Showing 12001 words to 15000 words out of 27847 words
Chapter 5 - KUCAKAR KISHIYA Hausa Novels By Aisha Muhammad Sani.txt
ba domin ita aganinta bata da damuwarsu sai yau tayi sallama tayi sa'a kuwa Aunty *Shaxee* na online ta amsa mata Bayan ta amsa ne ta sanar da ita cewa girki takeso tayi kuma bata iya ba adan koya mata me sauki.
Anan ne Shaxee ta mata bayanin yadda zatayi saukakkakiyar jallop din taliya.
Aiko tana koya ma ta ko godiya babu ta sauka ta daura tukunya akan gass sannan ta soya mangyada ko soyuwa bai yi ba ta zuba wata katuwar albasa da kayan miya tukun ta dibo su karas da koren wake ta raba su bibbiyu suma ta zuba,ta dibo ruwa ta maka akai ko zafi bai fara ba ta dauko taliya leda daya ta juyo,sannan tasa magi guda ashirin.
Sai murna take adole yau tayi girki hakan yasa ta daura ruwan zafi adaya bangaren.
Taliyar bata kai minti goma ba aka sauke akasa a flas din abinci sannan aka juyo ruwan da ko ta fasa bai yi ba aflas din tea.
Da sauri ta koma daki tayi kwaskwarima ta feshe jiki da turare sannan tadawo ta jera abincin akan dinning table tukun ta nufi bangaren Amaan domin ta sanar dashi yazo suci abinci .
Sai wani tafiyar kasai ta take kamar wadda kashi ya taru mata aciki.
Tana zuwa....
Page 36
Tana zuwa ta Domin ta sanar da Amaan tagama hada musu abincin karyawa.
Da ta je kwofar dakin sai ta kasa budewa domin ita kanta kunya take abinka da basa ban ba.
Tafi minti biyar atsaye sai chan da ta ji motsinsa kawai ta daure ta bude kwofar dai-dai da isowar Amaan kwofar kenan.
Dukansu su ka tsaya kallon juna domin kuwa Amaan yasan inba neman masifa ba ba abinda yake kawota bangarensa.
Amaan ne yadaure yace"Lafiya kuwa Hamlat."
Ta gyada kai alamar eh sannan tadaure tace"Dama na ma na abinci karyawa ne nazo na fada ma."
Amaan yayi murmushi sannan yace"Kinnsan dai ni bana karyawa sai karfe TARA kuma yanzu bakwai da rabi ne."
Hamlat ta shagwabe fuska tana"Haba yayana pls na yau fa kadai."
Ba da son ran Amaan ba yace"To muje."
Suna tafiya Hamlat na kisisina kamar baza ta tafi shiko Amaan azuciyarsa cewa yake"Koma miye dai na fi karfin ku da ikon Allah."
Suna zuwa ta bude flas din taliyar shikan shi kamshin in mutum yaji sai cikinsa ya burga haka Amaan yadaure duk da ya fara jin Amai kafin ma yaci .
Ita kuwa oganniyar sai murmushi take tana ta zuba jagwalgwalon ta aflet ta gama zuba mai kafin ta miki masa ta dibo Ruwan tea a cup ta zabga uban suga da madara ta mika masa tare da taliyan.
Tuni Amaan yaji numfashin ya fara daukewa yaso yadaure Amman ina ai cikinsa ya fara gurnani da gudu yatashi ya nufi bayan gida.
Page 37
Yana zuwa sai Amai tun abinda yaci jiya shine yake dawowa .
Hamlat ta biyoshi ta tsaya abayansa Hannu rike da k'ugu tana fadin"lallai ma rainin wayon yayi yawa tsabar bakason cin abincin da nayi shine za ka tsiri amai?
Shi dai Amaan bai kulata ba ya na ta k'ak'a tun amansa .
Ta ci gaba da cewa"lallai ma gaskiya da sa ke."
Da k'yar Amaan yasamu amannan ya tsaya ya kurkure bakinsa ya juya kenan zai fita yaga Hamlat ta tare hanya .
Araunane yace"Hamlat dan matsa banajin dadin jiki nah."
Ta kallesa ta galla masa harara tare da tsake sannan tayi gaba.
Da k'yar Amaan yake tafiya Amman wannan bawair Allahn ko tausayinsa ba ta yi sai ma bala"i da ta ke ta faman surfawa haka yadau jakarsa ya barmata gidan .
Da ya je motar ma da k'yar yake tukin haka yadaure har ya isa office dinsa anan ne ya kira likitansa domin yazo ya dubasa.
Hamlat kuwa tunda yafita ta kira mumy da maama tasanar musu abinda yafaru anan ne maama take sanar da ita cewa"ai Amaan yabawa su Ahlam gida."
Hamlat tace"lallai matsiyatan nan basu daddara ba ko?
Hmmmm
Anan suka yi sak'e sak'ensu Kafin ta shirya ta nufi office yadda dai aka saba waje tsaf ciki tsami.
Bayan an idar da sallar azahar Amaan yasamu karfin jikinsa sose ya nufi gidan su Ahlam.
Yana bud'e k'ofar gidan Ahlam ya gani zaune tana ta karatun ta yanzu tunda tayi ciwon nan ba magana ta cika son yi ba ko tsokanarta bakamar da ba.
Tana hangoshi tayi murmushi ta tashi kenan zata zura da gudu ai tuni ta tuna fa tana da ciwo hakan yasa ta fara jan kafar.
Amaan yace"Ke Ahlam miye haka tsaya mutafi tare."
Batasan lokacin da ta tsinci kanta da tsayawa da sai ji tayi anriko hannunta ana cewa"Muje mana."
Ta bude baki kenan za ta yi magana.....
Page 38
Taji Amaan yace"Kanwa Tah? Ahlam ta dago ta kalleshi Alamar bai fada dai-dai ba hakan yashi yin murmushi sannan yace"Auh sorry Aunty Ahlam ya jikin?
Ahlam ta washe baki tare da cewa da sauki.
Sun karasa shiga falo suna shiga Ahlam ta fisge hannunta ta nufi inda baba ta ke ta zauna kan cinyarta.
Amaan yayi murmshi yana"lallai ma wato guduna kike zaki sani."
Baba tace"Hmm ai Wannan sai ahankali dama ta gun tsokana ne ta fi kauri."
Amaan yayi murmushi yace"Ina hini baba?
Baba ta amsa cikin sakin fuska tare da tambayarsa mutanen gidan.
Bayan sun gama gesawa ne Amaan ke tambayar shin ko su na da wani abun bukata.
Annan ne Baba takara masa godiya tare da fadin suna da kome ai .
Bai tambayi baba ba domin kuwa yasan Baba baya nan yabude masa shagon sai da atampopi a sabuwar kasu da ke yan tifa.
Dan haka yatashi domin tafiya yayiwa Baba sallama har ya kusa fita yaji Ahlam tace"kanina!
Sai kuma tayi shiru,
Ya juyo tare da murmushin sa yace"kanwa Tah zo ma na."
Ita ma da murmushin ta takarsa wajen sa.
Amaan yace"yane Aunty? Yana kallon idon ta.
Ahlam tace"Dama fa naji sauki ne kuma banje skul nakarbo takardar gama aji uku na ba."
Amaan yaji dadi domin ya kara tabbatar da cewa Ahlam yar kirkice me son karatu.
Yace"toh shikenan ki ba ri zanje da kai na karbo miki da ga nan sai ma muyi maganar cigaban ki."
Ahlam taji dadi sosai hakan ya sa ta ma sa godiya sannan ta ko ma cikin gida.
Washe gari da safe kuwa Amaan ya shirya ya nufi gidansu bayan sun gesa da Daddy ne yake sanar masa cewa"ai sunyi zama da Baban Ahlam yace kawai duk sanda suke da bukatar ayi bikin ba matsala."
Amaan yaji dadin hakan matuka yanason ya Ma Dady magana Amman yakasa Dady ya fahimci akwai magana abakinsa hakan yasa yace"Ina ga asa bikin nan da wata ko?
Dasauri Amaan yadago yana murmushi alamar eh.
Dady yace"toh shikenan bakome Allah yama Albarka ."
Amaan yace"Ameen."
Sannan yatashi ya nufi bangaren babansa.
Yana zuwa yasanar da Baba abin da ake ciki .
Baba ma yasa masa albarka sannan Dady yakara kiransa akan anjima zasu gidansu Ahlam din.
Abangaren su Hamlat kuwa sunshirya tsaf ita da kawarta maama tare da wawiyar mahaifiyarta domin zuwa su gidansu Ahlam sukara ci musu mutunci.
Mumy ce taje tasamu Dady akan bara takai Hamlat asibiti domin ciwon ta na kwokarin tashi.
Dady yace"Adawo lafiya inda shima yanufi gun motarsa."
Basu san Amaan nacikin motar Dadynba shiko ya hangosu domin bai sanma Hamlat bata gun aiki ba azuciyarsa cewa yake"Allah yakyauta da mata irin wannan."
Maganar Dady ce dawo dashi yace"Amaan muje mufara dauko mallam sai muje gidan nasu."
Amaan yace"toh."
Sun zuwa suka tarar da malam ya fito su kawai yake jira hakan yasa basu bata lokacinsu ba Suna isa gidan Amaan ya hango motar Ahlam achan gefe inda suko su Dady ko lura basu yi ba,tuni gaban Amaan ya fara faduwa addu"ah kawai yake azuciya har suka shiga gidan sannan yayi hamdala tunda bai ga su mumy ba.
Suna shiga Amaan yaje yakira Baba .
Suko su maama sai yanzu suka fito amota domin sun tsaya kitsa irin wulakanci da zasu musu.
Mumy ce gaba suna binta abaya.
Baba yafito suna gesawa da su Dady sukaji anwani bankado kofa idonta rufe da masifa tashigo tana"Ina matsiyatan marasa zuciyan suke ?
Duk kansu kowa ya kame banda Baba wanda yatafi duniyar tunani ko wacece wannan.
Hamlat da Maama ma kamewa su kayi ganin Dady Da Amaan na wajen.
Mumy ta ci gaba da cewa"wai bazaku fito bane talakawan banza da wofi."
Ta ga dai shirun yayi yawa tana bude ido ta cii karo da Dady tuni ta fara rawar murya domin tasan yau ta kawo karshe hakurin Dady.
Tana"ba fa ba fa nan mu mu ka zo ba maama meyasa zakusa muzo nan nibance muzo ba ba fa."
Dady yace"ku fita agidannan inba kwaso ranku ya baci ."
Yana fada tare da nuna musu kofa.
Dasauri mumy ta fita inda Hamlat da maama suka bi bayan tah.
Dadyne yabawa Baba hakuri.
Baba yace"Bakome ai mata sai hakuri haka suke."
Anan dai Dady yama Baba bayanin yadda su ke son auren anan kuwa akasa karshen watan satin ban nan .
Suka yi sallama da su Baba sannan suka nufo hanyar gida.
Mumy kuwa tana nan tarasa ina zata sa kanta domin ita bawai ma ganin Dadyn bane ya fi damunta kar ace maganar aure su ka je yi.
Dady na shigowa yanufi bangarenta .
Tana ganinsa ta mike tana"...
https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation
🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬
*KUCHAKAR KISHIYA*
🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬
*ZAMANI WRITERS ASSOCATION🤝🏻*
__________________________
*we are here to educate,motivate, and entertain our readers.*
__________________________
*Story and Writing*
*by*
*Aysherth Mohammed Sani*
_(Preety Xayyeesherth)_
*PAGE* 39
------------------------------------------------------------------------------------------
~AuntyNah AuntyNah banji zafin mutuwarki ba sai yau danazo gida naga yaranki hmm Allah ya jikanki AuntyNah Dukanmu muna kewarki~
_Wannan shafin sadaukarwa ne agareka Amsard dina Yayana Abin Alfahari nah_
Tana, "Haba Alhaji ya za ka min haka wai harda kai za'a hada baki domin a wulakan tah yar ka?
Dady ya mata alamu da hannu yana fadin ,"Da ka ta!
Yanzu duk abinda ki ka je kika aika ta bai yi ba sai kinzo gida ma kinyi wani?, toh wallahi ya isheki na gaji da irin wannan mummunan halin , gashi har kin fa ra ko ya wa yar ki Ko ince har ma ta ko ya."
Mumy tayi rau da ido domin tunda take Dady bai taba fita mata agiya ba irin na yau.
Dady ya kara da ce wa, "Kuma wallahi indai kikayi sanadiyar fasuwan auren nan to abakin naki auren."
Ya na gama fada ya yi ficewarsa abinsa mumy kuwa ta zube agefen gado azuciyar ta ce wa ta ke, "Ah lallai akwai aiki agaba na har abin ya kai ga anamin bara za na da aure na hmmm zan bari ayi auren nan amman wallahi yar matsiyata sai kin gwanmace kidi da karatu."
Bayan ta gama tunanin ta ne ta kira Hamlat awaya ta sanar da ita kome sannan yanzu zasu fara shirin biki.
Hamlat ba ta so hakan ba amman ya ta iya duk jarabar mahaifiyarta ma ta kasa bare ita kuma ita awa."
Washe gari
Da sassafe mumy ta nufi bangaren Dady bayan ta geshe sa ne ta neman Afwan akan abinda tayi jiya .
Shiko Dady yaji dadin hakan inda ita kuwa azuciyarta ba haka bane.
Mumy tace, "Tou yaushe akasa bikin?,kasan mu mata akwai mu shirye-shirye gwara afada tun huri."
Dady ya gyara zama yana, "Haka ne fa toh ance dai karshen watan nan inaga asabar din da za to akarshen watan nan shine ranar d'aurin auren."
Mumy tayi murmushin dole tare da fadin, "Toh Allah ya kai mu."
Dady ya Amsa da, "Ameen."
Mumy na barin falon Dady ta kira Hamlat awaya bayan ta gama bayyana mata yadda suka yi da dadyne take cewa, "ki barni dasu wallahi Allah yakai mu ayi Auren da kafar ta zata fita wallahi."
Hamlat tace, "Hmm mumy ki barni da ita wallahi indai wannan mitsitsiyar yarinyar ce ai kaman nagama da ita."
Mumy tace, "Hmm ina nan ina kara mana wani babban shiri."
Ahaka hirar tasu ta kare ba abin arziki sai yadda za ashuka tsiya ake tsarawa.
Amaan ya fito zai tafi office , Hamlat nazaune afalo ,ya kalleta yakau da kai alamar bai ma ganta ba.
Har yaje kwofar fita , Hamlat tace , "........
Urs preety xayeesherth
https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation
🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬
*KUCHAKAR KISHIYA*
🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬
*ZAMANI WRITERS ASSOCATION🤝🏻*
__________________________
*we are here to educate,motivate, and entertain our readers.*
__________________________
*Story and Writing*
*by*
*Aysherth Mohammed Sani*
_(Preety Xayyeesherth)_
*PAGE* 40
------------------------------------------------------------------------------------------
~Life without you will be like going to sleep and never having sweet dreams~❤❤❤
Haba ango ba magana? ai dai yaci ka tsaya mu gesa .
Amaan ya juyo da murmushin nasa wanda bai kai zuci ba yace, "Au uwargida ai ban lura kina wajen ba."
Wannan kalma sai da ta taba zuciyar Hamlat Amman ta daure domin ba tason nuna masa tsarinsu ya baci tace, "Hmm Ango kenan To Ina kwana?"
Amaan yace"lafiyalau fatan kin tashi lafiya?"
Tace, "lafiyalau, ya kanwar tawa?"
Amaan yace ,"Wace kanwa kuma? Daman kina da Kanwa ne? ko Amrin kike nufi?"
Hamlat tayi murmushin dole tare da fadin, "Wace kanwa kuma nake da ita bayan Amarya ?"
Amaan yace, "Oh ai sai kice min Ahlam dinah toh tana lafiya kuma tana geshe ki."
Hamlat ta kasa magana tsabar takaici sai Hmm.
Amaan yace, "Toh nikam natafi sai nadawo uwar gida."
Hamlat ta so yin magana sai kuma ta tuna da abinda mumy ta fada mata awaya ai ko tuni tace, "Adawo lafiya."
Amaan ya ji mamakin jin hakan kawai cewa ya yi, "Ameen." sannan ya fita office.
Yana fita kuwa ita ma ta tashi ta nufi gidan su Maamah sai ta je sun gama tseguminsu sannan ta nufi office itama.
Amaan kuwa yana zuwa yakirawo uncle Salim awaya yazo ya sa me shi a office .
Ba bata lokaci uncle Salim yazo .
Yana zuwa bayan sun gesa Amaan yake sanar masa cewa ,"biki fa ya karato ya kamata mufara shirye-shirye."
Uncle Salim yace, "Haba dai Har abun ya matso kusa haka?"
Amaan ya ce, "kwarai ma kuwa karshen watan nan."
Salim yace, "Ah dole musan abin yi ."
Da ganan suka tattauna yadda abin zai kasance .
Sun dade sose suna hira sannan suka rabu akan Anjima zasu hadu suje gidan su Ahlam tare.
***************
Misalin karfe hudu da minti arba"in Amaan ya bar office yaje domin su hadu da Salim.
Suna haduwa Salim yace, "Kaga kamata yayi muje shagon babanta yanzu musanar masa tsarinmu."
Amaan yace ,"To shikenan muje."
Suna zuwa gun Baba suka gesa cikin girmamq juna bayan nan ne Salim yake sanar da Baba ce wa, "Suna so in anyi auren Ahlam ta tafi kano karatu sai ta karasa zata dawo kafin ta kara girma."
Ba karamin Dadi Baba Yaji ba Domin yana so Ahlam tayi karatu.
Baba yace, "Masha Allah ai hakan ma yayi."
Ahaka suka rabu cikin girmama juna.
Suna barin gun Baba Suka Nufi filin sukuwa gidan su Ahlam.
Suna isa suka shiga ciki Baba ce zau ne atsakar gida tana yanka *latas*.
Da sallamarsu suka shiga ta amsa cikin fara'ah.
Ba ta musu iso ga su shiga cikin daki bayan sun shiga ne suka gesa Anan ne Baba take cewa, "Oh Ahlam fa yau narasa meke damunta taki walwala sai zaman daki tun safe."
Salim yace, "To anya kuwa lafiya?
Baba tace, "Toh wayasan mata bara nakiro muku ita ko ku ta fada muku."
Baba ta tashi ta nufi dakin Ahlam ta sa me ta akwance tace, " to Ahlam kinyi baki kizo ana jira."
Ahlam tace, "umm Baba tah ni fa bana son fita."
Baba tace, "Kiyi hakuri kinji auta tah."
Dakyar Baba ta shawo hankalin Ahlam ta taso Ta nufi falo Baba kuma ta nufi kichin.
Tana zuwa....
Urs preety xayeesherth.
https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation
🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬
*KUCHAKAR KISHIYA*
🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬
*ZAMANI WRITERS ASSOCATION🤝🏻*
__________________________
*we are here to educate,motivate, and entertain our readers.*
__________________________
*Story and Writing*
*by*
*Aysherth Mohammed Sani*
_(Preety Xayyeesherth)_
*PAGE* 41
------------------------------------------------------------------------------------------
~Your love warms my heart like the glow of a candle light in a midsummer night's dream.~
```WANNAN SHAFIN NAKUNE KU KADAI YAN GRP DINA KUCHKAR KISHIYA FANS MY AMBEBY ZAINAB ADAMU MATAR KAWU MY SISTER MY WALIDA MY MOMIN YASMIN MY HAFSAT MY MMN SHAHEEDA MY HUSAINA KAI KUNA DA YAWA FA DUKANKU INA JIN DADIN COMMENTS DINKU KUMA INA ALFAHARI DAKU AMATSAYIN MASOYANA GA PAGE DINNAN KUYI YADDA KUKESO DASHI SAI WA INNDA KUKA ZABA ZASU KARANTA🥰🥰 XaYeesherth luvs u oll❤❤```
Ta ga Uncle Salim ne da Amaan
Ta washe baki sai kuma ta tuna da wani abu tuni ta bata rai.
Uncle salim yace, "Haba yar kanwata ya yau ku murmushin ma babu."
Ahlam ta turbune baki kamar za ta yi kuka tace, "Uhum bayan Wannan kanin nawa ne yaki zuwa ya duba ni yau fa kusan kwana uku?"
Amaan da Uncle Salim suka yi murmushi .
Amaan ya durkusa kasa ya kama kunnensa sannan yace, "Afwan ranki yadade."
Ahlam ta washe baki tace, "Uhum to ba ka ce min Aunty ba."
Amaan yace, "Au to aunty nah."
Tace, "Toh tashi kazauna."
Shiko Salim gaba daya hankalinsa ma yatafi wata duniyar azuciyarsa cewa ya ke, "Dama ni ne da Ahlam mana da na nuna mata cikakkiyar soyayya amman abota tafi kome dole nabarwa Amininah."
Sai da Amaan yatabo sa tukun hankalinsa yadawo jikinsa.
Amaan yace, "ya dai mutumi nah?"
Salim yace, "bakome naga ai kuna ta soyayya neh."
Ahlam tace, "Uncle ya maganar sakamakon jarabawar mu neh ."
Salim yace, "Ai sai dai mugodewa Allah tunda duk kun haye sai sarai da cigaba."
Amaan yace, "kunga hirar nan taku baza ta kare ba gashi ana kiran sallah, Ahlam bamu buta muyi alwala."
Ahlam ta tashi taje tadauko musu buta ta basu .
Suka fita tsakar gida sukayi alwalarsu bayan sun idar ne Amaan ya kira Ahlam ta karba sannan suka yi sallama .
Har yaje kwofa zai fita tace , "saura gobe ma karka zo sai nasaka tsallen kwado yasin."
Uncle Salim ya kyal-kyale da dariya yana cewa, "Ahlam wato dai har yanzu halin na nan ko?"
Amaan yace, "Ai sai ma wanda yakaru kuma fa innazo ba bari na take na tafi ba yau ma dan ta ganka neh."
Ahlam ta galla musu harar sannan tace, "Eh din Nayi."
Ta musu gwalo sannan ta shiga gida da gudu.
Suka fita suna ta dariya Salim yace, "Wallahi yarinyar nan na birgeni kullum kara girma take amman intama wani abu kamar yarinya in taso kuwa tafi babbar ma hankali da basira."
Amaan ya numfasa sannan yace, "Salim bazan bo ye ma ba wallahi ina matukar kaunar Ahlam fiye da yadda ake tsammani tun tanq yar karama inaga ma batafi shekaru hudu ba lokacin tafara zuwa makaranta nake zuwa kwofar gidansu domin kawai inganta Kuma ahakan ban taba bari taganni ba sai da ta fara girmab nan domin tsoro nake ji kar ta ce bata so na ko kuma iyayenta su hanani, haka kuma duk randa bangan ta ba kuwa wallahi bana iya barci, shiyasa yanzu inna