Showing 36001 words to 39000 words out of 44450 words

Chapter 13 - HARIJIN SARKI COMPLETE HAUSA NOVELS BY OUM HAIRAN.doc

18 Nov 2025

6236

hatiminsa, haske ya sake bayyana ya shiga jikinsa nan take Numfashinsa ya dawo sannu a hankali.
Ya buWe ido, idanunsa sun koma fari.
 Samha&  ya faWa cikin sanyi.  Kinyi nasara... duhu ya fara ja baya.
Ta murmusa cikin hawaye.  Ba ni ba... Imani ne. Sultan rashin imani da Allah Waya duk shine Ummul aba'isin wannan halin da muka tsinci kanmu babu shiri".........

*61-62*

Washe gari bayan tashin lamarin hatimi, masarautar Zirkan ta tashi da firgici da ban tsoro.
Sarauta tayi shiru, dabbobi sun yi tsere kamar suna gudun wani abu da ba a gani, iska ta Wauki ?amshin ?asa mai ?onewa.

A cikin fadar sarki, Rashid yana zaune bisa gadon mulki, jikinsa yana daure da wani farin zani me zanen hatimin tsafinsu.
Likitoci sun zagaye shi, ciki har da Samha, wadda take rike da littafin rubuce-rubucen da ta samu a cikin Wakinsa jiya bayan haWuwarsu da duhu.
Tana karanta rubutun cikin sanyi:
 Jinin sarauta biyu ne na haske da na duhu.
Idan suka haWu, ko mulki zai rushe ko duniya zata sake sabo tabbas sabon shine ?addarar da duhu ta tsana.
Ta Wago idanunta ta kalle shi, cikin damuwa tace
 Sultan& wannan rubutun yana nufin akwai wani jinin sarauta daban, ko?
Ya kalleta cikin gajiyawar rai, amma idanunsa suka nuna tsoro da damuwa.
 Na san akwai wanda aka Soye.
Kuma nayi tunanin ya mutu...
amma na fara jin numfashinsa tun jiya da dare.
Samha ta Wan ja baya, tana jin sanyi yana ratsa jikinta tace
 Wane ne? Kuma me yasa kake jin numfashinsa? Rashid ya lumshe ido. Yace  ?an uwana& Sultan Ameer.
Cikin sauri Samha ta zaro ido ta kalleshi da mamaki, zuciyarta ta dinga dukan uku-uku.
 Jin numfashinsa? Rashid& wane kake nufi? Ya mi?e a hankali, ya Wauki takalmin sarauta ya saka, kamar wanda yake son ya tafi wani wuri amma zuciyarsa na ja da baya.
 Na daWe ina ganin mafarki, Samha.
A cikin mafarkin nan, wani yaro nake gani yana kiran sunana, yana cewa  ka karSe ikon da aka bari.
Daga farko nayi tunanin sa?o ne daga ruhin mahaifina... amma yanzu, ba mahaifi nake ji ba shi nake ji
Samha ta tsaya, idanunta suka kaWa tace.  Shi wa?

Rashid ya Wago idanunsa, cikin rauni da murya mai cike da nauyi yace:  ?an uwana... Ameer.
Samha ta Wan ja baya kamar wacce aka cusa mata wuta. Amma Rashid& Ameer dai an ce ya mutu! Gobarar da ta ?one sashen mahaifinku ita ta kashe shi kai ma a lokacin ka faWi, sai Allah Ya tsare ka!
Rashid ya girgiza kai, ya furta cikin murya mai sanyi:
 Ba gobara bace, Samha.
Wani abu ya faru a daren nan wani tsafi da mahaifinmu ya so ya kare mulki da shi.
Amma tsafin ya juyo a kansa.
Ameer bai mutu ba, kawai an Wauke shi daga duniyar nan zuwa wata duniyar duhu ta hatimin da aka Soye.
Sai ya dur?usa, yana ri?e kansa yace.

 Na dade ina jin motsinsa a cikin ruhi, amma jiya ne karo na farko da numfashinsa ya dawo kusa da ni.
Ina jin shi yana kiran sunana daga waje, yana cewa  Lokacinmu ya cika, Rashid. 
A hankali Samha ta matsa kusa dashi, ta ri?e hannunsa.
 To me kake nufi da hakan? Me yake nufi da lokacin da ya cika?
Ya kalleta cikin idanu, muryarsa ta ?asa.
 Yana nufin lokacin dawowarsa.

Kafin su ?ara magana, sai aka buga ?ofar Wakin da ?arfi.Wani ma aikacin sarauta ya shigo da gaggawa yana haki ya zube a ?asa yace.
 Mai martaba! A gaban masarauta akwai tutar da ba mu taSa gani ba!
Ana cewa wanda ke ri?e da ita yana da hatimin sarauta biyu Waya fari Waya ja!
Rashid ya tsaya cak.
 Tutar hatimi biyu?& 
Samha ta Wan girgiza kai cikin tashin hankali.
 Rashid& wannan alamar jinin duhu ce. cewar Samha,
Ya nufi taga da gaggawa, yana kallon nesa ya ga wani rukuni na mutane cikin ba?a?en kaya suna tsaye,
a tsakiyarsu kuma wani mutum sanye da riga me kalar ruwan shuWi me duhu,
idanuwansa suna suna haske da ja, kamar wutar da ta fito daga cikin duhu.
Rashid ya faWi da sanyi cikin murya mai Wauke da zafi da tsoro yace
 Ya tabbata& Ameer ya dawo".....


***************


*RAYUWAR AMEER A DUNIYAR DUHU*

Wanda aka ?one, amma bai mutu ba.

A cikin zurfin wani kogo mai ba?in duhu, ?asa tana motsi kamar tana numfashi.
Wata rana, shekaru ashirin da takwas da suka wuce  lokacin da fadar masarauta ta ?one, wani ?aramin yaro ya faWi cikin ramin da aka Soye ?ar?ashin fadar sarauta.
Wurin da ya faWa ba rami ne na duniya ba ?ofar duhu ce.
Daga nan ne Sultan Ameer ya shiga wani wuri da ba rana ko wata ke haskakawa ba sai ?amshin wuta, hayaki, da murya.
 Yaron da jini ya zaSa& ka tashi. yaji an faWa
Ya buWe ido, yana kallon wani hali me kama da mutum amma ba mutum ba.
Idanunsa kamar duwatsu masu wal?iya, muryarsa mai cike da iko.
Shi ne Sarkin Duhu, wanda ake kira Al-Mazhur  wanda ya taSa bautar tsoffin sarakuna kafin a rufe ?ofarsa.Ameer yana rawar sanyi, yana kuka yace.

 Ina mahaifina?... Me yasa komai duhu ne?... Me yasa nake numfashi amma ina jin zafi?
Al-Mazhur ya kalli yaron cikin taushi da Wan tausayi na mugun hali.
 Saboda kai jinin sarauta ne kuma an ?i karSar rabinka.
Jinin haske na Rashid ya fi, amma na duhu& shine naka.
Ameer ya Wago kai cikin hawaye yace  To me yasa sai ni?
 Saboda jarin zuciyarka. Duhu baya samun iko sai akan wanda zuciyarsa ta yi kuka da gaskiya.
Daga wannan rana, Al-Mazhur ya fara horar da Ameer.
Yaron ya koyi karanta kalmomin da zasu iya narkar da ?arfe, ?ulle zuciyar mutum, ko canza surarsa.
Shekaru suka ja, Ameer ya girma cikin wuta, yana Wauke da zafin ?iyayya da rashin amincewa.Lokacin da yake cikin shekaru talatin da bakwai, sai Al-Mazhur ya bashi hatimin duhu  alamar ?arfin da ba kowa yake rayuwa da shi ba.
 Hatimin nan yana da ikon rushe mulki da kafa sabo.
Amma yana da sharadi guda Waya zai ci gaba da rayuwa ne idan zuciyarka ba ta da soyayya.
Ameer ya Wauki hatimin ya saka a kirjinsa, sai wata rana ya farka yana jin numfashin Rashid daga sararin duhu.
Ya zuba ido a cikin madubin wuta, yana ganin Wan uwansa yana zaune a gadon sarauta cikin haske da mutane.
Yana rayuwa, yana da kowa, yana da duniya...
Ni kuwa, a nan cikin duhu nake, ina cin abincin ruhohi.

Sai ya kalli sama mai duhu, ya Waga hannunsa cikin murya mai ?arfi.

 Na rantse da jinin da muka fito daga shi
Zan dawo, Rashid!
Zan dawo in karSi rabona na duniya, koda kuwa da jini ne!

A wannan lokaci, duhu ya fara juyawa kamar guguwa, Al-Mazhur ya bayyana, yana dariya.
 Idan ka fita daga nan, ba zaka iya komawa da sau?i ba.
 To ba na son dawowa.  To sai ka bi ?a ida ka sha jinin wanda kake son maye gurbinsa.
Sannan nan zaka iya rayuwa a sarautarsa.
Ameer ya saki murmushi me taushi da mugunta.

 Zan sha jinin Wan uwana.
?ofa ta buWe da haske mai baki, iska ta tashi daga ?asa ?ofar dawowarsa duniya.
Wannan rana ce ta farko da duniya ta sake jin kamshin jinin duhu bayan shekaru Ashirin da takwas

*63-64*
A cikin daren da babu hasken farin wata, sararin samaniya ya rufe kamar ana zubar da jini daga sama. Kogunan da ke kewaye da masarautar Zirkan sun fara yin wani irin motsi kamar ana turzura su daga ?asa.
Sultan Rashid yana tsaye a saman Hasumiyar Zinare wadda take mafi tsayi a fadar. Gashinsa na rawa cikin iska, idonsa na kallon dogon sararin da yake ci gaba da yin duhu fiye da yadda ake gani da ido A cikin zuciyarsa yana jin wani abu da bai taSa ji ba numfashin wanda aka Soye.
 Na san kana raye, Ameer& 
Ya furta da murya mai sanyi amma cike da iko.
 Ka Soye shekaru ashirin da bakwai, saidai jininmu Waya ne. Idan ka dawo, to, wannan sarauta Waya ce da mutum Waya ne zai rayu a cikinta Wata iska mai sanyi ta hura ta ratsa masa cikin jiki, kamar wani ya yi dariya daga cikin iska.

 To ni nake raye, Rashid& 
Wata murya daga nesa ta amsa.
 Na dawo ne ba don sarauta ba sai don zuciya da ka lalata kafin haihuwarta

Cikin Wan lokaci, hasken wuta ya fara yawan wal?iya daga ?ofar Haikalin Al-Balad, wuri da aka rufe shekaru da dama saboda tsafin da ke cikinsa.
Tsafe-tsafe suka fara tashi daga ?asa, ruhohi masu kama da ?ura suna yawo cikin iska suna yin wani irin kukan ban tsoro.
A Sangaren Dr. Samha tana cikin asibitin fadar, tana ri?e da wani tsohon littafi wanda Granny ta bata  littafin da ke Wauke da sirrin hatimin jini da kuma yadda ake karya la anar da ta haWa jinin sarauta biyu.
Tana karantawa cikin rawar murya, tsoro na shigar mata saboda kalmomin suna kama da suna magana da ita kai tsaye
 Wanda aka haifa daga tsafin jini ba zai samu salama ba sai ya haWu da wanda Allah ya zaSa masa wadda zata iya Waukar zafin jikinsa kuma ta iya ?ona duhun da ke cikinsa da haskenta"
Ta runtse idonta da ?arfi zuciyarta ta buga tace
 Ni ce& ? Ta tambayi kanta cikin tsoro.
 Ko kuwa ni ce makamin da Allah ya halitta don Rashid, ko kuwa akwai wata bayan ni?

Wani zafi ya ratsa jikinta, jikinta na rawa, zuciyarta na bugawa da sauri kamar ana kiran sunanta daga wani wuri da ba'a gani.
A lokaci guda kuma, a waje, iska ta narke, ?asa ta motsa, kuma wani haske mai kama da toka ya bayyana daga tsakiyar ?asa Sultan Ameer ya bayyana cikin sutturar duhu, idanuwansa ja kamar wuta.
 Lokaci yayi, Wan uwana&   Lokacin da haske zai sadu da duhu, kuma duniya ta zaSi wanda zata bi
Cikin ?arfin zuciya Rashid ya janye takobinsa takobin Nurul Malik, wadda aka ce ba zata iya sare mutum ba sai wanda yake Wauke da jinin sarki
Suka tsaya suna kallon juna zuri a guda Waya jini Waya ?addara Waya, amma zuciyoyi biyu da Allah Ya raba da sirrin duniya.
Sun jima suna kallon juna kafin Rashid yace  Saboda Soyyayar halittar da duk duniya Ni kaWai nasan da wanzuwar ta cikin cikin matata Samha ka dawo duniyarmu yakai Wan uwana Ameer, kayi sani zuciyata ta fara barin imanin tsafi tana komawa ga Allah Waya wanda aka haife mu akan addininsa amma sai aka cuWanyamu da gargajiya da tsafi, na rantse da Allah wanda yake kare Samha a lokacin da Soyayyun ruhohi suke bibiyar sawunta, bazaka samu nasara akan Mata da jaririn haske dake cikinta ba domin ya an kasantar dashine tsakanin fitar wata da shigarsa, tabbas wannan ruhin abin kaWaicewa da imani ne"
Murmusawa Ameer yayi ya Wago jajayen idanunsa yace  ba don shi kaWai ba harda kai zan sha jininka don kafuwar ikona, an horar da zuciyata kada naso kada a soni saidai daga fitowata saman duniya na farajin ?amshin abinda nake bu?ata, a binciken da nayi kai ka rigani mallakar wannan ruhin da nake bu?ata don haka zanyi duk me yiwuwa na karSi abuna dake hannunka" ya faWa yana ?ya?yacewa da dariyar mugunta ya riga yasan Wan uwansa bashi da ?arfin tsafin jayayya da ikonsa, yana gama dariyar ya Sace yabar Rashid tsaye cikin wani yanayi daya kasa ganewa, cikin duhun dare..........


*Paid book 500 for regular, 1k for VIP, 1500 for V-VIP via 9031307566 Fauziyya Tasiu Umar Opay evidence of payment 09031307566*


*Oum Hairan*

*65-66*
Haka musayar kalamai da sihiri ta yawaita tsakanin jini Wayan suna ya?ar junansu ta ?arkashin ?asa Sultan Rashid ya gano mugun shirin da Wan uwansa Ameer yakeyi akansa da uwargidansa Samha da jaririn cikinta da kwanaki yasa yake girma har takai da ta daina fita ko ina kullum tana Sangarenta sai Granny ce ta dawo Amzir domin kula da ita da abinda take tare dashi, kasancewar itama Najjisa ta kasa ha?ura kullum cikin yi miyagun jefe jefe take wa Samha da abinda ke cikinta, saidai abinda ke bata mamaki yanda tsafinta yake juyawa gareta kullum.
To Samha ta kasance cikin halwar addu'a kullum da ko yaushe tana neman tsarin Allah daga tsafi da kaidin Aljanun gadon wannan masarauta tana kuma barranta Wan cikinta da duk wani abu daya shafi tsafi tare da faWawa Allah ya basu kariya ita da mijinta da Wansu daga wannan guguwa data mamaye gidan sarauta.
A cikin dare mai cike da iska, Samha ta farka daga barci da bugun zuciya mai karfi. Idanunta suka buWe cikin duhu amma ta fahimci wani zafi yana ?ona mararta.
Tana ri?e da cikinta, tana jin kamar ana ja ne daga ciki da wani irin ?arfin da ba a iya gani.
Ta furta da murya mai rauni: Subhanallahi& ya rabbil arshil Azeem...& 




A gefe guda, Sultan Rashid yana tsaye a tsakar fadar Hasumiyar Zinariya, yana tsaka da ya?in ruhi da Wan uwansa Ameer.
Iska na busowa kamar ana ihu, kuma wutar tsafi na wal?iya tsakanin hannayensu biyu.
 Ameer! Ka bar komai ya koma ga Allah!
 Allah?! Ameer ya faWa yana dariya mai cike da tsoro.
 Tun lokacin da aka haife ni cikin duhu, Allah Winka bai taSa waiwayeni ba! Na nemi haske, amma da aka ganni cikin ruWani, sai aka kulle ni a duniya ta ?asa! Yanzu ni zan hallaka duk wanda yake Wauke da jinin ka da nake ?i har da cikin da yake jikinta! Cikin wannan magana, Ameer ya Waga hannunsa sama ?ura ta fara tashi daga ?asa, iska ta rikiWe zuwa kalar toka, kuma wata murya daga cikin duhu ta fara kiran sunan Samha.
A cikin Wakinta, Samha ta dur?usa bisa darduma, idanuwanta sun cika da hawaye, hannayenta suna rawa tana Waga su sama.
 Ya Allah! Na sani babu wanda zai iya kare ni da wannan cikin face Kai. Idan duniya gaba Waya ta haWu da tsafi, Kai ne Mai Tsarki, Mai kariya daga kowanne sharri. Ka tsare min cikin nan da sunanka Ya Qahhar, Ya Hayyu, Ya Qayyum!
Da ta faWa hakan, haske ya fara bayyana a cikin Wakin nata fari kamar hasken safiya, yana fita daga jikinta.
Ameer da yake nesa, sai yaji wani abu ya tsaya masa a ?irji, ya ja baya cikin tsoro.
 Me ke faruwa?!
Ya furta, yayin da wutar hannunsa ta fara mutuwa.
Rashid ya tsaya yana kallonsa, idanuwansa sun cika da hawaye ko kaWan bai burin zama sanadin hallakar Wan uwansa yace  Wannan ba ?arfin tsafi ba ne, Ameer. Wannan ?arfin addu a ne& daga ita da jaririn da Allah Ya sanya a cikinta. Wannan shine ?arfin da baka da shi.
Ameer ya furta cikin Sacin rai:

 Jariri?!

Cikin fushi, ya saki wata annoba ta tsafi, wadda ta nufi gidan Samha kai tsaye kamar wutar duhu mai ?ona haske.
Amma kafin ta kai ga gidanta, wani sautin Addu ar Annabi Yunus (AS) ya ratsa iska, daga bakinta:

 La ilaha illa Anta, Subhanaka inni kuntu minaz-zalimin&  Sai ?arar wani ?arfe ya bugu da tsafin Ameer ya watse, duhun da ya aika ya rikide zuwa haya?i mai fari ya Sace.

Samha ta fadi a ?asa tana kuka, tana ri?e da cikinta, amma zuciyarta cike da natsuwa ta san cewa Allah ne Ya kare ta, ba Rashid, da tsafi ba.
Rashid da yake a fadar, sai yaji zuciyarsa ta yi sanyi, yana jin muryar addu ar da ta kare duka fadar yace.
 Samha& Kin zama garkuwar masarauta, ba don jini ba, sai don imani. Ameer ya tsaya da ido jajaye yana kallonsu daga nesa, yana fitar da huci yace
 Idan addu a ta kare ku yau, ba zata kare ku gobe ba& 
Ya Sace cikin duhu, iska ta koma sanyi amma sarauta ta san cewa rigimar haske da duhu bata ?are ba, sai jaririn da ke cikinta ya shigo duniya.


*SHU?EWAR WATA UKU*


Daren bai taSa yin shiru haka ba a masarautar Zirkan.
Ko iska ta tsaya, ko hasken fitila ya dushe, tamkar duniya ta tsaya jiran abu Waya, haihuwar wanda sama da ?asa ke jira.
A cikin Wakin Uwar Gida, an kunna ?ananan turare masu ?amshi. Samha ta kwanta, fuskar ta cike da zufa, amma idanunta na cike da haske hasken da yake fitowa daga zuciyarta.
Granny tana gefenta tana karanta Suratul Maryam da murya mai taushi, yayin da Dr. Mahraz ke lura da lafiyarta da tsoro a idonsa.
Rashid yana tsaye a bakin ?ofa, hannunsa na sa?ale a ?irjinsa, cikin damuwa fuskarsa na nuna tashin hankali.

 Ya Allah Ka kareta. Ka kare su duka. ya faWa a lokacin da ya tabbatar bashi da wata gudunmawa da zai bawa Samha.


A gefe mai nisa, cikin duniyar duhu, Ameer yana zaune gaban wani kwano mai jini.
 Idan wannan jariri ya rayu, ya ce cikin muryar mugunta,  to ikonmu zai ?are har abada. Ba zan bari haske ya sake rayuwa cikin jininmu ba.
Sai ya Waga hannunsa sama, ya haWa jini da ?ura, ya furta kalmomin tsafi:
 Tashi duhu, ka shiga jikinta, ka kashe abin da duniya ke kira alheri! Iska mai hucin zafi ta tashi daga ?asa, ta nufi fadar Zirkan.
Fitilu suka fara rawa, turaren wuta ya ?one, ?asa ta fara girgiza.
Samha ta yi ?ara tana ri?e cikinta, tana jin zafin da ba ta taSa ji ba azabar ciwon na?uda me neman Waukar rayuwa bakinta dauke da addu'o'i da Iklasin cewa Allan ta yana tare da ita a daidai wannan lokaci ne wuyar tsallakewa, tace
 Granny! Zafin nan yayi ?arfi yana ?onani!
Granny ta Waga murya cikin Neman taimakon Allah tace
 A uzu billahi minash shaitanir rajimRashid A'uzu bikalmatullahi tammat min sharri ma kala?" wannan ?urar tsafi ta hudo ta window ta shigo da gudu, tana kallon hasken da yake wal?iya daga jikin Samha, Granny tace
 Samha! Ki daina kallon ?urar tsafi Ki rufe idanunki! Ki karanta Ayatul Kursiyyu!

Da ta fara karantawa, muryarta ta canza  ta koma mai ?arfi fiye da yadda mace mai juna biyu zata iya.
 Allahu la ilaha illa Huwa, Al-Hayyul Qayyum& 

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login