Showing 1 words to 3000 words out of 12217 words
Chapter 1 - JUNAINA BOOK COMPLETE BY OUM SHARIFAT.docx
👩🏻✈️👩🏻✈️JUNAINA👩🏻✈️👩🏻✈️
1_2
JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION TAKEN MU ALKALAMI YAFI TAKOBI
Na
Khadija Umar Abdullahi
(Garkuwar jarumai ce)
بسم الله الرحمن الرحيم
Sassanyar iska ce ke ka dawa bayan dauke ruwan sama ga yanayin garin gwanin ban shaawa ga shuke shuke sunyi luff gwanin ban shaawa cikin unguwar porestry dake jihar kano sabanin inguwoyin talakawa da wani layin ma idan aka yi ruwa baya biyu ba.
Wata bakar range Rover ce tayi perking kofar wani katon gida wanda get dn sa ma kadai abn kallo ne an dauki lokaci da tsayawa baa fito daga cikin motar da sai can aka bude murfin motar ,wata matashiyar budurwa ce wacce ba zata gaza shekara ashirin da biyar ba ta fito sanye da kayan likitoci a jikin ta fuskar ta rufa da mask da kuma bakin glass ba abnda ake gani a fuskar ta, wayar ta kirar iPhone+14 ta dakko ta fara duba wa hoton gidan dake gaban ta da dakko ta kalla sannan ta jijjiga kai alamar tabbatar wa ta rife motar ta nufi gidan.
Nocking ta fara yi get man ya leko dn jin waye ganin ta da kayan likitoci ga kuma first eid box a hannun ta ya sashi washe baki yana yi mata sannu da zuwa tare da matsawa gefe ta wuce tana masa godiya.
Cikin gidan ta karasa ta shiga har cikin palourn tare da sallama a bakin ta, shiru babu wanda ya amsa ta cigaba da tafiya tana duba tsarin gidan a wayar ta.
A kofar wani daki tayi sallama daga ciki aka amsa tayi murmushi ta kutsa kanta ciki tare da ajiye box dn hannun ta ta juyo ta dubi tsohuwar dake kwance kan gado lullube da blanket tana karasawa wajan ta ce"" brka da yamma hajiya cikin muryar tsofaffi tsohuwar tace "" yauwa se yanzu kika ga damar zuwa ko? Saboda ba uwar ki bace kin barni da ciwo na neman kashe ni"" .
Wata yae siririyar dariya tayi ta ce"" ni ban isa na hana ki mutuwa ba saidai idan lokacin ki beyi ba kuma I think time is off kallon ta kawai tsohuwar take yi cikin izza ba tare da ta fahimci abnda tace ba .
Cire rigar likitocin tayi ta ajiye gefe ta dakko abn gwajin numfashi ta fara auna numfashin ta tayi murmushi tace"" numfashin ki kalau yake saidai kashh time is off cike da bacin rai tsohuwar tace"" nifa banason iskanci time is menene ne ? Ya ishe ni kinji ina so na huta nayi bacci ciwo ya hana ni kinzo zaki Bata mn rai yar iskar yarinya mara mutunci Naga dana biya yake dk abnda zaa yi mn ba kyauta zaki duba ni ba dole kiyi aiki ko nasa a sallame ki ga likitocin nan nema ske ma wani me kudin ya dauke su aiki kamar dana Amma kin samu kina wasa shashash kawai, fada tsohuwar ke tayi wai a haka mara lafiya ce.
Still kara yin murmushi tayi tace "" yanzu ai zaki huta kiyi bacci baccin da ba wanda ya isa ya tashe ki sai Allah tana fada tana hada magunguna da allurai .
"" To da waye ya isa ya tashe ni kinsan ko ni wacece? Da Dana akw juya kasar nan mune masu kasar abnda muka fada shi ake yi.
Har yanzu murmushi ne akan fuskar ta ta rike hannun tsohuwar tayi mata allurar jijiya sannan ta dago kanta ta bata magani ta maida ita ta kwantar.
Maida rigar ta tayi ta hada kayan ta ta ajiye a gefe ta dawo kusa da tsohuwar ta jawo dressing mirror ta zauna ta fuskan ce ta tace "" yanzu zakiyi bacci Kuma zaki samu hutu idan nace hutu ina nufin zaki huta ta karasa maganar tana sakin wani killer smile, sannan tace bari na baki wani lbr kafin baccin ya dauke ki.
Gyara maza tayi ta kalli pop dake dakin tace nidai suna nan Junaina yar gidan malam bukar dake unguwar dorayi wato dai limamin tsohuwar unguwar ku kafin dan ki ya ci zabe.
Nuna ta tsohuwar ta fara yi da hannu tana son tayi magana Amma ina ta kasa wani tari ta fara yi daga bisani kuma ta kwanta numfashin ta ya dauke.
Sake dakko abn gwajin numfashin tayi ta kara gwadawa inda ta tabbatar da tsohuwar ta mutu sannan ta lullube ta ta fice daga dakin megadin Yana mata sannu da fitowa ta daga masa kai ta fice daga gidan direct wajan motar ta ta nufa ta shiga tayi mata key ta fice daga unguwar.
Bata yi wata doguwar tafiya ba ta iso wani madaidaicin gida tayi horn aka bude get dn ta tura kan motar ta ciki gefe tayi perking ta cire mask dn da glass dn ta fito ta rufe motar ta nufi palourn dake gidan.
Wani matashi ne yayi mata oyoyo suna murmushi suka rungume juna directly wani daki suna nufa saida ta waro idon ta ajikin glass dn kofar dakin sannan ya bude wato dai kwayar idon ta shine key dn dakin.
Suna shiga ta ajiye kayan hannun ta ta nufi wani bango Wanda aka lika hotuna da yawa na mutane ciki har da tsohuwar da ta mutu yanzu.
Cancel dn hoton tsohuwar tayi sannan ta yayyaga shi ta mikawa wannan matashin saurayin ya kone hoton,
Kara matsawa gaba tayi ta dauki jar maka ta zagaye hoton wani mutum shima sannan suka fito daga dakin.
daga nan dakin ta ta shige inda ta shiga toilet tayi wanka tare da alwala sannan ta tada sallah ,
Ta jima tana addua a wajan tana kuka mai ban tausayi sannan ta fito daga dakin ta nufi palourn dan saurayin da naji ta kira da Junaid ya taho Yana murmushi suka nufi dianing.
Kashe gari tn 7:30 Junaina ta shirya tsaf cikin wata riga blue da bakin wando inda ta dora Dan karamin bakin hijab akan rigar p cap itama baka ta dora akan hijab dn sannan ta saka belt ta dauke kugun ta dashi juyowa tayi da nufin fita daga dakin, nayi mamakin ganin ta da kaya irin na manyan yan sanda daga gaban rigar an rubuta ASP JUNAINA BUKAR a gurguje ta fito ta nufi dianing inda Junaid ke jiran ta yana ta duba agogo ganin ta fito yasa shi washe baki yace"" sannu da fitowa auny na murmushi tayi tace yawwa sannu Junaid kana sauri ko ? "" eh aunty ina da lecture safe ne Junaid ya fada yana hada wa junaina tea tare da mika mata ""thank you tace tana karbar kofin ta fara sipping a hankali.
Tare suka fito a mota saida ta ajiye shi a school sannan ta wuce wajan aikin ta , maza ne sosai a wajan yan sanda ka kala amma dk inda Junaina ta wuce saidai kaga an kame alamar girmamawa.
Har saida ta shiga wani office sannan ita ma ta kame cike da girmamawa tace gani sir Wanda Junaina ta kira da sir ya kalle ta yana lashe baki kamar tsohon Maye yace"" dama dazu ne muka samu case dn kashe mahaifiyar commissioner me gadin ta ya bamu tabbacin macece ta zo gidan Kuma likita ce daga lokacin ba wanda ya sake shiga gidan saida commissioner yazo sannan ya tarar an kashe ta Kuma har rufe ta da bargo.
So wannan case dn na damka shi a hannun ki kiyi kokarin gano makashin ya karasa fada yana mika mata file dn .
Karba Junaina tayi sannan ta kara kame wa ta sara masa tare da cewa consider it done sir, sannan ta fice daga office dn tana wani killer smile....
WAI WACECE JUNAINA YAR SANDA KO LIKITA
DOMIN JIN WANNAN AMSAR KU BIYO GARKUWAR JARUMAI KAWAI KUDAI KUYI COMMENT KUGA TYPING.
👩🏻✈️👩🏻✈️JUNAINA👩🏻✈️👩🏻✈️
3_4
JARUMAI WRITTERS ASSOCIATION TAKEN MU ALKALAMI YAFI TAKOBI.
KHADIJA UMAR ABDULLAHI (GARKUWAR JARUMAI CE)
بسم الله الرحمن الرحيم
Office dn ta ta shiga ta zauna kan kujerar dake gaban wani katon table jujjuya wa ta dnga yi tana sakin wani murmushi wanda ya kawata fuskar ta.
Ta jima a haka kafin ta dauki land line ta fara waya, ba jimawa sai ga wasu yan sanda maza guda biyu da mace guda daya sun shigo office dn tare da kame wa suka Sara wa Asp Junaina Bukatar. Fuska babu walwala Junaina ta dub mazan tace"" ina son ganin mai gadin gidan commissioner da masu aiki gaba daya har da driver.
Sannan ta dubi macen tace "" ke kuma muje gidan commissioner kamewa suka sake yi sannan mazan suka fita don tattaro masu aikin gidan commissioner yayin da ita kuma macen ta tsaya Junaina tayi gaba ita kuma ta bita a baya.
A cikin motar Junaina suka tafi ita da captain Bosey, tuki take yi a hankali cikin nutsuwa har suka kai gidan commissioner daga bakin gate ta tsaya ta nuna I'd card dn ta sannan ta shiga da motar ta tayi perking a.perkin lot sannan tayi gana captain Bosey ta bita baya aka yi musu iso zuwa fadar commissioner.
Da sallama suka shiga palourn suka tsaya suka.kame tare da sarawa ga commissioner wanda gaba daya hankalin sa baya tare da su Banda hawaye babu abnda commissioner yake yi koda gaisuwar mutane baya iya amsawa, mahaifiyar sa kadai ta rage masa tasha wahala a kansa tayi kulle kulle kala kala wajan ganin ya zama commissioner ta koya masa dabaru kala kala na yakar makiyi yayi nasara ya zama abnda take so ya zama gashi ko sati bai yiba da shiga office ba lokacin da ya kamata taji dadin.yakin da tayi Amma an kashe ta.
I'm sorry sir Allah ya jikan hajiya maganar Junaina ta dawo da commissioner daga duniyar tinanin da ya lula Amin yace yana Mike wa tsaye tare da nuna mata wani karamin palour yayi mata alama da su shiga ciki kallon Bosey Junaina tace tare da cewa jira ni anan da to Bosey ta amsa tana gyara zama.
Commissioner na gaba Junaina na binsa a baya tana yi masa kallon tsananin kiyayya da sake sake kala kala a ranta.
Zama commissioner yayi ya nuna wa Junaina waje ta zauna suka fuskanci juna sannan ta kara yi masa taaziyya da amin kawai yake amsawa lokaci lokaci Yana goge idon sa da tishue.
Ranka ya dade yaushe rabon ka da gidan hajiya? Kara goge fuska commissioner yayi tare da shan majina yace "" shekaranjiya naje gidan da safe ban dade ba na fito sai Kuma jiyan naje da yamma shima dai ban dade ba .
Amma meyasa baka dade wa idan na fahimta tsufan da hajiya tayi tana irin rigingimun nan na tsufa ko? Shiyasa idan kaje baka dade wa?
Eh kwarai tana yi cewar commissioner sannan ya kara da cewa hajiya rigimammiya ce sanna akwai ta da yan korafe korafe so wani abun ba zai yiwu ba shiyasa idan ya fara rigimar sai na yi mata sallama na fito kawai.
Murmushi Junaina tayi ta karkata kai sannan ta dora kafa daya kan daya tace shiyasa kayi maganin abun? Daga kai commissioner yayi yace "" eh to amma magani kamar me? Wannan shegen murmushin na gefen baki Junaina ta sake yi sannan tace "" shiyasa ka kashe ta?
Zabura commissioner yayi ya fara nuna Junaina da dan yatsa cikin daga murya yace """ ashe ke shashash ce? Ashe baki san aikin ki ba? Ni zaki dorawa alhakin mutuwar mahaifiya ta ? Calm down sir Junaina ta fada tana sakin murmushi sannan ta dakko wata yar karamar camera ta kunna ta nuna masa.
Coton commissioner ne ya bayyana aciki lokacin da ta fito daga motar sa ba tare da gurd dn sa ba ya shiga gidan hajiya tsahon minti talatin sanan ya fito yana murmushi bayan kamar minti a shirin da biyar ya Kuma dawo wa shine bai dade a ciki ba ya fito yana kiran mai gadi anan yake sanar da mutuwar hajiya.
Vedion na kare wa wani gumi ya karyo wa commissioner yasa tishue ya goge sannan ya bude baki dakyar yace ""wllh bani na kashe hajiya ba hasalima ba bangaren ta naje ba bata ma san nazo ba na dai tambayi mai gadi ya hajiya ta tnda yana shiga wajan ta shine yace mn yanzu wata likita tazo ta duba ta ta tafi .
Wajan wa kaje a gidan? a tinani dai hajiya ce kadai a cikin gidan ko da wanine?
Kame kame commissioner ya fara yi kafin ya hade rai yace"" naje wajan me mata wanki ne , kara gyara zama Junaina tayi sannan tace "" alakar ka da mai wanki har tayi girman da zaka zo wajan sa hajiya bata sani ba? Wannan wace irin alaka ce?
Sake share gumi commissioner yayi a karo na biyu ya dubi Junaina yace"" yana zuwa guess house dina ne to kwana biyu ya dena zuwa Kuma banajin dadi rashin zuwan nasa shiyasa na biyo shi kuma ya amnce zai zo ahiya na fito naje na dawo sannan na shiga wajan hajiya to a nan ne nasamu an rufe ta da bargo da farko na zata bacci take saida nayi ta magana naji shiru saboda hajiya bata da nauyin bacci ko motsi.akayi seta tashi shine na bude barbon na tarar ta mutu.
Jinjina kai Junaina tayi sannan tace """ yanzu kam na tabbatar da babu hannun ka.a mutuwar hajiya murmushin jin Dadi commissioner yayi Yana godewa Allah daya kubutar dashi daga zargi
Muryar Junaina ya tsinkayo tana cewa tnda yanzu wannan vedion na zuwan ka gidan ya baza ko ina a duniya ina ganin saka cire kunya ka fada wa jamaa kaje wajan abokin aikata luwadi ne wata irin zabura commissioner yayi yace ke mahaukaciya ko? Taya zan Fadi wannan maganar to bari kiji wllh wannan zancen ya fito sena raba ki da rayuwar ki,
Murmushi Junaina tayi sannan tace " ai dama ni kun dade da raba ni da rayuwa ta , saidai yanzu dole ayi abu daya kodai ka Fadi wannan maganar ko kuma ka amsa kashe hajiya dk da nasan ba zaka iya cewa duniya kai Dan luwadi bane .
A fusace commissioner ya mike tsaye cikin bacin rai yace " to sai me? Menene dan ni dan luwadi ne? Ai ba ni kadai bane dk manyan kasar nan kashe tamanin cikin dari suna luwadi sai ni ne zanji kunya manya na suna yi ai.
Yana gama fada Junaina ta mike da murmushi a fuskar ta tace I'm sorry sir zan tafi idan ka huce na dawo domin mu samu matsaya guda daya tana gama fada ta wuce tayi gaba Bosey ta bita suka fice daga gidan.
A office ta ajiye Bosey ita Kuma ta wuce ta dauki Junaid suka wuce gida.
Wanka tayi sannan tayi sallah ta shiga kitchen ta dafa musu indomie with egg , a tare suka dakko abinci suka fito palourn a kasa suka zauna fuskar Junaina fal farin ciki haka take cin abncin kamar babu wata damuwa a tattare da ita.
Junaid kasa jure wa yayi ya dube ta shima da murmushi a fuskar ta yace """ Yaya Junaina na dade banga irin wannna farin cikin a fuskar ki ba na dade Banga kunci abnci kamar haka ba menene sirrin a bani nasan nima zai sani farin ciki.
JUNAINA
JARUMAI WRITTERS ASSOCIATION TAKEN MU ALKALAMI YAFI TAKOBI
GARKUWAR JARUMAI CE
MANAGE PLEASE👏🏼
بسم الله الرحمن الرحيم
Dariya Junaina ta shiga yi kmar ba zata dena ba har da hawaye sannan ta tsaya ta dubi Junaid Ido cikin Ido tace """ dole nayi farin ciki yau naga hawaye a fuskar commissioner yau naga rudu a fuskar sa Junaid yau naga tsoro a fuskar commissioner ta karasa fada tana fashe wa da wata dariyar shima Junaid dariyar yake zuciyoyin su fal farin ciki.
Sun dauki lokaci suna dariya kafin suyi shiru su cigaba da shirya plan din su , wata karmar naura Junaina ta dakko daga aljihun wandon ta ta kunna saiga muryar commissioner ta fito radau a ciki , computer Junaina ta janyo ta fara edition record din, saiga muryar commissioner na cewa """ naje gidan hajiya ne wajan me wanki yana zuwa guess house dina ne to kwana biyu ya dena zuwa Kuma banajin dadi rashin zuwan nasa shiyasa na yanke hukuncin zuwa wajan sa da kaina sai kuma akayi shiru can sai ya cigaba da magana ""ai ba ni kadaine dan luwadi ba manya kasar ma yawanci dk su ne """.
Wani account Junaina ta bude da sunan unknown sannan ta saka wannan record a ciki.
Bayan kwana uku Junaina fito da safe zata wajan aiki saida tayi nisa da gida sanna ta tsaya a bakin hanya ta dakko karamar wayar ta ta saka layi a ciki sannan ta tura wannan record dn da sunan unknown zuwa Facebook Twitter Instagram da tiktok tana gamawa ta karya layin ta zubar dashi a wajan sannan ta wuce wajan aikin ta.
Karfe biyu ta tashi daga wajan aiki ta wuce hospital inda take matsayin dalibar likitanci ta cikin hukumar yan sanda, zuwa yamma zance ya baza gari cewa ashe commissioner dan luwadi ne sannan manyan kasar nan suma dk suna yi cewar commissioner, nan fa gari ya hargitse dk wanda yasan yana yi cikin manya hankalin sa ya tashi kowa yana zargin commissioner dashi yake.
Commissioner yana gidan sa labarin yazo masa tsananin kunya da madamar abnda ya fada sun cika masa zuciya a ransa yanq tunanin irin hukuncin da zai yiwa Junaina sai dai idan ya tina kowa yaji sanda yace idan maganar ta fito ze kashe ta sai hankalin sa ya kara tashi, waya kuwa babu kakkautawa haka ya dinga amsawa daga manyan sa Wanda suka san suna cikin harkar kowa da.irin barazanar da yake masa.
Zama ya gagari commissioner da ya zauna se ya mike kamar an tsikare shi nan da nan hawaye ya fara sintiri a fuskar commissioner yana cikin wannan halin takardar sauke shi daga kujerar sa ta riske shi dalilin an gano