Showing 30001 words to 33000 words out of 33181 words
Chapter 11 - MAJANUNI BOOK 4 BY BINTA UMAR ABBALE.txt
cire wani babban zani akwatina ne a jere guda bakwai sababbi kar kuma daka gani masu tsada ne.
Ya juyo yana kallo na kafin ya ce." Ga kayan lefanki nan na jima da had'a miki, duk yawanci a dinke suke, akwai komai na bu'kata a ciki kama daga kayan kwaliyya rigar nono kayan bacci wando siket da dai sauran abubuwan b'ukata na mata, daga yau kada ki sake amfani da kayan dake wancan sashen, tunda dai wasan kwaikwayon ya 'kare."
Murmushi nayi wanda yayi kama dana dole na kaucewa maganarsa ta hanyar fad'in"Ga abinci Hajiya ta kawo" na nu masa kwadon dake cike da kwanukan abinci.
Yana 'ko'karin sauke akwati nan 'kasa ya ce." Ni kam a 'koshe nake kin manta ban jima da jin abinci ba, ko da zan ci wani sai an jima, amma dai ke ina bu'katar ki ci abinci sosai! Yana maganar ne yanda zan ji sosai! don ya riga ya saba da d'aga sauti idan zai min magana.
Na ce"Nima na 'koshi."
Girgiza kansa yayi a lokacin da yake 'ko'karin zama a kusa da ni hannunsa ri'ke da wata figalalliyar riga, da kuma sababbin pant da brez.
A cinya ta ya ajiye min pant da brez din kafin ya fara warware! rigar yana fad'in" Yau wannan rigar za kiyi min ado da ita."
Gabana ya yanke ya fad'i! kallonsa nayi naga sai dudduba rigar yake mussaman ma'ajiyar nonon dake jikinta kafin ma nayi magana na ji yana fad'in" Anya kuwa Wannan gurin be miki kad'an ba ?"
Ya fad'a yana nuna min gidan nonon rigar. da saurin gaske na kawar da kaina kunya kamar na nutse a gurun.
Abubuwan da yake kamar wani matashin saurayi! na lura shima kunya tayi masa 'karanci.
Ya sake maimaita maganar. Na ce" Nima ban sani ba.
Sai kawai na ji saukar hannunsa a :kirjina yana lalubawa! a gigice! na sauka daga gadon! ina harararsa! dama abinda yake bu'kata kenan! a ganinsa wannan ba harara bace kallon soyayya ne.
Ido ya kashe yana bina da wani shu'umin kallo! duk sai na tsorata, kamar na bud'e dakin na fita, amma sai na daure, na zauna kan kujera gabana na cigaba da fad'uwa! babu shakka akwai babban al'amarin da zai faru a tsakaninmu.
Kira ne ya shigo wayarsa na ji yana fad'in" Yaushe ka dawo babu labari?"
Shiru na 'yan second biyu kafin ya ce." Allah ya kai mu lafiya idan ka shigo sai ku gaisa da amarya ta."
Dariya naga yayi kafin ya ce." Ai babu wasa a tsakaninmu, wallahi da gaske nake nayi aure kimanin wata uku da suka wuce."
Shiru yayi yana sauraransa kafin ya ce." To Idan ka zo zaka dai tabbatar da magana ta, Allah ya ba mu alheri."
Kashe wayoyinsa yayi duka ya ajiye kan dirowa kafin ya kalle ni, babu wasa a fuskarsa ya ambaci sunana da sautin da zan ji maganarsa.
Amsawa nayi nima ina kallonsa.
Ya ce." Za mu yi sallah ta godiya ga Allah ko?"
A sanyaye na d'aga kaina.
Sai ya tashi ya nufi band'aki! ya bar ni a zaune ciki tararrabi da fad'uwar gaba!
Alwala yayi ya fito nima na shiga nayi alwalar na fito na same shi ya shimfida mana babbar dadduma!
Hijabi ya mi'ko min na kar'ba nasa a jikina, na tsaya a bayansa ya tayar da sallar.
Raka'a biyu mu kayi, ya daga hannu sama, ya dinga kwararo addu'a har sai da na tausaya masa jin yana rok'on haihuwa da samun wadatacciyar nutsuwa da kwanciyar hankali a tare da ni, da kuma zuria masu albarka, muryarsa sai rawa take kamar zai fashe da kuka yake fad'in "Ubangiji Allah kasa nayi auran nan kenan! mutuwa ce zata raba ni da matata, ya rabbi ka bani zuria da yawa da ita, kasa na samu nutsuwa da ita, Wahidun ahadun! kayi min wannan arzi'kin don alfarmar Annabi Muhammadu S.A.W."
Hawaye ne suka fara zuba a saman fuskata, gabad'aya tausayinsa ya gama kashe min jiki, ro'kon Allah yake akan ya samu zuri'a da ni, ya na kuma bukatar ya samu nutsuwa da ni, duk ni kad'ai! tabbas Allah yayi min tagomashi! kuma yayi min kyautar da ba kowace mace ba, domin samun nagartaccen namiji a wannan zamanin sai anyi dace.
Bayan ya shafa addu'ar ya juyo yana kallo na, lokacin na kasa tsayar da kukan da na ke yi, hannuna ya ri'ke kafin ya ce." Menene?" zuciyata ta sake karyewa, hawayen suka cigaba da zuba, yasa hannu yana goge min, ya ce"Zubar hawayenki yana min zafi a cikin raina, yau babbar rana ce a gare ni, na had'a ki da girman ALLAH ki daina yi min asarar hawayen nan"
Kallonsa nayi, naga yayi wani irin rama a gabana, kamar mai neman gafara sai rarrashina yake da kalamai kyawawa! na ce" In sha Allahu! zan zama farin cikin ka, ai ban za ci 'kaunata ta kai haka a cikin zuciyarka ba.
Murmushi yayi wanda yake 'kara masa kyau! ya ce." Kin wuce haka a can cikin zuciyata, domin k'aunar da nake miki tayi nisa ta bi ilahirin jinin jikina gabad'aya idan babu ke rayuwata zata salwance, a kanki na san meye so! duk matan dana aura akwai dalili, amma ke ce ra'ayi na, buri na shine ki bani dukkanin kulawarki, kuma ki zauna lafiya da ni."
Hannuna na ri'ke a karo na farko! ban ji nauyin had'a yatsuna da nasa ba, na ce" Zanyi 'kokari in sha Allahu."
Murmushi kawai yake yana jifa na da wani irin kallo, wanda yasa nayi saurin sunkuyar da kaina kasa.
To duk da ya ce a 'koshe yake sai da ya taya ni cin abincin, nima ba wani da yawa na ci ba saboda fargaba, kad'an na tsakura, na shiga bandaki nayi wanka tare da wanko bakina na fito, duk jikina babu 'kwari, domin ina jin tsoron abinda zai wanzu a tsakaninmu, yanayin kallon 'kurrulan da yake min, shi yake tabbatar min da cewa; da wuya yau wani abu bai faru ba.
Rigar ya mi'ko min yana kashe min ido.
Kasa 'karba nayi saboda kunya, na sa hijabi a jikina.
Ya tashi ya je ya kashe fitilar dakin, da ya dawo ya zauna yana lalube na.
Can gefe na matsa tsigar jikina sai tashi take.
Sai da ya lalubo ni, ya rike hannuna sosai kafin ya fara kici-kicin cire min hijab, dama kuma daurin kirji ne a jikina.
Kuka nasa masa ina ture shi, ni gabad'aya al'amarin banbarakwai nake jin sa.
Bai damu da yanda nake kuka turje-turje ba, haka ya cire hijan din jikina ya ajiye ya kwantar da ni saman gado.
Ni dai tun daga lokacin na shiga d'imuwa, domin kasa fahimtar kaina nayi, don jikina saki yayi tunda ya d'ora min nauyinsa, ban san ya akayi ba har ya gano abinda na fi muradi, nan naga ya mayar da hankalinsa a gurin, har ya samu kaina na dinga biye masa ina rawar jiki, sai dai kuma lokacin da mai afkuwa ta afku na raina kaina mutuka gaya! domin dai nan na gane cewa maza suna suka tara, dattijon 'karfi! ne dashi sosai! ya k'urewa duk wata fitina ta, kuka na dinga rizga tare da kokarin kwatar kaina daga hannunsa, a lokacin da shi kuma yake kan ganiya, ya hana ni k'atabus! jikina ya laushi sarrafa ni kawai yake ta kowace siga, yana yi tare da numfarfashi!
[1/12, 11:30 PM] GARKUWAR MATA: 92&93
Ba zai iya tantance wane irin hali yake ciki ba sakamakon tarayyarsa da yarinyar. ita ce mace ta uku da wata mu'amula ta shiga tsakaninsu. amma ya bata lamba ta d'aya a cikin jerin matan da ya yi mu'amula irinta ta auratayya. babu shakka Ubangiji baya tarawa bawa damuwa! domin ko da ya halliceta cikin jerin masu rangwamin gata sai kuma ya wadata ta da ni'ima tare da sauran abubuwan da ba kowace mace ke da irin shi ba, shi dai ya tabbatar da cewa; yarinyar ta zarce duk matan da yayi tarayya da su don ya samu gamsuwa da ita sosai, babu wani abu da yayi saura a mararsa, sakayau! ya ke jinsa tare da wani irin nishad'i da bai ta'ba shigarsa ba, lallai dole ya godewa Allah bisa ni'imar da yayi masa gurin azurta shi da 'yar baiwa wacce take da tarin nagartattun abubuwa masu alfanu a gare shi.
Da wannan tunane-tunanen bacci mai nauyi ya d'auke shi ya matse ta tsam-tsam! a jikinsa.
Da gari ya waye kuwa duk hidimar da ya kamata na yi da kaina shi ya yi min, yanda yake nuna kulawarsa a kaina hakan ya faranta min raina mutuka! sosai nayi farin ciki da ya samu budurci na domin kuwa shine abin alfaharin kowace 'ya mace, da kansa ya kai ni band'aki tare da had'a min ruwan wanka yana tattare hannun riga ya ce" Ko nayi miki wankan ne?"
Kai na girgiza! alamar A'a na tsuguna sai kace wata sabuwar maijego gabana ciwo kawai yake min, ba tare da na kalle shi ba na ce" Ka d'an had'a min wani ruwan amma kada yayi zafi sosai.
Da sauri ya had'a min ya taimaka min na shiga ruwan na zauna, rintse idona nayi sosai lokacin da zafin ruwan ke ratsa jikina, zugi da zafi suka sanya hawaye zubo min.
Duk sai ya tashi hankalinsa yana ta bani hakuri, juye-juye kawai naka a ruwan kamar na fito, wata zuciyar ta hana ni, nasan cewa ruwan zafin shine zai dakusar da ciwon dake gurin.
Hannunsa ya tsumbula cikin ruwan yana so ya ta'ba gurin "Ko dai na sa likita ta zo ta duba ki?" yana maganar yana so yasa hannanusa a gurin, ina kaucewa, na ce" A'a zai daina ciwon insha Allah.
Ya ce." Ina so na gani ne domin hankalina ya kwanta.
Kallonsa nayi naga da gaske yake maganarsa, na ce"A'a ba sai ka gani ba.
Cikin wata irin murya mai taushi ya ce." Saboda me? bayan na zama wani jigo a rayuwarki, kin zama ni, na zama ke, meye abin jin kunya.
Shiru nayi, domin bana tsammanin zan nuna masa.
Ya fara 'kokarin tayar dani tsaye wai dole sai ya gani, kuka nasa tare da ri'ke bahon ruwan ina ture hannunsa da fad'in" Ka fita ni dai."
Fita yayi ya bar ni a band'akin ba don ransa ya so ba.
Na jima cikin ruwan d'umin. sannan nayi wankan tsarki! na fito na d'aure da towel mai girma a jikina.
Ko da na fito baya cikin d'akin, amma ga kaya na nan, ya ajiye min a kan gado.
Na shirya cikin atamafa java mai ruwan ganye kuma dinki yayi min cif! a jikina, mai kawai na shafa tare da fesa d'aya daga cikin turarunkansa dake jibge a kan madubi, na gabatar da sallar asubah da ta wuce ni, kafin na rarrafa na hau gado na kwanta bacci ne fal a cikin idona, ga wani irin ciwo da jikina keyi min, abu dai goma da ashirin! sun dabaibaye ni, jiya dai na yabawa aya za'kinta, har bana so na tuna gumurzun da mu kayi saboda tsigar jikina ce take tashi, amma na godewa Allah da ni'imar da yayi min, duk isar mace mutuncinta ta kai budurcinta gidan mijinta, na yi farin ciki da ya same ni cikakkiyar mace, kuma yanda na fahimta ya samu gamsuwa da ni ko ga irin addu'ar da yake min tare da d'aukar min al'kawari iri-iri, cikin zuciyata nake adduar Allah yasa hakan yake a zuciyarsa, don gaskiya bana k'aunar kishiya duk da na san umarni ne na Ubangiji amma ni kam na fi buk'atar na zauna ni kad'ai da mijina.
Tare suka shigo d'akin da Hajiya, sai nayi saurin rufe idona, kunya nake ji kada ta fahimci wani abu ya faru. ashe zuwa yayi ya fad'a mata abinda ya ke da akwa. shine ta shigo ta duba ni.
Kamar na fashe da kuka saboda takaici! ban iya cewa komai saboda nauyi da jin kunya baccin 'karya na tsira, ina jin suna ta maganganu nayi luf! sai da ta fita daga dakin sannan na bud'e idona na kalle shi. yana zaune kusa da k'afafuna yana waya!
Cikin dubara na tashi zaune na d'an jingina da fuskar gado! ganin na tashi yasa ya katse wayar da ya kalle ni, cikin kulawa ya ce." Sannu kin ga yanzu Hajiya ta fita ta shigo duba ki."
Zum'bara baki nayi tare da fad'in" Me yasa ka fad'a mata wani abu ya faru a tsakaninmu?"
"Me yasa ba zan fad'a mata ba? bayan ta damu da nayi aure na haihu, sannan kuma yanda ki ke kuka da gurin shi ya bani tsoro na je na sanar da ita ko da wani taimakon da za tayi mana." Yafad'a idonsa a tsaye a kaina.
Na ce" Gurin fa zai dusashe in sha Allahu.
To "Allah ya yarda, amma na yi waya da likitana duk nayi masa bayani abinda ke da akwai, ya bani tabbacin cewa; idan ana bu'katar gurin ya zama normal sai an 'kara wani abun, shine na ce ko zaki bari nayi wani yanzu ko da sau d'aya ne.
"Bangane ba." Na fad'a gabana na duk uku-uku! don gabad'aya hankalina ya tashi jin abinda ya ke fad'a.
Sai ya fashe da dariya yana kallona. Ganin haka yasa na juya masa baya domin na fahimci tsokanata yake.
Da sauran dariyar a tare da shi ya ri'ke hannuna da fad'in" Da wasa nake miki my love ba zan miki komai ba sai gurin ya warke in sha Allahu."
Ba tare da na juyo ba na ce" Ka tabbata?"
Shiru yayi be bani amsa ba.
Shukura ta shigo da'kin da sallama a bakinta. shi ne ya amsa, ni kam kunya tasa na rufe idona, ina 'kokarin 'kwace hannuna dake cikin nasa, ya ri'ke da kyau!
'Bangaran Shukura kuwa ganin ta, kwance lakadan a gadon mahaifinta, sai wani bakin ciki ya turnu'ke ta, ga shi kuma a zaune ya kusa da ita hannunsa cikin nata, kamar ta kurma ihu! saboda takaici.
A sanyaye ta ajiye kwandon abincin dake hannunta, ta ce"Daddy ina kwana?"
Ya amsa cikin kulawa yana nazarin fuskarta domin ya hango damuwa a tare da ita.
Sai da ta daure zuciyarta sannan ta ce" Antina ina kwana."
Ba tare dana kalle ta ba na amsa da "Lafiya lau." daga haka ban ce komai ba, amma cike nake da mamaki ya akayi yarinyar ta sauko har take gaishe ni.
Ta ce"Daddy Hajiya ta ce na kawo muku abin karin kummalo idan anti ba za ta iya saukowa 'kasa ba"
Hankalinsa gabad'aya yana kaina ya bata amsa da cewar" To babu laifi hakan."
Hanyar fita ta nufa jikinta duk a sanyaye. sai kuma ta kasa daurewa ta tsaya tana kallonsa kafin ta ce"Daddy ya maganar da mu kayi da kai kwana biyu da ya wuce?"
Ya ce." Wace magana kuma?" domin shi ya manta ma sunyi wata magana.
Ta ce" Akan dawowar Mommyna d'akinta da kuma al'kawarin da kayi min."
Tsawa! ya buga mata tare da nuna mata hanyar fita. " Wuce ki bani guri shashashar banza."
Da saurin gaske ta bud'e k'ofar ta fita tana sgare hawaye.
Na kalleshi sai na ga duk babu walwala a tare dashi.
Na ce" Ya za ayi ka kore ta har kana yi mata tsawa! kada fa ka janyo min 'bakin jini, Shukura 'yar ka ce bai kamata kayi haka ba."
Babu fara'a a tattare dashi ya ce." Ke a ganinki abinda tayi ya da ce?"
Ido na tsira masa da fad'in." Magana kayi da ita har kayi mata al'kawari lefi ne don ta sake tuntu'barka da maganar.
Ya ce." A'a ni ban yi mata al'kawarin dawo da mamanta ba, ta dame ni da maganar sai na ce mata zan duba na gani."
Dama abinda nake so na ji kenan daga bakinsa.
Sai kawai nayi shiru raina gabad'aya ya 'baci! ban san me yasa ba haka kawai nake jin kishin matan da yayi tarayya dasu duk da cewa a yanzu basa tare, amma haushinsu nake ji sosai!
Shiru d'akin yayi na 'yan mintina, kafin ya kalle da cewa" Ki tashi ki ci abinci ga farfesu Hajiya tayi miki." Yana 'kokarin bud'e fulas din yake magana.
Motsi ban yi ba ballanatana yasa ran zan sauko na ci wani abu.
Ya gaji da maganarsa ya had'a shayi da kansa ya karya ya sha, kafin ya zuba farfesun ya dangwala da biredi.
Cikin bacci da ya fara fizgata na ji shi yana laluben hannuna dake cikin bargo, ya saka min wasu takardu.
"Tashi zaune za muyi magana."
Yafad'a babu wasa a muryarsa.
Sai da na mula tukkuna na tashi zaune. har yanzu na kasa sakin fuskata, duk na damu jin maganar dawo da uwar gidansa.
Cikin nazari ya ce " Duk kin sauya fuska saboda wani dalili mara tushe! kada fa ki damu, na riga na shafe babin Fatima a rayuwata, domin da zan dawo da ita to da tun kafin na aure ki na dawo da ita, don haka ki samu nutsuwa.
Daurewa nayi na ce'' Waye ya fad'a maka na damu? kaina ne fa yake min ciwo ba wani abu ba.
Murmushi kawai yayi tare da fad'in ''Ai na gane ana 'kaunata yanzu tunda na ga kishi 'karara a cikin idonki."
Shashantar da maganar nayi ta hanyar fad'in" Wannan takardun fa?"
Ya ce" Naki ne."
Na tsira masa ido domin yayi min 'karin bayani.
Ya fuskance ni sosai kafin ya ce." Kasancewar na samu abu mai muhimmanci a gurinki yasa nayi miki wannan kyautar. takardu biyu ne a hannunki, akwai na gidan mai da kuma na rumfar kasuwa dake kwari, yanzu haka ana cigaba da hada-hada na kasuwanci a kowane sassa, abinda aka samu duk ya zama mallakinki, ina miki fatan alheri.
Na kalle shi da mamaki mai yawa a tare dani, na ce"Saboda kawai ka samu budurci a tare dani zaka bani gidan mai sukutum! nayi me da shi to?"
Sai ya 'bata fuska da fad'in" Ba wai ba ne a gurina, kuma budurcinki ya cancanta da komai. domin zan iya tattare duk abinda