Showing 9001 words to 12000 words out of 12217 words
Chapter 4 - JUNAINA BOOK COMPLETE BY OUM SHARIFAT.docx
"" kuna son makarantar boko a tare muka hada baki wajan amsa mata harda Junaid wanda a lokacin ajin sa daya a primary muka dena zuwa ,
Zama tayi kusa damu tace "" indai zaku dnga tashi da wuri kuna yin aikin ku zaku dnga zuwa boko zan samo almajiri y dnga karbo.kwanuka da safe ku sai ku dnga yi da yamma tn da makarantar daren ana biya muku komai ko? Nan ma muka amsa da eh sannan muka yi alkawarin zamu dnga tashi da wuri munayin aiki.
Abu kamar wasa haka aka fasa bankunan mu mama Rabi ta cika mana tayi mana uniform aka kaimu makaranta , bayan anyi mana interview aka kaimu aji hudu shima Junaid aji biyu aka ajiye shi.
Haka muka cigaba da rayuwa mama Rabi ta dauke mu tamkar yayan cikin ta da asba bayan munyi sallah muke yin wanke wanke da shara sannan mu dama kunu mu karya mu wuce school.
a makarantar dare ma dai Alhamdulillah ana biya mana qur'an da sauran littafai kuma muna iya wa sosai.
Haka rayuwa ta dinga tafiya cikin kaanciyar hankali da nutsuwa rayuwar farin ciki mukeyi a wannan lokaci har muka gama primary muka shiga secodary.
Kamar yanda muka saba muke yin aikin gida daba daya har girkin abincin ma mune mukeyi ranar da babu makaranta, idan sallah tazo ko maulud haka zaa fasa bankin kowa ayi mana kayan sallah da na maulud babu wanda zaice mu marayu ne har muka gama secondary
*JUNAINA
17-18
GARKUWAR JARUMAI
CE
JARUMAI WRITTERS ASSOCIATION TAKEN MU ALKALAMI YAFI
بسم الله الرحمن الرحيم
Bayan munyi candy ne kuma mun kara girma na kara fahimtar zafin wutar daukar fansar dake ruruwa a zuciyar Junaina hankali na ya rabu biyu da tnanin wasiyyar mama da kuma burin daukar fansar daga nawa bangaren nima ba jimawa muka je mukayi jamb muna jira ta fito mugani mu cigaba da karatu , a wannan lkcn ne wata ranar jumaa ina zaune ina wanke wanke mama Rabi na tsaye a kaina batare da na sani ba saida na gama komai sannan ta kira ni dakin ta , da sallama na shiga dakin na zauna na sunkuyar da kaina , jin muryar mama Rabi nayi yane cewa "" juhaina me yake damunki ? Da sauri na dago kaina ina Shirin yin magana mama Rabi ta daga mn hannu tare da cewa idan har kinsan abnda zai fito daga bakin ki ba gaskiya bane kar ki fada mn idan kuma kin dauke ni matsayin mahaifiya to ina sauraren ki ta karasa fada tana gyara zama.
Banida wani zabi wanda ya wuce na fada mata gaskiya hawayen daya fara sintiri a kumatu na na share na fara magana.
"" Ranar da aka kai mama kurkuku ranar da baban mu ya kaimu har naga tana kuka tana neman yafiyar sa amma ya ki kulata zuciya ta tayi zafi domin a duniya idan kika cire Allah da manzon sa babu abnda nafiso kuma nake kin damuwar sa kmr mama haka baba ya finciko mu zamu wuce Junaina ta bishi tana waiwayen mama tana kuka ita da Junaid amma ni haka na ja tunga na dage naki tafiya ganin haka yasa mama ta tsuguna guiwar ta a kasa ta kama fuska ta cikin hawayen ta wanda yaki goguwa daga idanu na tace """ ina horon ki da ki kasance mai yafiya da kuma kore rike mutum a ranki dk abnda wani zai miki ki sani cewa a cikin manzannin Allah da manyan bayin sa da suka wuce anyi musu sama da haka kuma sunyi hakuri daga karshe ma yafiya suke yi sun kasance masu rubanya kyautata wa ga wadanda basa kaunar su saboda su sufita hakkin su sannan ki gujewa daukar fansa kiyi hakuri da komai wannan kuma umarni ne tana gama fada mn haka ta juya ciki ina kallo aka rufe taa ban sake ganin ta ba sai sanda ake jifan ta.
A daidai nan na tsaya da bawa mama Rabi labari inda muka kasance cikin zubar da zafafan hawaye nida ita , hakuri sosai mama Rabi ta shiga bani , na share hawaye na tare da jijjiga kaina nace "' yanzu burin Junaina ta shiga aikin yan sanda ta dauki fansar abnda aka yiwa mama idan har ina tare da ita dole saina taimaka mata kuma bazan iya ba sbd mama tace wannan umarni ne sannan idan na fadawa Junaina itama zata fasa daukar fansar wannan shine abnda ya damu zuciya ta .
Cike da tausaya wa mama Rabi ta kira wata kawar ta mai saida abnci ita ma a kaduna ta bata labari a kaina Kuma tace zan koma can da zama na roke ta akan kada Junaina ta sani to dama muna soyayya da wani Dan makarantar mu Kuma a lokacin Junaina ta nuna Bata so har mun samu dn sabani a kansa to Rana daya aka wayi gari babu ni kuma na bar wa Junaina wasika akan kar ta damu ina cikin koshin lafiya .
dk halin da ake ciki ina sani ta hanyar mama Rabi Junaina ta zata saboda soyayya na guje musu bata wani daga hankalin ta ba taci gaba da karatun ta da kuma lissafi akan daukar fansar ta .
A can kaduna ma na samu mama hadiza mutuniyar kirki ta dauke ni tamkar yar da ta haifa na cigaba da karatu na a can akwai Dan ta guda daya ya girme ni bayan na kammala degree namuka hada kai dashi muka shiga neman dangin iyayen mu ,
cikin saa kuwa muka samu matar malam kabiru ta sanar damu garin su baban mu amma bata san gidan su ba .
Bayan yan kwanaki muka shirya muka tafi inda muka sauka a wani hotel kwanan mu uku muna neman Wanda yasan iyayen mu amma babu wanda yasan mu har na sare nace mu koma gida ranar da zamu dawo ne muka fita da safe muka hadu da wani makaho ze fada rami muka taimaka masa muka raka shi har gida yana ta sa mana albarka daga nan muma muka sanar dashi abnda ya kawo mu cikin saa kuwa ashe makocin kakan mu ne haka y sa aka raka mu har gidan kakan mu , mukayi sallama muka shiga tn kafin nace komai mutanen gidan suka fara Kiran junan su suna kallo na seda suka cika akaina kafin wata tsohuwa ta fito itama har inda nake aka matsa mata ta karaso ya shiga shafa fuska ta tana hawaye tace ke jini na ce ke yarinyar Bukar ce kafin ta gama maganar ta nima kukan ya kufce mn na tsuguna nayi sujjada nagodewa ubangiji daya nuna mn ahali na .
Nan fa aka shiga aika yara gona suna Kiran mazan gidan kafin kace kwabo an cika haka na dinga bada labarin mu muna kuka , yan uwan Abban mu suka fusa ta da kyar na shawo kansu na sanr dasu halinda ake ciki a yanzu naki bari na kawo su wajan su Junaina saboda kar na katse mata kokarin ta dk abnda takeyi ina sani kuma ina zuwa kano saboda su ina ganin su ina komawa kaduna.
Ana haka wani a bokin Dan mama hadiza wato Abdallah muka shirya plan dashi mukaje dorayi muka tarar da karima a cikin gidan mu an gyara gidan sosai ya zama kato tana cikin walwala da jin Dadi,
Ya nemi ta siyar masa da gidan tace ba zata siyar ba sai yayi mata barazanar yasan komai Kuma idan Bata siyar masa ba zai tona mata asiri nan fa jikin ta ya fara rawa abn mara gaskiya ta sa Dan ta Nura ya siyar masa da gida cikin karamin farashi dk yanda sukayi da karima yayi recording munso kaita ga hukuma sai muka ga yanayin kasar ta mu gashi danta ya fara zama wani sannan ya shiga siyasa sai muka bari Junaina ta gama aikin ta koda zaa gano ta muna da hujjoji a hannun mu.
Nazo wa Junaina da Junaid a yanayin da nazo ne saboda nasan koda Junaid ne zai tausaya wa halin da suke tinanin na jefa kaina su tafi dani gidan su tnda aikin ya kare kuma inaso na dawo mu rayu tare , na bata kiran Junaina a waya tace kar na sake neman ta ta cire ni daga cikin yan uwanta ranar na kwana ina kuka saboda ni kullm.jira nake naga ta gama aikin ta munda wo da rayuwar mu mai dadi fiye da ta da wannan ne yasa nazo da wannan yanayin.
Amma ni ban taba zina ba ban taba shan kayan Maye ba dk surutan da nake ina sani nake yin su.
Wannan shine Abdallah juhaina ya fada tana nuna wanda yake kusa da ita sannan ta dora da cewa muna soyayya dashi kuma zamuyi aure amma har sai Junaina ta fitar da wanda zata aura sannan a hada ,
Da sauri Junaina ta kalli juhaina ta waro Ido tace ni kuma waye zai aure ni nayi kisa ba daya ba ba biyu ba waze iya zama dani?
"'nine zan aure ki kuma na zauna dake na baki soyayya da kulawa idan kin amince DC ya fada yana kallon Junaina.
*JUNAINA*
19-20
JARUMAI WRITTERS ASSOCIATION TAKEN MU ALKALAMI YAFI TAKOBI
NA
KHADIJA UMAR ABDULLAHI GARKUWAR JARUMAI CE 💪🏽
بسم الله الرحمن الرحيم
Ita ma kallon sa tayi sai ta sunkuyar da kanta kasa tana dan murmushi tasowa yayi yazo dan nesa kadan da ita ya zauna yana fuskantar ta yace """ najima ina dakon soyayyar ki a zuciya ta saidai na fahimci ko wasa bakya yi da mutane bakida lokacin kowa ko da kawaye kuwa na shiga bibiyar rayuwar ki inda na gane ku kadai kuke rayuwa keda kanin ki Junaid bande na bibiyar ki ba sannan na fara nuna miki alamun soyayya saidai koda yaushe nuna mn kikeyi baki fahimta ba duk da ina da tabbacin kin fahimci inda na dosa , ban hakura na cigaba da binki to a dazu ne naga zaki shiga wajan assistance shiyasa na biyo ki Kuma naji abubuwa da dama wanda suka daure mn kai dk da nasha zargin ki akan kashe kashen da akayi domin kuwa dk inda akayi kisa nasan kinje wajan saidai yadda da amincin dana baki yasa na hana zuciya ta yarda da zargirn ynzu kuma naji komai game daku hakika na girgiza kuma nayi mamaki sannan kuma na jinjina miki hakika irin ki kadan ne cikin mata salon ki ya burge ni abnda bamu sani ba yanzu shine menene ya raba ku da mama Rabi?
""Hawaye Junaina ta share sannan tace shekara biyu da tafiyar juhaina mama Rabi ta fara ciwo ko tashi bata iya yi nice nake mata komai kllm takanyi mn nasiha sosai akan rayuwa sannan ta dinga dakko mn abubuwan da ta mallaka ta na damka mn shi ta bar mana , nidai a lokacin dauka nakeyi kawai zafin ciwo ne na ajiye komai nace idan ta ji sauki zan mayar mata kayan ta cikin daren wata alhamis ciwon yayi tsanani na fita da gudu naje makotan mu na kira mai napep yazo ya taimaka mn muka saka ta a ciki muka tafi asibiti , likitoci suka karbe ta suka shiga da ita ciki mudai muna ta zagaye nida mai napep dn hankalin mu a tashe yake domin mama Rabi mutuniyar kirki ce kowa tana zaune dashi lfy cikin mutuntawa muna cikin haka likita ya fito da sauri muka nufe shi muna tambayar sa jikin ta amma haka ya kalle mu yace saidai muyi hakuri Allah ya karbe ta"
Nan take jiki na ya fara rawa kafafuwa na suka kasa dauka ta na rasa a wace duniya nake still dai mun kara rasa gatan mu wani irin Kuna nake ji cikin raina harshe na yana bani dandanon daci ido na ya soye hawaye suka kasa kawo mn agaji a lokacin rashin mama na ya kara dawo mn sabo a da na zata munyi bye bye da maraici ashe zamu kara fadawa ya Allah shine kadai abnda na iya furtawa na zube a wajan nayi zaman yan bori, saida safe aka saka gawar mama Rabi a mota aka tafi da ita gida akayi mata sutura aka kaita gidan ta na gaskiya , nan fa aka shiga zaman makoki har na tsawon kwana bakwai ranar da ta cika kwana goma da sassafe wani mutum yazo y dnga sallama a kofar gida haka na saka hijab na fito na same shi jingine da gidan mama rabi har kasa na tsuguna na gaida shi amma ya dauke kai yace ba gaisuwa ta kawo shi ba , nan yake sanar mn cewa gidan da muke ciki na sane haya mama Rabi takeyi abn ya bani mamaki tnda muke gidan bamu taba ganin yazo ba Amma banida ja haka na amsa masa da to kwana bakwai ya bamu yace ze kawo wanda ze zauna.
Amsa masa nayi da to na dawo na fara shirye shiryen tashi daga gidan nida Junaid na dakko sarka da yarin da mama Rabi ta bani naje kasuwa na siyar da su sannan na shiga makota na sanar dasu halin da ake ciki kowa yayi mamakin abnda wannan mutumin yazo dashi amma tnda bamuda hujja haka aka samo mna wani gidan hayat muka koma na cigaba da sanaar saida abnci lkcn da banida lecture haka dai muka cigaba da rayuwa nida Junaid har sanda na kammala degree na shi Kuma Junaid yana 100 level cikin ikon Allah a wannan lokacin na siya mana Dan karamin gida sannan na fara online business rayuwa mai kyau mukeyi cike da farin ciki saidai farin cikin na gushewa ne duk sanda muka tuna Abban mu da mama da Yaya Aliyu da Kuma juhaina haka muke binsu da addua .
Na fara neman aiki ina cigaba da addua cikin ikon Allah na samu na fito da matsayi me kyau to daga nan ne na fara daukar fansa ta har zuwa yau da na kawo karshen aiki na.
Tasowa Junaina tayi tazo kusa da juhaina ya tsuguna tana kuka tace "" kiyi hakuri ki yafe mn hakika na zarge ki da abubuwa da dama bata karasa ba juhaina ta rufe mata baki tare da girgiza mata kai tace """ aa bakiyi laifi ba ko.wacece a matsayin ki irin tunanin da zatayi kenan rugume juna sukayi suna kuka harda Junaid da kyar DC da Abdallah suka rarrashe su sukayi shru basu tafi ba sai dare da niyyar give da safe zasu tafi maiduguri wajan dangin iyayen su.
Ranar kuwa Junaina da juhaina da Junaid babu bacci hira kawai sukeyi irin ta yan uwa masu kaunar junan su abn gwanin ban shaawa .
Kamar yanda suka tsara haka akayi karfe goma na safe suka dauki hanyar maiduguri a motar DC yayin da wani dan sanda yake tuka su tn suna hira har kowa yayi shiru , kasancewar tsakanin Kano da maiduguri akwai nisa yasa suka dade a hanya sai magrib suka isa har kofar gidan kakan su aka sauke su inda suka shige da gudu suna duban ta inda zasu fara hango dangin su .
Aikuwa kamar hadin baki mutane suka fara fitowa suna rungume Junaina da Junaid cike da doki, komawa gefe juhaina tayi tana turo baki kamar zatayi kuka kanin Abban su ne ya farga ya dube ta yace ""aa Aisha sarkin kishi lafiya ko "" kara turo bakin tayi tace "" ba kune duk kunfi farin cikin ganin su ba ni ko kulani bakuyi ba "" dariya gaba daya suka saka suna mamakin kuruciya irin ta juhaina "" taho nan.kinji kawas cewar kishiyar kakar su tana rike hannun juhaina kafewa juhaina tayi a jikin ta tana yiwa su Junaina gwalo.
Sai da aka turo yaro.karbar ruwan alwala sannan suka.tina sun taho tare da baki .
Bayan anyi sallar isha'i yayye da kannnen kakan su Junaina suka zauna da Usman wato DC da kuma Abdallah inda suka tsaida magana Akan zasu turo iyayen su neman auren Junaina da juhaina.
Kashe gari Usman da Abdallah suka shirya juyawa kano saida aka tambayi Junaina da juhaina raayin su akan auren suka amince sannan aka basu dama su turo ayi maganar auren.
Zagaya aka dinga yi dasu cikin dangi daga bisani aka kaisu gidan su maman su nan ma fa murna baa magana kamar zasu cinye su nan aka barsu su kwana biyu suga dangi .
Bayan sati daya iyayen su Usman da Abdallah suka zo suka kawo kudin aure aka tsaida ranar aure wata uku masu zuwa.
Soyayya mai tsafta mai cike da kulawa suke gudanar wa hankali kwance cikin dangi babu maraici.
Yauma kamar koda yaushe Usman zaune kan daddu ma yayin da Junaina ke can gefe kanta a kasa tana Wasa da zoben hannun ta "" baby Usman yace yana son kallon fuskar Junaina amma taki dagowa kunyar sunan da ya saka mata take ji wai baby saida ya kira ta sau uku sannan ta dago kanta a kunyace cike da shagwaba tace nidai ba sunana baby ba dariya Usman yayi yace """ nidai a waje na ke baby ce saboda haka sunan da nasa miki kenan Kuma haka zan dnga kiran ki ,
Dama ina so.muyi wata magana ne ko nace alfarma sosai Junaina ta maida hankalin ta gare shi shima ya fuskance ta yace "" idan babu damuwa ina so ki ajiye aikin damara ki cigaba da karatun science dnki kinfi kyau a likita baa yar sanda ba ba wai dn hakan yayi muni bane aa kawai dai ina kishin ganin ki da kayan yan sanda""" shiru Junaina tayi na tsahon lokaci sannan ta dago ta dube shi tace "" na zabi zama yar sanda ne saboda daukar fansar iyaye na amma ba wai dn shine raayi na ba kuma nima ina da shaawar ajiye aikin dn haka da ga yau ma na ajiye dk yanda kace haka zaayi baby ta na fadar babyn ta tashi ta shige ciki da gudu .
Dariya sosai Usman ya dnga yi yana mamakin yawan