Showing 45001 words to 45466 words out of 45466 words

Chapter 16 - SON ZUCIYA COMPLETE BOOK BY MIMI QUEEN.txt

wai itace abokiyar firarsu, itace zata ɗebe musu kewa a lokacin da suke tsaka da kaɗaici acikin gida"
-
"Wasu kuma idan suna cikin wani ƙunci ko damuwa, wai sai su kunna waƙa da zimmar itace zata kawar musu da raɗaɗin dake cikin zuƙatansu, wannan daga matan har mazan ma, sun manta da cewa ai yin hakan suna daɗa ɗorawa zuciyar tasu nauyin damuwa ne"
-
"Babu kyakkyawar nutsuwa ko kaɗan acikin sauraron kaɗe-kaɗe da waƙe-waƙe, haƙiƙanin samun nutsuwa yana cikin yawan saurãren zantukan Allah ta'ala, (wato karatun alƙur'ani mai girma), idan kuwa waƙar ta kwantar miki da hankali ta sakaki nutsuwa, to tabbas zata rage miki soyayya daga gurin mahaliccinki, ba don komai ba sai don zata shagaltar dake ne daga barin ambaton Allah ta kuma nesanta ki daga cikin masu yawan ambaton Allah buwayi a kowane hali suke"




WATAN SHA'ABAN WATACE ME GIRMA.




HALIN MAGABATA A CIKIN WATAN SHA'ABAN


An ruwaito daga sahabi Uthman bin Affan Allah ya kara yarda agareshi yana cewa alokacin da Ramadan ta kusanto "Wannan itace watan fidda zakkanku, dan haka duk wanda yasan ana binsa bashi to ya gaggauta biya domin ya samu daman fidda zakkarsa, idan ya gama biyan bashinsa to sai ya fidda zakka daga cikin abunda ya rage na dukiyar".


An ruwaito daga magabata cewa idan watan sha'aban ta kama suna fidda zakkar dukiyoyinsu domin su karfafawa mai rauni da miskinai gwiwa wurin azumtar watan Ramadan (zasu basu zakkan domin su samu damar yin sayayyan kayan abinci saboda samun damar azumtar Ramadan cikin nishadi, batare da fargaban rashin samun suhur ko buda bakiba)


An ruwaito daga sahabi Anas bin Malik Allah ya kara yarda dashi yace "Sahabban Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallama sun kasance idan watan sha'aban ta kama sun dukufa akan Alqur'ani suna karantashi, sannan su fitar da zakkan dukiyarsu su karfafi masu rauni da miskinai akan azumin watan Ramadan, sannan musulmai su kira bayinsu suce mun yafe muku harajin dake kanku awatan Ramadan (Abun nufi sun yafe musu, babu biyan haraji akansu har Ramadan ta wuce) Shuwagabanni kuma su kira yan fursuna wanda yake da hukuncin haddi sai ayi masa, Wanda kuma laifinsa babu haddi sai a yafe masa asakeshi ya tafi".


إخراج الزكاة لابن رجب ٢/٦١٦






_ALLAH UBANGIJI KA BAMU IKON AMFANA DA DAN TAKAITACCEN TUNATARWAN NAN, ALKHAIRIN DAKE CIKIN WANNAN LITTAFIN ALLAH KABAMU IKON AMFANI DASU SHARRIN DAKE CIKI KUMA ALLAH KA BAMU IKON YIN WATSI DASU_






```INA NEMAN GAFARANKU MASOYANA A KARO NA BIYU, WA'INDA NAYIWA LAIFI CIKIN SANI DA WA'INDA BAN SANIBA HAKIKA NASAN NA B'ATAWA WASU DA DAMA A RUBUTUN NAN DA NAYI BISA RASHIN SANI, TO DUK WANDA NAYIWA WANI LAIFI DAN ALLAH YA YAFEMIN CIKIN SANI KO RASHIN SANINA, KUSANI NI NA YAFEWA DUK WANDA YAMIN WANI ABU.


ALLAH UBANGIJI YA HADAMU DA ALKHAIRY A CIKIN LITTAFINA NA GABA NAGODE DA YANDA KUKA BANI KULAWARKU```.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login