Showing 6001 words to 9000 words out of 12217 words
Chapter 3 - JUNAINA BOOK COMPLETE BY OUM SHARIFAT.docx
rawa yace"""hakika mun tafka babban kuskure wanda ya ke bibiyar mu tsawon shekara goma sha biyar, mun rasa farin ciki da nutsuwa, mun samu kudi da mulki dk inda muka so muna zuwa a fadin duniya mata masu kyau da aji suke bibiyar mu saboda kudin mu harkar mu ta bin maza bamu daina ba saboda shine silar dukiyar mu saidai ubangiji ya cire nutsuwa daga zukatan mu ya sanya razani a ciki, hakika faduwar gaba masifa ce dn a rana daya nakanji faduwar gaba sama da sau goma jiki na yana nishadi amma zuciya ta taki karbar nishadin dk iya tnanin da zanyi nayi amma na kasa gano matsala ta daga bisani na gane babban kuskuren da muka tafka, lkc ya kure bakin alkalami ya bushe babu wata hanya da zamu bi wajan gyara kuskuren mu.
Alh Bashir shima wata karuwa ce ta ba da jinin sa ga matsafa.
Shan majina asisstance yayi ya sauka daga kan kujerar da yake yace na tabbata ni mai laifi ne a gare ku laifin da ban cancanci koda hada ido kuyi dani ba saidai ina so ku sani dani aka aikata laifin farko amma wllh babu ni a kashe malam Bukar da Aliyu.
mikewa Junaina tayi rike da hannun Junaid tace kalli asisstance tace """magana ta kare kunyi abnda kuke yanzu kuma kun riski abnda bakwaso, wllh badon manzon Allah saw ya hane mu azabtar da abnda zaa kashe ba koda kuwa dabbar yanka ce da saina sa kunyi mutuwar wulakanci mutuwar da ko iyalanku ba zasu gane gawar ku ba.
Naji dadin jin irin mutuwar da Alh Bashir yayi kuma kuje can ku tarar da wadanda kuka tura , tana gama fada ta juyo rike da hannun Junaid, turus tayi ta tsaya ta kasa magana ganin dc tsaye a bayan ta da alama yaji dk abnda suka tattauna.
Sauke ajiyar zuciya dc yayi yace"" Asp Junaina Bukar muje ki rage mn hanya a motar ki"" babu musu Junaina tayi gaba Junaid na biye da ita har wajan mota, ta bude ta shiga yayin da dc ya shiga kusa da ita Junaid a baya.
Tnda suka fara tafiya ba wanda yace komai har sukayi nisa a bakin hanya Junaina ta tsaya ta kalli dc tace ""ina zan kai ka sir ? ""gidan ku dc yace yana kallon gefen hanya.
Kara tada motar Junaina tayi ta nufi gida a kofar gidan tayi perking Junaid ya fita ya bude kofar ta shiga da motar ta ajiye ta a perking lot sannan ta fito dc ma ya fito suka shiga cikin gidan,
Tn daga baranda suke jiyo karatn qur'an cikin wata daddadar murya, da kokonto a ran Junaina cikin sauri ta karasa palourn inda ya iske juhaina zaune saman carpet sanye da hijab tana biyo hadda, wani mutum daga nesa da ita shima saman carpet dn da alama shine yake jin haddar.
Karasa shiga ciki Junaina da Junaid sukayi suna bin juhaina da kallon tsantsar mamaki har suka zauna akan kujera, ita ma Junaina tsayar da karatn tayi tana bin su day kallo fuskar ta fal murmushi.
Dc da ba wanda ya bashi wajan zama ya nemi waje ya zauna sannan ya kalle su gaba daya yace """ su yawe ku? Menene labarin ku? Meyasa kuke kashe su commissioner?.
Gyara zama Junaina tayi da dubi dc tace """
Unguwar dorayi unguwa ce ta talakwa da masu kudi zaman lafiya sosai akeyi a cikin unguwar kowa yana mutun ta kowa ...
Manage please
👩🏻✈️JUNAINA👩🏻✈️
15-16
JARUMAI WRITTERS ASSOCIATION TAKEN MU ALKALAMI YAFI TAKOBI
NA
KHADIJA UMAR ABDULLAHI (GARKUWAR JARUMAI CE)
بسم الله الرحمن الرحيم
Limamin unguwar sunan sa malam Abubakar amma ana kiran sa da Bukar abnda muka sani kawai yazo ne daga maiduguri shida matar sa Fatima yana da yara guda uku na farko Aliyu bayan Aliyu ya shekara biyar sai Allah ya azurta malam Bukar da samun yan biyu mata, ranar suna yara suka ci sunan mahaifiyar Bukar da ta Fatima wato Aisha da Salma ana kiran Aisha da Juhaina Salma kuma Junaina haka rayuwa ta cigaba da tafiya cikin kaanciyar hankali bayan wani lokaci yara snyi wayo matar Malam Bukar ta haifi dan ta namiji aka saka masa suna Junaid.
Malam Bukar matafiyi ne yana zuwa cin kasuwa dk ranar jumaa da yamma sai ranar lahadi yake dawowa , mai unguwar dorayi mutumin kirki ne dk da kasancewar sa dattijo amma ya zama tamkar aboki ga malam Bukar a ranaku uku cikin sati malam Bukar na yiwa matasa da masu aure karatu bayan sallar magrib zuwa lkcn sallar isha'i .
Allah ya azurta malam Bukar da tarin dabbobi inda yake kiwon su a wani kango da ya siya a jikin gidan sa, tn daga kan shanu har zuwa kaji suna da yawan da gani daya bazai yiwu ka kirga su ba, da haka iyalan malam Bukar ke rayuwa cikin walwala da farin ciki da ragowar mutanen unguwa kowa na cin arzikin malam Bukar kasancewar sa mutum mai son mutane da kuma kyauta bai yarda yaga wani cikin damuwa saidai idan bashida yanda zeyi ya yaye masa to zai taya shi da addua.
Kari ma wata mata ce da mijin ta ya rasu tana da yaro guda daya sunan sa Nura baya jin magana kwata kwata a yanda lbr ya riske mu ko sanda mahaifin sa na da rai bata bari yayi masa fada har zuwa lkcn da Allah yayi masa rasuwa, wannan kenan.
Misalin karfe uku na yamma ranar jumaa malam Bukar ne rike ta dan karamin buhu a hannun sa ya fito tsakar gida kamar yanda ya saba kowa naira biyar biyar haka yabi yaran sa da shi matar sa tayi masa rakiya har kofar zaure tana yi masa addua ya tafi , yana tafiya ta dawo ciki ta zauna kusa da Aliyu tace "" baba na kaje gidan malam kace inna ta baka maganin basur ka zo na dafa maka naga kwana 2 ka canza baka zama sosai ina tinanin basur ne ya kama ka , da to Aliyu ya amsa ya fice daga gidan, ba jimawa ya dawo da kullin magani a leda, haka mama ta karbi maganin ta tafasa ta bawa Aliyu ya fara sha har zuwa dare.
Cikin dare Aliyu ya kasa bacci wani irin zullo yake yi kmar me kmn aljanu hankalin mama yayi matukar tashi ta shiga tofa wa Aliyu adduoi kala kala har ya samu yayi bacci,
Kashe gari da safe mama ta hada markaden kunu ta bawa Aliyu nan da nan jikin Aliyu ya fara rawa ya fara ja da baya yana girgiza kai, tsayawa kawai mama tayi tana kallon Aliyu kafn tace "" zo nan baba na bai zoba Kuma jikin sa be daina rawa ba.
Kasancewar karime mace marar hakuri yasa mama tayi zaton ko Aliyu yayi mata wani laifi shiyasa yake tsoron zuwa gidan .
Murmushi mama tayi tace ""baba na mai kayi musu a gidan waye baka son gani idan kaje "" Nura"" Aliyu yace idon sa na zubar da hawaye, damm kirjin mama ta buga nan ta ke ta tafi tnani wata rana ana suna a unguwar taji ana zancen Nura yana lalata yaron mutane maza kuma karime ta na cewa ana yi wa dan ta sharri firgigit mama ta dawo daga tunanin da take yi kamar ta farka daga bacci, cikin tattausar murya mama ce fada mn baba na me yayi maka idan ka fadamn zan baka dk abnda kake so"" yace ze kashe ni kuma in dena ganin ku .
Wani karin bugu kirjin mama yayi jikin ta ya fara rawa hankalin ta ya kai kololuwa wajan tashi zuciyar ta ta karye amma haka ta daure ta rike hannun Aliyu suka fice sai gidan karime.
Ciki ciki mama tayi sallama a gidan karime ta dube ta tana washe baki tace binta yau da kanki ? Bata ce komai ba sai turo Aliyu gaban karime tayi tace ""fada mata me Nuran yayi maka ? Still har yanzu jikin Aliyu rawa yake yace "" idan na fada ze kashe ni in dena ganin ku .
Da fa kafadar Aliyu mama tayi tace "" karime ashe abnda ake fada gaskiya ne ashe kinsan abnda Nura yake yi amma kika hana ayi masa hukunci kike karya tawa?.
Shiru karime tayi da kyar ta bude baki tace binta wannan fa dk sharrin makiya ne kuma asiri akaiwa kabiru kwata kwata baya shaawar mace sai namiji amma ina kan nema masa magani dn Allah kuyi hakuri ku rufa mana asiri.
Wani kallon banza mama tayi mata sannan ta fara magana cikin bacin rai bakin ta har daci daci yake yi tace """ a cuce ni a lalata mn rayuwar yaro sannan kice in rufa muku asiri ? Wllh bazan iya ba bari malam ya dawo wllh kotu zamu shiga daku tana kaiwa nan ta fice daga gidan, ranar haka mama ta kasace wani ubu ke mata yawo a zuciya mai zafi yaki sauka bare ta samu tayi hawaye dk.sanda ta kalli Aliyu sai taji zuciyar ta tukuki kmar zata fasa kirjin ta ta fito.
Ranar lahadi da safe karime tazo domin kara bawa mama hakuri amma mama tayi mata korar kare tace ta jira sammaci.
Har kofar gida mama ta biyo karime tana fadin ba zata yarda ba babu kowa a wajan sai abokin baba malam kabiru jin abnda ake fada ya sashi saurin tasowa ya dubi karime yace ana dai kam ba zamuyi shiru ba wllh yau malam Bukar zai dawo Kuma ni zan rakashi muje kotu muyi karar ku
Kmr yanda aka saba da yamma baba zai dawo haka akayi saida sabanin yanda ya saba dawowa fuskar sa babu annuri baya kula kowa harda ita kanta mama ranar ma a masallaci ya kwana.
Kashe gari da safe aka aiko daga wajan mai anguwa yana neman mama cike da mamaki mama ta canza kayan ta ta saka hijab ta bisu suka tafi, a hanya banda zancen zuci babu abnda mama takeyi ta rasa dalilin kiran ga damuwar rashin ganin walwala a fuskar ba a haka har suka karasa gidan mai unguwa.
Har cikin palourn sa suka shiga anan ne ta tarar da baba da mai unguwa da wani babban malami wanda ake ji dashi a unguwar da kewayen ta gaba daya gefe kuma malam kabiru ne wato abokin baba sannan sai karime da dan ta Nura da abokan sa gusa hudu.
Zama mama tayi tana tnanin ko.malam kabiru ne ya sanar da baba abnda ya faru da Aliyu.
Wani irin zullo zuciyar mama tayi tare da mikewa tsaye a lokacin da ba ta ma san ta mike ba jin wai ana zargin ta da aikata mashaa da malam kabiru abokin baba, tsananin razani da kaduwa ya hana mama cewa komai kallon kowa takeyi amma bakin ta ya gaza furta koda kalma daya bare ta kare kanta da kyar ta rarrafa wajan baba ta kama kafar sa zata fara magana baba ya tunkuda ta sannan ya bita da harara yace"" kin bani mamaki binta kin cuce ni keda kabiru bazan taba yafe muku ba .
Haka mama ta koma gefe ta takure tana raba idanu tana ganin abn kamar a mafarki wai ita aka kama turmi da tabarya da malam kabiru.
Bata kara tsinkewa da lamarin ba saida malam ya fara tambayar shaidun daya bayan daya suke bada shaida dk da kuwa malam na fadar rantsuwa suna maimaita wa , a kunnen mama kuma a gaban idon ta malam yace "" ni wane sai me bada shaidar ya fadi sunan sa yace "" na rantse da girman Allah da Ido na naga binta da Malam kabiru turmi da tabarya sai gaba daya wajan a dauki kabbara .
Duka mutum hudun haka sukayi hadda karime wacce tace tazo wucewa ne sai ta leka zata bawa binta canjin markade shine taji nishi a daki data leka shine taga binta da Malam kabiru turmi da tabarya shine ta fita ta kira Nura da abokan sa su hudu suna zaune domin su shaida Kuma sun shaida har lokacin binta da Malam kabiru basu bar abnda sukeyi ba hasalima dk basu san me ake yi ba.
Kamar yanda addinin musulunci ya tanada shaidun zina mutum hudu masu hankali kuma balagaggu haka suka shaida akan mama .
Mama tana kuka tana komai tana waiwayen ko Allah zai kawo wanda zai Fadi gaskiya tana kallon karime koda zata janye maganar ta Amma ina haka aka yanke wa mama da Malam kabiru hukuncin kisa ta hanyar jifa Kuma aka saka ranar jifan sannan aka tafi dasu kurkuku aka ajiye.
Bayan kwana biyu aka fito da mama da Malam kabiru dama a lokacin unguwar daji ne sosai a ciki haka aka je bayan gari aka haka dogon rami aka saka mama da Malam kabiru a tsaye iya wuyan su kadai ake gani.
Shela akayi cewa ina makusantan ta baba ya fito yana hawaye zuciyar sa na kuna ya dauki duwatsu guda uku ya jefi kan mama da su,
Nan fa aka hau kabbara a gaba na nida Junaina da Junaid da Yaya Aliyu aka dinga jifan kan mama da malam kabiru idan aka jefa ta dama sai kan ya lankwashe yayi hagu idan aka jefa hagu se ya koma dama wasu zafafan hawaye ne ke zuba a fuskar mama a lokacin da muke kallon juna mu da ita muma muna kukan abnda ake mata dk da a lokacin bamusan manufar hakan ba.
A gaban ido na kan mama ya dena rawa ya tsaya cak a gefen dama idon ta ya dena rawa shima ya tsaya cak yana kallon mu jinin ya wanke fuskar mama haka shima malam kabiru daidai nan kuma aka dauki kabbara gaba daya wajan.
Junaina tana zuwa nan a labarin ta ta fashe da wani kuka mai tsuma zuciya hadi da ban tausayi yayin da numfashin ta ya fara sama yana kasa..
*GARKUWA CE*
Da sauri juhaina na mike ta nufi fridge ta dakko ruwa ta dago kan Junaina ta bata, a hankali Junaina take sauke ajiyar zuciya wasu zafafan hawaye na zuba a idon irin hawayen da ta dade tana fatan zubowar su amma sun gagara fitowa sai yau.
Juhaina ta koma gefe ta zauna sanna ta dubesu ta dora daga inda Junaina ta tsaya.
Daga nan aka kara gyara ramin kan mama da Malam kabiru suka shige ciki, da daddare shiru haka gidan mu ya kasance babu wani mai walwala a cikin mu har shi kansa Abban mu haka muka dnga rayuwa kllm muka tambayi Abba yaushe Mama zata dawo sai dai yace zata dawo kawai.
Gidan mai unguwa muka koma da kwana kfn Abba yayi wani auren saidai yaya Aliyu bai yarda shidai yana tare da Abba.
A daren ranar wata lahadi wacce ba zamu taba mantawa da ita ba wacce ta zana cikamakin lalacewar farin cikin mu shine ranar da aka wayi gari anyi wa Abba da yaya Aliyu yankan rago, babu Wanda ya sani sai azahar da aka ga bai fito sallar asba kuma har anyi sallar azahar bai fito ba duba da halin da yake ciki akayi tinanin ba lafiya ba shine aka haura aka samu gawar su an yan ka wuyan su jinin har ya bushe a jikin su.
A wannan lokaci dk wani mai imani saiya tausaya wa rayuwar mu da iyayen mu.
Sai a lokacin aka fara tinani akan hukuncin da akayi wa mama, sai a lokacin mutane suka fara tinanin rashin adalci aka mata.
Binciken gawa aka fara yi nan sai aka samu sperm a bayan yaya Aliyu tabbacin saida akayi luwadi dashi sannan aka kashe shi to daga nan ne mutane suka fara hasashe akan gaskiyar mama, daga nan ne mutane suka fara tinanin shaidar da aka samu akan mama ta fito daga gida daya, sannan kowa ya fara tina zargin da ake wa Nura akan lalata yara maza.
Dk iya binciken da akayi babu wata alama da zaa gane wanda ya kashe Abba da yaya Aliyu bayan wani lokaci abubuwa suka lafa zancen ya mutu babu wanda yake cewa komai akai muna rayuwa a gidan mai unguwa duk da rayuwar ba mai dadi bace, ban da hantara da gori babu abnda ake mana kowa ce uwa bata so muyi Wasa da yayan ta babu mai bamu abnci sai dare idan mai unguwa ya dawo muci nasa tare wanka kuwa babu shi haka muke rayuwa kllm saboda babu me taba mu saidai muyi jika jikar su musa kaya babu ilimin addini bare na zamani
Ko shekara bamuyi a gidan mai unguwa ba rayuwa ta kara juya mana shima ya dena kula damu to a wannan lokaci ne kuma muka hada yan kayan mu muka bar gidan mai unguwa muka bar unguwar gaba daya babu inda zamu kwana dn haka muka shiga cikin almajirai munayin bara da rana da daddare muna kwana cikin wasu gine gine Wanda baa karasa ba haka muke rayuwa koda ana ruwan sama ne haka yake Zane mu har mu bushe ga kuruciya kuma ga rashin matallafi bayan mun kai shekara goma ne kuma wata mai abnci ta dauke mu muna yi mata wanke wanke da karbo kwanuka idan anci abnci da kuma mika abncin yanda muka saba da aiki a gidan mai unguwa yasa muke ganin nata aikin ba komai bane wannan yasa ita kuma take ganin kokarin mu ta ce mu dawo gidan ta , haka muka dawo muna murna muka cigaba da yi mata aiki tana bamu abnci mu koshi sannan ta saka mu a makarantar dare kuma tana bamu hamsin hamsin kllm sannan ta sai mana banki muna zuba kudn a ciki.
Zuwa makarantar dare yasa mukayi kawaye masu zuwa makarantar boko nan fa muka fara tina karatun mu na da lokacin Abba da mama suna nan .
Abun yana bamu shaawa saidai babu yanda zamuyi sai hakuri, kmr yanda muka saba lokaci lokaci mukan zauna muyi ta hirar makarantar boko wata rana muna hirar mama Rabi taji , da mamakin mu sai muka ji tace