinsu duk yafi su rufin asiri.

Kallona yayi a lokacin dana gama yi masa bayani, ya girgiza kansa da fadin." Lallai Sani yana cikin jarrabawa, Allah ya ba shi lafiya" na amsa da "ameen" ina jin sanyi a zuciyata, domin duk a zato na zai taimaka mana, kawai sai ji nayi ya ce." To Saddiku kasan dai yanda rayuwa take, duk wanda ka ga yana nema to saboda iyalinsa yake, saboda haka zan taimaka daga abinda naga zan iya domin kuwa ba zan takurawa kaina ba." Yasa hannu cikik aljihu ya dauko kudi d'aure da kyaure ya zaro dubu daya ya miko min da fadin." Ga wannan a hada a saya masa maganin, Allah ya ba shi lafiya."

Jikina a sanyaye na kar'ba da fadin." Allah yasa ka alheri ." Ya amsa da ''ameen" tare da shigewa cikin gidansa ya bar ni tsugune a gurin.


To koda na shedawa Hajiya abinda ya faru, sai cewa tayi ai sunyi 'kokari ma a hakan, abinda yanzu wahala tayi wa kowa yawa, wa zaka je ka daura nauyinka"

Sai na kasa fahimtar inda maganarta ta dosa, wato tana nufin ta goyi da bayan abinda sukayi kenan daidai ne a gurinta. girgiza kaina kawai nayi na tashi na bar gurin, zuciyata cike da jin ciwon rashin kulawar da take akan mahaifina kamar ba ita ce ta haife su duka ba.


Wani abokina ne ya bani shawarar zuwa gidan redio domin na kai kuka na, cikin ikon Allah kuwa kwana biyu da zuwa na wani bawan Allah ya biya kudin maganin, sosai nayi farin ciki, addu'a kuwa munyi masa sosai dani da mahaifiyata da k'anwata Sadiya.

Cikin ikon Allah yana fara shan maganin sai sauki ya fara samuwa, muna ta murna da godewa Ubangiji, sai dai kuma mune muke haukanmu ashe saukin na tafiya, daran alhamis ya rasu! da kalmar shahada a bakinsa.

Mutuwar mahaifina ba zan ta'ba mancewa da ita a tarihin rayuwata ba."

Shuru yayi, ya kasa cigaba da bata labarin. saboda yanda mutuwar ta dawo sabuwa, kukan zucci kawai yake,

Lokacin ita kuma tausayinsa duk ya gama mamaye zuciyarta, sai ajiyar zuciya take saukewa tana sake shigewa jikinsa kukan da take dannewa ne ya su'bce! sai sautinsa ya ji a kunnensa! sosai take zubar da hawayen tausayinsa.

Hankalinsa ne ya tashi ya dinga rarrashinta cewa tayi shuru saboda dare yayi sosai! sautin kukan zai iya fita, duk da cewa gurin da suke da tazara mai tsayi da cikin gidan.

Ganin ta'ki ta daina kukan ne yasa ya d'auke ta kai tsaye d'aki ya nufa da ita a rungume a jikinsa yana cigaba da lallabata, kan kirjinsa ya kwantar da ita ya matseta tsam! da zai samu shima kukan zai yi domin komai ya dawo masa sabo.
[1/12, 11:25 PM] Binta Umar Abbale: 71&72
"Ina gurin aiki sai ganin Sadiya nayi a kaina. Na san dama hakan zata faru, ko ga yanayin da naga yarinyar, idanuwanta sunyi jawur! da alama ta ci kuka ta 'koshi. na ce" Menene? nan take sheda min cewa gida babu lafiya na je ana nema na." hankalina na kan babur din da nake gyarawa, na ce "taje kawai gani nan zuwa."

Koda na shiga gidan hayaniya hayaniya ce kawai take tashi. muryar Hajiya tafi ta kowa sai sababi take, ta inda take shiga ba tanan take fita ba. shigowata yasa suka saurara, Inna Samira ce 'kanwar mamana, suke musayar yawu da Hajiyan, yayin da mahaifiyartawa ke cikin d'aki tana zubar da hawaye, wannan shine abinda ya d'aga min hankali, kuma nayi nadamar abinda na aikata, wanda na san shine musabbabin tashin hankalin da yake afkuwa a gidan.

" Ka shige ciki zanyi magana da kai." Hajiya ce ta bani wannan umarnin, ban yi mata jayayya ba, na bi bayanta. nan na gan su a zaune ita da mahaifinta wato Baba Auta fuskarsa a murtuke! ina mika masa hannu domin mu gaisa amma bai ko kalle ni ba.

Na samu gefe na tsuguna ina sauraran abinda zai biyo baya.

Ta fashe! da kuka! fuskarta kaca-kaca da hawaye! take fadin" Saddiku cin mutuncin da za kayi mana kenan? saboda 'kasa ta rufe idon ubanka, shiyasa kake nuna min iyakata, babu damar na yanke hukunci a gidan nan, sai kasa kafa ka tsallake, amma kara wannan, idan mahaifiyarka ta ajiye baka iya tsallakewa saboda kana gudin 'bacin ranta, amma ni dana haifi ubanka ka raina ni, Sadiya ta shirya maka karya da gaskiya ka hau kai ka zauna, shin yaushe Fatima ta zagi uwarka da har zaka sake ta, akan wannan dalilin da bashi da tushe ballanatana maka ma."

Zanyi magana ya daga min hannu da fad'in" Dakata" sai nayi shuru ina kallonsa. yayi 'kwafa! yana girgiza kansa da fadin" Aure duka wata hud'u da 'yan kwanaki har ka soma wulakanta min yarinyata! menene abin jin haushi anan, saboda kawai ta nemi hakkinta na aure shine zaka sake ta, idan baka da lafiya ba sai ka fada mana ba, a nema maka magani."

Murmushin takaici nayi na ce" Lafiyata lau, kawai ban yarda da nayi kwanan aure da ita kai tsaye ba, sai mun je asibiti likita ya aunta, domin gabad'ayanku kun san abinda yake faruwa.

Sai ya fusata! ya rufe ni da fad'a zagi ta uwa ta uba! duk ina kallonsa ina kuma 'kara jin haushin 'yarsa a cikin zuciyata, an aura min ita ba don ina sonta ba, amma ana bina da cin mutunci.

Ta sassauta murya da fad'in" Saddiku kada ka bani kunya mana kayi wa Allah da annabi ka dau aniya a zuciyarka ka mayar da matarka dakinta, kada ka manta fa 'yar uwarka ce, duk abubuwan da suka faru a baya ka daina tunawa, ka fuskanci abinda abinda yake gabanka.

Ganin ta sassauta yasa na ce"To shikkenan zanyi shawara akan al'amarin... ya katse ni ta hanyar fadin." Kada ma Allah yasa ka mayar da ita mana, ko ka d'auka kai kad'ai ne namiji a duniya shashasha mara mutunci kawai"

Na ce" Baba auta idan an ciza a hura! kai babba ne kuma kanin mahaifina, ka dinga sanin irin maganar da zaka fada a kaina, domin ina tsoron watarana ka fusatani na mayar maka da martani"

Da kumfar baki ya ce" Ka mayar mana, ai babu lefi tunda kana ganin ka isa"

Ta ce" Ya isa haka Auta abi komai a sannu a hankali, domin shima duk abinda yake yana da hujja akai saboda haka rarrashinsa za ayi"

Shuru yayi yana cin magani. ita kuma Fatiman sai ta hau kuka! tana fadin" Sai Allah ya saka mata a kan zargin da ake mata, tunda ita dai bata ta'ba sanin wani d'a namiji ba.

Ni dai tashi nayi na bar su a gurin suna mayar da magana, na shiga dakin Mamana na same su a zaune jigum! Inna Samira na kwantar mata da hankali, itama zuwanta gidan kenan, sai ta riski irin cin zarafin da akewa 'yar uwarta, wannan dalilin yasa ta shiga ciki fad'an, domin kare mutuncin yar uwarta.


Ta kalle ni kafin ta ce" 'Dan gaske, wannan ya zama na farko kuma ya zama na 'karshe! kada ka kuskura wani sa'bani ya sake

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login