Showing 1 words to 3000 words out of 27847 words

Chapter 1 - KUCAKAR KISHIYA Hausa Novels By Aisha Muhammad Sani.txt


*KUCHAKAR KISHIYA*



*STORY AND WRITEN BY AYSHERTH MOHAMMED SANI(PREETY XAYEESHERTH)*



*PAGE* 1


------------------------------------------------------------------------

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM INA ROKAN ALLAH YASA NA KAMMALA LITTAFINNAN LAFIYA KAMAR YARDA NAFARA KUMA YASA YA ANNFANAR DA MUTANE KAMAR YADDA NA TSARA*

Amman ne yashigo tare da sallamarsa
Kayan takaici abin da yasaba gani amman har yanzu baya juran ganin hakan.
Hamlat ce kwance akan kujera tana ta zabga uban barci ga daki kacha kacha kamar anyi dambe da alamu ma dakin yafi wata ba agyarashi ba.
Ran Amaan yayi matukar baci hakan yasa ya dibo ruwan sanyi yamakawa hamlat afuska.
Afusace ta farka tare da fadin kan ubancen wani dan iskan ne ya watsamin ru.......
Ganin Amaan tsaye agabanta ne yasa takasa karasawa .
Sai da taja dogon numfashi sannan tace"toh uban yan tsurfa andawo kenan nikuma banda sukuni".
Shikuma Amaan tsaye yake agabanta tsabar bacin rai ko magana ma yakasa kawai kallonta yake.
Sai da takara da cewa dallah malam ka matsamin akai ko?
Amaan yayi murmushi sannan yace"kingama?
Ina ke bakisan darajar kanki ba bare na mijinki?.
Da duk kan alamu tunda nabar gidannan ba agyarashi ba kusan wata kennan fa.
Kuma wai da sunan mijin ki yadawo daga tafiya ko ajikinki.
Sai rashin mutuncin dakika tanada kika fara zubamin.
Yana maganganun nan hamlat na hararasa tare buga kafa akasa.
Bata bari ya kammal abinda zai fada ba tace"dakata dan matsiyata nifa ba bai warka bace karka kuskura kanemi batamin rai .
Bawai dankaga ina dan ragama yanzu ba to wallahi zan dawo yafi nadama domin bana daukar raini kai kafi kowa sani".
Amaan yace"wai ina mijinki kike fadamin maganganun nan toh wallahi daga yau inzakiyi rashin kunyarki ta tsaya akaina batare da kin hada da iyayena ba".
Hamlat taja dogon tsaki tare da fadin"su iyayen naka suwaye ai bansan su ba bare nasan da zamansu domin kasan bana harka d matsiyata kaima dai lalurace tasa nake zaune dakai domin kasan inba haka ba da tuni na dade ba barinka.".
Tana kaiwa karshe tayi tsaki tare da bangaje shi tukun tashiga daki.
Amaan binta yake kawai da kallo bamusan me yke aiyanawa azuciyarsa ba .
Yafi minti talatin yana tsaye ba abinda yake illa tunani .
Daga karshe kuma yace"Allah yakyauta".
Alokacin yafara gyaran falon nan yafi awa sannan falon yafara kyan gani kuma duk da hka ba bai gyaruba yadai rage neh

Page 2

Amaan yana gama gyaran falon nan yashiga dakinsa domin yin wanka Allah yatai makesa yagyara dakin kafin yayi tafiya kuma daman hamlat bata cika shiga ba hakan yasa dakin bai baci ba sai yar kura da dakin yayi.
Hakan yasa yayi wanka sannan yafito yashirya cikin kananun kaya domin bai damu da manyan kaya ba.
Yana gama shiryama yanufi inda motarsa take ko ta kan hamlat bai yi ba domin yasan ynzu zata iya bata masa rai fiye da haka.
Yana shiga motarnan ba inda yanufa sai *layin zana* gudu yake amota kai kace wani gari zai je.
Abin da yabani mamaki shine naga yayi paking akusa da wani gida wanda bai da mara ba dana laka domin inba kasan garin birni bne inka gidannnan kace na karkarah neh.
Yana paking naga yafito kawai yatsaya ajikin motarsa sai kallon wata yarinya yake wace da alamu batafi shekara 15 amman duk da hka alamu sun nuna yarinta shakaf natare da ita domin kuwa wasan kassa take da uniform din skul ajikinta.
Amaan sai murmushi yake yana kallonta har ya manta ma da damuwar dake ransa kawai kallon yarinyar nan yake.
Ita kuwa batama san yanayi ba sai wasan ta take .
Tana cikin wasa sai taga wata me tallen doya .
Aikuwa karaf tafaracewa"musu gari da tallen doya".
Tanayi tana murguda baki.
Aikuwa aguje me doyarnan tabi yarinyar .
Ita kuwa yarinya me xatayi banda gudu menaci ban baka ba.
Duk abinnan da ake Amaan yana kallonsu
Sai murmushi yake tare da karajin sonta azuciyarsa.
Tana zuwa kwofar gidansu ta turo kofar galan galan din tare da yima me doya gwalo.
Shiko Amaan me zai yi banda dariya .
Haka me doya ta hakura ta tafi abinta.
Shima Amaan duk da bai gaji da kallonta ba amman haka ya hakura yashiga mota yanata kwasan dariya tare dafadin"inaga watarana yar nan sai ta kumburamin ciki dan dariya".
Sannan yacigaba da driven dinsa.
Akullum indai Amaan nagari sai yazo layin zana inya tashi daga aiki dai dai da lokacin dayasan yarinyarnan nadawowa daga skul .
Aduk ranar da bai gantaba toh sai yayi zazzabi.
Domin tazama masa kamar mahadin rayuwrsa.
Daga nan ba inda Amaan yanufa sai family house dinsu inda suke zaune duka harda iyayensa.
Yana shiga ba inda yafara nufa sai Falon Alhaji .
Yana shiga kuwa yatarar da hajiya ma tana falon suka gesa cikin sakin fuska .
Sannan Alhaji yace "ya hanya .
Amaan ya amsa da"lafiyau".
Sannam hajiya tace"ya hamlat dafatan dai kuna lafiya".
Amaan yace"tana nan lafiya".
Bayan sun dan gaggaisa ne yanufi shashin babansa.
Yana shiga kuwa yatarar da ummansa sai washe baki take.
Ita da baba .
Sai da suka gesa sannan suka tambayi lafiyar dan nasu.
Ananne umma take cewa"amaan nasan kana hakuri amman kakara akan nada".
Shidai Amaan kawai murmushi yake domin yana matukar gudun abin da zai batawa iyayensa rai.
Dole nema yasa sukasan halinda suke ciki shida hamlat.
Sai da suka masa nisiha meshiga jiki sannan umma tazuba masa abinci yaci.
Sai da yayi dak sannan yanufi hanyar gida.
Yana isa gida kuwa yatarar da hamlat har takara birkita falon .
Tana ganinsa tafara toh karamin munafika anje ankai ni kotu neh ko?.
Toh wallahi kasani kayi kadan domin ko ina zaka nafi karfinka.
Shidai amaan kawai murmushi yake domin hankalinsa ma baya wajenta shi tunanin little babynsa yake.
Hamlat data fahimci hankalinsa baya wajenta ai tuni ta matsa garesa tare da rike masa kwalar riga.
Tace"ni zaka mayar mahaukaciya?.

Page 3

Amaan yakasa magana domin abin hamlat din yafara basa tsoro da har ace zata iya chukume shi.
Hamlat tace"wai ba magana nakema bane dan gidan matsiyata?.
Alokacin idon Amaan yayi jajir sannan yacika da hawaye sana diyar kiran iyayan da sunan matsiyata da hamlat tayi.
Gaba daya rikice jikinsa har rawa yake
Da sauri yadaga hannu domin marin hamlat.
Har yakai fuskarta itakuwa duk tsiwarta sai da tayi shiru ta rufe ido domin tsorata.
Shiko Amaaan yana kai hannu ya tsaya domin yayi tunani me mahimmaci arayuwarsa hakan yasa kawai ya zuciya yafasa
Yasauke hannun.
Ita kuwa hamlat tana nan ta kame domin jiran jin saukan mari take sai ko taji shiru ai tuni ta bude ido tare da galla ma Amaan harara.
Sannan ta huce ta bar falon.
Amaan yana tsaye amman ba abinda yake illa hawaye dayake zirarowa daga idanunsa.
Ahaka har hawayen nan yakame sannan shima yashiga daki ya dauro alola yayi sallah sannan yadauko QUR'ANI domin yakaranta ko zai ji dadi aransa.

Ita kuwa hamlat tana shiga sharar dakinta tadauko waya domin kiran kawarta me sata ahanyar yan bori
Takira kuwa aka dauka.
Hamlat tace"hello sweet maama ya banganki bane ?
Kinsan fa dan matsiyatn yadawo gari kuma bakimin lectures ba shiyasa ma yasa tarba me dan mutunci".
Maama ta sheke da dariya sannan tace"oh Aminiya ai yaci ace namiki free kinfara karawa da naki".
Hamlat tace"tab nidai gaskiya kizo ko bakya bukatar abin neh?
Maaama tayi saurin cewa"nina isa?
Ai dolema nagarzayo miki da kayan aiki".
Hamlat tace",dax my sweet maama sai kinzo".
Maaama tsce"ok byeee.
Washe gari
Da sassafe Amaan yashirya domin tafiya office yayinda ita hamlat ko tashi ma daga barcin batayi ba.
Amaaan yana kammala shirinsa yanufi shashin hamlat tunda yanufi shashin yakejin wani irin mugun wari me wagiza cika.
Yana tafiya yana toshe hannci azuciyarsa kuwa cewa yake kazamiyar bnza sai shegen iyayi ba abin da aka iya .
Sannam yana mamakin yanda take rayuwa cikin kazantar nan.
Bai ma ga kome ba sai daya shiga bedroom dinta kasa hadiye yahu yayi.
Dakyar ya iya cewa"ke hamlat tashi kishiyar d huri yau muna da meeting karfe 9".
Hamlat batace kome ba sai harara data gilla masa alamar taji din
Shikuwa daman kaman akan kaya yake fit yafita adakin .
Yana fita kuwa yafara zabga amai.
Sai da yalafa sannan yasamu damar fita.
Ba inda yanufa sai layin zana .
Isar sa keda wuya yahango Ahalaam tafito daga gida ita da babanta zataje school Aikuwa sai rigama take masa akan sai yasiya mata chocolate.
Baba yace"haba auta kinsa fa yau banda kudi kuma gashi ke bazaki yarda ki taka akafa ba sai a mota kuma sauran chanjin kennan".
Tuni Ahalaam tafara buri tare da cewa"to ma nina fasa zuwa skul din kai kaje kawai".
Duk abin nan da ake idon Amaan nakansu.
Sai murmushi yake wanda shi kansa bai san dalilin hakan ba.
Ahalam tace"laaa baba kaga wani mutum achan yanata min dariya".
Baba yace"to kirabu dashi inaga ba dake yake ba mutafi karki sa amiki duka".
Ahalam tace"tab yssssn sai nima narama tunda yamin dariya.
Shiko Amaan bai san ma tagansa ba domin yatafi duniyar tunaninta.
Akullum in Ahalam zata tafi skul sai ta bata lokaci ko da kuwa awajen tsokana neh sai sunfi 30minit awaje.
Da gudu Ahalam takarasa wajen da Amaan yake .
Tana zuwa....

Page 4

Ahalam nazuwa takama kunnen Amaan
Tana fadin"wato kai bakajin magana ko?
Ance katafi makaranta kazo kana tsokanata harda dariya ko?.
Tsabar abin yabawa Amaan mamaki kasa magana yayi sai wata dariya data kara kubuce masa.
Ahalam ta zabga ihu tare da cewa"baba kaga mutumin nan ko?.
Baba kam ma yakasa motsi domin abin ahalam mamaki yake basa.
Amaan yadaure yace"haba yan mata sakemin kunnan mana da zafi fah".
Ananne Ahalam ta shekye da dariya tare da fadin"ashe dai kaji zafi daga yau ka kuma min dariya ai .
Ko zaka kuma ne?
Amaan yayi murmushi tare da cewa"Aa ai naji zafi".
Baba yazo da saury tare da cewa"ahalam munyi letti kizo ga abin hawa munsamu".
Ahalam ta gallama Amaaan harara sannan tame gwalo tare da bin baba.
Baba yajuyo yna bawa Amaan hakury Amaaan yace"bKome ai".
Sai da Amaaan yAdau lokaci yana tunanin Ahalam yana dariya sannan yanufi hanyar office dinsa.
Ahalam kuwa tana zuwa skul taga anfara tare letti ai tuni tayi kalar marasa lafiya.
Tana tafiya da kyar .
Tana isa wAjen itama tayi nildown .
AnAta duka uncle Salim yazo kanta kenan tafara kuka tare dacewa"sir nifa banda lafiya".
Tafara mirgine mirgeni akasa.
Duk ta sakar me jiki da shagwabarta.
Tuni uncle salim yace"oya to tashi kitafi aji ai dama bakizo bA'.
Dasaury Ahalam ta mike ta mantamA da karyar rashin lafiyarta.
Tana tashi tana yan wajen gwalo.
Sannan ta zura da gudu.
Yan wajen sai haushi suke suna un uni.
Wasu kowa sunce sai sunma Ahalam duka.
Amaaan yana isa office ba jimawa suka shiga meeting sai da sukafara meeting sunkai minti 30 tunkunnna hamlat ta isa ta na wani shekan kamshi .
Jikinta tatas sai kamshi dake tashi kamar ba itace ke rayuwa cikin kazanta ba .
Ta gyara jikinta Amman gida akazance .
Tana tafiya tana yamutsa fuskar kamar tana kyamar kowa bayan kuma itace abin kymar.
Haka tashiga dakin meeting dinnan cikin tafiyar kasaita tare da nuna isa .
Ba wanda ta kula sai wajen zamanta data nufa.
Amaaan ko kallon inda take baiyi ba dan takaici.
Suko sauran ma aikata sai gesheta suke ita ko tana musu kallon raini.
Amaaan yacigaba da jawabinsa.
Kowa nasaurara aman bnda hamlat domin ita charting dinta ma takeyi.
Amaaan yakalle ta ya girgiza kai sannan yacigaba da jawabinsa.
Ahaka taro ya watse.
Kowa yakoma kan aikinsa.
Ahalam sun fito break suna zaune ita da kawarta hanan .
Ahalam batada wata kawa banda hanan domin tsokanarta tayi yawa jininsune yazo daya da hannan ma yasa suke shiri.
Hanan tana matukar son Ahalam duk da wani lokaci ahalam na hulakanta ta amman bAta dai na son kawarta ta ba.
Sannan kuma hanan yar masu kudice amman hakan bai sa ta guji ahalam ba.
Suna zaune suna cin kayan break dinsu.
Sai ga...

Page 5

Sai ga amrah nan tazo tana fadin"toh yar matsiyata wato ke skul dinma sai kinnuna halin talakawan ko?.
Ke kuma hanan kina yar babban gida amman kina bin yar me kwosai gidan laka?.
Alokacin ahalam ta razana ta miki zumbur Tare da chukumo amrah tana fadin"ke wai ni sa ar wasan kice?.
Wato ke yar masu kudi ko.
Idon Amrah yaciko tayi zuru zuru.
Ahalam takara dacewa"toh inaga ma kudin uban naki nasata neh kum wlh inkika kara cemin matsiyaciya sai naci miki mutunci.
Hanan tayani mulakada banza.
Aiko hanan da ahalam suka hadu suka dunga xabgawa amrah duka tun tana kuka har tayi shiru sai nishi.
Duk sun kumbura mata fuska anfasa baki.
Students sun hadu sai murna suke yau amrah ta hadu da wadda tafita masifa.
Sai ga wata malama nan dakyar tasamu tarabasu sannan tasasu nildown .
Aka kira uncle salim domin musu hukunci dan kuwa yafi kowa iya duka amakarantar dan hka ma in dalibai sukayi laifi shike dukan su amman sabida bala"i na ahalam shi gudun laifinta yake dan yasan tsagwarar rigima gareta .
Yana zuwa yaga ahalam aikuwa sai da gabansa yafadi ganinta da yayi awajen.
Yace"ahalam yadai lafiya dai ko?
Keda baki lafiya meyakawo ki nan?.
Aituni ahalam ta shagwabe sannan tace"uhumm ba wannan yarinyar bace take zagina.
Shine fa nafasa mata baki".
Amrah tace",kut ni zakima shari?.
Uncle salim yama amrah tsawa me girgiza mutum dukansu sai da suka razana.
Sannan yace"nasan halinki sarai amrah bakyajin magana kece baki da gaskiya domin nasan ahalam batada lafiya barata taba shiga harkar ki ba .
Dan haka maza kitashi kibar wajen nan'.
Amrah ta tashi tana tafiya dakyar.
Shiko uncle salim yace"pls sister kidai na dukan mutune haka kinga fa watarana inbana nan sai an rama musu abin da kike musu".
Ahalam tace"kuttt wallahi inta karamin sai na fasa mata hanci".
Hanan dai tanajin su tayi shiru tna ganin ikon Allah dan tasan uncle da ahalam sai Allah.
Uncle salim yace"to naji nidai tashi kikoma aji kinga tun dazu akakoma".
Ahalam tace"wallahi bazani ajinba gida zanje abuna inci kwosai".
Uncle salim dakyar yashawo hankalin ahalam sannan ta yarda sai antashi.
Lokacin tashi yayi daidai da lokacin tashi daga office din Amaan da hamlat.
Ahalam tana tafi tana tsokanar mutane.
Dreban su hanan yazo amman taki yarda tabisu domin tafiso tana tafiya tana tsokanar mutane.
Aiko tana cikin tafiya taga wasu mutane na fada.
Da alama ma mata da mijine.
Mijin yana cewa"ke baki da hankali ko akan titinma sai kin nuna halinki .
Kafin matar takara magana yafara dukanta.
Ahalam tana hangosu tazura da gudu tana zuwa tadau katon dutse ta dane bayan mijin tana buga masa dutsen aiko kuwa tuni ta fasa masa goshi.
Tana fadin mugu kawai saketa.
Yanajin zafi kuwa yasake matar itakuma ahalam ta dirka abayansa.
Matar tana dagowa taga jini agoshin mijinta tafara kuka tana ke miye hka wayace kifasa masa goshi tafara goge masa jinin.
Ita kuwa ahalam sai dariya take tana cewa"wayace kadaketa aigashi narama mata".
matar ta biyo ahalam dagudu.
Aikuwa ahalam kafa menaci banbaka tana gudun amman tana cew"wawiya kawai ta tsaya wani garde nadukanta narama mata amman tanajin haushi.
Har matar tagaji da gudun ta tsaya amman ahalam bata tsaya ba .
Ahalam tajuyo tana mata gwalo aiko sai gashi karaf tabige me mangoro.
Me mangoro akasa mangoro ma akasa.

Page 6 & 7
*ASALIN LABARIN*

*SHIN AMAAN DA HAMLAT SU WAYE*?
*SANNAN KUMA WACECE AHLAM*?
*SHIN AMAAN DA HAMLAT SU WAYE*?

Amaan dane ga mallam sani tare da mahai fiyarsa baba nafi.
Su biyune kadai awajen iyayensu daga Amaan sai kanwarsa Amrin
Asalin sunan Amaan Ahamed ita kuwa Amrin Amina.
Baban Amaan shine babba a familynsu daga shi sai kaninsa
Alhaji sulaiman
Asalinsu yan garin kanone Amman kasuwanci yadawo dasu garin jos.
Alhaji sulaiman me arzikine na gaske domin kuwa ya ninka yayansa adukiya.
Yanada kampani dayawa wa inda yasa ake lura masa dasu .
Sanadiyar hakan shiyake daukan dawainiyar yayan yayansa .
Alhaji sulaiman shine mahaifin Hamlat wadda asalin sunnanta halima itace ya daya tak awajensa.
Tare da mahaifiyarta hajiya salma.
Alhaji sulaiman yana matukar son Amaan sabida kyawawan halayensa.
Akan hakan yabasa kamfani guda.
Itakuwa hajiya salma sam bata kaunar Amaan sabida tana ganin Alhaji sulaiman yafi nunawa Amaan so akan hamlat.
Tare Amaan da Hamlat suka taso duk da ya girmeta amman kome nasu tare alhaji yke musu.
Karatuma tare sukayi har suka gama.
Kwatakwata Amaan bayason hamlat sabida halinta na nunawa talakawa suba mutane bane sannan ga nuna isa ga kowa.
Amman ita ahakan tadaurawa kanta son sa duk da bata nuna masa hAkan.
Tasamu hajiya salma tasanar mata ita kuwa hajiya salma taji dadin hakan domin atunaninta hanyar da zasu ceto dukiyar Alhaji daga hannun Amaan kenan.
Da aka sanarwa da Alhaji yaji dadi sose dan hka yaje yasanarwa da yayansa shima yanuna amincewarsa duk da kuwa yana jiyewa dan sa mugun hali irin na hamlat.
Da aka sanar da Amaan ya girgiza sose Amman dan biyayya haka ya hakura akasa biki batare da bata lokaci ba.
Alhaji sulaiman shi yadau nauyin kome domin acewarsa shine uban ango .
Ankashe nera kamar ba asan zafinta ba.
Bayan aure Amaan yaso adaukan musu yar aiki sabida yasan tsabar kazantar hamlat amman taki.
Wai ita adole me kishi tana matukar kishin Amaan amman bata taba nuna mai soyayya ba koda kuwa ta minti daya sai zagi da cin mutunci.
Ahaka Amaan yake juran zama da hamlat sai dai inshi yaso yagyara gidan ko kuma yakira Amrin ta gyara.
Kuma ita intazo ta tsiya suke ravuwa da hamlat domin Amrin bata barin takwana anamata abu
take ramawa.
Hamlat bata taba neman Amaan sai bukatar ta tashi tukunnah.
Koda Amaan yayi niyar wulakantata inya tuna da maihinsa da nata sai yafasa.
Wannan shine takaitacen tarihin Amaan da hamlat.

*WACECE AHLAM*?
Ahlam ya'ce ga mAllam Rabi"u da baba maryam.
Asalin sunan Ahlam Aisha wadda akamata lakabi da Ahlam.
Mallam Rabi"u talakane fitik dan haka inkaje gidansu ma kazata awata karkara kake domin kuwa gidan lakane sannan kuma dan karami.
Baba kuwa suyan kosai take kwofar gidansu
Asalinsu yan niger ne cirani yakawo mallam jos hakan yasa yatawo da matarsa.
Mallam nakoyar da manyan mutane addini tahaka ne yakesamu damar biyawa Ahlam makaranta da bukatunta.
Ita kuw baba intayi suyanta tasamu riba anan take musu cefanan abin da zasuci.
Ahlam takasance ya me rikice da shagwaba ga tsokanar mutane.
Mutane dayawa suna sonta domin tana gwarjini awajen mutane ko ina taje anasonta.
Duk ranar ba ba school kuma ba madarasa sai ankawo karar fin sau goma.
Inko aka hanata fita tata kuka kenan ko kuma tazauna ta ta tsokanar baba.
Da mallam.
Intaso tata jama baba kumatu tana cewa"babata yar kyakkyawa me kumatun cincin".
Tun baba na dariya har sai tagaji tacewa"ahlam taje wasa".
Kadan daga cikin tarihin Ahlam kennam.

Page 8 & 9

Ahlam na ganin haka ta dauki katon mangoro acikin mangororin dasuka zuba sannan ta kara zurawa da gudu.
Sai mutanen wajen ne suka taimakawa me mangoron nan yatashi sannan aka kwashe .
Shiko me mangaro baya ma ta sauran mangoron sai ta wanda tadauka dominn kuwa duk aciki shine babba kuma me kyau.
Yaso yabita amman ina ahlam tafi karfinsa domin acikin minti daya har yadai nah hangota.
Ahlam kuwa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login